Chapter 54 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   54 / 70

159K to 162K   out of 210K words

kawowa yana son yara sosai ba,sai da ta ga yadda yake mata rawar k'afa
akan cikin. Tafiya yake cikin mota a hanyarsa na dawowa gida daga gurin aiki,sanda
ya k'araso line ya tsaya dai² get yace "sorry dear.. I just call to tell u bazan
dawo gida yanzu ba" Badriyah dake parlor a zaune tana numfasawa da kyar tace "me
zai hanaka dawowa yanzu?" Yayi murmushi cikin zolaya yace "aiki ya rik'e ni,so kiyi
hak'uri ko zan dawo think sai zuwa dare" ajiyar numfashi tayi tace "alright! Allah
dawo min da kai lafiya" yayi murmushi sanda yaji ta ce haka da wani sanyayyar murya
yace "baki yi fushi ba?" Tace "fushin me zanyi tunda aiki kace ya rik'e ka?" Yayi
murmushi a hankali yayi horn,get keeper d'in gidan nasa ya bud'e masa,ya shigo
compound yana k'ok'arin yin parking yace "da wasa nake miki ga ni a compound,yanzu
zan shigo" tace "da gaske?" Yace "fito ki gani sai ki tabbatar" murmushi tayi ta
mik'e da kyar ta nufi windows,ta d'aga curtains d'in gurin tana fad'in "ka san.."
Bata k'arasa fad'in abunda ke bakinta ba idanunta suka gano mata sojoji suna
shigowa gidan da gudu,cikin rud'ewa tace "my appeal me yake faruwa naga sojoji suna
shigowa?" Yace "I don't know.. But ina zuwa plaese" ya katse wayar ya juya yana
kallon sojojin da suka zagayesa yace "what happened? Mene ne yasa za ku shigo min
gida ba tare da neman izini ba?" Sojan dake tsaye gabansa yace "ka biyomu muje"
Fawad yace "ina zan biku? Mene ne ya had'a ni da ku da zan biku?" Sojan yace "idan
munje can za ka sani" Badriyah ta fito da sauri,hankalinta ba k'aramin tashi yayi
ba da ta zo gurin da suke,a tsorace ta dunga kallon sojojin dake k'ok'arin rik'esa
suna son fita da shi daga gidan,cikin wani irin firgici Badriyah tana kallonsa take
fad'in "my appeal me yake faruwa wai? Me ya had'a ka da su?" Girgiza mata kai yayi
yace "ban sani ba,nima ganin su kawai nayi" ta juya da sauri tana kallon sojan dake
bada umarni tace "Malam me yayi muku kuke son tafiya da shi?" Sojan ya bita da
kallo yace "Hjy umarnin kamashi kawai aka bamu,bamu san me yayi ba,but idan kuna
neman k'arin bayani za ku iya binmu.." A rikice Badriyah tace "zuwa ina?" Yace
"koma ina ne idan munje za ku gani.." Yana fad'in haka ya juya ya kalli yaransa
yace "ku fita da shi.." Tashin hankali wanda ba'a sa masa rana,Badriyah tana ji
ance a tafi da shi ta kurma ihu ta shiga gaba ta tsaya fad'i take "wallahi babu
inda za ku tafi min da miji,me yayi muku da za ku kamasa?" Sojan dake mata wani
kallo yace "Hjy za ki hana mu tafiya da shi ne?" Cikin kuka Badriyah tace "laifin
me yayi muku da za kuce sai kun tafi da shi? Wallahi bazai biku ba" tasa hannu tana
kakkare shi,murmushi sojan yayi yace "za ki hanamu yin aikin mu kenan?" Ta girgiza
kai tace "ni bazan hana ku aikin ku ba,amma me ya muku da za kuce sai kun tafi da
shi?" Shi dai Fawad yana tsaye yana kallon ikon Allah mamaki ya hanasa magana,ana
haka sai ga Seeyama itama cikin tashin hankali ta fito,rabon za ta san abunda yake
faruwa lokacin tana kwance bedroom d'inta ta tashi ta nufi gurin window za ta gyara
curtain d'in gurin da ya d'age tana tsaye gurin ta hango sojoji,hankali tashe ta
k'araso tana musu kallon tsoro tace "what happened? Yaa Fawad me ya kawo sojoji
gidan mu?" Murmushi yayi yana d'aga shoulders yace "ni kaina har yanzu ban san me
ya kawo su ba" Seeyama ta kalli Badriyah dake kuka kamar ranta zai fita,ta juya
jikinta sai kyarma yake ta kalli sojan tace "Yallab'ai me yayi muku?" Sojan yace
"muma ba'a sanar da mu laifin da yayi ba so an bamu details d'insa ne kawai akace
mu kamasa duk inda muka gansa" yana gama fad'ar haka ya kalli Fawad yace "Malam
kada ka b'atawa kanka da mu lokaci,kada kuma kace za kayi taurin kai,kawai ka
biyomu mu tafi" Fawad ya kalleshi yayi murmushi,ya juya ya kalli Badriyah da
Seeyama dake kuka yace "don't mind i'll be back.." Yana fad'an haka ya kalli sojan
yace "muje" a gaba suka saka shi,suna fita daga gidan Badriyah ta fasa k'ara ta
fad'i k'asa.....




#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.


Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.



#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




_Nobody can be more powerful than Almighty Allah himself. If u trust in
Allah,nobody can be more powerful than u.._
5⃣0⃣




Da gudu Seeyama tayi kanta,cikin kururuwa take kiranta hawaye sai zarya
suke akan fuskarta,Badriyah kam bata ma san ina kanta yake ba tunda ta
fad'i,Seeyama ta durk'usa kusa da kanta tana kuka tana jijjigata cikin tsananin
firgici,get keeper d'insu da ya jiyo ihunta bayan sojojin sun tafi da Fawad akan
idanunsa ya shigo da gudu,sanda ya zo shi ya kula da jinin dake bin jikin
Badriyah,hankalisa a tashe yace "Hjy fa jini ke fita daga jikinta" Seeyama ta d'ago
idanunta da hawaye ta dunga gyad'a masa kai ta kasa magana sai kuka take,juyawa
yayi kai tsaye ya nufi cikin gidan ya kira maids d'insu,da taimakonsu suka saka
Badriyah a mota amma still Seeyama ta kasa shiga tayi driven,sai k'ok'arin kiran
Madeeha da tayi a waya,sanda Madeeha ta d'auka tayi sallama,cikin kuka Seeyama tace
"dear! Please.." Kafin ta k'arasa Madeeha ta tari numfashinta tace "me ya faru naji
muryar ki haka?" Seeyama tace "Yaa Fawad ne" bata k'arasa ba Madeeha tayi saurin
katseta "me ya samesa?" Cikin kuka Seeyama tace "sojoji ne suka zo suka tafi da
shi,Badriyah kuma ta fad'i yanzun jini ya b'alle mata,i don't really know how to
handle all this.. Please ku zo yanzu,i need ur help,ku zo da sauri dan Allah,muna
cikin tashin hankali" tashin hankali sosai Madeeha ta shiga,jikinta ya dunga rawa
tun bata gama sauraren abunda Seeyama ke cewa ba hawaye har sun fara sauka kan
fuskarta,a gaggauce tace "alright! Ga mu nan zuwa" ta katse wayar tana maimaita
fad'in "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Allahumma ajirna fiiy musibatin
wa'aklufna khairan minha." Kallonta Naina tayi saurin yi tace "me ya faru na ga
hankalinki ya tashi?" Cikin kuka tana saka slippers a k'afarta tace "tashi mu
tafi!" Naina dake mata wani kallo tace "wai me ya faru? Waye bai da lafiya? Ina
kuma za muje?" Madeeha ta girgiza mata kai cikin kuka ta fad'a mata abunda Seeyama
ta sanar mata,hankalin Naina a tashe da sauri ta sauka daga kan gadon tace "muje"
ko mayafi babu wadda tayi tunanin d'auka cikinsu suka fita da gudu²,Naina ta
k'arasa bedroom d'in Mami tana nemanta,sanda ta shiga bata ganta ba ta fito tana
kwala kiran "Mami!²" cikin firgici,Mami dake parlor tana waya da Jawahir ta jiyo
irin kiran da Naina take mata tace "ya akayi ga ni a parlor" da gudu Naina ta shigo
fuskarta duk ya b'aci da hawaye tana kuka take sanarwa Mami abunda yake faruwa,ta
nan Jawahir ta ji duk abunda yake faruwa cikin tashin hankali itama ta fara kiran
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Mami cikin tashin hankali ko katse wayar da
suke yi bata yi ba tace "maza kuyi sauri kuje yanzun zan yi waya da Hjy Haajar za
mu zo mu same ku.." Gyad'a kai Naina tayi da sauri ta juya suka fita,ko barin gidan
su Naina basu yi ba Mami ta kira Mom d'in Fawad tace ta shirya za suje hospital
yanzu,jikin Hjy Haajar ya gama ba ta ba lafiya ba akwai wani abu dake kan faruwa,ta
fara tambayar Mami,Mami tace "Hjy yanzu ba lokacin tambaya bane,ki shirya dai yanzu
za muzo da driver" tana fad'an haka bata jira ba ta katse wayar ta fita itama while
tana kiran Daddy. Cikin k'ank'anin lokaci da faruwar al'amarin tuni labarin ya
zagaya both family'n su Fawad da na Badriyah,da yake kuma Proff Junayd da Daddy'n
Ismat duk suna da alak'a da governor nan da nan maganar ya baza gari ana ta neman
inda aka tafi da Fawad,su Mami da Mom d'in Fawad da tuni suka k'arasa AKTH a nan
suka tarar da su Naina,tsakanin Ismat/Jawahir da su Seeyama duka dake tsaye gaban
theater room tin bayan da aka shiga da Badriyah baza ka tab'a gane wanda yafi wani
shiga tashin hankali ba sannan baza ka tab'a gane wanda yafi wani juriya ba,kuka
kawai suke yi gaba d'ayansu an rasa mai bawa wani hak'uri,da yake tun kafin su zo
aka shigar da Badriyah theater nan suka tsaya cirko²,ita kanta Mami dan tana da
k'arfin zuciya ne har take rarrashin Hjy Haajar,tun suna hanya da ta sanar mata
abunda yake faruwa take kuka har suka shigo hospital d'in,a nan ne ma Mami taji
labarin Mom ce da wasu likitocin akan Badriyar. Bayan wasu awanni kowa ka kalli
fuskarsa tsakaninsu da suke gurin banda zallan tashin hankali babu abunda za ka
gani,su Daddy kuwa zuwa Dr Fadl,Aadil banda zaryan barracks da waya babu abunda
suke yi,daga air force base zuwa vockabo barrack basu san sau nawa suka je ba suna
binciken ko an kai Fawad d'in can,duk inda suka sani sun je dan bincika asalin inda
aka kaisa sai dai gaba d'aya babu labarin yana cikin Kano ma,abu tun yamma har aka
kira maghreb shiru zuwa lokacin kaf family babu wanda bai girgiza ba sanda suka ji
labarin cewa ba'a san takamaiman inda aka tafi da shi ba,hospital kuwa da gaba
d'aya suka tare a can kamar dan su aka bud'esa sun had'u gaba d'ayansu,Badriyah dai
har lokacin bata san inda kanta yake ba,bayan an samu nasarar tsayar da jinin da
take zubarwa aka yi mata aiki aka cire mata d'anta namiji kafin aka fito da ita aka
wuce da ita d'akin hutu,sanda Mom ta fito tana share zufa Ismat ta k'arasa gurinta
ta fad'a jikinta tana kuka,securely Mom ta rik'eta tana shafa kanta tace "be quite
please sweetheart! Ba kuka za kiyi musu ba,kiyi musu addu'ah kinji,in sha Allah
komai zai yi sauk'i" kai ta dunga gyad'awa Mom ta kasa yin shiru,Mom ta zaunar da
ita kan kujera itama ta zauna tana sauke numfashi,sanda ta kalli Mami tace "Mr's
NADIA ya ake ciki game da maganar inda aka tafi da yaron?" Mami ta girgiza kai
cikin rashin tabbas tace "Dr case d'in nan yana bani tsoro,kaf garin nan ace an
rasa inda suka kaishi,yanzun haka fa maganar da Daddy yake sanar min wai ba'a san
su waye ma suka d'auke shi ba" cike da jimami Mom ta jinjina kai ta ja numfashi
tace "idan ba sojojin da akace sun d'auke sa ba,su waye ne za su tafi da shi? Ina
kuma za su kaisa?" Mami tace ''abun tambayar kenan" Mom tace "bari muji me Barraq
zai ce akan maganar" Mami ta gyad'a kai tayi shiru tana jimamin abun a ranta,kiran
Barraq Mom tayi sanda ya d'auka tace "Barraq ya ake ciki?" Barraq yace "Mom gaskiya
case d'in nan ban san ta ina zan fara sanar miki ba" Mom tace "ina saurarenka me
yake faruwa?" Yaja numfashi ya sauke yace "yanzun dai mun samu labarin inda yake"
hamdala Mom tayi wanda ya janyo hankalin sauran mutanen dake gurin gaba d'aya suka
dawo sauraren abunda take cewa,Barraq yace "wani friend d'ina ya kira ni daga abuja
yanzu yake sanar min can sojojin da suka kamashi suka tafi da shi" Mom tace "abuja
kuma?" Yace "sure Mom" numfashi ta sauke kafin tayi magana yace "muna airport yanzu
tare da su Daddy za mu tafi,duk abunda ake ciki zan sanar miki" Mom ta gyad'a kai
tace "shi kenan Allah sauke ku lafiya" ya amsa "ameen" suna ajiye wayar Mom ta fara
yiwa Mami bayanin yadda suka yi da Barraq,Hjy Haajar dai har sannan bata yi shiru
ba kuka kawai take yi. Cikin k'ank'anin lokaci su Daddy suka sauka abuja tare da
lawyers d'insu,sanda suka isa barrack d'in da aka kai Fawad suka b'ukaci
ganinsa,nan suka ga bonu domin kuwa gaba d'aya aka hana su ganinsa,hatta lawyers
d'in da suka tafi da su matsayin wad'anda za su tsaya masa suma ba'a barsu sun
ganshi ba,sai da Daddy suka yi waya da governor yake sanar masa ko damar ganinsa ma
basu samu ba,a nan yace kada su damu bari yayi waya yanzun,cikin mintuna da gama
wayarsu aka bawa su Daddy damar zuwa su gansa,da yake Barraq ya san wasu cikin
sojojin gurin kuma it was there aka barsu duka suka shiga ganinsa,sanda yayi magana
da wasu cikin su kuma here ya fara jiyo asalin kan case d'in,Daddy suna shiga inda
aka ajiye Fawad,sanda suka ganshi babu wani abu da aka masa kawai dai yana
tsare,Aadil ya bishi da kallo lokacin da Daddy yake tambayarsa "laifin me ka aikata
Fawad haka? Aka tada mana hankali?" Fawad da zuwa lokacin ya gama saddak'arwa ya
girgiza kai yace "Daddy nima kaina har yanzu abunda ban sani ba kenan,ni ban yiwa
kowa wani abu ba" yayansa Khulayd ne yace "idan ba gagarumin laifi ka aikata ba me
yasa mutanen nan za su hana mu ganinka? Ka fad'a mana abunda kayi aka kama ka"
kallon yayan nasa yayi yace "me yasa zan b'oye muku idan har na aikata wani laifi?"
Barraq da ya shigo lokacin yana masa wani kallo yace "meye tsakaninka da Major
Abdulwahab?" Fawad ya kalleshi yace "waye shi? Ban sanshi ba" Barraq yace "baka
sanshi ba? Idan baka sanshi ba ya akayi shi ya sanka?" Fawad ya runtse idanu yace
"me yasa zan yi muku k'arya wai? Idan na sanshi mene ne ribata da zan b'oye muku?
Ban sanshi ba,ban san waye shi ba" Barraq yace "maganar da akace har da kai aka
damfaresa shima baka sanshi ba?" Ya girgiza kai cikin kad'uwa yace "damfara? Ni
kuma aka ce na damfaresa?" Daddy da Abbuh mahaifin Fawad cikin firgici suka
maimaita "damfara?" Barraq ya d'ago yana kallonsu yace "wannan shi ne maganar da
naji,kuma shi ne gaskiyar abunda ya faru har yasa suka kawosa nan" cikin firgici
Fawad yace "me yasa zansa kaina cikin irin wannan case d'in? Ban tab'a damfarar
kowa ba" Daddy ya jinjina kai cikin kad'uwa yace "lallai case d'in babba ne" Barraq
yace "koma dai waye ya aikata laifin,photon ka suka nuna min yanzu,saboda haka idan
ka san wani abu akai ka fito ka sanar mana,saboda mu san ta inda za mu b'illowa
lamarin" girgiza kai Fawad yayi har lokacin ya kasa yarda da abunda ke faruwa da
shi yace "ku yarda da ni ban san komai akan maganar nan ba" Barraq yace "shi kenan
koma dai waye yayi tunda ka ce ba kai bane,zuwa da safe idan Major ya k'araso za mu
sani.." Sanda ya juya ya kalli Aadil yace "think ya kamata mu nemi inda za mu kwana
kafin da safen mu san abun yi" Aadil ya gyad'a masa kai,gaba d'aya shi al'amarin ma
ya d'aure masa kai ya kasa magana,tare suka fita da Barraq suka kama musu d'akuna a
hotel mafi kusa da barrack d'in. Around 3:00am Badriyah ta farko,tsananin azabar
ciwo da abubuwan da suka faru da suka dunga dawo mata kamar yanzun suke faruwa yasa
ta fashewa da kuka,Ismat da ta kafe tak'i tafiya gida babu jimawa bacci ya d'auketa
kukan da Badriyah take yi yasa ta farkawa ta tashi a hankali ta kunna haske,sanda
ta matsa jikin gadon ta rik'o hannun Badriyah tace "sannu.. Bari na kira Mom" ta
juya da sauri ta fita,babu jimawa suka dawo tare da Mom,suna
shigowa Mom taga Badriyah na kuka,ta b'ata rai tace "ke yanzu daga tashin ki baki
ga situation da kike ciki ba? Shi ne za ki tada hankalinki muma ki tada mana namu?
Idan baki sani ba bari na fad'a miki,aiki aka miki aka cire abunda ke cikin ki,d'an
k'aramin abu yana iya janyowa a samu matsala,idan haka kike fata to ki ci gaba da
kukan,idan kuma kin damu da lafiyarki wanda mu muke buk'ata to ya kamata kiyi shiru
ki barmu muji da abu d'aya,ki godewa Allah ma da zuwa yanzun aka san inda aka
kaishi,sai dai fatan Allah ya fitar da shi lafiya daga hannunsu.." D'ago idanuwanta
da suka sauya launi Badriyah tayi ta kalli Mom,Mom ta shafa kanta cikin lallashi
tace "ki daina kuka haka nan,in sha Allah komai zai zo da sauk'i,babu abunda zai
sameshi" ajiyar zuciya Badriyah tayi amma har lokacin hawaye basu daina zubowa daga
idanunta ba sai dai ta daina kukan,Mom ta fara share mata hawayen ta juya tana
kallon Ismat da tayi fuskar kuka tace "had'a min tea sweetheart ki bani" jikin
Ismat a sanyaye ta gyad'a kai ta juya ta fara aiwatar da abunda Mom tasa ta,sanda
ta had'a thick tea ta mik'awa Mom,ta karb'a a hankali ta daga Badriyah ta dunga
bata tana fad'a mata maganganu masu sanyi har Allah yasa ta sha da d'an yawa kafin
ta ce ya isheta,Mom ta ajiye cup d'in tana kallonta tace "baki tambayi Baby ba ko
bakya buk'atar ganinsa?" Saurin juyowa tayi ta kalli Mom,kamar za tayi magana sai
kuma ta fasa wasu hawayen suna sake zubowa daga idanunta,Mom ta girgiza mata kai
tace "na ce ki daina kuka nan haka kou? Tunda Allah ya sa babu abunda suka masa,ko
iya haka ya isa mu godewa Allah,in sha Allah zuwa gobe suma za su dawo.." Cikin
daren haka Mom da Ismat suka zauna da Badriyah,duk da Mom ta mata nasiha sosai akan
yawan kukan da take yi amma idan abun ya ciyota ta tuna yadda komai ya faru sai
taji zuciyarta ya karye ta kasa daurewa,a hakan kuma addu'ar da Mom take cewa tayi
masa bata fasa ba,wasa² suna nan a zaune suna bata hak'uri aka fara kiran sallar
asubah,Mom tace Ismat taje office d'inta tayi sallah a can ita za tayi a nan,Ismat
ta amsa ta fita,sanda ta shiga office d'in Mom ta bud'e toilet ta shiga ta d'auro
alwala,bayan ta fito ta shimfid'a pray mat ta kabbara sallah,sanda ta idar ta zauna
tayi addu'o'i a nan bacci ya d'auketa. Da safe tun kafin ace Badriyah ta sake tashi
daga bacci Mama da Jawahir ne suka fara zuwa,babu jimawa Mami da Mom d'in Fawad
suma suka iso da kayan karin kumallo,a nan suka had'u aka fara jajantawa juna
abunda ya faru,wajen 8am sai ga su Seeyama tare da su Naina suma sun iso,a nan ne
Mama tace da Mom ya kamata taje gida ta huta,tun jiya take abu d'aya lokacin da ya
kamata ace ta huta kuma a nan d'in ne aka samu matsalar da ake kan fuskanta,Mom
tayi murmushi tace "Haba Hjy Layla ya kike maganar naje na huta? Wane hutu kuma a
gurina ni da yanzun haka na shiga lokacin aiki?" Mami ta kallesu tana jinjina kai
tace "gaskiya Dr kuna k'ok'ari kuyi ta aiki wani lokacin ko hutu babu?" Mom tayi
murmushi tace "ya za'ayi haka namu aikin yake" Mom d'in Fawad tace "ai ku kam sai
dai Allah ya biya ku,amma dan wani salary idan da shi mutum ya dogara ma babu
abunda zai yi muku.." Murmushi still Mom tayi sai dai bata ce komai ba,sanda Mami
ta waiga ta kalli occupants d'in dake cikin d'akin tana squeezing fuskarta kamar
tana neman wani abu tace "ina daughter na ta

54 / 70