Chapter 15 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   15 / 70

42K to 45K   out of 210K words

kamar za ta nutse a
wajen,Mami dake kallon Naina da rashin fahimta tace "Surukata?" Naina ta kad'a kai
tana dariya,Mami dake kallonta har lokacin tace "How comes?" Naina tace "i just
know,but ki tambayi akhiiy idan baki yarda ba" juyawa Mami tayi tana kallon Aadil
da ya wani had'e rai,tunda Naina ta fad'i maganar ya tsuke fuska yake juya spoon
yana sake tauna tooth d'insa da babu komai cikin bakin ya kasa k'ara kai abincin
bakinsa,da mamaki sosai a fuskar Mami data juya tana kallonsa tace "Son! Da gaske
ne wannan maganar?" Yadda yayi kicin² ya k'i d'agowa though baima san da shi Mami
take ba sai da tace "Am i not talking to Aadil?" Da sauri ya d'ago idanunsa yaga
shi Mami take kallo,but still kafin amsa sai da ya juya ya kalli sides,Mami ta
had'e rai tace "Da kai fa nake magana,kou akwai wani mai irin sunan bayan kai?"
Juyowa yayi yana kallonta yana k'ifta idanunsa fuskarsa babu wani annuri ya hadiye
saliva's da kyar yace "Ni Mami ya za'ayi na sani,ga wanda za ki tambaya nan" ya
k'are maganar yana mik'ewa tsaye da nufin barin wajen,Mami da mamaki yasa ta bishi
da ido bata iya cewa komai ba har ya bar wajen,then ta dawo da hankalinta kan
Naina,before she made any attempt Naina dake dariya k'asa² tayi tsagal tace "Mami
dama fa ba shi nake nufi ba nima" shiru Mami tayi tana kallonta da rashin
fahimta,Ismat kuwa duk ta wani sake takure kanta ta kasa d'agowa,Naina dake ktayi?
on direction d'in Fawad tace "Akhiiy! Ka fad'awa Mami maganar" wani murmushi ya
saki lokacin yana kallon Ismat da tak'i yarda ta d'ago kanta ta kalleshi,yadda tayi
sai da ya kusa yayi dariya ya dai danne bai yi ba,a nutse bai yarda ya kalli Naina
ba ya furta "I know nothing akan maganar kin nan da kike" zaro idanu Naina tayi
tace "Kaiii! Akhiiy Allah ka sani" dariyar da ya bayyana hak'oransa yayi ya saci
kallon Ismat while yana fad'in "Mmm! Zan miki k'arya kenan?" Naina tayi saurin
girgiza kai tace "No! But ai!" Da sauri yace "But what?" Tace "ba kai kace ma na
bata hak'uri ba ranar dinner akhiiy Fadl?" Ya zaro idanu yana kallonta yace "Ni na
aike ki kou dai sharrin naki ya fad'o kaina yau?" Still tayi tana kallonsa,ya
d'auke kai yana sakin murmushi yace "Mami ni ban san maganar da take yi ba" wani
mugun bayyanannen ajiyar zuciya Ismat tayi,Naina dake kusa da ita ta kalleta da
sauri tace "Sweetheart! Ki fad'awa Mami gaskiya please" murmushin yak'e Ismat ta
k'irk'ira sai dai ta kasa magana,jikinta a mugun mace ta fara k'ok'arin barin gurin
Naina tayi maza ta rik'o hannunta,a sad'ad'e ta tsaya sai dai bata juyo ba,kamar
Naina za ta fashe da kuka tace "Please! Kinga basu yarda ba fa" Ismat dake tsaye ta
juya baya tayi k'arfin hali da kyar tana runtse idanunta tace "Sorry frnd but i
know nothing" zaro idanu Naina tayi cikin tsoro tace "Ke ma haka za kice?" Kamar
Ismat za ta fashe da dariya saboda yadda Naina tayi furucin,Fawad kam da sauran
mutanen wajen ba'a bisu bashi ba duka suka sa dariya,Naina tana ganin haka ta fashe
da kuka tace "Shi kenan tunda duk kun mayar da ni mak'aryaciya,ai dai wata rana
abun b'oye zai fito sarari ku gansa da idanunku" da sauri ta tashi ta bar musu
wajen,a yadda ta wuce tana matsar k'walla yasa jikin Ismat yin sanyi,ta rufe
idanunta a hankali tana jin babu dad'i har ranta,shin ita yaya ne za tayi? Kawai
sai ta amsa tace haka ne maganar da Nainan ta fad'a? Wannan ma ai abun kunya ne,sam
baza ta tab'a iyawa ba.

Parlor ta wuce a sad'ad'e bayan wucewar Naina ta zauna jiran Badriyah ta
kammala su wuce gida,Badriyah da tasan ita Ismat ke jira tai ta jan jiki har after
8pm sannan da kyar ta kammala ta taso,Ismat da take jin kamar tana kan k'aya tayi
zumbur ta mik'e,agurguje suka yima Mami sallama then su Jawahir da yake ba a ranar
za su wuce gidansu ba,Mami ta had'a musu manyan turaruka da kayan make-up masu kyau
da tsada,tana ta yima Ismat tsiyar tak'i sakin jiki bayan nan d'in idan ta zauna
kamar tana gida ne,kou da babu Jawahir za su iya zuwa a gaisa,Ismat dai murmushin
yak'e kad'ai take tana kuma jin Mami,inwardly kam addu'arta bai wuce su bar gidan
ba duk ta sunkuyar da kai,Naina ta fito da kyar bayan ta gama fushin tayi musu
rakiya har bakin motar da suka zo da shi,suka yi sallama suna d'agawa juna hannu
suka fice daga gidan. Wani irin ajiyar zuciya Ismat tayi idanunta a lumshe lokacin
da motarsu yafito daga gidan,a ranta kuwa k'issimawa take this must be the first
and last zuwanta gidan,Badriyah dake side ta harareta ta ci gaba da driven ba dai
tace komai ba saboda mugun haushin da ya cikata,har suka zo gida bata cewa Ismat ba
itama bata ce mata ba,tana gama parking kafin ma tajuyo tuni Ismat tayi sauri ta
fice,a fusace Badriyah dake fitowa a motar ta fara masifa cikin d'aga murya tun
Ismat bata yi nisa ba "Ke dai sweetheart wallahi ba ki da hali sam,kawai daga zuwa
guri ki fara cewa a tafi,ni dai gaskiya ba na son haka,idan kin san duk sanda muka
fita za kice mu dawo tou gaskiya sai dai mu raba fita,kiyi tafiyarki na same ki
kawai,kou ni na tafi ki same ni,amma gaskiya ba na son haka" tsayawa Ismat tayi cak
a inda take har Badriyah ta k'are maganar da take yi,a hankali ta kad'ai lokacin da
take waiwayowa ta zuba idanunta cikin na Badriyah tana mata wani kallo,a dake tace
"Haka kika zab'a?" Badriyah dake kallonta a masife tace "Ehh! Na fad'a d'in" ta
sake kad'a kai sai dai bata ce komai ba ta juya ta ci gaba da tafiya abunta,daren
ranar gaba d'aya haka suka kwanta kowa tana jin haushin y'ar uwarta.

Almost two weeks da dawowar su Jawahir Nigeria,tun daga ranar da suka sauka
Jawahir take kiran Ismat tana son tazo akwai maganar da take son suyi,but kullum
sai Ismat ta bata uzurin wani abu daban,har Jawahir ta fara nuna jin
haushinta,Ismat na ganin haka ranar ta kirata via phone tana maimaita fad'in ta k'i
zuwa,ta fara bata hak'uri tace za ta zo kou zuwa anjima,Jawahir cikin jin haushi
tace "Kada ma kizo,kiyi ta zama" dariya Ismat tayi tace "I'm sorry big sis,zan zo
fa nace" Jawahir tayi murmushi tace "Tou sai na ganki,saura ki shanya ni" Ismat
tace "A'a bazan yi ba" suka yi sallama,bedroom d'in Mom ta wuce with intention of
ta sanar mata,Mom tace "Allah tsare,ku gaisheta" had'e rai Ismat tayi tace "Ni fa
mom ba da kowa zan tafi ba,ni kad'ai na zanje" Mom ta kalleta tace "Ba tare za kuje
da habibtiiy ba?" Tayi sauri ta kad'a kai tace "A'a!" Mom da ta zuba mata idanu
tace "Ko saboda me?" Directly tace "Ita tace kowa yayi tafiyarsa daban waccan
ranar" Mom couldn't stop looking at her da mugun mamaki tace "Akan wane dalili kuka
raba tafiya?" Everything da ya faru ranar ta kwashe ta sanar mata a lokacin,Mom
tayi shiru tana mamakin al'amarin Badriyah though babu wani bak'on hali na ta da
bata sani ba,Ismat ta mik'e tace "Mom bari na shirya kada rana yayi" Mom ta rakata
da idanu ta kasa magana har ta fita daga room d'in ta rufe mata k'ofa.

Since Ismat taje gidan Jawahir ranar suka zauna suna hira Jawahir take ta mata
k'orafin abunda Badriyah tayi mata kafin su baro gidan surukanta,abunda Ismat bata
sani ba bayan dawowar su Jawahir,sai da suka yi sati d'aya a can,but zuwan Badriyah
gidan yayi wajen uku banda zuwan da suka yi tare da Ismat ranar da suka sauka
k'asar,a duka zuwan kuma ba ta tab'a tafiya da wuri,Ismat taita bawa Jawahir
hak'uri ta kasa cewa komai kan maganar though abun ya mugun d'aure mata kai da yake
duk idan ta tambayeta cewa take gidansu taje,sun jima sosai suna hirar kafin Ismat
tayi k'ok'arin kautar da maganar suka fad'a wani,suna cikin hira lokacin after asr
prayer kiran Fawad ya shigo wayata,Jawahir da ta fi kusa da wayar ta hango *"LOVE-
LOCK!"* b'aro² yana yawo ta zaro idanu tana dariya,da sauri Ismat ta tashi tabar
wajen rik'e da wayarta tana sakin murmushi,Jawahir ta d'aga murya ganin Ismat ta
wuce hanyar d'aya daga cikin bedroom d'inta da suke downstairs tace "Lallai lil sis
kice mun kusa shan biki" Ismat tayi dariya bata ce komai ba ta shige da sauri tana
kai wayar kunnenta daf kiran zan katse,muryarsa ta jiyo a sanyaye yana fad'in
"where have u been har kira yana shirin katsewa baki picking ba?" Tayi murmushi
lying onto the bed a hankali kamar ba ta son yaji tace "Ba ko ina" yace "Amma kina
kallo ina kira baki answering ba?" Ta girgiza kai a hankali tace "Not at all" yayi
shiru yana jira yaji ta ce wani abu sai tayi shiru,a hankali yace "Kina ina
yanzun?" Jim tayi then a hankali tace "na je gidan Yaa Jawahir" yace "tun wane
lokacin?" Tace "tun d'azun" yayi shiru da farko kamar yana nazari,a hankali kuma ya
sake cewa "When za ki tafi gida?" Directly tace "not too long" ajiyar zuciya yayi
yace "za ki jira nazo nan d'in?" Kamar ba ta son hakan ta daure tace "toh!" Yace
"Sai na zo?" Ta sake gyad'a kai a fili tace "Ehh",after sun gama wayar ta fito
Jawahir ta bita da kallo tace "yawwa lil sis zo ki fad'a min wane ne love-lock
d'innan!" Dariya Ismat tayi tana takowa cikin parlon tace "Kai Yaa Jawahir nima fa
ban san shi ba" Jawahir dake kallonta tace "Wasa kike yi kou?" Ismat ta b'ata rai
tace "A'a'a! Da gaske nake" murmushi Jawahir tayi tace "Tou yayi,idan lokaci yayi
za mu sani ai" dariya Ismat tayi bata sake cewa komai ba,lokacin da Fawad ya
k'araso waya ya fara yi mata,ta kalli wayar a hankali kafin ta d'auka ta kai kunne
da sallama,yace "Za ki iya fitowa waje ina jiranki?" tayi shiru da farko kamar baza
ta yi magana ba,a hankali kuma sai tace "toh" Jawahir ta bita da kallo ganin yadda
tayi,after ta ajiye wayar ta yi shiru tana tunani Jawahir dake kallonta tace "Ya
dai lil sis?" Ismat tace "wai fa yana waje yace" Jawahir tace "tou mene ne abun
damuwa a nan? Kice ya shigo mana,ai bai kamata ku tsaya can waje ba kou though nan
babu ruwan kowa da al'amarinka" tab'e baki tayi bata ce komai ba ta mik'e ta d'auki
vail d'inta tace "barin je sai na fad'a masa" Jawahir tace "alright! But za dai ki
gyara fuskarki ba haka za kije masa kamar kina takara ba kou?" Dariya ta fara
Jawahir tace "ai na sanki ne yanzun sai kice a haka za kije" ta girgiza kai tana
rik'e dariyar da take tace "A'a'a!" Jawahir taharareta tace "Ehh dama mana,yanzun
kou saboda maganar da nayi ai baza kije a haka ba" murmushi ta saki ta wuce a
hankali ta koma bedroom d'in da ta shiga,time d'in data fito a nutse ta dunga
tafiya cikin compound d'in kamar tana counting steps har ta zo get,sabon get man
d'in gidan ya taso da sauri yana rusunawa ganin tana nufar hanyar fita yace "Hajiya
da kin kawo an je miki aiken" Ismat tayi saurin kallonsa fuskarta a sake tana kad'a
kai tace "No! Ba aike bane,na gode" tana fad'a ta wucesa yana mata addu'ar dawowa
lafiya ta amsa,since ta sako k'afarta waje Fawad dake zaune cikin mota ya zuba mata
idanu har ta k'araso ta tsaya a side d'insa tana matse fingers d'inta,sauke glass
yayi yana kallonta a hankali yadda tayi bala'in kyau though ba wani shahararren
kwalliya tayi ba daga powder sai chapstick sai kajol a idanunta,cikin cool voice
d'insa yace "Baza ki shigo ba?" Tayi saurin d'agowa ta kalleshi,ganin yadda yake
kallonta a hankali ta fara janye idanunta tana girgiza kai tace "A'a kazo dai mu
shiga ciki kai" murmushin da bai niyyar yi ba yayi idanunsa akanta har lokacin yace
"Me yasa?" Ta d'auke kai tana kallon k'asa tace "Yaa Jawahir tace na sanar maka"
murmushi ya kuma yi kamar bazai sake magana ba,then a hankali ya bud'e motar ya
fito,k'ananun kaya ne sanye a jikinsa da suka yi matuk'ar amsarsa,bayan ya rufe
motar gently ya dunga takowa har ya k'araso kusa da ita,k'amshinsa da ya cikata
yasa ta lumshe idanunta a hankali tana jin wani irin sanyi yana ratsata
everywhere,da cool voice d'insa yana sauke mata wani irin kallo yace "Let go" ta
juya a hankali tana kallon unguwar da yake shiru babu wani hayaniya ko masu wucewa
kasancewar arean duk manyan gidaje ne,yaga ba ta da niyyar wucewa yayi still yana
zuba both hannayensa a aljihun trouser d'insa ya kafeta da idanu,tayi jiyar zuciya
a hankali ta sunkuyar da kanta k'asa ta fara k'ok'arin tafiya,ya tsaya kallonta ya
k'i binta su tafi tare,har ta yi gaba ta waigo tana kallonsa yadda taga yake
kallonta yasa ta turo baki bata ce komai ba taja ta tsaya tana b'ata rai,yayi
sanyayyan murmushi har sannan bai daina kallonta ba sai tambayar da yayi mata "What
happened?" Tana sake tsuke fuska tace "Ba kaine kake kallona ba" yace "Ke kuma ba
kya son hakan kou?" Ta gyad'a masa kai da sauri,ya gyad'a kai yace "ni kuma ina
so,yanzun ya kenan?" D'auke kai tayi tace "Ni dai ba na so tou" yayi murmushi yace
"ba kya so na dunga zuwa na ganki kenan?" Saurin kallonsa tayi ya d'age eyebrows
yace "Ehh mana" ta d'auke kai tace "A'a ni bance haka ba" yace "kin ce mana" rau²
idanunta suka yi tana kallonsa eye in to eye tace "ni yaushe kaji na ce haka?" Yayi
murmushi yace "Cewa fa kika yiba kya son na kalleki" tace "tou ai bance ka daina
zuwa ba dai" dariya yayi sai bai sake cewa komai ba,ta lumshe idanunta a hankali
lokacin da wayarta ta fara k'ara,a hankali ta kai idanunta kan wayar taga sunan
Jawahir yana yawo,ta d'ago a hankali ta kalleshi,shima d'in ita yake kallo sai tayi
sauri ta d'auki kiran ta kai wayar kunne,Jawahir tace "me yasa baku shigo ba?"
Shiru tayi da farko then tace "Yanzu za mu shigo" Jawahir tace "Okay" sai ta fara
katse kiran,tana sauke wayar a kunnenta bata yarda ta kalleshi ba tace "za ka shigo
da motar ne?" Ya kad'a kai a hankali yace "No! Ba jimawa zan ba" ta kad'a kai a
hankali tace "Let go inside tou" yace "alright" a nutse suka jera suna tafiya kamar
wasu couples har suka k'araso balcony,ita fara shiga parlon yana binta a baya,babu
kowa cikin parlon ta nuna masa armchair ya zauna then ta zauna itama,sun samu over
1 hour tare har Jawahir ta fito suka gaisa tana ta mamakin dama shi ne saurayin
Ismat d'in amma ranar can suka raina musu hankali,yadda suka nuna kamar basu san
juna ba abun yayi ta ba ta darita,bayan ya tafi Jawahir ta fito tana yiwa Ismat
d'in wani kallon asirin ki ya tonu fuskarta da murmushi tace "Wato gulma ne yasa
ranar kuka nuna baku san maganar ba?" Ismat ta fara dariya ta b'oye fuskarta jikin
kujera,Jawahir tace "Lallai lil sis,ai kuwa zan sanarwa Mami duk ranar da naje
gidan" saurin d'agowa Ismat tayi tana zaro idanu tace "Kiyi hak'uri Yaa Jawahir dan
Allah kada ki fad'a mata" Jawahir tayi dariya tace "kou saboda me?" Ismat tace
"Allah kunyarta nake ji ni dai" Jawahir ta rik'e baki tana kallonta tace "kiji
shirme zuwa gidan kike da za kice haka?" Ta girgiza kai da sauri tace "A'a tou idan
muka had'u wani wajen fa?" Jawahir tasa dariya tace "gaskiya kina da abun mamaki
sweetheart,ke yanzu dan Allah ina kike tunanin za ku had'u?" Ta bud'a hannu tace
"abun ai na Allah ne" Jawahir ta kad'a kai tace "haka ne" cike da zolaya,sai after
6pm sannan Ismat ta yima Jawahir sallama,Jawahir ta rakata har bakin mota sai da
taga fitarta daga compound d'in gidan sannan ta koma tana jin kewar Ismat d'in,dan
ma Ismat d'in ta k'i zama kamar yadda Jawahir d'in ta so,amma kou kad'an bata yi
niyyar barinta ta tafi ba a ranar.

Motarta yana shigowa compound d'in gidansu after ta yi parking a carport ta
fito rik'e da wayarta da keys ta wuce hanyar apartment a nutse,tana shigowa parlor
da sallama kamar ance ta d'aga kai idanunta suka sauka kan Barraq dake zaune
Badriyah a gefensa sai surutu take masa thouhg ba ma saurarenta yake yi ba
hankalinsa na kan phone d'insa da yake dannawa,zaro idanu Ismat tayi surprisingly
take kallonsa ta tsaya cak inda take,almost two minutes tana tsaye ta kasa sake
takawa,sai data gama tabbatarwa shi d'in ne da gaske babu wasa,tana sakin k'arar
murna like a rattle ta nufi wajensa cikin k'arajin murna take fad'in "Bhai na
oyoyo" duka suka d'ago a tare shi da Badriyah,fuskarsa a sake unlike kafin yaji
maganarta yake jifanta da wani irin murmushin k'auna,Ismat dake shigowa quickly
tana k'arasowa wajensa ta fad'a jikinsa tana dariya,d'agota yayi saurin yi yana
kallonta ya b'ata rai yace "ke wai baki san kin girma ba?" Ta fara k'ifta idanu
tana kallonsa kamar za tayi kuka ta sauka daga jikinsa tace "ni dai ban girma ba"
tab'e baki yayi yana kallon Badriyah ta gefen idanunsa,yadda tayi kicin² abun ya
mugun bashi mamaki,bai damu ya tambayeta lafiya ba ya maida hankalinsa kan Ismat
dake k'ifi² da idanu yace "baki girma ba kike iya tsayawa da saurayi?" Zaro idanu
tayi tana komawa baya a tsorace tace "saurayi kuma?" Ya kafeta da idanu yace
"k'arya aka miki?" A hankali ta fara girgiza kai tana kallon Badriyah data had'e
rai ta k'i kallonta tace "inji wa yace haka?" Tab'e baki yayi yace "Ohoo miki,wanda
suke tare dake ai sun sani,but tunda na dawo garin yanzun zan sani ai idan ma ba
gaskiya bane" washe baki tayi tana matsowa ta rik'e masa hannu tace "Da gaske bhai
ka dawo nan?" Ya kad'a mata kai yace "sure" tayi ihu ta sake fad'awa jikinsa tana
sambatun murna,da sauri ya janyeta yana fad'in "kee! Nutsu or else yanzun na
faffalla miki marin da zai nutsar da ke" zaro idanu tayi tana kallonsa ganin how
serious he's da sauri ta fara matsar idanu,a shagwab'e tana kumbura fuska tace
"kuma daga zuwa sai duka?" Harararta yayi yace "try me and see!" Kukan k'arya ta
fashe da tana shura k'afafu,ya zaro idanu da sauri yana kallonta kafin yayi magana
Mom dake tsaye sama ta furta "what happened sweery?" Tashi tayi da sauri wiping
away her tears tace "tou ba bhai bane yace zai doke ni" Mom ta zaro idanu tace
"akan wane laifin?" Sum² Barraq ya mik'e yana k'unshe dariya zai bar wajen,Mom tace
"laifin me tayi maka Barraq?" Juyowa yayi yana sakin murmushi yace "ni fa Mom ba
haka nace ba" Mom ta zuba masa idanu tace "da dai ban san halinka ba,sai ka fad'a
min haka" murmushi yayi yana shafa kansa ya dawo kusa da Ismat data had'e rai a
hankali ya furta "tell me who's the guy?" Saurin kallonsa tayi,ya d'auke kai bai
kalleta ba yace "am asking" juyawa tayi inda Badriyah take kamar za

15 / 70