Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
tace "Friend ba za ku gaisa da
Aakiiy na ba?" Da sauri Ismat ta d'ago tana kallon Naina ta k'irk'iro murmushi
cikin cool voice d'inta bata yarda ta kalleshi ba tace "Ina yini?" Wani lumshe
idanu Aadil yayi a hankali yace "Lafiya lou,ya taro?" Tayi k'asa da kai tana matse
fingers tace "Alhamdulillah" idanun Aadil akanta har lokacin but idan ba kula mutum
yayi ba bazai tab'a cewa ita yake kallo ba yace "Maa sha Allah,Allah sanya alkhairi
ya tabbatar musu da zaman lafiya" Ta amsa "Ameen" suka gaisa da su Badriyah ma da
su Aanisah,sannan Naina ta sake masa hannu ya wuce tana yi masa dariya.
Har misalin 10pm mutane basu gama watsewa a gurin dinner ba,Ismat da taji
k'afafunta sun fara ciwo babu shiri taja hannun Badriyah tace "habibtiiy gaskiya mu
wuce ni dai k'afafuna sun fara ciwo" Badriyah ta fara dariyar mugunta tace "Ba dai
na ce kisa flat shoe ba idan za kiyi rawa kik'a ji na,ni kinga babu ruwana ban wani
gaji ba" Ismat ta tab'e baki tace "tou ni dai muje,kada Mom ma tayi min fad'a,mu
tafi gida haka tunda an tashi ma",tashi Badriyah tayi tana kallonta tace "muje tou"
suka fito suna tafiya gwanin burgewa har sun kusa fita daga hall d'in Ismat ta d'an
tsaya kad'an tace "Habibtiiy! Ki jira ni a mota na yi mantuwa" Badriyah ta amsa ta
wuce,ita kuma Ismat ta juya,gurin Mom taje suka yi magana after then ta juyo tana
tafiya a hankali Naina dake nemanta tun d'azun da wayar Ismat data bata ta rik'e
mata ganin za ta fita tayi calling sunanta out *"ISMAT!"* Juyawa Ismat tayi da
sauri jin ana kiranta,tana waiwayawa ta hango Naina tana d'ago mata phone d'inta,ta
bud'e idanunta da sauri tana cewa "Tabbb'! Na manta fa na baki ajiya" Naina tayi
murmushi lokacin da take k'arasowa tace "Ni ai ban manta ba" suka yi murmushi ta
mik'awa Ismat wayar,Ismat ta sake yin murmushi tace "Thank u" Naina tace "what a
compliment here dear?" Ismat dake sakin murmushi tace "duk da haka dai" suka yi
dariya tare,Naina tana kallonta tace "ba dai tafiya ba?" Ismat ta kad'a mata kai
tace "K'afafuna sun fara ciwo ne,shi yasa za mu wuce gida" Naina tana kallonta da
tausayi a kan fuskarta tace "Eyyah! So sorry dear,Allah k'ara sauk'i" Ismat ta amsa
suka yi sallama,a hankali ta juya ta fara tafiya tana jan k'afarta da take jin sun
fara rik'ewa,ta fito kenan with intention of taje wajen da suka yi parking motarsu
da yake already Badriyah har ta wuce mota tana jiranta,kamar daga sama tana cikin
tafiya taji an sake rik'e mata hannu,ta fara juyawa fuskarta d'auke da murmushi a
tunaninta Naina ce take son tsokanarta,tana waigawa here idanunta suka sauka
kansa,a mugun firgice ta zaro idanu tana kallonsa,then ta bi hannunta da ya rik'e
da idanu,a matuk'ar firgice ta dunga juya hannunta tana son k'wacewa,kusan mintuna
uku suna tsaye sai son k'wacewa take ta kasa,shi kuma yana tsayen bai yi magana ba
kuma bai sake mata hannu ba yana dai rik'e da ita har lokacin,Ismat ganin mutane
sun fara tsayawa kallonsu wasu suna k'us² lokaci d'aya da zuciyarta tayi wani irin
tunzurota,a fusace tana d'aga hannu bata san lokacin da ta wanke masa fuska da mari
ba,ji kake tass sound yayi arisen.....
#The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300 via my details.
*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*
1.ACCOUNT DETAILS.*
Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone number:08165726609
City:Kano city.
*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*
*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*
08165726609
*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*
For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.
#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2020.
*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/NV64fA4cR6
🆓 Pᴀɢᴇ..
»9⃣
9⃣ :#Nᴇɢᴀᴛɪᴠᴇ ᴇᴍᴏᴛɪᴏɴᴀʟ
Wani irin lumshe idanu yayi a hankali ya sake bud'e idanunsa ya sauke su
akanta,fuskarsa d'auke da kinda beautiful smile,idanunsa sun d'an yi wani irin
sauyawa na lokaci d'aya yana kallonta ya sake mata hannu,hawayen bak'in ciki da
suka kawo idanunta suka gangaro saman fuskarta a guje,duk kuma ita ba komai ya fi
b'ata mata rai ba a lokacin sama da yadda yake jifanta da murmushi,sosai abun ya
k'untatawa zuciyarta,tana kallonsa da wani irin b'acin rai a cikin idanunta bata
iya cewa komai ba hurriedly ta juya za ta bar wajen hannayenta rik'e da gown d'inta
data tattare,ta tsinto asalin muryarsa cikin wannan cool voice d'in san da ta sani
yana fad'in "Thanks dear!" Wani irin k'amewa Ismat tayi a gurin kamar wacce aka yi
pausing,jin muryar da ko cikin taron arfa ta had'u da mai shi baza ta tab'a iya
mantawa da shi ba a cikin kunnuwanta da kwakwalwarta yana mata yawo,a rikice ta
waigo tana yi masa wani irin surprised look hawaye suna ci gaba da saukowa saman
fuskarta,ya sake yi mata murmushi a karo na babu adadi,a hankali ba tare da ya sake
yin magana ba daga haka ya juya ya fara tafiya.
Aadil dake zaune cikin mota tun d'azun after ya gama yiwa su Naina lik'i yana
jiran Fawad ya fito su wuce gida,kamar ance ya d'ago daga nan inda yake zaune cikin
mota,his illuminated eyes suka sauka kan Fawad dake rik'e da hannun yarinyar da
Naina tasa suka gaisa not too long,wani irin fad'uwa yaji gabansa yana yi sakamakon
abunda ya gani a hankali ya zuba musu idanunsa,babu zato yana kallonsu da wani irin
yanayin da ya kasa gane na mene ne kawai yaga yarinyar ta fallawa Fawad mari,abunda
ya faru akan idanunsa lokaci d'aya ya matuk'ar girgiza shi,sai dai bai san ma
lokacin da wani irin smirk ya kufce masa ba,ya sake lumshe idanunsa ya bud'e ya ci
gaba da kallonsu cikin wani irin yanayin da ya kasa rarrabewa farin ciki yake ko
damuwa? Gani yayi Fawad ya yi murmushi then a hankali ya sake mata hannu,abun da ya
faru ya mugun bawa Aadil mamaki ya d'aure masa kai,but bai gama mamaki ba sai da
yaga lokaci d'aya yarinyar da take niyyar fara gudu,saboda a yadda ta tattare riga
kana kallo za ka san a shirye take ta k'arawa k'afafunta sauri,kawai sai yaga ta yi
wani irin juyawa tana kallon Fawad d'in da fuskar mamaki hawaye suna sauka kan
fuskarta,bud'a idanu ya sake yi sosai yana kallonsu gabansa sai fad'uwa yake,still
a nutsen yaga Fawad ya sake yi mata murmushi bai yi magana ba ya fara tahowa wajen
motar da yake ciki. Aadil couldn't stop looking at them har lokacin da Fawad ya
bud'e motar ya shiga side na mai zaman banza,ya waiwaya continue looking at him
lokacin yana kwantar da kansa jikin seat had'e da lumshe idanunsa ya kasa
magana,almost 5minutes yana kallonsa then ya sake juyawa ya kalli inda take,har
lokacin tana nan yadda Fawad ya barta rik'e da gown d'inta ta kasa tafiya,Aadil dai
mamaki duk ya hana masa tada motar su tafi,sai da Fawad ya d'ago a hankali yana
tura hular kansa baya yace "Muje mana,tsaiwar me muke yi kuma?" Tab'e baki Aadil
yayi a nutse ya d'auke kai ya tada motar ya fara riding,sun d'auki hanyar komawa
gida motar yayi wani irin shiru,though dama hakan ba sabon abu bane a gurinsu,a
nutse Aadil ya katse shirun ta hanyar watsowa Fawad tambayar "Me ya had'a ku?"
Lumsassun idanunsa Fawad ya bud'e a hankali,kamar ba zai yi magana ba da farko ya
dunga kallon Aadil then a hankali yace "Nothing" Aadil ya waiwayo ya kalleshi
kad'an yace "Haka kawai ta mare ka kenan?" Saurin bud'a idanu Fawad yayi yace "Na
fad'a maka babu komai" Aadil yayi murmushi yace "Akwai abunda kake b'oyewa my
friend" a d'an fusace Fawad dake kallon waje yace "Tunda ka sani mene ne abun
tambaya?" D'age eyebrows Aadil yayi a hankali ya tab'e baki yace "Saboda ina son
sani" siririn tsaki Fawad ya saki then kamar ba ya son cewa komai ya fara sanar da
Aadil d'in alak'arsa da Ismat,Aadil dake driven lokacin suna tsayawa dai² get d'in
gidansu ya dunga kallon Fawad da wani irin mamaki,but bai ce komai ba yayi horn
malam Jibrilla ya bud'e masa get,yana riding motar zuwa cikin compound d'in gidan,a
hankali kamar ba ya son magana yace "U made a mistake!" Saurin kallonsa Fawad yayi
yana bud'a idanu yace "Mistake wane iri?" Aadil yana gyara parking a carline yace
"Me yasa za ka rik'e mata hannu daga had'uwar ku?" Shiru fawad yayi yana
kallosa,Aadil yace "U know! Kai ba muharraminta bane right? Besides baku had'a ko
wane irin alak'a na jini ba,hasalima baku tab'a ganin juna ba,on ur own speculation
nake so ka fad'a min,me ya kamata kayi a had'uwar ku na farko wanda zai bawa
alak'ar ku damar d'orewa? Me kake tunanin ita za ta d'auki abunda ya faru tsakanin
ku yanzun? Daga had'uwa ka rike mata hannu,duk wacce ta san mutuncin kanta yaya za
ta d'auki al'amarin,and then mene ne ya kamata tayi wanda zai ba ta kariya,mutane
ba za suyi zarginta ba a matsayin y'a mace da aka ga namiji ya rik'e?" Wani irin
kallo Fawad ya dunga yi masa,sai dai ya kasa magana,a hankali Aadil ya bud'e motar
yana fita yace "A nawa ganin bata yi ba dai² ba dan ta yi haka,saboda haka kada ma
ka fara ganin laifinta because ta yi abunda ya dace a matsayinta na mace da bata
tab'a saninka ba!" Fitowa Fawad yayi ya kasa magana har lokacin sai kalaman Aadil
dake masa yawo a cikin kai,daga haka babu wanda ya sake magana suka fara tafiya
zuwa flat d'insu.
Ismat kam since Fawad ya barta tsaye a gurin,gaba d'aya taji jikinta ya
kasa motsawa,duk wasu veins dake taimakawa jikinta lokaci d'aya suka yi wani irin
rik'ewar da all joints dake jikinta suma suka yi mata wani irin nauyin da even
index finger d'inta ya gagareta d'agawa bare ta iya motsa harshenta,shin idan ma ta
bud'e bakintan mene ne take da shi da za ta fad'a masa har ya saurara? Wane magana
za ta iya furtawa a yanayin da take ciki? Cewa za tayi yayi hak'uri ko kuma yaya za
tayi? Haka ta bishi da wani irin kallon tsoro ba tare da ta iya tsinana komai ba
har motar da ya shiga ya bar gurin,while a gefe guda kuma abunda ya faru tsakaninsu
tuni y'an gulma sun kai rahoton sa cikin hall d'in,jin kunnen Mom taji wai Ismat ta
mari wani a waje yanzun,amma ba'a san me yayi mata ba an dai ganshi ya
rik'eta,hankalinta a tashe ta fito wajen tare da su Mama,tana hango Ismat tsaye tun
kafin ta k'araso ta fara kiranta "Sweetheart!" In a kinda frightful voice,Ismat
dake tsaye tun d'azun kamar wata statue banda hawaye babu abunda yake sauka kan
fuskarta,Mom tana zuwa ta rungume ta tana dudduba ta da fad'in "What happened dear?
Ya miki wani abu ne?" Fad'awa jikin Mom tayi hurriedly ta fashe da wani irin kukan
da kamar ana fizgar mata rai,hankalin Mom da su Mama ya sake tashi ganin irin kukan
da take yi,babu shiri Mom ta rik'eta securely a jikinta,Badriyah dake cikin mota
tana jiran Ismat taron jama'ar da ta hango yasa ta fito da sauri daga mota tana
ratsawa,Mom tana ganinta tayi saurin rik'ota hankalinta a tashe a rud'e tace "Maza
habibtiiy wuce muje gida" tana maganar tana had'a hannayensu duka tana
rik'ewa,because a lokacin Dr Hinda ta mugun tsorata da yadda taga gudan jininta
tana wani irin kuka mai ban tsoro,da kyar Mama suka samar musu hanya suka fita
cikin taron mutane,a gaggauce tana saka su a mota ta shige ko sallamar da su Mama
suke yi mata bata iya tsayawa ta amsa ba tasa driver yaja motar suka bar wajen da
mugun gudu,tunda suka taho tunani iri² suke kawowa ran Mom,zuciyarta ta yi wani
irin rauni musamman ganin yadda Ismat take kwance jikinta ta kasa daina kuka,suna
k'arasowa gida ko parking bata jira driver ya dai²ta ba ta fito rik'e da hannun
Ismat suka wuce cikin gidan,bata saketa ba sai da suka je bedroom d'inta,tana
kallon Ismat da har lokacin hawaye sunk'i daina zuba a fuskarta da wani irin fuskar
damuwa ta rik'e kafad'unta tana kallonta,cikin sanyayyar magana irin na lallashi
mai cike da tsoro ta furta "Sweetheart!" Ismat bata iya amsawa ba,Mom tace "Kalle
ni,maza d'ago idanunki ki fad'a min ya miki wani abu ne?" Kasa d'agowa Ismat tayi
ta kalli Mom,Mom cikin wani irin tashin hankali ta sake furta "Sweetheart! Maza ki
sanar da ni abunda guy d'in yayi miki,me ya miki? Ya rik'e ki ko kuwa? What
happened between ke da shi? Ki fad'a min kafin na kira Daddy ko Yayanki!" Wani
mugun fad'uwa gaban Ismat yayi jin Mom tana ambaton za ta sanar da Barraq hurriedly
ta d'ago idanunta da suka fara kumbura fuskarta kansa yayi wani irin jaa abunku da
farin mutum,tana kallon Mom tashin hankali k'arara cikin idanunta ta fara girgiza
kai alamun a'a,Mom cikin damuwa tana share mata hawaye ta furta "idan ba kya so
Daddy ko Barraq suji maganar nan,maza tou ki sanar da ni abunda yayi miki" da kyar
muryarta har ya dashe ta bud'e baki tace "Hannu kad'ai ya rik'e min" tana fad'an
haka tayi shiru bata sake cewa wani abu ba,Mom tana jin abunda Ismat ta fad'a bata
san lokacin da ta sauke wani mugun ajiyar zuciya ba ta rungume ta tightly,a hankali
ta lumshe idanunta tana shafa bayanta ta furta "Alhamdulillah alaa kulli halin" sai
kuma ta sake d'agota ta zaunar da ita gefen bed and to sit next to Ismat d'in tana
calming nata,a hankali ta kamo Ismat ta kwantar a jikinta tana shafata da wani irin
murya tace "Allah ya taimakesa iya nan ya tsaya.." Saurin d'agowa Ismat tayi da
kumburarrun idanunta tana kallon Mom tace "Mom!" Sai kuma tayi shiru ta kasa cewa
komai,Mom tana kallon wani guri ta furta "Da ace yayi kuskuren tab'a min
mutuncinki,surely ba zan tab'a barinsa ya sha ruwa cikin salama ba,dole ne ya biya
zunubin da ya aikata.." Wani irin kallon Mom Ismat ta dunga yi a hankali tana zare
jikinta daga na Mom tace "Mom please! Ni ki bar cewa komai kan maganar" a hankali
Mom tana shafa kanta tana kallonta ta girgiza kai tace "Baza ki fahimci damuwar ba
baby,amma tunda Allah ya tsare alhamdulillah,yanzun maza ki tashi kije kiyi
wanka,sai ki kwanta kada kanki yayi ciwo" lumshe idanunta tayi a hankali tana turo
baki cike da shagwab'a tace "Ni dai a gurinki zan kwanta yau" Mom ta lumshe idanu a
hankali tayi tak'aitaccen murmushi tace "Ita kuma habibtiiy'n ki barta ita da
waye?" Shagwab'a Ismat ta fara yiwa Mom tana cewa "ni dai gaskiya Mom a nan zanyi
bacci na" Mom tace "A'a kije bedroom d'inku" a hankali Ismat tace "shi kenan bari
na tafi tunda korata kike yi" murmushi Mom tayi kad'an tana kallon Ismat dake
k'ok'arin sauka a jikinta tace "Ni ban kore ki ba,na dai ce kije d'akin ku,za ki
bar Badriyah ne ta kwanta ita kad'ai?" Turo baki tayi cikin shagwab'a tace "Tou Mom
mu zo mu kwanta a nan duka?" Mom ta girgiza kai tace "Ni dai kada kuzo ku lalatamin
bed,dama kuyi zamanku a can" kamar za tayi kuka ta tashi tsaye tana rik'e gown
d'inta,bata sake cewa komai ba ta fara tafiya,Mom ta bita da kallo tana sauke
ajiyar zuciya,dai² lokacin kiran Mama yana shigowa sai bata sake cewa Ismat komai
ba har ta fita,a hankali ta juya tana kallon wayarta dake ajiye gefe,ta kai hannu
ta d'auko tare da answering call d'in ta kai wayar kunne da fad'in "Assalmu
alaikum! Hjy Layla kun koma gida ne?" Mama dake cike da damuwar abunda ya faru ta
furta "Dr komai lafiya dai kou?" Mom tayi ajiyar zuciya a hankali tace
"Alhamdulillah! Lafiya k'alau Hjy" Mama tayi ajiyar zuciyar samun nutsuwa tace "Maa
sha Allah,dama abunda na bugo naji kenan,since kuka tafi hankalina ya kasa
kwanciya,ina ta kira ma wayar yak'i tafiya sai yanzun" Mom tace "Allah
sarki,network bai da kyau cikin kwanakin nan" Mama tace "Tou tunda komai lafiya
Alhamdulillah,but gaskiya ina ga ki abunda yafi ki tambayeta ko ta san yaron" Mom
tace "Ba na tunanin haka gaskiya,because duk abunda take ciki ina sani,ba na jin ta
san shi at all" Mama tayi shiru a hankali tana tunani sai kuma tace "tou shi kenan
dai,amma da kin fara tambayarta ko wani abu ya tab'a had'a su,ni ina jin tsoron
irin wad'annan samarin,gara idan da wani problem d'in tun yanzun a yiwa tufkar
hanci" Murmushi Mom tayi tace "Babu damuwa Hjy in sha Allah zan tambayeta naji zuwa
da safe,yanzun ta gama min rikici ma ta fita" Mama tayi murmushi tace "Auta
kenan,tou Allah ba mu alkhairi zan je gurin bak'i,Allah k'ara kiyaye mana su" Mom
tayi dariya tace "Ameen,a gaishe da yallab'ai,sai na shigo" suka yi sallama,Mom
tana ajiye wayar ta yi shiru ta fara tunanin maganar da suka gama da Mama,bayan
wani lokaci ta mik'e a hankali ta fara rage kayan jikinta.
Since suka shiga flat d'in babu wanda ya sake magana da d'an uwansa,Aadil kam
dama suna shigowa kai tsaye ya wuce hanyar bedroom,while shi kuma Fawad here ya
kwanta saman armchair had'e da lumshe idanunsa ya fad'a duniyar tunanin abunda ya
faru not too long,yana kwance zuciyarsa sai sak'e² da tunanin abunda zai faru next
yake but ya rasa mafita d'aya da zai rik'e,a haka har Aadil yayi wanka ya fito
cikin wasu lightweight pyjamas da suka karb'esa,lokacin da yake fitowa daga bedroom
ya d'an saci kallon Fawad dake kwance kamar mai bacci a hankali ya tab'e baki ya
k'araso cikin parlor'n ya zauna had'e da d'aukan remote yayi powering TV,Fawad da
tun shigowarsu ya rasa tunanin da zai yi,ya bud'a lumsassun idanunsa then ya tashi
ya fara tafiya slowly kamar yana counting steps,binsa da kallo Aadil yayi har ya
shige ciki ya sake tab'e baki ya mayar da hankalinsa kan TV,bayan Fawad ya shiga
bedroom ya fara cire kayan jikinsa a nutse ya d'aura towel a waistband d'insa ya
wuce bathroom fuskarsa babu wani walwala,jikinsa duk ya yi wani irin mugun sanyi,a
haka ya daure ya had'a ma kansa ruwan wanka ya shige,d'umin ruwan dake ratsa shi a
hankali ya fara taimaka masa tunaninsa ya fara warwarewa,zuciyarsa da tayi wani
irin k'ullewa lokaci d'aya ta fara dawowa dai²,almost 35 minues ya d'auka a cikin
ruwan yana ta tunane² kafin yayi wankan ya fito,as he finished ya fito sanye da
pyjamas y'an ubansu da suka sake fito da asalin kyaunsa,banda k'amshi babu abunda
yake yi mood d'insa kad'ai ne da ya sauya shi ne ya so b'oye kyaunsa,a hankali jin
takun tafiyarsa Aadil ya d'aga kai ya kalleshi,bai ce masa komai ba har ya wuce ya
zauna had'e da d'aukar wayoyinsa da ya zube saman table,ya zauna saman rug ya mik'e
k'afafunsa and leaning his back against chair dake nan kusa da shi,so yake ya
kirata sai dai ya rasa ta ina zai fara,zuciyarsa duk a cunkushe yake tunda
incidence d'in ya faru,ga wani irin tsoron da ya kama zuciyarsa har zuwa yanzun da
yake ganin kamar ya samu mafita,but k'irjinsa bai daina bugawa very fast ba,a
hankali