Chapter 8 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   8 / 70

21K to 24K   out of 210K words

kenan. Har ila yau d'aya daga
cikin al'amura masu tasiri a fagen gadar da kwanciyar hankali da nutsuwa ga jariri
a cikin mahaifiyarsa shi ne:Irin mutanen da mace mai ciki take rayuwa tare da su a
k'ark'ashin inuwa guda,gwargwadon irin matakin da mutanen da suke rayuwa da mace
mai ciki suka faranta mata rai a irin hirarrakin da suke gudanarwa da
ita,kwatankwacin irin kyakykyawar tasirin da hakan zai yi a kan jaririn da ke
cikinta,kamar haka ne idan mace mai d'auke da juna biyu tana zama da mutanen banza
masu furta munanan maganganu ko take halartar wuraren batsa da alfasha,hakan zai
iya yin mummunar tasiri a kan jaririn da ke cikinta a bayan zuwansa duniya. An
ruwaito hadisi daga Annabi (S.A.W) yana bayyana cewa:"Maganganun abokin zama na
gari,kamar misalin mai sayar da turare ne,idan har bai yayyafa maka turaren ba,to
duk da haka zaka amfana daga k'amshin turaren,haka nan maganganun abokin zama
mutumin banza,kamar mak'eri ne,idan har tartsatsin wutar k'irarsa bai k'ona ka
ba,to mummunan warin wutar k'irar zai yi tasiri a kanka." Sakamakon haka dole ne a
kan mace mai juna biyu ta d'auki matakin kiyaye hukunce²n shari'a ta hanyar
nisantar ayyukan laifi da suke haramun gwargwadon iyawarta ciki har da furta
munanan maganganu da suke matsayin alfasha tare da nisantar da kanta daga majalisin
gulmace² da yi da mutane. Hak'ik'a matakin gudanar da addu'o'i da zikirin Allah
suna da gagarumin tasiri a kan cikan lafiya da amincin jaririn da mace mai juna
biyu ke d'auke da shi. Tabbas mace mai juna biyu kamar mai jihadi ne a tafarkin
Allah da addu'arta ke saurin karb'uwa a wajen Allah mad'aukaki,hak'ik'a gudanar da
addu'ah da neman buk'atu a wajen Allah suna daga cikin mad'aukakin matsayi da ke
fayyace kasantuwar mutum a matsayin hak'ik'anin bawa ga Allah,kamar yadda ya zo
cikin Suratul-Furk'an a aya ta 77 cewa:"Kace Ubangijina ba zai kula da kuba,ba
domin addu'arku ba." Sakamakon haka ya zama dole a kan mahaifiya matuk'ar tana
buk'atar zuri'ah ta gari da y'ay'a masu kyawawan dabi'u ta kasance ta zage dantse
tare da dawwama a kan addu'ah da neman kusanci a wajen Allah. D'aya daga cikin irin
wad'annan addu'o'i shi ne kamar yadda ya zo cikin alk'ur'ani mai girma Suratu-aali
imraan aya ta 38 cewa:"Ya Ubangiji ka azurta ni daga gare ka zuriya
tsarkakakkiya,hak'ik'a kai mai karb'ar addu'ah ne." Har ila yau a cikin Suratul-
Furqan aya ta 74 Allah yana cewa:"Kuma wad'anda suke cewa "Ya Ubangijinmu! Ka ba mu
sanyin idanu daga matanmu da zuri'ar mu,kuma ka sanya mu abun koyi ga masu
tsoronka." Hakika mahaifa miji da mata za su iya kiyaye irin wad'annan addu'o'i da
suka zo cikin alqur'ani wajen rok'on Allah kan ya azurta su da yara nagari masu
k'oshin lafiya da cikar halitta.." Wani irin tafi gaba d'aya theater ya d'auka
saboda yadda bayanin da yayi ya masifar shiga zuk'atan students d'insa,but duk da
hakan abun duk bai wani ba shi mamaki ba,haka yayi ta fayyace musu bayanai tare da
ayoyi da hadisai cike da k'warewa,gogewa tare da amfani da d'umbin iliminsa,da yake
course d'in 3 credit ne duka har lokacinsa yayi babu wanda ya farga,after ya
tabbatar babu mai sauran tambaya ya kwashe belongings d'insa ya fice cikin takun
isa.

K'atuwar ajiyar zuciya Ismat tayi tana d'ago idanunta ta sauke kan Badriyah
dake chat abunta hankali kwance,ta jinjina kai a hankali tace "habibtiiy lets go
please ina son shan ruwa" amsawa Badriyah tayi a nutse ta mayar da wayar jaka ta
mik'e tace "let's go" tashi Ismat tayi suka fito a hankali suna tafiya,wunin ranar
duka a skul suka yi shi sai 4pm sannan suka dawo gida a mugun gajiye,Mom kam ita
bata dawo daga aiki ba time d'in,haka suka wuce kowa tana fad'in wash,wanka suka
fara yi da yake Ismat dama suna shigowa ita ta fara,lokacin tana fitowa ta wuce
wajen phone d'inta dake ajiye saman bedside,daga ita sai towel dake d'aure
jikinta,his length duka bai wuce cinya ba,ta zauna bakin bed ta kunna network then
ta ajiye wayar ta mik'e,gaban mirror ta wuce ta fara murzawa jikinta lotion,ta yi
applying chapstick ma lips d'inta,as she finished ta wuce closet d'insu,wani
fitinannen crazy jean ta d'auka blue daga cinyarta duk a bud'e kamar an sa abu an
yayyankasa,fresh skin na thighs d'inta da yake fara sol a bayyane kana kallo kamar
ka tab'a jini ya fito,tasa y'ar k'aramar sleeveless pink da ta kama jikinta mai
adon blue d'in flowers ta gaban,gashin kanta kam bata tsaya b'ata lokaci a kansa
ba,tana gama gyarawa tasa clips ta matse shi,ta fesa turarukanta masu sanyin
dad'i,a hankali ta fara takowa wajen data ajiye phone d'inta,tana d'auka ta wuce a
nutse tace "habibtiiy ki same ni parlor please" tana fad'a ta wuce ta fita tana
mak'ala earpiece a kunnenta.....




#The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300,VIPs ₦500.

*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*

*1-ACCOUNT DETAILS.*

Acct name-Hauwa Muhammad Usman
Acct number-0060746882
Bank name-Access bank.

*Sai a tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609*

*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*

08165726609

*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*

*3- OTHER WORLD REMITS*

Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone number:08165726609
City:Kano city.

For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.



#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2020.



*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))



*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/NV64fA4cR6

🆓 Pᴀɢᴇ..

»7⃣
7⃣ :#Bᴀsᴋᴇᴛʙᴀʟʟɪɴɢ

Kusan a tare motar Aadil da na Fawad suka shigo compound d'in gidan,but
Aadil ne a gaba then Fawad,yana gama gyara parking ya bud'e motar,a nutse ya juya
d'aukan jakar laptop d'insa da wayoyinsa dake seat d'in mai zaman banza,Fawad ya
k'araso yana yi masa wani irin kallo yace "Ina ka shiga yau baka je office ba?" Sai
da ya gama tattara belongings d'insa tsaf ya d'ago,a hankali kamar ba zai yi magana
ba da farkon yana rufe motar a tak'aice yace "BUK!" Kallonsa Fawad yayi da mamaki a
fuskarsa yace "Me kaje yi can?" Yana gama locking motar ya fara tafiya a nutse ya
furta "Daddy ya sani zuwa na karb'i Aakiiy" Fawad ya fara biyo bayansa yace "When
akayi hakan?" Bai damu da tsayawa ba yana tafiya zuwa hanyar flat d'insu yace "It
was yesterday" Fawad ya gyad'a kai a hankali bai sake cewa komai ba,suna shiga
parlor Aadil ya zube all his belongings saman table ya wuce bedroom,zaunawa Fawad
yayi saman armchair yana zube wayoyinsa shima da car keys d'insa,a hankali kuma sai
yayi relaxing kansa saman armchair yana mik'a because ya yi mugun gajiya,shi kad'ai
yaje hospital yau duk wasu ayyuka da meetings kuma da suka taso shi ya jagoranta
tunda baiga Aadil d'in bama bare suyi 50².

Almost 35 minutes da shigar Aadil bedroom ya fito sanye da bathrobe bak'i
wanda yayi masifar k'ara fito da hasken fatarsa ya sake bayyana shi matsayin
kyakykyawa ajin farko,cikin takunsa na zaratan maza mai tattare da nutsuwa yana
k'arasowa bai kalli inda Fawad yake ba ya d'auki d'aya daga cikin wayoyinsa ya fara
making call,in less than 3 minutes aka d'auka,idanunsa a lumshe yana matsa forehead
d'insa da hannun hagunsa,cikin wani cool voice ya furta "please help and make some
coffee,ki kawo yanzun" d'an jim yayi then ya cire wayar daga kunnensa ya ajiye,ya
juya ya koma bedroom,lokacin da yake fitowa bayan ya shirya cikin k'ananun
kaya,polo t-shirt ne sanye a jikinsa da trouser white sai d'an adon bak'i kad'an a
jiki da aka yi rubutu,sumar kansa gwanin sha'awa ya sha gyara kamar ba'a saka masa
ruwa,bai gama zaunawa ba aka yi knocking door,a hankali yace "Come in" turo k'ofar
akayi a hankali da wani siririn murya aka furta "Assalamu alaikum" ya amsa bai damu
ya kalli gurin ba,farar kyakykyawar k'afarta ta fara saukewa cikin parlor'n then a
hankali ta shigo tana d'an waigawa ganin bata ga mutum ba,kyakykyawar matashiya ce
wacce duka a shekaru da wuya ta k'arasa su Ismat sai wara manyan idanunta take
yi,tasowa yayi daga cikin chair da ya nutse ganin bata k'araso ba a hankali yace
"Ba ni nan" saurin kallon direction d'insa da taji maganarsa tayi sai kuma tayi
murmushi ta fara takowa hannunta rik'e da medium tray na silver,samansa da flask da
cups biyu because ta san yana wahala ace shi kad'ai ne,kamar yadda tayi tunani kuwa
ta gansu taren dama ta sani yadda suke kamar twins kullum suna manne da juna,tun
yarintarsu ma da Mami take bada labari d'aya baya rabuwa da d'aya shi yasa komai
nasu tare suke yinsa,yanzun ne da girma ya fara zuwa aka fara samun wasu changes
suka fara intervene tsakaninsu,saman table ta ajiye a hankali tace "Masa'al khair
Akhiiy" yana lumshe idanunsa ya furta "Kaiifak?" Da yar siriruwar maganarta tace
"Alhamdulillah" ya sauke numfashi kad'an yana d'aukan cup,da sauri ta d'auka tace
"let me help",ajiyewa yayi ya koma baya,ta matso a hankali ta d'auki cup d'in ta
sunkuya tana zubawa,Fawad ya bud'e idanunsa yana tashi zaune,da sauri ta bud'e
idanu tace "Akhiiy! Dama ba bacci kake ba?" Yayi mata murmushi a hankali yace
"Yeah! Yau nayi stressing kaina da yawa shi yasa" ta yi murmushi kad'an tace "Good
evening" yace "Evening,how are u?" Tace "Alhamdulillah! Ya aiki?" Lumshe ido Aadil
yayi yana karb'ar cup da take mik'o masa a hankali cikin rashin son magana yace "U
can now leave" d'an bud'a ido tayi za tayi magana ya bud'e shanyayyun gray eyes
d'insa ya zuba mata su,da sauri ta tashi tana tura baki ta fara tafiya,tana daf za
ta fita Fawad ya kalleta yana sakin murmushi yace *"NAINA!"* A hankali ta waiwayo
bata amsa ba,yace "Mami ta dawo?" Tace "Ehh! Tana tare da Daddy ma" yace "Alright!"
Juyawa tayi ta fara tafiya Aadil ya bita da kallo har ta fita,a hankali ya d'an
tab'e baki ya fara shan coffee.

Mik'ewa Fawad yayi bayan fitar Naina,yana kallon Aadil da ya had'e rai kamar
wanda aka yiwa wani abu yace "Kai dai halinka sai kai" yana fad'a ya wuce hanyar
bedroom,Aadil dai bai ko kalli inda ya bi ba ya ci gaba da sipping coffee d'insa
har sanda Fawad d'in ya fito cikin k'ananun kaya da suka ainihin amsar jikinsa,yana
k'arasowa ya d'auka cup ya tsiyaya coffee ya koma saman rug ya zauna had'e da mik'e
k'afafunsa and leaning his back against chair da yake zaune kusa da yayi powering
TV,because shi dai bai shirya ma zaman shirun da suke yi ba,even though idan da
sabo ya kamata ace ya jima da sabawan,saboda dama haka suke yi idan su biyu ne
kamar wasu kurame sai dai kowa yayi abunda yake ga zai fishshesa,kasancewar shi
Aadil tun asalinsa dama mutum ne da bai cika son yawan magana ba,idan yana guri ko
baya nan ma ba ganewa ake ba saboda masifaffen miskilancinsa,matuk'ar kaga yana
magana kuma tabbatar shi da Mami ne,tsayin rayuwarsa da ita kad'ai ne yake iya
dogon hira,a bayanta kuwa har yanzun ba'a samu na biyu ba,duk adadin shak'uwarsa da
Fawad ba sosai za ka gansa suna magana ba,idan kaga suna dogon magana kuma sai dai
abunda ya shafi company,while shi kuma Fawad tun asalinsa ya kasance mutum mai
yawan magana,idan har ya zo guri dole sai an sanshi,sannan ba shi da wahalar sabawa
da mutane,wannan dalilin yasa lokuta da yawa bai cika son zaman gidan ba tun da
suka kammala PhD d'insu suka dawo Nigeria sai lokaci²,saboda shi a d'abi'unsa ba ya
son zaman shiru,sab'anin da can baya kafin su tafi karatu da komai nasa yake
gidan,since aka yaye su yake hannun Mami,ita ta rainesu tare da Aadil kasancewarsa
d'a agurin k'anwar Proff Junayd Mutallab mahaifin Aadil.

Waigawa yayi inda ya ajiye wayoyinsa ya d'auka,a hankali ya bud'e net ya shiga
dandalin sada zumunta na whatsapp,yana sakin sanyayyan murmushi yaje kan contact
d'inta yayi mata sallama because yau tun safen da ya tafi office bai samu lokacin
kansa ba,da yaga text d'in yayi delivered sai ya sake yin murmushinsa mai kyau,ya
san tana kusa baza'a jima ba zai ga ta yi replying,da aka jima kad'an ya ji ta
shiru,here ya fara tunanin kiranta yaji,as soon as kiran wayar ya shiga,a time d'in
Ismat ta kammala shirinta kenan ta fito daga bedroom,tana jin ring d'in da wayar
yake tayi murmushi because ta san waye zai kirata a irin lokacin,sai da wayar ya
d'an jima yana ring har kamar zai yanke then tayi answering call d'in,da yake akwai
earpiece a kunnenta tana ci gaba da tafiya tayi masa sallama,Fawad dake zaune ya
mayar da kansa ya kwantar saman kujera ya lumshe idanunsa,jin sanyayyar maganarta a
kunnensa yasa he didn't know when ya sauke ajiyar zuciya,tayi murmushi kad'an tace
"Good evening" a hankali da wani irin kasalar dake cin jikinsa ya furta "Evening
dear,how are u?" Tace "Alhamdulillah,ya aiki?" Yace "Aiki Alhamdulillah,ya skul
fa?" Tayi ajiyar zuciya kad'an tace "Mun baro shi" amsar ta ne ya bashi dariya yace
"Mmm! Sai gobe kenan?" Ta kad'a kai first then tace "Ehh!" Ya kad'a kai a hankali
yace "Maa sha Allah,Allah kaimu" tace "Ameen" shiru suka yi dukansu daga
haka,lokacin ta gama sakkowa kenan daga stairs ta hango Mom tana shigowa parlor da
sauri tace "Mmm! We will talk later please" idanunsa a lumshe har lokacin yace
"Kina wani abu ne yanzun?" Da sauri tace "Ehh!" Yace "Alright! Ya za'ayi na sani
idan kin gama?" Saurin katsesa tayi tace "I'll call" yayi murmushi yace "Alright!
Bye" tayi sauri tace "Bye!" Sai ta fara yanke wayar,da d'an gudunta ta nufi Mom
dake shigowa tana fad'in "Oyoyo Mom!" Mom da bata ganta ba sai dai maganarta da
taji ta waiwayo a hankali tana sakin murmushi tace "Sweetheart! Kun dawo?" Ta kad'a
kai tana sakin murmushi ta rungume Mom tace "Sannu da dawowa Mom,ya aiki?" Mom da
ta bud'a idanu tana kallon y'arta kamar yau ta fara ganin ta saka irin kayan tace
"Waw! U look breathe taken sweetheart!" Dariya Ismat tayi ta karb'i handbag d'in
Mom tace "Thank u Mom" Mom ta rik'e hannun Ismat suka fara tafiya kamar wasu
friends tace "Ina habibtiiy'n ki?" Murmushi kwance saman fuskar Ismat tace "Tana
bedroom" mom tace "Ba za ta fito ba?" Da sauri tace "Tana shiryawa ne" Mom tace
"Alright!" Dai² lokacin suna shiga bedroom d'in Mom,Ismat ta wuce wajen da take
ajiye bags ta sak'ale,ta dawo ta wuce bathroom tana b'ata rai take cewa "Mom! Kuma
kinga ba mu yi test d'in ba" Mom dake rage kayan jikinta tace "Why?" Ismat ta bud'a
hannu tace "Wai Dr ba ya nan,shi ne sai ya turo k'aninsa,but Mom kin san wani abu
kuma?" Mom dake jira Ismat ta gama had'a mata ruwan wanka tace "Sai kin fad'a" ta
juyo tana kallon door d'in duk da ba ta hango Mom da murmushi a fuskarta tace
"Allah duka y'an gidansu sunji dad'i Mom,suna da ilimi sosai both boko da
addini,idan kinga k'aninsa kou sai kinyi mamaki,duka ba zai wuce sa'an Bhai ba
fa,amma kuma shima Dr ne,sannan ya masifar iya lecture,ni dai Mom kinga ba na son
zama da yawa,but yau duk 3 hours da ya share yana lecture gani nayi sun tafi kamar
ma fa bai fi 30 minutes da shigowa ba,wai sai cewa yayi lokaci yayi sai wani
had'uwar" Mom dake sakin murmushi tana sauraren maganar da Ismat take yi tace
"Lallai sweetheart da alama yau kinji dad'in lecture d'in Dr" tayi murmushi tana
juyowa za ta fito tace "sure Mom,ko lecture Dr Fadl ban tab'a jin dad'in sa ba
kamar na k'aninsa,ko don yana takuramu saboda ya sanmu ne ohoo! Yayi ta tambayar
mutane kamar mu kad'ai yake koyarwa,ni dai dama zan fad'i ma Yaa Jawahir tace yayi
hak'uri ya daina tambayata,duk ya tambaye ni Allah rikicewa nake na kasa amsashi
yadda ya dace" Mom dai dariya tayi tace "Idan da rabon ya saki lecture wata rana
kuma maga yadda za'ayi" zaro ido tayi tace "Tabbb' Mom ranar ai nutsewa kad'ai ne
bazan yi ba" Murmushi Mom tayi tace "Lallai sweetheart! Bari na fito kou?" Tayi
murmushi tace "Ok Mom" ta wuce wajen kayan da Mom ta ajiye saman bed,d'aukansu tayi
a hankali tana sakin murmushi ta wuce da su laundry,almost 15 minutes Mom ta fito
sanye da bathrobe pink colour gashin kanta nad'e a cikin pink d'in towel,tana
kallon Ismat dake kwance saman bed d'inta ta wuce gefen mirror ta zauna saman stool
bata yi mata magana ba,a hankali ta d'auki hand dryer ta kunna,Ismat ta bud'e
idanunta a hankali ta taso,ta fara tura phone d'inta a cikin pocket ta nufo inda
Mom take,Mom tana kallonta tana murmushi tace "je kiyi kwanciyar ki sweetheart na
san kin gaji yau" murmushi tayi tace "No! Mom kawo nayi miki" kad'a kai Mom ta sake
yi then ta bata dryer d'in,ta san indai Ismat na kusa ba za ta bari tayi da kanta
ba,she always use to help her,matuk'ar ba rashin lafiya take yi ko ba ta kusa
ba,idan ta fito wanka ita take gyara mata gashinta,even ruwan wanka indai tana nan
ba ta bari ta had'a da kanta,sai da ta tabbatar ta gyarawa Mom kyakykywan gashinta
then tayi mata kalba da shi guda d'aya daya sauka ta gefen wuyanta,ita dama Mom
haka take yi idan ta dawo daga aiki ba ta saka ribbon a jikin gashin,Ismat tana
gamawa tayi murmushi tace "Bari na jiraki a parlor Mom" Mom tace "Alright" a
hankali Ismat tace "Sai kin fito" Mom ta shafa gefen fuskarta,Ismat tayi murmushi
then ta juya ta fara tafiya,har ta kusa door Mom tace "Yayanku fa?" Ismat ta d'an
tsaya kad'an tace "Ni dai ban gansa ba" Mom ta kad'a kai tace "Shi kenan" wucewa
Ismat tayi ta fita,Mom ma ta mik'e ta wuce arean closet.

A parlor Ismat ta tarar da Badriyah kwance saman armchair,ta zauna kad'an
kusa da ita Badriyah ta bud'e idanu tana kallonta,a hankali tace "Ina kika je
kuma?" Murmushi Ismat tayi tace "Ina tare da Mom" Badriyah ta tashi zaune tace "Ta
dawo ne?" Ismat ta kad'a mata kai tace "Yes! But yanzun za ta fito ma" komawa
Badriyah tayi ta kwanta had'e da d'ora kanta a thighs d'in Ismat tana lumshe idanu
tace "alright!" Ta ci gaba clicking wayarta dake hannunta. While itama Ismat here
ta fara making call as she promised him idan ta gama za ta kira,kiran yana tafiya
ya katse ya kirata,ta zubawa wayar idanu na wasu seconds tana murmushi then ta
d'auka ta kai kunne,hira sosai sukayi but idan ba wanda yake kula da motsawar
bakinta ba sam ba zai ce ga abunda take yi ba,hatta Badriyah dake kwance saman
k'afafunta da yake hankalinta na kan phone d'inta sam bata ma san me Ismat d'in
take yi ba.
In just a short period of time,wani irin shak'uwa mai k'arfin gaske ya shigo
tsakanin Ismat da Fawad,even though basu tab'a sanin juna ba four about 3 weeks da
fara alak'arsu,hasalima basu tab'a ko da ganin pic d'in juna ba,since ya tambaya
tace ba ta tura pic bai sake tambayarta ba,but he always use his chance suyi hira
ya ga tana farin ciki,ko wane lokaci abunda yake buri shi ne yasa ta cikin
nishad'i,yayin da zuwa lokacin ita kanta a nata b'angaren ya kasance idan ma bai
kirata ba ita za ta kira

8 / 70