Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
will turn out,maza garzaya ki/ku/ka biya because
daga yau free pages is no more,it's ₦300 transfer/VTU/recharge card duk d'aya ne
babu batun VIP,sai na ji-ku masoya,Real Smasher tana maraba da ku a ko wane lokaci.
Zan ci gaba da post cikin tak'aiccen lokaci,though yanzun mun d'an samu matsalar
NEPA 2 days ago,but da sun kammala gyare² za mu ci gaba in sha Allah. Na bar ku
lafiya..😍*
#The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300 via my details.
*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*
*1-ACCOUNT DETAILS.*
Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone number:08165726609
City:Kano city.
*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*
*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*
08165726609
*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*
For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.
#Share pls.
#Asli Smasher.
[9/5, 11:45 AM] Asli Smasher 💕: *MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
1⃣6⃣
A gefen Ismat kam since Daddy ya kira su Mom,bayan wucewarsu da kyar ta iya
jan k'afafunta ta bar wajen saboda wani irin nauyin da jikinta ya mata,tana shiga
bedroom ta kwanta shiru a saman bed,duk ta rasa tunanin da za ta yi,tun jiyan rabon
da suyi waya kou even chat ma da Fawad,ga shi har yanzun shiru bai kirata ba,damuwa
ya rufeta saboda rashin jinsa da bata yi ba,hawayen da bata san daga ina suke ba
suka fara bin fuskarta,haka taita kuka ita d'aya babu mai cewa ta bari,ita kanta
kuma da za'a tambayeta a lokacin me yasa take kukan ba lallai ta san dalilin ba,abu
d'aya kad'ai za ta iya badawa matsayin evidence da zata kare kanta,shi ne tace
bata jisa ba tun jiyan,tana nan kwance lamo ita kad'ai bata san lokacin da wani
irin wahalallen bacci ya d'auke ta ba,ba ita ta farka ba sai can yamma,kasancewar
ranar ya zo mata tana fashin sallah,kou da ta farka lokacin it's already 4:45pm
ne,since ta farko take jin jikinta duk ya sake yi mata nauyi,tana jin jikintan a
wani irin mace,but a hakan ta lallab'a ta wuce bathroom tayi wanka ta shirya kanta
cikin favourite dress d'inta,as she prepared herself ta fito cikin purple d'in t-
shirt with black skinny trouser fuskarta sam babu walwala ta dunga tafiya a hankali
har ta sakko,yunwa take mugun ji a lokacin but ba ta jin sha'awar cin komai because
she feels ta rasa appetite,Mom dake zaune cikin parlor tun d'azun bayan da Daddy ya
gama sanar da ita matsalar da aka samu ta yi jigum ta rasa abunda yake mata dad'i
ta d'ago kai ta bi Ismat d'in da kallo,yadda take tafiya a hankali gwanin tausayi
kana kallonta za ka gano damuwa k'arara a fuskarta,tun ma bata san da wancan
matsalar da ya faru ba,Mom dake kallonta daga nesa taji wasu hawaye suna neman zubo
mata da sauri ta kauda kai gudun kada Ismat d'in ta hango halin da take ciki and
praying to Allah yasa abunda zai faru kada yayi affecting child d'in nata because
ta santa da saka abu arai,bare wannan da take ganin kamar her life is depend on
loving Fawad d'in since ranar farko da ta fara jin labarinsa a bakinta,hannu tayi
saurin sawa ta k'arasa share hawayen da suka k'i daina zubowa jin Ismat kwance a
jikinta,a hankali cike da k'arfin hali ta juyo tana sakin murmushi bata bari sun
had'a ido ba ta shafa fuskarta bakinta yana fad'in "Roohii! Kin farka kenan?" Ismat
da idanunta suke kulle tun da ta kwanta jikin Mom ta gyad'a kai bata ce komai
ba,sai ajiyar zuciyar da take saukewa,Mom ta zuba mata idanu tana kallonta cike da
tausayi,sun kusa awa a haka babu wanda ya iya sake yin magana,Mom da tayi tunanin
bacci ya d'auke Ismat a jikinta ta tab'a ta a hankali tana kiran sunanta,Ismat ta
bud'e idanunta bata amsa ba,Mom tana mata kallon tuhuma tace "kin ci abinci kuwa??"
Lumshe idanu tayi a hankali tace "No Mom" Mom tace "tashi maza kije kici tou sai ki
dawo" juyi tayi a jikin Mom tana sake kulle idanunta tace "ni ba na jin son cin
komai Mom" mom tana mata wani kallo tace "ba na son haka sweetheart,ta shi kou
kad'an kije ki ci" kamar za tayi kuka take kallon Mom idanunta da hawaye a cikinsu
tace "bazan iya ci ba ni" shiru Mom tayi tana kallonta fuskarta da damuwa tace
"Haka za kiyi ta zama da yunwa tou?" Kai ta kad'a a hankali tace "No Mom,zan ci
anjima,ina jin bakina babu appetite ne" kallon tausayi Mom ta dunga mata ta kasa
sake cewa komai,da aka jima Mom taga da gaske ba ta da niyyar sawa cikinta wani
abu,da kanta ta had'a mata banana milkshake saboda yadda ta dage baza ta iya cin
komai ba har abincin da ta zuba mata kasa cinsa tayi,shima milkshake d'in though
Mom ta saka ta gaba da kyar ta sha rabi tace ta k'oshi.
Barraq kuwa since ya samu ya silalo daga parlon Daddy lokacin da Mom ta rufe
idanunta ta fara yiwa Daddy zazzagar fad'a akan magabar,after ya samu kansa a
corridor a gurguje ya bar gidan,kai tsaye daga gidansun bai jira ba ya wuce jan
bulo because yana tunanin babu inda Badriyah za ta nufa da ya wuce can d'in,a yau
ji yake idan baiyi idanu hud'u da Badriyah ya hukunta ta ba Allah ma bazai yafe
masa had'a jini da yayi da Ismat ba,yana tafe a mota shi kad'ai sai tauna tooth
d'insa yake,nerves d'insa da suka yi rad'a² kamar za su tsaga forehead d'insa,gudu
yake kamar dai idan ya samu chance zai tashi sama,but duk da hakan sam ba ya ganin
saurin tafiyar,lokacin da ya iso gidan yayi horn get man d'in gidan ya bud'e masa
yana masa barka da zuwa because ya san Barraq d'an gida ne,kou ta kansa Barraq kam
baibi ba saboda a fusace yake ya gyara parking ya wuce da sassarfa,but kafin ya isa
balcony kuma kawai sai ya cake ya kasa k'arasawa,shi kad'ai ya dunga tuhumar kansa
why was he here? Me yasa zaizo nemanta a nan? Shin idan ya ganta me zai mata? Zai
daketa gaban mahaifanta ne kou kuwa mene ne ya shirya yi? Bai gama yanke abunda ya
dace yayi ba quickly ya juya without ya jira ya tada motarsa,yadda ya shigo a
zafafe haka ya sake ficewa hausar nan da Malam bahaushe kance "kou kunya ma tana
tsoron idanun mahaifi.." Tana amsa kuwwa a duka kunnuwansa,tabbas Allah ya
taimaketa yanzun,but muddin ta bari suka yi four eyes anywhere shi da ita,mai iya
cetota a gurinsa sai dai ubangijin da ya haliccesu kuma.
Daren ranar kaf gidan babu wanda ya iya samun bacci cikin nutsuwa,kowa ka duba
akwai damuwar da take k'asan ransa,shi kansa Daddy a wannan ranar sai da yaji inama
ace wani alak'a bai tab'a had'a shi da Proff Junayd ba bare har maganar neman aure
ya kawosu garesa,because a yau d'in sanadin buk'atar da suka zo masa da shi ya kai
shi ga ganin canjin da bai tab'a tunanin a duniyarsa zai had'u da shi ba ta
b'angaren zamansa da Mom. Ismat kuwa dama ita kusan abu biyu zuwa uku suka had'e
mata kai,na farko rashin samun wayar Fawad da tayi,na biyun rashin jinsa a tsayin
yinin ranar,shi bai kirata ba and then babu sak'o,abu na ukun kuma shi ne rashin
ganin Badriyah a duka yinin ranar ta rasa ina ta shiga,though ba wai suna bawa juna
muhimmanci ba a yanzun kamar da,but ganinta a kusa da ita kou baza su cewa juna
komai ba yana rage mata kaso mafi yawa daga damuwar da take shiga,tunda ta kwanta
haka nan dai take jinta wani iri saboda rashin sabawa da kwanciya ita d'aya,banda
juye² babu abunda take yi,har after 12am ta kasa samun bacci,wayarta dake kusa da
ita kuwa ta d'auka yafi a k'irga tana dubawa kou za ta ci karo da sak'onsa but
shiru kamar dai an aiki bawa garinsu,daga k'arshe ne da taga baccin ya k'i zuwa ta
sauka a hankali ta wuce bathroom ta d'auro alwala,ta fito ta shimfid'a pray
mat,since ta hau kai take sallah tana addu'ah,ba ita ta tashi a gurin ba sai da
taji bacci yana neman kayar da ita,da kyar ta ja k'afafunta ta haura saman bed
bacci mai k'arfin gaske ya d'auke ta.
Da safe kafin ma ace ta farko daga bacci,tuni Aunty Khadijah k'anwar Mom
(Mamar Hasna) ta zo gidan saboda kiran da Mom ta mata a waya tana son ganinta
urgent,lokacin Barraq ya fito zai wuce ganin auntyn nasa ya zauna suna gaisawa sai
ga Hjy Layla mahaifiyar Badriyah hankalinta duk a tashe ita da Dr Haroun,Jawahir ma
suna gidan ta k'araso,duka cikinsu babu wanda fuskarsa take bayyanar da jin dad'i
kou goyon baya bisa ga abunda Badriyah tayi,Barraq dai duk jinsu kad'ai yake
lokacin da ake maida maganar yana son wucewa amma babu halin yin hakan,Hasna dake
sharce hawaye jin abunda ya samu Ismat a hankali ta tashi za taje ta duba halin da
Ismat d'in ke ciki ta mik'e da niyyar zuwa bedroom d'inta a saman ta hangota tsaye
a saman stairs da alamun kamar ma ta gama jin duk abunda ake tattaunawa a cikin
parlon,Hasna dake kallonta with suspicion ta kasa rarrabe Ismat ta ji abunda aka ce
kou bata ji ba bakinta yana karkarwa ta furta "Sweetheart!" Because duk family
kusan da sunan suke kiranta kamar yadda Badriyah ke yi,wani kallon da Ismat ta yi
mata idanunta sunyi wani irin birkicewa shi ya kashe mata k'warin guiwa kafin ta
sake yin magana Ismat ta fara tahowa da nufin sakkowa amma sai me? Bata yi aune ba
k'afarta d'aya ta gurd'e saura kad'an ta gangaro tayi sauri ta dafe bango,on the
other hand kuma tana kokawa da numfashinta dake mata barazana,Hasna dake tsaye daga
k'asan lokacin da taga Ismat na shirin gangarowa a firgice ta kwala kiran sunan
Ismat tana haura stairs d'in a gurguje,kiran sunan Ismat da tayi ya bawa sauran
jama'ar dake parlon damar waigowa hankalinsu duka ya koma inda suka jiyo ihun
Hasna,Barraq ne ya fara tashi sai Mom dake jin wani irin zafi yana taso mata,basu
jira komai ba suka nufi gurin su Ismat wacce Hasna ta rik'e suna tahowa cikin
parlon,zuwa lokacin kam tuni fuskar Ismat ta gama appearing damuwarta,bin mutanen
gurin kad'ai take iya yi da kallo amma magana kam ya kasa fitowa a bakinta.....
#😢😢 Manage pls..
#Asli Smasher.
[9/7, 4:45 PM] My number 1: *MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
1⃣7⃣
A gefen Hjy Layla mahaifiyar Badriyah since Abbah ya dawo daga guesthouse d'in
Daddy taga yanayin da ya shigo ta fara zargin an samu matsala,but sai bata takurasa
akan lallai sai ya fad'a mata ba because ta ga mood d'insa,she know yana buk'atar
hutawa sai ta bari har ya dawo dai²,shiru tana tunanin zai fad'a mata da kansa
without even asking him but abu har dare bai ce da ita komai ba sai cewa da yayi
mata goben ta shirya taje gidan Yayansa,here Mama ta gaji da shirun da yayi mata ta
fara tambayarsa abunda ke faruwa,but still yace babu komai idan taje ko wane irin
abu ne ma za ta sani,duk yadda gabanta ke fad'uwa haka ta danne ta amsashi,lokacin
da Mama tazo gidan taji abunda ke faruwa a lokacin Mom tana kan sanar da Aunty
Khadijah,kwakwkwaran motsi kasa yi tayi a gurin,saboda wani irin kunya da bak'in
cikin abunda take hangen Badriyah ta aikata duk yasa taji jikinta ya mata nauyin da
ta kasa sake iya d'aga idanunta bare ta kalli Mom,Barraq ma dai tunda ya zauna
bayan gaisawa da suka yi da Mama ya sunkuyar da kai bai sake cewa komai ba because
dole ya san za'ayi zaman,on the other side kuma damuwar halin da sister d'insa za
ta shiga idan maganar ya fasu ta san abunda ke faruwa duka ya hana masa samun
nutsuwa,haka nan dai suke zaune jigum kowa yana jiran fitowar Daddy,ana cikin hakan
parlon yayi shiru kuma sai suka jiyo ihun Hasna lokacin tana kiran sunan Ismat d'in
da muryar tashin hankali.
Since Ismat ta k'araso wajen ta kasa tsayawa guri d'aya,k'afafunta banda
rawa tana wani irin rangaji kamar iska zai d'auketa a gurin babu abunda
take,without ta iya ce musu wani abu ta dunga kallonsu kamar yadda suma occupant
d'in wajen suke mata,sai da ta shafe tsayin lokaci a tsayen tana kallonsu cikin
wani irin k'unar da take jin zuciyarta tana mata,wanda sakamakon abunda kunnuwanta
suka ji da bata tab'a tsammani ba,abun ya zo mata a wani irin haguncen da take jin
she can't take it any more any longer,iya k'arfinta ta dage ta fasa k'ara,because
daga sanda ta tsinci maganar here taji komai ya tsaya mata,ta daina gane komai da
kowa,ta runtse idanunta da take ji sun mata nauyi ga wani irin zafi da take ji
kamar wanda aka watsa mata yaji a cikinsu,hannuwanta biyu a dafe da k'irjinta ta
tafi za ta fad'i,gigitaccen ihun da tayi da tafiyar da gangar jikinta yake
k'ok'arin yi shi ya haddasa duka suka yo kanta kowa da abunda yake fad'a,but kafin
su k'araso tuni ta kai k'asa jiki da numfashinta at the same time went on strike.
Tun bayan faruwar komai hankalinsu duka yake a tashe sakamakon jin bak'in labarin
da ya kunno musu cikin family d'in,Mom kam dama ta fi kowa shiga damuwa,tunda aka
kawota hospital d'in suke tsaye sunyi chirko² suna jira suji daga Dr d'in da ya
amshi Ismat d'in da har lokacin bai fito ba,fuskar kowa a gurin ka kalla damuwa ne
kwance k'arara. After a long time data d'iba kwance aka samu ta farfad'o da
kyar,Mom da take Dr ganin Ismat d'in ta koma kamar wata corpse (gawa) a gabanta sai
duk ta rud'e ta kasa yin komai because hankalinta ya mugun tashi tana ganin kamar
shi kenan ta rasa ta,since ta farko daga suman da taje duka family'n suka kewayeta
suna kallonta cike da tausayi amma babu mai magana a ciki kowa ya yi shiru ya zura
mata idanu,ita kam Ismat a lokacin banda wani irin kuka mai ban tausayi babu abunda
take iya yi,duk tsayin lokacin kuma an kasa samun even a single person wanda zai
iya rarrashinta,Barraq da tun farkowarta yake kallonta tana kuka ya zuba mata idanu
saboda yana ganin kamar idan tayi mai isarta za ta hak'ura ta bari,kou da yaga ba
ta da niyyar dainawar,ransa a mugun b'ace ya dunga jifanta da wani kallo duk uban
oxygen dake mak'ale bakintan da condition data shiga da har a time d'in didn't stop
her from crying,sadly bayan ya sake d'aga kai ya kalli occupants d'in wajen dake
kewaye da ita da aka rasa samun mutum d'aya wanda zai bata hak'uri yayi k'wafa a
fusace ya mik'e ya nufo inda take,no one thought abunda zai yi kenan,yana isowa ya
d'agata sai da ta zauna dai²,yana ci gaba da jifanta da wani irin kallon b'acin rai
da husky voice d'insa ya furta "Za ki yiwa mutane shiru,ki bari muji da abu guda
kou saina faffalla miki mari?" Su Mama dake wajen suka masa caa za suyi magana,bai
juya ya kalli kowa ba ya d'aga musu hannu a zafafe yace "Kada wanda ya shiga
maganar mu! Wannan tsakanina da ita ne!" Ya sake rolling idanunsa masu cike da
b'acin rai a kanta yana fesar da wani irin zazzafar iska a hankali ya furta "Get
up! We need to go home!" Da sauri duka occupant d'in wajen suka bishi da kallo za
suyi sharhi,but yadda suka ga ya koma sai aka kasa samun wanda zai dakatar da
shi,idanun Ismat suna tsiyayar da hawaye ta kallesa very weakly ta tattara words
d'in "Pleasee! Bhai! I can't even bear! Ba zan iya jure ganinsu tare ba!" Uban
kallon da ya watsa mata shi yasa ta yin shiru bata kai k'arshen abunda take son
cewa ba,a fusace Barraq ya kaalleta cike da hayaniya yace "Idan baki saita bakinki
kin daina yiwa mutane maganar wannan sha³n ba,yanzun jikinki zai yi tsami,sakarai
kawai wacce bata san ina yake mata ciwo ba!" Kuka ta sake fashewa da shi jin abunda
yace,a fusace Barraq da tun d'azun ya gaji da jin kukanta yana d'agowa ya bige mata
baki,without even ya kula da bata gama warwarewa daga rashin lafiyan da ya sameta
na gaggawa ba,cike da hayaniya yana watsa hannuwa sama kamar zai daketa ya fara
sirfa fad'a as if idan ya samu baki zai aro,Ismat banda kuka babu abunda take
saboda yadda take hangen b'acin ransa k'arara,damuwa da tashin hankalin b'ata masa
rai da take zargin kanta da yi suka sa ta k'arasa zare oxygen d'in a hankali ta
sauke k'afafunta k'asa,bata yarda ta kalli fuskarsa ba maganarta a low tone ta
furta "Forgive me please bhai,bazan sake ba,na daina kukan" tana sake share hawayen
da suka k'i daina zubowa,Barraq da yaga ta yi kalar tausayi kanta a k'asa tak'i
yarda ta kalli fuskarsa lokaci d'aya yaji jikinsa yayi sanyi,here ya tsinci kansa
da yin shiru daga fad'an da yake mata,a hankali ya tako ya k'arasa zama next to her
ya rik'o hannunta calmly yana sauke ajiyar zuciya,suka yi shiru tsayin lokaci bai
iya cewa komai ba har Dr ya shigo ya sake duba jikinta,Dr ya fara masa bayani
sallamarta sai dai suyi hak'uri su bari har zuwa gobe idan jikinta ya sake
warwarewa due to condition da suka kawo ta amma sai Barraq d'in yace a'a ya rubuta
musu sallama kawai idan sunje gida suna da wanda zata kula da ita,babu yadda Dr
zaiyi dole haka ya basu sallama suka taho gidan.
Dai² shigowarsu gidan kou zama basu k'arasa ba Dr Haaroun mahaifin Badriyah
ya shigo hankalinsa a tashe lokacin yana maimaita kiran "Brother *IMRAAN* where are
u!?" Daddy da fitowarsa kenan daga parlonsa cikin shigar manyan kaya zai fita ya
jiyo d'an uwan nasa yana kiransa ya biyo hanyan staircases d'in da sauri ya hango
su zaune cikin parlon kamar masu zaman makoki,fuskarsa cike da mamakin zaman da
suke yi ya fara sakkowa a nutse yana k'are musu kallo,but before he made any
attempt Dr Haaroun dake kallonsa bai jira kou gaisawa suyi ba ya furta "Shin ka ga
abunda saurin yanke hukuncinka ya haifar? Me yasa dama za ka amince musu? Yanzun ga
shi kai ka amince da su suna neman ha'intarmu,da suka ce ba Ismat ba sai a hak'ura
duka,amma sai ka yi gaggawa ka amsa musu akan batun Badriyah" Idanun kowa a kansa
jin maganar dake fitowa daga bakinsa,Ismat da idanunta suka k'ank'ancewa,fuskarta
ta yi wani irin jaa ita kanta bata san lokacin da ta mik'e tsaye rik'e da k'irjinta
dake mata zafi tana yiwa Abbah wani kallo ba ta furta "Ita d'in zai *AURA.!?"*
'Dago kai Barraq yayi da sauri yana kallon k'anin mahaifin nasa dake magana without
yana iya had'iye yahun bakinsa,a nutse ya rik'o Ismat ya mayar da ita ta zauna then
ya mayar da idanunsa kan mahaifin nasa dake kallon d'an uwansa ya kasa magana,Dr
Haaroun dake kallon Yayansa da har sannan bai ce komai ba yaci gaba da magana yace
"ka san wane irin yaro ma kake shirin bama auren yarinyar nan? Ka san wane ne shi?"
Duka lokaci guda suka sake zubo masa idanu kowa yana jira yaji me zai