Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
ta cikin wayar yayi murmushi yace
"Ohh! Ki bata hak'uri please,na ga mun yi laifi duka" Badriyah ta harari Ismat tana
sake kallon wayar dake hannunta k'iran IPhone 8 Plus tace "Rabu da ita kawai wata
irin mai duhun kai ce itan,but ni babu yadda za tayi da ni" Ismat tana kallon
Badriyah kamar za ta yi kuka tana nuna kanta tace "Ni kike cewa mai duhun kai?"
Badriyah dai bata sake tanka maganar Ismat ba sai sauraron abunda yake fad'a
take,Fawad ya sake yin dariya lokacin da Ismat ke fad'in haka yace "I'm really
sorry ma'am." Almost 30 minutes suka d'auka suna magana yana sake bawa Badriyah
sak'on ta bawa Ismat d'in hak'uri then suka ajiye wayar lokacin tana kallon Ismat
da taji haushi ta rufe idanu kamar mai bacci tace "Idan ba ki da duhun kai me yasa
kika bawa Yaah Barraq dama yake hana mu fita a gidan nan? Wai idan bamu samu
freedom yanzun ba sai wane lokaci ne? Nifa gaskiya ba na son zaunawa a gida,zama
guri d'aya tsautsayi inji kifi,so why bazan fita na sha iska ba tunda i gotta
chance?" Ajiyar zuciya Ismat tayi a hankali ta bud'e lumsassun idanunta tana kallon
Badriyah ta yada kai gefe ba dai tace komai ba,Badriyah tayi tsaki ganin Ismat ba
ta da niyyar yin magana tace "Ko yanzun abunda yasa ni ba zan fita ba raina ne a
b'ace da ko baza ki ba ni kam sai na je" still Ismat bata ce komai ba,sai tashi da
tayi ta nufi hanyar entrance za ta fita,sai da ta kusa door a hankali tace "Ni kam
na je wajen bhai!" Badriyah ta rakata da mugun kallo a masife tace "Allah raka taki
gona" murmushi Ismat tayi tana rik'e da handle na bedroom door d'in cikin zolaya
tana kallon yadda Badriyah tayi kicin² tace "Ko za kije ne mu tafi tare?" Badriyah
ta kyab'e fuska tana yi mata wani kallo tace "Huh! Allah tsare ni da zuwa
wajensa,yanzu kam ina zuwa ai ban san me zai yi min ba kuma" saurin fita Ismat tayi
tana cewa "kanku ake ji,but ni duk na kasa gane muku always fad'a ba kwa shiri"
Badriyah ta tab'e baki tace "Shi dai da bai so a zauna lafiya,mutum kullum fuska
kamar wanda ake aikawa sak'on mutuwa."
Ismat da ta fita tayi dariya tana tafiya cikin nutsuwarta,sanda take sakkowa da
taga babu kowa a parlor,tana gama tsallako staircases d'in ta wuce hanyar bedroom
d'insa,a bakin door d'in ta tsaya ta fara yin knocking,Barraq dake kwance yana
operating laptop ya d'ago kansa yana tambaya "Who's there" Ismat dake tsaye cikin
cool maganarta tace "It's me bhai" tab'e baki yayi yace "come in" a nutse ta murd'a
handle d'in ta tura k'ofar,yana adjusting kwanciyarsa daga rub da ciki ta shigo,ya
zuba mata tsumammun idanunsa har ta k'araso kusa da shi da sallama a bakinta,yana
sake kallonta bayan ya amsa yace "Ya aka yi?" Fuskar damuwa tayi wearing tace
"Bhai! Dama zuwa nayi na baka hak'uri,in Allah ya yarda ba zan sake yin abunda za
kayi fad'a ba" yana kallon yadda take matse yatsun hannunta yace "Gaskiyar da nake
fad'a shi ne nayi miki fad'a kou Ismat?" Saurin kad'a masa kai tayi idanunta suna
tara hawaye tace "A'a kawai na fad'a ne,but na sani gaskiya kake fad'a" ya kad'a
kai yana tab'e baki yace "Ok then?" Tayi shiru,komawa yayi ya kwanta yace "na ji
tafi ki ba ni wajen Allah kiyaye" still tayi ta kasa motsawa,ya d'ago a fusace yace
"Tafi mana,tsaiwar me kike yi min a kai kuma?" Ta d'ago kanta tana kallonsa hawaye
har sun fara sintiri saman fuskarta tace "Please bhai bazan sake cewa haka ba,kayi
hak'uri har abunda Mom tace please!" Idanunsa yayi saurin rufewa because a
rayuwarsa ya tsani yaga tana kuka,but abunda yake shirin yi yanzun ya san dole ne
ya fara koyan yadda zai jurewa ganin zubar hawayenta,a dak'ile bai yarda ya sake
kallonta ba yace "Uhn! Will u get out please my friend?" tana kallonsa tace "Toh"
da muryar tausayi,a sanyaye cike da wani irin mutuwar jiki ta juya ta fara tafiya
tana share hawaye,ya bita da kallo har ta je bakin k'ofa za ta fita yayi calling
sunanta out "Ismat!" Tayi saurin juyowa tana amsawa yace "Ina Badriyah?" Tace "Tana
can bedroom" yace "Kice tazo ina nemanta,ku taho tare" amsawa tayi da sauri ta
fita,sun jima sosai kafin su zo saboda Badriyah bata yarda Barraq yana kiranta
ba,har sai da Ismat d'in tayi mata rantsuwa sannan ta yarda ta biyota suka
taho,suna shigowa Ismat tayi sallama,ita kam Badriyah tana had'a rai tace "Ga ni
ance kana kira na!" Ya d'ago idanunsa ya zuba mata su saboda jin a yadda tayi
maganar da raini,inwardly yayi k'wafa yana saita yanayinsa yace "Yeah! I just want
to say sorry kan abunda ya faru d'azun" tayi saurin kallonsa taga ita yake kallo
shima sai tayi fuska tace "Uhn! Babu komai" yayi murmushin gefe a ransa yana wani
tunani yace "Shi kenan za ku iya tafiya" Ismat da ta ji dad'in abunda yayi da sauri
taje ta rungume shi tace "thank u bhai,i love u" yayi murmushi ya shafa kanta,ta
juya da sauri ta kalli Badriyah dake shirin fita tace "Habibtiiy why didn't u say
u're sorry too to bhai?" A fusace Badriyah dake tafiya ta juyo za tayi masifa suna
had'a ido da Barraq da ya kafeta da kallo,quickly ta lumshe idanunta tana jin yadda
gabanta yake fad'uwa saboda idanunsa ba k'aramin kwarjini suke yi mata ba,duk
iskancin da take ji da shi ko fitsara ta shirya yi masa a mafi yawan lokuta da sun
had'a ido da shi take jin ta kasa,muryarta tana rawa ta kasa sake kallonsa tace
"I'm sorry Yaah Barraq,nima bazan sake cewa komai ba" idanu suka zuba mata jin
abunda tace a k'arshe,Ismat ta fashe da wani irin dariya tana satar kallon Barraq
daya tab'e baki tace da Badriyah "Ba fa haka ake cewa ba,kice baza ki sake ba" da
sauri Badriyah ta kalli Ismat rai a b'ace but ta yi k'ok'arin dannewa,tana aike
mata sak'on harara k'asa² tace "Yeah! This is what i want to say ai hausar ne ya
gudu" lumshe idanu Barraq yayi ya juya because ya san baza ta tab'a fad'a dai² ba
duk da anyi mata gyara,ya riga ya san halayyarta na girman kai ba tun yanzun ba,ba
wai iya fad'a ne baza tayi ba kawai bata yi niyya bane,strictly bai yarda ya sake
juyowa ba yace "Ya wuce,za ku iya tafiya" daga haka ya ci gaba da aikinsa,suka yi
masa sallama Ismat a baya,Badriyah a gaba sai cika take kad'an bata fashe ba suka
fito.
Suna fitowa za su wuce Mom ta kallesu ganin suna fitowa daga bedroom d'in
Barraq ta bisu da idanu da tambayar "Me kuka je yi a room d'in Yayan naku ku kuma?"
Ismat cikin farin ciki tace "Shi ne yace mu zo" Mom ta bita da kallon tuhuma tace
"Yayi muku mene ne?" Y'ar dariyar jin dad'i tayi tace "Kawai fa Mom ya bawa
habibtiiy hak'uri ne kan abunda ya faru" Mom tayi murmushi tana kad'a kai saboda
jin dad'in abunda Barraq din yayi tace "Alright! Ya kyauta",saman armchair Badriyah
ta kwanta tana had'e rai saboda ba ta son maganar a hankali tace "ni na baro phone
d'ina a bedroom,sweetheart kira wancan yarinyar please ta kawo min" Ismat tayi
murmushi tace "No bari na je zan d'auko nawa dama" ta fad'a tana wucewa hanyar
staircases,Badriyah ta tab'e baki ta bita da wani kallon takaici tace "ki fad'a
mata ta kawo mana,ko dole sai kin je da kanki?" Murmushi Ismat dake tsallake stairs
tayi tace "Tana aiki ki jira zan kawo miki" Badriyah ta sake yin tsaki a fusace
tace "Ke wallahi *ISMAT* kina da problem,wasu lokutan kina ba ni haushi,idan za
kiyi aikin gidan why not ba'a fasa kawo maidservant ba? Kina sane aikinsu ne but
sai ki dage kice za kiyi" Mom dake zaune tayi murmushi tana kallon Badriyah but she
couldn't talk har time da Ismat ta dawo rik'e da phone biyu iri d'aya a
hannunta,tayi murmushi lokacin tana mik'awa Badriyah da tayi kicin² phone d'inta
tace "take please habibtiiy!" A fusace Badriyah ta fizge tana harararta,baiwar
Allah duk da hakan bata ji haushi ba ta zauna next to her tana yi mata sanyayyan
murmushinta tace "I'm sorry." Mom dake kallonsu a hankali ta kad'a kai cikin ranta
kuwa mamakin halayensu da yayi daban da na juna take yi,even though they're from
one family but d'abi'un su sam babu kama,a nasu side d'in su kam da suke zaune
closer to each other,duk da kowa da abunda ke ransa,tunanin kowa kuma daban,but
kamar had'in baki a lokaci guda suka bud'e network d'in wayoyinsu,k'arar shigowar
sak'onni a jere cikin wayar Ismat lokacin,nan take yaja hankalin Badriyah da sauri
ta d'ago kai a yangancen ta kalleta tana sake had'e rai tace.....
#The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300,VIPs ₦450.
*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*
*1-ACCOUNT DETAILS.*
Acct name-Hauwa Muhammad Usman
Acct number-0060746882
Bank name-Access bank.
*Sai a tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609*
*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*
08165726609
*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*
*3- OTHER WORLD REMITS*
Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone Number:08165726609
City:Kano city.
For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.
#Don't missed.. Ba'ayi komai ba,bare a fara...😍
#Share pls.
#Asli Smasher.
#4/August,2020.A.D.
💠💠💠💠💠
©®2020.
*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/NV64fA4cR6
🆓 Pᴀɢᴇ..
»2⃣
2⃣ :#Sᴇɪᴢᴇs
_In sha Allah yadda kuke gwada min soyayya,ba zan tab'a ba ku kunya
ba,maganar saka english da kuka yi,u dont need to worry about it,if Allah wills za
ku samu littafin Maktoub yadda kuke buk'atarsa,farin cikinku a kullum shi ne
nawa,but dalilin da yasa littafin *'DAN MACE* ban canja daga yadda na fara
ba,firstly dai rayuwar su kansu leading role d'in duk ba'a k'asar nan bane tunda
ana abroad ne sai hak'uri,sai kuma wad'anda suka farfad'o min magana akan
labarin,wannan dalilin yasa na k'i canjawa daga hakan,but for now feel
free,littafin *MAKTOUB* zai zo a sauk'ak'e kowa zai karanta in sha Allah.. But
don't forget to vote,idan babu voting zan yi baya da sakin update akan lokaci.
ILSYM my people.♥_
*The hole todays page is going to HABIBTIY,My Mammah,one in a
millions,Hajiya Maryam Alhassan (Jikar Kulu),Allah ba ki hak'uri Mammah,na san ni
mai laifi ce,but kaina bisa wuya,hope my apology later zai karb'u,and za ki yafe
min laifina😢,anaa ahabbak-thtiir Yaa Mamah.❤*
💕
Da sauri ta d'ago kai a yangancen ta kalleta tana sake had'e rai tace
"please either ki sa wayar ki a silent ko kuma dai ki san yadda za kiyi ya daina
damuna!" Murmushi Ismat tayi ta kad'a kai a hankali saboda akwaita da sanyin rai ta
sake bawa Badriyah hak'uri,daga hakan bata sake bari wayar yayi k'ara ba ta mayar
da shi silent,tana shiga dandalin sada zumunta na whatsapp here ta fara gamo da
rututun sak'onni daga number da ake yawan kiranta,tayi shiru tana kallon screen
d'in wayar fuskarta d'auke da wani irin mamaki had'e da damuwa,then a hankali ta
fara k'ok'arin bud'ewa with intention of ta ga me aka turo da yawa har ya kai
20,sak'on farko sallama ne aka yi sai na bada hak'uri da suke biye da shi wanda
yake d'auke da wasu irin tausasan kalamai masu tsayawa a rai bila adadin,deeply
tayi ajiyar zuciya jikinta yayi sanyi then ta fara replying masa amsa na sallamar
da yayi hannunta har wani shaking yake da ta kasa gane na mene ne? Message d'inta
yana yin delivered kafin ta fita taga ya turo mata sak'on godiya,quickly ta kalla
taga baya online kuma,sannan bata ga lokacin da yake typing ba,ta ji gabanta yayi
wani irin fad'uwa haka kawai da sauri ta fita,kusan mintuna biyu duk sai tunani
take yi ta kasa duba wasu messages d'in tana sake kallon number,can tana tunani sai
taga sak'o ya sake shigowa daga number dai still,bata yarda ta shiga ciki ba ta
tsaya dubawa taga yace "why are u keeping me waiting dear?" Tayi still tana tunani
kamar kada ta duba,sai kuma taga dacewar hakan,b'im ta sake ganin wani sakon ya
fad'o,tayi shahada ta bud'e tana sauke ajiyar zuciya here taga ya ce "Why za ki
barni alone? Alhalin kin san sak'on ki kad'ai ne nake da buk'ata a halin yanzun?" A
hankali ta had'iye saliva's uwa munafiki ya ji tsoron a k'uresa tana satar kallon
Badriyah da Mom then ta fara typing masa "Sak'on mene ne?" Ko minti d'aya ba'a yi
ba ya amsa "Kawai ina jin son yin hira da ke" strictly tace "Ni ban iya hira ba"
emoji ya turo mata yana zare idanu,then yace "Why? Ba ki da abokan fira ne?" Tace
"A'a ina da su,kawai bana son magana sosai" yayi murmushi ya tura mata "Ni kuma
kinga ina da surutu sosai and idan na zauna guri da wuri ake sani na" tace "Ka ji
dad'in ka" yace "Kema haka" murmushi tayi saboda abunda yace daga haka sai bata ce
komai ba,da yaji ta yi shiru bata sake magana ba yace "Dear! Kina mene ne yanzun?"
Tace "Ni wai?" Yace "Yeah!" Tace "Ina zaune a parlor" yace "Ohh! Kina hutawa
kenan?" tace "Mmm!" Yace "but please! Can i ask u something?" Tace "akan mene ne?"
Yace "Kawai na ji ina son friendship da ke and idan babu damuwa za ki iya sending
min picture d'inki na gani?" tayi murmushi tace "Ba na tura pic a social media"
yayi murmushi yace "Sai a ina?" Tace "Babu ko ina" murmushi ya sake yi bai sake
cewa komai akan pic ba,sai yace "Ina sister d'inki da muka yi magana fa?" Tace "Ga
ta kusa da ni,ko na bata yanzun ma kuyi magana?" Da sauri yace "No! But ki fad'a
mata ina gaisheta" tace "Zan fad'a" yace "Yaushe?" Tace "Ko yaushe" yace "Me yasa
ba zaki fad'a yanzun ba?" Tace "Mom tana nan" yayi murmushi yace "Kina jin kunyar
Mom ne?" Tace "Sosai ma,not a little" ya tura mata emoji na thumbs up,tayi murmushi
da sauri tace "Sai an jima" yace "Kina aiki ne za ki gudu ki barni?" Tace "No! Ina
son yin karatu ne" yace "Ok! Kina wane school ne?" Tace "BUK!" yace "Mmm! Kice
babba ce ke? Ina shiga school d'in sosai wajen uncle d'ina,he's a Proff and a
Chancellor of the school also,kin sanshi ai?" Ta ware ido da sauri tace "Proff
Junayd Mutallab right?" Yayi murmushi yace "kin sansa ashe?" Tace "Yeahh! Waye ma
bazai sansa ba? Besides kuma he's my Daddy's friend ma" daga haka sai bata sake
cewa wani abu ba ta b'oye masa sauran maganar,Fawad yayi wani murmushi yace "Woah
bravo! Maybe mun san juna ma fa tunda kin san uncle d'ina and matsayinsa na abokin
Daddy,maybe ma har gidan ku na sani kou?" ita dai Ismat dariya kad'ai tayi tace
"bye for now" yace "Ok! Bye za muyi maganar later,but kafin lokacin ki tanadar min
labari mai dad'i please" murmushi tayi tace "Ban iya labari ba" yace "Har ni ma
baza ayi min hiran ba kenan?" Ta tura masa emoji da ya rufe ido alamun ta ji
kunya,yayi murmushi yace "shi kenan ni zan baki labarin,kina son jin nawa?" Tace
"Sure" yace "Ok later" tace "thank u." Tunda suka gama magana tana ajiye wayar ita
kad'anta ta fara blushing tana wani lumshe idanu,Badriyah dake gefenta ta kalleta
kad'an bata ce komai ba,a hankali Ismat tayi k'asa da voice tana sakin murmushi
tace "Ana gaishe ki" Badriyah data zuba mata ido tana gesturing face tace "Waye
yace?" Cikin muryar rad'a tace "Na d'azun da kuka yi magana da shi a phone" ta
lumshe ido tace "Na gode" daga haka bata sake magana ba ta mayar da hankali kan
phone d'inta,Ismat ta kwantar da kanta a saman shoulder d'inta kad'an tace "U know
what habibtiiy?" Badriyah cikin gajiya da magana tace "Sai kin fad'a" tace "He is
so kind and nice.." Kafin ta k'arasa Mom ta kallesu tace "K'us² d'in me kuke yi
bakwa so naji?" Ismat tayi murmushi tace "Nothing Mom" Mom tace "Idan yayi wari za
mu ji ai" Ismat tana sake yin murmushi ta bud'a idanu tace "ba zai yi ba Mom" da
wani muryar shagwab'a,Mom tayi murmushi tace "Allah yasa." Daga haka itama sai bata
sake musu magana ba ta ci gaba da aikinta.
Yana kwance da rufaffen ido yana wasa da phone d'insa k'irar company'n
apple,iPhone 11 pro gold colour da ya gama chart aka turo k'ofar bedroom d'in da
sallama cikin wani irin romantic and husky voice mai tattare da kwarjini,hurriedly
ya d'ago daga rub da ciki da yayi,ya sauke madaidaitan idanunsa da a kowane lokaci
suke k'ara ma halittar fuskarsa kyau matsayinsa na cikakken namiji mai ji da
gayu,k'udi da ilimi uwa uba kyau,akan d'aya guy d'in dake shigowa,ransa a b'ace ya
kalleshi cikin yanayin fusata da fad'in *"AADIL!* wane irin iskanci yasa ka barni
ina jiranka sama da awanni hud'u? Kawai ka fice ka sa ni zama a d'aki ni ba mace
ba?" Kyakykyawan matashin da ya shigo da sauri wanda a shekaru bazai wuce thirty
four ba,mai matsaikaicin tsayi,ma'abocin faffad'a kuma murd'ad'd'en jikin da ya
bayyana a cikin shirt da ya ainihin kama jikinsa saboda tsaban workout mai launin
red wine,da yayi asalin bayyana siffar sa na cikakken namiji,mamallakin doguwar
fuska,shanyayyun grey eyes wanda za'a iya kira da "blue" at first glance,but they
tend to have flecks of gold and brown,har ma a wasu lokutan they may appear to
change color from gray to blue to green depending on clothing,lighting,and mood
(which may change the size of the pupil,compressing the colors of the iris),dogon
hanci da madaidaicin bakinsa wanda kyakykyawan bread d'insa ya zagaye,ya k'araso
rik'e da glasses da yake rufe idanunsa idan zai fita,though a mafi yawan lokaci
yana ta'ammali da glasses ne ba don yana so ba,but he just wear saboda idanunsa da
ba ya son ana yawan maganarsu ana tankawa,yana shigowa yana unbuttoning wuyan shirt
dake jikinsa,kamar ba zai yi magana ba da farkon ya daure bayan ya d'auki lokaci ya
furta "Sorry Broah Mami ta tsayar da ni tun d'azun,u know tunda abubuwa suka yi
kusa haka ba ni da wani isashshen lokaci yanzun idan ba an gama hidimar nan
ba,kamar wani dai ni ne zan yi auren duk an takura ni!" Tab'e baki na kwancen yayi
yace "Alright! Ka shirya mu fita" da sauri Aadil ya waiwayo ya kalle shi yace "Ina
ne za muje *FAWAD* da wannan lokacin?" Saurin juyowa Fawad yayi a fusace yana
jifansa da wani irin kallo yace "Wai kai me yasa idan aka yi maganar fita sai ka
tambaya?" AADIL dake wucewa rik'e da shirt da ya cire a hannunsa ya tab'e baki yace
"Ka fi kowa sanin ba na son zuwa gurin da ake hayaniya.." Kafin ya k'arasa Fawad ya
tashi yana fad'in "Idan ba za kaje bane Malam kawai ka fito kai tsaye ka fad'a,ai
ka san bazan ji haushi ba tunda ba yau aka