Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
yayi yace "sai an
jima?" Ta kad'a kai kamar tana gabansa tace "Allah ya kaimu" yace "ayi karatu
lafiya" tayi murmushi tace "thanks" ya lumshe idanunsa a hankali yana relaxing
kansa a saman bed yace "alright! Bye" tace "bye" sai suka ajiye wayar tare,juyi ta
sake yi ta mirgina,tana sakin murmushi aka bud'e k'ofa da k'arfi har sai da ta
tsorata ta juyo,idanunta suka sauka kan Badriyah da ta shigo tana hawaye,cikin
tsoro Ismat tayi sauri ta tashi a firgice ta rik'ota tana kallonta hankalinta duk
ya tashi ta fara magana "what happened habibtiiy? What's wrong with u? Me aka miki
please?" Kuka Badriyah ta fashe da ta zauna saman bed,da sauri Ismat tayi kneeling
a gabanta idanunta sunyi rau² kamar za ta fashe da kuka duk ta birkice tace "please
talk to me dear,waye ya tab'a ki? Ke da waye please?" Badriyah ta kasa magana sai
kuka take,jikin Ismat ya fara tsuma da sauri ta d'auki wayarta hannunta banda rawa
babu abunda yake yi ta fara kiran line Jawahir,mintuna biyu Jawahir ta d'auka da
fad'in "Hello dear!" A firgice Ismat ta furta "Yaa Jawahir me aka ma habibtiiy take
kuka?" Jawahir ta fara dariya tace "Me kuwa za ayi mata? Kema kin san halin
mutuniyar ki ai" hurriedly Ismat tace "please Yaa Jawahir ki sanar min abunda
akayi,kinga fa kuka take tunda ta shigo" bud'a hannu Jawahir tayi tace "tou ni dai
ban san me aka yi mata ba,amma ki tambayi Yaa Barraq ko da shi ne suka samu
matsala" Ismat ta zaro ido a tsorace tace "tare suka zo?" Jawahir tace "Ehhh!"
Ismat tace "Alright! Sai an jima" Jawahir bata gama amsawa ba Ismat ta katse
kiran,Jawahir tayi murmushi ta bi wayar da kallo kafin ta ajiye ta fita,juyowa
Ismat tayi tana kallon Badriyah da har lokacin ta k'i yin shiru tace "please
habibtiiy wani abu ya had'a ki da Bhai?" Banza Badriyah ta mata kamar bata ji ta
ba,ta sake maimaitawa for da second time tana tunanin Badriyah za ta amsa mata,but
sai taga ta k'i cewa komai,hankalin Ismat duk ya dad'a tashi,sai kallon Badriyah
take kamar za tayi kuka tace "shi kenan tunda ba za ki fad'a ba,amma kin san idan
kin ci gaba da kuka kanki zai yi ciwo kou?" Ta fad'a tana k'ok'arin sharewa
Badriyah fuska,still Badriyah bata kalleta ba tana ci gaba da sauke hawaye kuma ta
k'i cewa komai,kasa samun nutsuwa Ismat tayi a hankali ta sake d'aukan wayarta ta
fara kiran line Bhai d'inta,dai² lokacin shigowarsa kenan cikin gidan ya d'an tsaya
compound wajen mai wankin sa da ya kawo masa kaya,yana jin wayar yana ring ya wuce
bai d'auka ba sai da ya kai kayan bedroom ya ajiye saman resting chair,ya fito da
wayar daga pocket yana dubawa yaga Kid sis ce ta kira,a hankali yayi calling nata
back,cikin azama Ismat dake juya waya a hannunta tun d'azun da ta kira taji bai
d'auka ba tayi answering call d'in da fad'in "Bhai me ka yiwa habibtiiy take kuka
please?" Had'e rai yayi yace "ita tace miki na yi mata wani abu?" Ta kad'a kai a
hankali kamar tana gabansa tace "No! I'm just asking" yace "Ban sani ba,dama kiran
da kike yi kenan?" Ta marairaice fuska tace "Bhai ka ga fa tunda ta shigo take
kuka,kuma har yanzun bata bari ba" kafin ta sake magana ya katse kiran yana jan
tsaki,a fili ya furta "shirme",waistband ya rik'e yana tsaye a inda yake sai ya
rasa me zai yi? Because kiran wayar ya mantar da shi abunda yake niyyar yi,a
hankali ya juya ya fara k'arewa room d'insan kallo,ya sake yin tsaki sai kuma ya
juya ya nufi hanyar fita,da sassarfa ya dunga tsallake staircases yana zuwa
corridor ya tsaya k'ofar bedroom d'insu yayi knocking,Ismat dake tsugune gaban
Badriyah kamar mai neman alfarma tace "Yes!" Barraq ya turo k'ofar yana had'e rai
ya shigo da sallama,Ismat kad'ai ta amsa tana kallonsa kamar za ta fashe da kuka,ya
k'araso yana kallon Badriyah dake share hawaye a dake yace "Me aka yi miki kike ma
mutane kuka? Ko dan ban zane ki ba?" Saurin d'agowa tayi sai kuma ta sake fashewa
da kuka "Hey! Hey!!" Ya fad'a da wani irin murya a fusace yana nufarta,jikin
Badriyah ya fara rawa saboda ta tsorata ta fara ja baya,sai da ta kai k'arshen bed
sannan ta fara magana da muryar kuka "Ni dan Allah ka rabu da ni,kawai sai ayi min
abu kuma ace bazan ji haushi ba?" Wani kallo ya fara watsa mata cikin hayaniya yace
"uban me aka miki?" Ta sake fashewa da kuka tace "tou ba a gabanka tayi min ba?"
Matsowa ya fara yi gashin jikinsa sun fara mik'ewa yana kallonta yace "Idan kika
sake bakinki ya sake furta wani magana a nan gurin sai na b'arar miki da hak'ora,ke
sha³r ina ne? Jawahir ba gaba take da ke ba? Ohoo! Da kika ga ban zane ki gaban
Mama ba,ban yi miki maganar abunda kika yi ba shi ne kika samu bakin magana yanzun
wai wani anyi miki abu baza ki nuna fushi ba,tou nuna fushin naki mu ga!" Ya k'are
maganar cikin tsawa,saurin rik'e arm d'insa Ismat tayi cikin rawar murya ta furta
"I'm sorry bhai,please forgive her" sai tayi saurin had'e hannayenta tana rok'onsa
hawaye suna sauka kan fuskarta,saurin kallonta yayi yana making snapped muryarsa
cike da warning yace "Ki rufe min bakinki a nan wajen kema,ko na ce kiyi magana?"
Da sauri ta kad'a kai,ya juya a fusace yana kallon Badriyah "saboda kin iya rashin
kunya shi yasa ba kya ganin kowa da mutunci,kowa kin maida shi sa'anki,yaushe kika
zama haka? Nawa shekarunki suke duka?" Saurin d'agowa tayi tana tura baki,a fusace
ya kad'a mata hannu cike da gargad'i ya furta "mind u! Idan kika bari naji wani
kalma ya fito daga bakinki za kisha mamaki na yanzun" tura baki ta sake yi ta fara
k'unk'uni k'asa² sam bata tab'a zaton zai ji ba tace "tou ba ita ta tsokane ni ba?"
Gigitaccen marin da ya falla mata lokacin yasa bata tantance inda take ba sai da ta
d'auki wasu sa'o'i sannan ta dawo dai²,cikin masifa Barraq yana nuna ta with his
index finger ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba,sai da yayi mata tas² then ya
juya a fusace zai fita,a guje Ismat ta bishi tana ba shi hak'uri bai kulata ba har
suka sakko k'asa lokacin Mom tana zaune parlor tana magana a waya,tunda suka fara
tahowa take kallon su har suka sakko za su wuce,da sauri tace "za muyi magana
later,ina da wani d'an uzuri da ya taso min na gaggawa yanzun" sai ta katse
kiran,lokaci d'aya ta furta "Hey! Duka ku zo nan" a tare suka juya jin muryarta
because duk basu san tana zaune ba,Ismat tana share hawaye a hankali ta fara wucewa
kusa da Mom then Barraq dake had'e rai,suna zuwa ya zauna kad'an saman wani
armchair ya k'i yarda su had'a ido da Mom,but kallo d'aya za ka yi masa ka san
ransa a mugun b'ace yake saboda yadda yake tauna hak'ora kamar zai ci babu,yadda
nerves d'in kansa suka yi rad'a² kamar za su tsaga goshinsa su fito,Mom ta kalleshi
ta kalli Ismat a hankali ta furta "Maza ina saurarenku ku sanar da ni abunda yake
faruwa" saurin kallon Barraq Ismat tayi,ya kautar da kansa bai kalleta ba yace
"nothing Mom" Mom ta kalli Ismat tace "me ya had'a ku?" Kai Ismat ta fara girgizawa
then tace "ba da ni bane Mom" wara ido Mom tayi da sauri tace "ban gane ba? Idan ba
ke bace waye? Me kika yi nace?" Kallonsa ta sake yi then ta sake cewa "Mom ba ni
bace fa,shi da habibtiiy ne,ni hak'uri kad'ai nake basa" "habibtiiy?" Mom ta
tambaya da mamaki,Ismat ta gyad'a kai tace "Ehhh" da mamaki sosai akan fuskar Mom
tana bin staircases da kallo tace "when ta dawo gidan?" Ismat tace "yanzun babu
jimawa",juyawa Mom tayi tana kallon Barraq ranta a b'ace tace "didn't i told u of
what's right? Me kake son zama Barraq? Babban kwabo ko me? Kana so yaran nan su
raina ka kou?" Saurin kallonta yayi yana marairaicewa yace "Mom ba fa yadda kike
tunani bane,laifi tayi ban hukunta ta ba kuma ta zo tana yiwa mutane kukan banza"
wani kallo Mom tayi masa tace "laifi kace?" Ya kad'a kai yace "sure Mom" ta kad'a
kai tana kallonsa tace "wane laifi ne tayi maka? Yarinyar da ina kula wakenku sam
bai nuna tukunya d'aya? K'aramar yarinya ka maida ni da za kace min ta yi maka
laifi na yarda? Yaushe ma kuka zauna waje d'aya ban sani ba har tayi maka laifin?"
Ismat ta d'ago a hankali ta saci kallon Barraq yadda taga yayi shiru ya kasa
tankawa Mom ita kuma sai fad'a take masa a gabanta al'halin bata san abunda ma ya
faru ba,da sauri a wani irin sanyaye tace "but Mom kada kiyi hukunci da abunda baki
sani ba,tare suka je can fa" a fusace Mom ta juyo kan Ismat tace "how dare u told
me tare suka je?" A sad'ad'e Ismat tana sunkuyar da kai tace "I just know" Mom tana
yi mata wani kallo tace "saboda tare kuka je da su?" Ajiyar zuciya Ismat tayi tana
lumshe idanu tace "A'a Mom munyi waya da Yaa Jawahir ita tace sunje tare" kallonta
Mom ta dunga yi ta kasa magana,kusan mintuna uku then tace "je ki kawo min wayar
muga" a hankali ta tashi ta fara tafiya,har ta d'anyi nisa da fara haura stairs
d'in Mom ta daga muryarta tace "ku zo tare da Badriyah" ta amsa a hankali ta wuce
bedroom d'insu da niyyar aiwatar da umarnin Mom,tana shigowa ta tarar da Badriyah
ta fito daga bathroom fuskarta da alamun danshin ruwa,ta wuce ta fara d'aukar
wayarta then tace "kizo Mom tana kiranki" saurin kallonta Badriyah tayi tace "Okay"
suka wuce tare Ismat a gaba tana binta har suka sauko k'asan,tunda ta hango Barraq
dama taji gabanta ya fad'i a hankali wani irin tsoronsa ya dunga shiga jikinta,sai
tayi saurin sunkuyar da kai,bata yarda ta sake d'agowa ba har suka k'araso,Mom tana
kallon fuskarta da yayi jaa ta gefe tace "come here dear" tana mik'a mata
hannu,saurin tahowa tayi ta kwanta jikin Mom a hankali Mom ta zubawa fuskarta idanu
tana kallo tana shafa gurin tace "me ya same ki a nan nake ga kamar shatin hannu?"
Hawaye suka kawo idanunta a hankali tana tura baki tace "Yaa Barraq ne ya mare ni"
saurin kallonsa Mom tayi cikin fushi tace "Kana hauka Barraq za ka fidda hannu
k'aton namiji kamarka da ko wani namijin ka daka sai ka ji masa ciwo ka
mareta,laifin
me tayi maka kasa hannu ka daketa eh?" Sunkuyar da kai yayi a hankali yana
sassauta murya yace "I'm sorry Mom but it's not intentional" a fusace Mom tace
"it's not intentional kake cewa? Ni kake fad'a ma haka? Hauka kake za ka mareta?
Gaskiya na gaji Barraq da sa ni maganar da kake daga jiya zuwa yau,ni dai ka
tattara ka koma bakin aikinka Allah ba mu alkhairi" saurin kallon mahaifiyarsa yayi
jin tana cewa ta gaji da ganinsa kusa da ita,kamar zai fashe da kuka yana ci gaba
da kallonta yace "but Mom" a fusace tace "but what? Me kake da shi da za ka fad'a
min na saurareka?" Saurin kallon Ismat yayi yaga itama fuskarta duk ta yi rau²
kamar za ta fashe da kuka,a hankali ya sauke kansa k'asa yace "shi kenan Mom zan
tafi gobe in Allah ya kaimu,ki yi hak'uri in sha Allah bazan sake ba" yadda yayi
maganar cikin sanyin murya yasa Ismat jin wani irin tausayinsa a hankali ta share
hawayen da suka zubo mata ta kalli Mom tana tura baki tace "but Mom bafa ki san me
tayi ba kike masa fad'a kuma" juyowa Mom tayi kanta cikin fushi tace "kina son tare
masa ne saboda na yi magana? Ko kuwa dan ba ke ya yiwa marin ba?" Sunkuyar da kai
tayi a hankali tace "A'a Mom but kin sani ba'a hukunci da abunda aka ji ko aka gani
daga tsagi d'aya hakan yana iya zama kamar rashin adalci ne wa d'aya tsagin,and duk
gaskiyar da ake nema idan aka yi hukunci da abunda aka ji na gefe d'aya kin sani
Mom baza'a tab'a gane komai ba" still Mom tayi tana kallonta,tabbas maganarta
gaskiya ne,but ita ta san duk baza su fahimci dalilinta nayin haka ba,ta san wace
ce Badriyah fiye da kowa kasancewar rayuwarta kusan duka a gidan yake,tun tana zuwa
yi musu hutu lokacin tana yarinya har duka zamanta ya dawo gidan,kusan za ta iya
cewa a halayen Badriyah tabbas ta san 75% wanda ko uwar da ta haifeta ba lallai ne
ta sani ba,dole take dakatar da Barraq a wasu lokutan,because idan tana zuba ido
zafin zuciyarsa zai iya sawa wata rana ya ji mata ciwo ita kuma abunda ba ta fata
kenan ya faru,gyad'a kai tayi tana kallon Ismat tace "ko mene ne tayi masa bai
kamata yayi mata irin wannan marin ba,duba yadda shatin hannunsa suka kwanta mata a
fuska" Ismat ta d'ago tace "tou Mom ba zai sake ba ai in sha Allah ya fad'a fa"
harararta Mom tayi tace "rufawa mutane baki,ke ni ban san me yake damunki ba k'iri²
kina kallon abunda yayi kin san gaskiya amma sai wani support kike basa" murmushi
ne ya kufce mata tana satan kallon Badriyah tace "tou Mom ai kin san itama
habibtiiy ba jin magana take ba,kika sani ma ko wani abu yaga tana yi in
appropriate to her behavior?" Harara Mom ta sake sakar mata tace "za ki rufe min
baki a nan ko sai na b'ata miki rai?" K'ifta idanu tayi da sauri ta rik'e bakinta
da hannu tace "I'm sorry Mom na yi shiru Allah,but ki tambayeta ta fad'i abunda
tayi ya mareta muji idan itace da gaskiya dama za mu bata hak'uri" juyowa Badriyah
tayi saurin yi a fusace jin abunda Ismat take fad'a tace "ban gane na fad'i abunda
nayi ya mare ni ba?" Ismat ta d'aga kai a hankali tana kallonta tace "Ehhh! Ki
fad'a muji idan ba laifi kika masa ba me yasa zai doke ki tou?" Had'e rai tayi
cikin borin kunya ta fara ihu da fad'in "baza'a fad'a ba d'in,kawai dan kinga yana
yayanki shi ne za ki zab'esa ki bashi gaskiya,ai na gane abunda kike nufi" dariya
Ismat ta fara yi tana kallon yada Badriyah take yi tana k'ik'k'ifta idanu alamun
rashin gaskiya k'arara a fuskarta strictly tace "Kin gani kou Mom Allah ba ta da
gaskiya,ki tambayeta gata muji abunda tayi" a tsawace Badriyah ta mik'e tana yi
mata wani kallo tace "Kinga Ismat ba na son haka,meye ruwanki a cikin maganar ma
duka?" Ismat da dama halinsu d'aya da Jawahir gurin dariya ta dunga dariya tana
kallon Badriyah har saida hakan yasa Badriyah ta sake k'ulewa,Barraq da har lokacin
yake zaune bai ce da Mom ga abunda tayi masa ya mareta ba shi kansa sai da abunda
Ismat take yi mata yasa shi yin murmushin da bai yi niyya ba,Badriyah kuwa dama da
ta gama k'ulewa cikin fushi ta fashe da kuka,tana kallon Ismat dake tsagaitawa da
dariya tace "tunda kin zab'esa akai na dama yau ba sai gobe ba zan yi tafiyata,sai
kije kiyi ta zama alone,zan bar muku gidan kuyi ta zama ke da shi" tana fad'a ta
juya za ta wuce sama da niyyar ta tattare belongings d'inta tayi wucewar ta gida a
cewarta,Mom tayi saurin rik'o ta tace "haba habibtiiy me yasa za kice haka?" Ismat
ta d'age shoulders tana tab'e baki alamun bata damu ba tace "Mom let her be
please,maza ki gaida gida" a firgice Badriyah ta waiwayo jin abunda Ismat tace tana
kallonta because bata tab'a expecting such a words za su iya fitowa daga bakin
Ismat d'inba all because of bold relationship da take hangowa tsakaninsu tace "kika
ce me?" Strictly Ismat tace "cewa nayi ki gaida gida,kou kina ga bazan iya zama ba
a gidan mu idan kin tafi?" Yadda tayi furucin tana d'an zare idanu yasa duka su uku
suka bita da wani kallon mamakin anya Ismat ce da gaske take fad'in haka ko kuma
dai mafarki suke? Because kamar yadda suka yarda kuma suka sani abu ne mai wahalar
gaske ace kalaman daga bakinta suka fito,sun san alak'ar dake tsakanin su biyun sun
kuma san yaya ne matsayin Badriyah a zuciyar Ismat,tambayar farko da yazo wa duka
su ukun shi ne "Mene ne ya zo cikin tunanin Ismat lokaci d'aya har ta iya fad'in
idan ta rabu da Badriyah baza ta ji damuwa ba?" Jikin Badriyah banda tsuma babu
abunda yake yi tana sake bin Ismat da kallon mamaki tace "kin san abunda bakin ki
yake cewa Ismat? Do u really know of what ur mouth said? Kina cikin hayyacinki kika
ce hakan?" Ismat tayi murmushi tana lumshe idanuwa tace "of course ina cikin
hayyacina nace haka" ba Badriyah kad'ai ba hatta Mom ta ji matuk'ar mamaki da irin
kalaman suka iya fitowa daga bakin Ismat but ta kasa samun confidence tayi
magana,gyad'a kai Badriyah tayi a hankali tana yiwa Ismat wani irin kallon da na
kasa tantance na mene ne,then da sassarfa ta juya ta wuce sama tana fashewa da
kuka,tana barin gurin tunanin Mom ya dawo daga yajin aikin da yaje,tana kallon
Ismat da mugun mamaki tace "Sweetheart! What really come over ur head? Kin san me
kika ce da y'ar uwarki kuwa?" D'aga kai tayi tace "na sani Mom,barta muga idan za
ta iya tafiya d'in" Mom tayi still tana kallon Ismat da mamaki but couldn't talk
sai kallon da take yi mata duk inda tayi,Ismat tayi murmushi a hankali ta waiwaya
gurin da Barraq yake tayi masa murmushi a hankali ta nufesa,saman hannun chair ta
d'an zauna tana rik'e hannunsa duka tace "kayi hak'uri bhai da abunda tayi,ni dai
na san ba za ka daketa ba idan bata yi maka laifi ba dama,but please i'm begging u
daga yau ka daina saurin fushi,kaga ba shi da kyau,kuma ka sani Annabi (S.A.W) ya
hana mu yin hukunci a cikin fushi" wani irin sanyi yaji kalaman Ismat sun saukar
masa,a hankali yana kallon k'anwarsa da shekaru rututu suke tsakaninsa da ita yayi
murmushi yace "in sha Allah kid sis zanyi k'ok'ari na daina,thanks for the
reminder,i love u" murmushin jin dad'i tayi wanda ya bayyana hak'oranta tace "I
love u too bhai,but please ka daure kana yiwa Mom bayani idan ta tambayeka abu,ka
ga yanzun ni na san Badriyah ba ta da gaskiya,amma da ka yi shiru kaga Mom kai ta
yiwa fad'a ba ita ba,please bhai kaga bai kamata ace ana yi maka fad'a a gabanmu
ba,tunda kai Yaya ne,amma idan kayi bayani kaga babu wanda zai na ganin laifinka
kou?" Sanyayyan murmushi yayi yana lumshe mata idanu a hankali yace "thank u dear"
tayi dariya kad'an a hankali tace "tou ka fad'awa Mom yanzun abunda tayi,tunda ita
bata san rufa mata asiri ma kayi ba" saurin kallonta yayi yace "ya akayi kika
sani?" Tayi murmushi tana kallon Mom dake kallonsu ta kasa cewa komai tace "ban
sani ba kawai fad'a nayi,because na san halin bhai na ba ya tab'a yin abu babu
dalili,and habibtiiy too,na fi kowa sanin halinta because ni nake rayuwa tare da
ita" kad'a kai yayi a hankali yayi