Chapter 60 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   60 / 70

177K to 180K   out of 210K words

ajiyar zuciya ya tab'e baki ya biyo bayanta,tana ganin ya
shigo cikin toilet d'in ta bud'e idanu tana kallonsa tace "wanka fa zanyi ka shigo"
yace "waye yace kiyi?" Ta tsaya kallonsa da rashin fahimta,ya k'arasa kusa da ita
ya zare towel d'in yayi k'asa da pant d'inta,gaba d'aya ta k'ame a tsaye tana jinsa
yace "sai na ce ki cire?" Ta d'aga k'afarta da sauri,ya zare pant d'in ya cire pad
d'in ya nad'e ya ajiye,tana tsaye ya wanke pant d'in ya shanya,ya juyo ya kalleta
ganin irin kallon da take masa ya d'aga mata gira yace "me kike kallo?" Ta kasa ba
shi amsa,ya k'araso inda take ya riko hannunta ya kaita gaban tube d'in yace "Oyah!
Shiga muje" yauma d'in kamar da dare shi yayi mata komai sanda suka fito ya shafa
mata mai ya d'auko mata kaya riga da zani na wani red d'in atamfa tasa,ya zaunar da
ita gefen bed ya juya ya fita,bai jima ba sosai ya dawo da lafiyayyen breakfast,ya
k'araso da trolley d'in gabanta ya janyo kujera ya zauna,da kansa ya ciyar da ita
sai da tace masa ta k'oshi kafin ya kyaleta ya fita da kayan,da ya dawo ya ganta
jingine da gado idanunta a lumshe hawaye suna sakkowa fuskarta,ya k'arasa ya zauna
kusa da ita a hankali da wani sanyayyan murya yace "hala akwai abunda na kasa yi
miki?" Ta girgiza kai bata bud'e idanunta ba ta fashe da kuka,da sauri ta fad'a
jikinsa ta rungumesa,ya rik'eta da sauri yana b'ata rai yace "kukan me kike yi?" Ta
girgiza masa kai ta kasa magana,yayi cupping fuskarta ya zuba mata idanunsa yace
"open ur eyes" bud'ewa tayi saurin yi,yana kallon cikin idanunta yace "oyah! Tell
me what's ur problem?" Ta girgiza masa kai,yace "nothing?" Ta gyad'a masa kai,yace
"Mmm! What really makes u cry da safiyar nan?" Da muryar kuka tace "kai ne" ya zaro
gray idanunsa yace "ni?" Ta gyad'a masa kai da sauri,yace "ni da kaina nasa ki
kuka?" Ta sake gyad'a masa kai,ya gyad'a kai yace "lallai na ci ayi min hukunci
tunda na sa kika yi min asarar precious hawayen nan" ta girgiza masa kai alamun
a'a,yace "ba sai an hukunta ni ba?" Ta gyad'a masa kai da sauri,yayi murmushi da
wani irin sanyayyan murya yace "im sorry.. Kin hak'ura ko?" Tayi nodding kanta,ya
lumshe idanunsa a hankali ya kai bakinsa dai² idonta na dama,ta lumshe idanunta da
sauri,sanda ya tsotse hawayen ya mayar da bakinsa idonta na hagu shima ya shanye,ya
d'ago yana kallon yadda ta kulle idanunta,ya sauke idanunsa akan lips d'inta da
suke nan wasu irin baby pink sai d'aukar idanu suke suna k'ara fizgarsa yaji idan
bai kissing d'insu ba bazai samu nutsuwa ba,a hankali ya kai lips d'insa kansu yayi
sucking,sanda ya janye yana sauke ajiyar zuciya muryarsa a d'an dashe yace "good
morning humsafar.." Tana jin ya ce haka bata san sanda tayi murmushi ba,ta
rungumesa tsam da siririyar muryarta tace "morning,how are u my favorite?" Ya bud'a
idanu da sauri ya kalleta,ta d'aga masa gira kamar yadda yake yi idan bai son yin
magana,yayi murmushi yana kallonta yace "repeat please" tana kallon idanunsa da
wani muryar kissa tace *"FAVORITE.."* Yayi murmushi ya matso da fuskarsa dai²
nata,tana jin saukar numfashinsa ta d'aga idanu tana kallonsa,shima d'in kallonta
yake sanda ya kai bakinsa saman nata ya had'e su,suka sauke ajiyar zuciya tare ta
zagaya hannuwanta ta tallafe backhead d'insa giving him more access to her lips.
K'arar da wayarta yayi ya dawo da su,ya saketa da kyar ya kifa fuskarsa a k'irjinta
ya dunga sauke ajiyar zuciya,ta kai hannunta ta d'auko wayar,tana dubawa taga bhai
ta yi mamaki da ta d'aga kai ta kalli agogo,tayi murmushi dai ta d'auka,daga gefen
Barraq sanda tayi masa sallama ya amsa,a hanzarce da wani murya yace "kina lafiya
kuwa kid sis? Jikina ya bani kamar akwai abunda yake faruwa" tayi murmushi tana
kallon Aadil dake kwance jikinta idanunsa a rufe ta gyad'a kai tace "sure bhai
lafiya lou muke" yayi ajiyar zuciya yace "Alhamdulillah! Hankalina ya d'an kwanta
yanzun" kafin ya sake magana tace "and... Bhai u gotta new baby.." Ya bud'a idanu
da sauri yace "when? Kuma daga gurin wa?" Tayi dariya tace "da dare ne" yana jin ta
fad'i haka ya fahimci abunda take nufi ya sakin wani murmushi yace "so u give
birth?" Tace "ehh" a kunyace tana rufe idanu,ya gyad'a kai da wani irin farin ciki
kwance a fuskarsa gaba d'aya yaji ya rasa me zai sake cewa,da kyar ya iya tattara
words d'in ya furta "maa sha Allah! Let me inform Mom first.. Sai na zo" tayi
murmushi bata ce komai ba,ya fara katse kiran,ta bud'a idanunta tana sakin
murmushi,a hankali ta lek'a fuskarsa sanda ta fahimci kamar bacci ya fara
d'aukansa,tayi murmushi ta san jiya bai samu yayi bacci ba sosai,ta sa wayarta a
silent to avoid waking him then ta kunna network,tana yin online ta fara ganin
sak'onnin Badriyah da tace tana ta kiranta jiya bata d'auka ba hope lafiya,dama ta
kira ne ta fad'a mata ta koma gida lafiya,tayi murmushi ta amsa mata a nan ta sanar
mata maganar haihuwarta,ta shiga group d'insu ta tarar da Madeeha,tace "hey girl!
Na haihu fa" Madeeha ta fara mata dariya ta k'i cewa komai because kusan kullum sai
ta tsokane su tace ta haihu,da taga bata kulata ba sai dariyar da take yi tace
"hey! Me ya baki dariya?" Madeeha tace "na ji kince kin haihu,idan kiran haihuwar
kike Allah kawo miki ita a kusa,and za mu taya ki" zaro idanu Ismat tayi tace "Ohh!
Baki yarda ba?" Madeeha tace "ya za'ayi na yarda dama ai kin saba cewa kin
haihu,and kada ki manta jiya muka zo" Ismat tayi murmushi tace "so kina da ja
kenan?" Madeeha tace "Yeahh!" Wani murmushi Ismat tayi tace "me zanyi ya tabbatar
miki da gaske nake?" Madeeha tace "no! Ba sai kin wahalar da kanki ba" Ismat tayi
dariya ta juya gefen baby'n tayi snapping masa pictures ta tura musu,Madeeha na
ganin pic d'in ta mik'e zaune tace "please! Mar'at akhiiy da gaske kike ko wasa?"
Ismat tayi dariya tace "sai kin zo za ki tabbatar" tana fad'an haka tayi
offline,Madeeha na ganin ta sauka ta fara kiranta,tana kallon wayar tak'i d'auka
because ba ta son tayi abunda zai tashesa. Around 9am Madeeha sun fito za suje
gurin Mami saboda musun da suke yi kan maganar haihuwar Ismat d'in,suka tarar da
ita tana shirin fita Madeeha tace "Mami wai mar'at akhiiy ce tace ta haihu!" Naina
tace "Mami na fad'a mata da haske ne wannan karon,har fa pictures d'in baby'n ta
turo" Mami dake sakin murmushi tana kallonsu tace "hala sai yanzu kuka sani?" Suka
tsaya duka suna kallonta da mamaki,tace "maza kuzo zan aike ku" suka fara kallon²
Naina tayi murmushi tace "ai na fad'a miki dama kika dage akan jiya muka je,bai ci
ta haihu ba" mami tace "tun dare Yayanku ya kira ni ya fad'a min zancen" Naina tayi
ihu ta rungume Madeeha tace "yesssss!" Mami dai bata sake bi ta kansu ba ta basu
sallahun aikenta then tayi musu sallama,Naina tace "Mami unguwa za kije?" Mami tace
"zanje na duba su" Naina tace "Mami na zo muje?" Mami tace "a'a zanje na dawo,maybe
mu taho tare da su nan" suka amsata suna mata a dawo lafiya,tana fita daga d'akin
suka doka tsalle a tare suka sa ihu,Naina tace "amma mar'at akhiiy ta shammacemu"
Madeeha tace "ki bari kawai nifa ban yarda ba da take fad'a,thought kawai irin
wasan da ta saba yi mana ne" Naina ta gyad'a kai tace "nima da farko ban yarda
ba,but pictures d'in baby'n su suka sa na yarda." Sanda Mami ta isa gidan shiru ta
tarar da shi kamar babu masu rai ta kalli compiund d'in kafin ta kalli driver tace
"ka jira ni ba jimawa zanyi ba za mu koma" yace "to madam" ta k'arasa entrance tayi
knocking,maids da suke aiki suka bud'e mata,ta shiga tana sakin murmushi suka gaisa
kafin ta k'arasa parlor ta zauna ta fara kiran
line Aadil,cikin bacci ya dunga jiyo ring d'in wayarsa,ya bud'a idanunsa da kyar
yana shirin tashi yaji shi a rungume jikinta,mamaki ya hanasa motsawa,ya zuba mata
idanu ganinta a zaune ta jingina a jikin pillow,yayi ajiyar zuciya a hankali ya
zare hannuwanta ya tashi,yana d'aukan wayar kiran ya katse but ya ga wanda ya
kirashi,here ya fara kiranta back,Mami ta amsa tace "kana ina?" Ya lumshe idanunsa
masu cike da bacci yace "ina gida" tace "alright ga-ni downstairs" ya bud'a
idanunsa with suspicion da sauri ya juya zai fita,Ismat da tun tashinsa itama ta
tashi tace "ina za ka?" Ya tsaya bakin k'ofa sanda ya waigo yace "Mami ce ta zo" ta
gyad'a masa kai ta fara k'ok'arin sakkowa,ganin zai fita tace "baby'n fa? Ka
d'aukesa to ka tafi da shi" sai lokacin ya tuna ya juyo a nutse ya d'auko sa suka
fito tare tana biye da shi suka sakko,Mami ta bisu da kallo sanda suka k'araso tana
sakin murmushi tace "sannu daughter!" Ismat ta sunkuyar da kanta cike da jin
kunya,ta zauna saman throw pillow data sauke,a ladabce ta fara gaisar da Mamin,ta
amsa tana karb'ar baby'n da Aadil yake mik'a mata,ta zuba masa idanu tana kallonsa
fuskarta d'auke da farin ciki tace "maa sha Allah!" Ta yi masa addu'ah,sanda ta
kalli Aadil tace "za ta je gida ne?" Ya girgiza mata kai ba tare da ya yi magana
ba,tace "a nan kake nufin za ta zauna?" Ya d'ago idanunsa yana marairaicewa yace
"Mami nifa ba na son zuwan" tace "idan an barta nan waye zai na mata wankan kenan?"
Saurin kallonta yayi yace "zanyi mata" wani kallo ta masa tace "ba na son
shiririta,ina ka tab'a jin anyi haka?" Yayi murmushi yace "Mami ki tambayeta kiji
ko yanzun ma ni nayi mata" Mami tayi saurin kallon Ismat tace "haka ne daughter?"
Ismat kunya ta isheta ta kasa magana ta sunkuyar da kanta k'asa tana matsa fingers
d'inta,Mami ta hararesa tace "maza kaje ka shirya min kayansu zan tafi da su" kamar
zai d'ora hannu aka ya kurma ihu ya dunga kallon Mami ya kasa magana,sanda ta
kalleshi tace "lafiya kake kallona?" Ya marairaice yace "Mami kiyi hak'uri kada
kice za ki d'auke su please" yadda fuskarsa tayi gaba d'aya sai ya bata
tausayi.....
#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.


Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.



#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




_Doubt everything in the world but never doubt urself and ur
capabilities.._




5⃣5⃣




D'auke kai Mami tayi daga kallonsa,because yadda yake yi d'in nan zai iya
sawa ta fasa abunda tayi niyya,Aadil dake kallon Mami ganin ta d'auke kai ya san
bata karb'i uzurinsa ba da wani irin murya yace "Mami please.." Kallonsa tayi tace
"me zan maka?" Yace "dan Allah Mami kada kice sai kin tafi min da mata,i promised u
zan ba su kulawan da ya dace,ni ba na son wannan zuwa wankan da kuke cewa!" Wani
kallo ta tsaya tana masa mai tattare da mamaki,wai ita yau Aadil ya bud'e baki yake
cewa "matarsa" ba tare da kunya ba how on earth? Shin ya manta lokacin da aka yi
auren ne da abubuwan da suka biyo baya,wato yanzu ya san muhimmancinta shi yasa ba
ya son a rabasu? Tayi murmushin jin dad'i ta maida hankalinta kan baby'n dake
hannunta,ba tare da ta kallesa ba tace "kaje ka had'a min kayansu yanzu,driver yana
jiranmu za mu wuce" kallonta ya dunga yi ya kasa sake cewa komai,sanda ya juya ya
kalli Ismat da kanta ke k'asa yace "ni dai Mami gaskiya ba na so" tace "ni kuma ina
so" yace "but.." Da sauri ta katseshi tace "but what? Ba na son musu ka sani,ka
wuce ka had'a min kayansu nace" ajiyar zuciya yayi ya gyad'a kai,ransa a b'ace
sanda ya mik'e ya kallo inda take ya wuce sama a fusace,Mami ta d'aga kai ta bisa
da kallo kafin ta kalli Ismat da ta sunkuyar da kanta k'asa,ko da ya haura saman
bedroom d'inta ya fara shiga,ransa a b'ace ya zauna gefen bed ya zuba idanunsa akan
press d'inta ya kasa aiwatar da komai,Mami taji shirun ya yi yawa tace "daughter je
ki d'auko mayafinki mu tafi,duk sanda yaga dama ya gama had'a kayan ya biyo mu da
su" a sanyaye tace "toh Mami" ta mik'e ta fara tafiya,Mami ta bita da kallo kafin
ta d'auke kai,tana haurawa saman da sauri ta bud'e bedroom d'in ta shiga,ta ganshi
zaune bakin gado ba shi da niyyar aiwatar da abunda Mamin tace,ya d'ago idanunsa a
hankali ya kalleta,takowa tayi inda yake a hankali kamar wacce k'wai ya fashewa a
ciki ta zauna kusa da shi ta rik'o hannunsa,ya bita da kallo ya kasa magana,cikin
sanyin murya tace "me yasa kake son yin jayayya da hukuncin Mami eh?" Kai ya
girgiza mata zai yi magana ta rufe masa baki da hannunta tace "kayi hak'uri tunda
ta yanke hukuncin,kamar yau fa za mu dawo" ya zuba mata idanu sanda tayi shiru ya
janye hannunta ya rik'e gam,idanunsa a cikin nata da wani sanyayyar murya yace
"kina son zuwa?" Ta girgiza masa kai a hankali,yayi ajiyar zuciya kafin yace "why
didn't u help me ki fad'awa Mami kema ba kya so to?" Ta zaro idanu da sauri za tayi
magana,ya katseta "if u really don't want please muje mu fad'a mata yanzun,ni
gaskiya ba na so kuyi nisa" ajiyar zuciya tayi a shagwab'e tace "ni ce kuma zan
fad'a mata?" Yace "yeah! Shi ne za ta yarda" Ta girgiza masa kai tace "ni dai ina
jin kunyarta" yace "so baza ki iya ba kenan?" Ta gyad'a masa kai da sauri,ya
had'iye wasu irin yawu idanunsa a kanta yace "alright! Kije ku tafi" saurin
kallonsa tayi za tayi magana yace "no! Ba sai kince komai ba,jeki kawai ku tafi."
Kamar za tayi kuka ta dunga kallonsa,ya d'auke kai yayi shiru,da taga ya k'i kulata
ta mik'e a hankali ta fara tafiya har ta je bakin k'ofa kuma sai ta kasa fita,ta
tsaya a gurin tana kallonsa,yayi ajiyar zuciya a hankali ya koma ya kwanta ya dafe
kansa da hannuwansa,dawowa tayi da sauri ta fad'a jikinsa ta sa masa kuka,ya d'ago
da kyar yace "me aka miki kuma?" Cikin kuka tace "ni dai ba na son zuwa" yace "a'a
kina so mana" ta girgiza masa kai da sauri tace "i don't want.." Ya rik'o fuskarta
yana kallonta yace "idan baa kya so me yasa baza ki iya fad'awa Mami ta barki ba?"
Tace "ni kunyarta nake ji" yace "alright! Za ki iya fad'awa Mom maganar?" Ta gyad'a
masa kai da sauri,ya zuba mata idanunsa a hankali ya fara share mata hawaye yace
"okay! Shi kenan,daina kukan" juyawa yayi ya fara neman wayarsa,tace "me kake
dubawa?" Yace "my phone" tace "ka barshi a k'asa ai" yayi saurin kallonta kafin ya
tashi ya nufi hanyar fita,tayi ajiyar zuciya ta koma ta kwanta lamo,yana sakkowa
Mami ta kalleshi ganinsa shi kad'ai ta had'e rai tace "kai Malam ina kayan?" Ya
b'ata rai yace "Mami!" Da sauri ta katsesa tace "kada kace min komai dan Allah,na
gama fahimtar inda ka nufa ai" saurin kallonta yayi,tace "shi kenan,itama ja'irar
daga cewa je ki d'auko mayafi tak'i saukowa,ta biye maka tunda ba ka so itama baza
ta ba" yayi murmushi ya kauda kai yace "Mami itama fa ba son zuwan take ba" Mami
tace "ita ta fad'a maka ko kai ka tsara mata hakan?" Yayi murmushi yace "a'a Mami
kunyar ki take ji dai shi yasa ta kasa fad'a miki" Mami ta saki baki tana kallonsa
tace "ka ga bana son shirme,na san wannan duk aikinka ne,kaje ka fito min da
yarinya yanzu ina jiranka,idan baka gama had'a kayan ba ma ka biyo mu da su" ya
bud'a idanu yana sakin murmushi yace "Allah Mami dukanmu bama son zuwan,ki yi
hak'uri ki barsu,sai a nemo wanda za ta zauna" wani kallo ta masa tace "kai za ka
nemo ko?" Yayi murmushi ya gyad'a mata kai yace "ehh! Zan nemo" ta gyad'a kai tace
"ai shi kenan" yana jin ta ce haka yace "Mami.." Tace "me kuma za kace? Ina ce na
bar maka matarka?" Ya sosa backhead d'insa a hankali yace "dama su Naina zance ki
turo mana" ta kallesa da rashin fahimta kafin tace "me za su zo suyi muku kuma?"
Yace "za su tayata zama kafin.." Ta yi murmushi ta girgiza kai tace "baza ku had'a
baki ku rainamin hankali ba,sannan yanzu kuce na baku yarana" yayi murmushi yace
"pleaseee Mami kiyi hak'uri" tace "ai da banyi ba ka san saina tafi da su" motsin
da baby'n yake yi alamun zai tashi yasa Mami ta kallesa da sauri tace "kirata maza
ya tashi" wayarsa da ya dawo da niyyar d'auka ya d'auko ya fara kiranta,ta d'auka
tayi shiru,yace "kizo ya tashi" zaro idanu tayi a shagwab'e tace "ka kawosa,ni
bazan iya sakkowa ba" ya d'aga kai ya kalli Mami a hankali kamar mai rad'a yace
"kunyar wa kike ji wai?" Tace "Mami mana,ai na san ka fad'a mata ba na son zuwa,ni
bazan iya had'a ido da ita ba" wani murmushi ya fara yace "Ohh! Ni kuma saboda nine
sarkin marasa kunya zan iya karb'o miki ko?" Tace "to ba kai kaje ka fad'a mata
ba,da ka bari ai da yanzu mun tafi" ya zaro gray eyes d'insa yace "to ko dai na
bari ku tafi?" Tace "ai ka fad'a mata" Mami ta kalleshi tace "wai k'us² d'in me
kake ne nace ka kira min yarinya ka tsaya magana k'asa²?" Ya d'ago idanunsa ya
kalleta yace "wai baza ta iya sakkowa ba" Mami dake kallonsa tace "baka dubata ba
ne sosai da ta haihu?" Ya girgiza kai yana mata murmushi yace "not at all Mom! Wai
kunyar ki take ji" Mami dai mamaki yasa ta tsaya kallonsa,yayi murmushi ya tashi,ta
gyad'a kai tace "zo ka karb'esa to,ni bari na tafi tunda ba'ayi maraba da ni ba"
yayi murmushi yace "Mami waye yace ba'ayi maraba da zuwanki ba?" Tace "ai shi yasa
naga har k'asa aka watsamin a ido daga neman nayi gwaninta aka gwale ni" yace "kiyi
hak'uri to,Allah huci zuciyarki" tace "kai zo ka karb'esa ka kai mata,tunda zaku
iya kula da kanku Alhamdulillah!" Yace "Mami to kiyi masa wanka kafin ki tafi" ta
kallesa tace "da waye yayi masa?" Yace "ni nayi masa" tace "ita uwar fa?" Yana mata
murmushi yace "Mami ni nayi musu" ta zabga masa harara tace "sai yanzu dan kinibibi
za kace na tsaya nayi masa wanka?" Yace "Mami pleasee" ta juya tace "sai kayi
kuma,ai tunda za ka iya babu matsala,kace mata na tafi tunda ta biye maka bakwa son
abunda nazo da shi.. Allah k'ara lafiya." Ya amsa yana sakin murmushi cike da
tsokana yace "Mami bari na zo na raka ki" bata juyo ba tace "a'a na yafe,jeka kai
dai ka kai mata shi kafin ya fara kuka" yana tsaye sai da yaga fitarta kafin ya
juya ya nufi sama yana sakin kayataccen murmushinsa,yana bud'e k'ofar d'akin ta
d'ago da sauri,murmushin da ta ga yana yi yasa ta bisa da kallo har ya k'arasa kusa
da ita ya

60 / 70