Chapter 95 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   95 / 101

282K to 285K   out of 300.2K words

taba yi
musu aiken ko kwandaka ba kuma Jidda bata taɓa tambayarsa ko wani nasa wani abu ba, and they look
fine, they misses him of cause amma baya jin suna da wani financial problem. Fes, fes da su, full of
energy and laughter.



Sai ya tura su gida su ajiye kayan hannun su sannan su gaya wa mommyn su zai fita da su. Basu jima ba
suka dawo har uniform an cire musu an kuma saka musu kaya masu kyau. Sai ya dauke su a mota suka
fita, yana ta tambayar su game da rayuwar su da makarantansu su kuma suna bashi labari, a haka har sai
da suka nuna masa both bokon su da islamiyyar su ya gani sannan ya tafi dasu yawo ya kashe musu kudi
duk da shima ba kudin ne dashi isassu a hannunsa ba amma ya siya musu kayan abinci da kayan tea da
kuma tarkacen su biscuits da sweets da juice na zuwa makaranta. Ya so ya siya musu kayan sawa ma da
takalman makaranta amma kudin ba zasu ishe shi ba dan haka bai siya ba amma yayi niyyar zai turo wa
Jidda kudi ta siya musu, duk da yasan already ta siya musu.



Sai dare suka dawo, bayan ya kai su gida sunyi dinner tare sannan sunyi sallama da Mama da Baba
wadanda suka basu kuɗi, yaji dadin hakan dan dama ya so ya basu kudin amma bashi da su. Sai ya hada
kudin ya sakawa Yasmin a aljihun ta yace in sunje gida ta bawa mommy.



Da zasu rabu kuma sai yaji ba dadi, yaji zuciyarsa tana yi masa zafin rabuwa da su kuma yana jin tsoron
kar wani abu ya same su, amma daya tuna Abban Jidda da irin dagewar sa a gurin tarbiyya, ya kuma tuna
da ita ma Jidda irin kokarin ta sai yaji hankalin sa ya kwanta. Ya fahimci they will be safe there insha
Allah.



Washegari jirgi ya daga dasu zuwa garin Lagos......



*Jidda*



Ta karanta text din daya tura mata, ta sake karantawa amma ta kasa fahimtar ma'anar sakon. Me yake
nufi da gode mata dan ta gaya masa matarsa tana da ciki? Ko bakar magana yake neman gaya mata ne?
Har da wani love you a karshe. Love who?



"Love go kill you there"



Ta fada tare da jan tsaki. Ita yanxu kalmar love takaici take bata ma dan babu wani abu a cikinta sai
kunan zuciya da hawaye masu daci. Ta ajiye wayar ta kwanta akan kujearat tare da karo volume din TV,
anjima kadan ta kuma mikewa ta dauki wayar ta nemo number dinsa ta danna mata block. A ranta tana
godewa wanda ya kirkiri idea din blocking dan ba karamin saving rayuwar ta yayi ba dan ta tabbatar
Umar tunda ya dawo Nigeria ba zai barta ta kuma shakar iska mai dadi ba.



Kwanaki kadan bayan nan tana guri aikin ta tana chatting da customers dinta a waya sai ga kira da
number din da bata sani ba, babu bata lokaci ta dauka cikin fara'ar ta tana saka ran daya daga cikin
customers din nata ne , amma sai taji muryar da bata bukatar a gaya mata ta waye dan ko cikin bacci taji
ta zata gane ta, murya mai cike da karairayi da manipulations da pretence. Nan da nan farin cikin da take
ciki ya katse, fara'ar ta ta kau. Tace "me kake bukata ne wai Umar? Akwai sauran wani abu naka a gurina
da kake nema?"



Yace "eh. Forgiveness shi nake nema. Another chance nake bukata. A sympathy nake......"



"Dakata!" Nace masa. "Na fada maka tun ranar nan cewa I have forgiven you. And I wish you well a
rayuwar ka ta duniy da lahira. I just don't want to have anything more to do with you. Please please and
please, ni ban taba jin dadin rayuwa irin wadda nake ji yanzu ba. Ni ban taba samun nutsuwa da
kwanciyar hankali irin wanda na samu yanzu ba. Please don't try to bring back pain and agony into my
peaceful life. Please, stay away from my life"



Daga nan na katse kiran tare da jan dogon tsakin daya janyo hankalin abokiyar aikina, raina duk ya baci
duk nishadi na ya kauce. Na kashe data ta sannan na fara shirin tafiya gida tunda shift dina ya kusa
karewa dan wadda zata karbe ni har tazo dama na dan jira ne yamma ta dan kara yi saboda zafin rana.



Daga nan ban karasa gida ba sai da na biya na siyo waya irin ta yara amma wadda ake sakawa simcard,
sannan kuma na sayi sim card din. Ina zuwa gida na saka ta a charge sannan nayi wa Umar text da
number din sabon sim card din na sanar masa da cewa yake neman yayansa ta nan. Nasan legal excuse
din da yake da shi na kirana shine yayansa, yanzu kuwa babu kare babu bin dami.



Ina gama tura masa text din na sake blocking number din daya kirani da ita sannan na bi duk social
media accounts dina nayi blocking dinsa, sai kuma na chanja passwords din komai nawa dan nasan
halinsa tsaf zai iya shiga ta ciki yayi min magana ko kuma ya saka ido akan abinda nake yi a can.



Sai da na gama sannan naji hankali na ya kwanta, na bawa yara wayarsu suka yi ta murna amma sai na
nuna musu cewa na siya musu waya ne dan su daina daukan tawa suna karar min da charge, ba jimawa
ya kira su suka yi ta hira ina jin su and I moved on with my life har zuwa wasu kwanaki sai gashi ya kira
wayar su wai yazo yana waje, Amira da ta dauki wayar bayan naki dauka ta gayamasa suna islamiyya,
bayan sun dawo ne ya fita dasu sai can dare suka dawo da lodin kaya da kuma kudi suka gaya min wai
yace yana gaishe ni kuma zaiyi tafiya zuwa Lagos shi da Baba da Mama. Banji sun ambaci Asabe ba, A
lokacin na tuno da maganar Baffa Halilu na cewa yaje ya karbi business din Baba to keep him busy.



Na girgiza kaina "hmmm. Umar a Lagos ba tare da mata ba, Allah kadai ya san barnar da zaiyi. Allah ya
kyauta"



And I felt relieved da ya kasance am no longer his wife, duk abinda zaiyi ma will no longer affect me, ni
dai kawai kula da yayana da tarbiyyar su ce a gaba na.



Kwanaki kadan bayan nan Mama Sa'a tazo gidan, ta leko dakina muka gaisa lokacin na dawo daga office
ina cire uniform dina, sai ta tafi dakin Hajiya, daga baya kuma sai gata ta dawo ta tarar ina duba designs
na wasu furnitures sai ta zauna akan katifa a kusa dani tayi shiru, and I know magana ce ta kawo ta sai
na rufe system din gabana na juyo ina kallon ta.



Sai ta kama hannuna a cikin nata tace "Jidda nazo ne in kara baki hakuri akan abinda ya faru. Wallahi
wallahi Jiddah babu hannuna a cikin maganar nan, Hajiya ce da Mammy suka shirya kayansu sai da Abba
ya kira ni ma sannan na san da maganar"



Na zare hannuna daga cikin nata ina cewa "babu komai fa. Ni na yafe tuni" and I meant it har cikin zuciya
ta. T



Ta gyada kai. "Nagode. Ke kam gashi nan rayuwa tana tafiyar miki lafiya lau tunda baki da hakkin kowa.
Ni kuma duk da bansan hakkin wa na dauka ba rayuwar taki yi min dadi Jidda. Har yau ban gama shan
bakin cikin miji ba dana kishiyoyi sannan kuma gashi ina kan shan na ƴa"



Na sake mayar da hannu na cikin nata cikin kulawa nace "ban gane ba?" Tace "Mammy ta lalace Jidda,
tafi karfina, yanzu har ta kai matsay da takan iya barin gida taje wani wajen ta kwana. Uban yayi dukan
gar ya gaji, yanxu yace ya barwa duniya ita wai in duniya ta koya mata darasi zata shiryu"



Naji babu dadi a raina. Na girgiza kaina da sauri ina tuno da abinda ya faru da rayuwar Zuwaira da yadda
ta koma a karshe.



Nace "uhm uhm kar kuyi haka dan Allah. Mammy amana ce da Allah ya danka muku kuma in baku kula
da ita ba tabbas sai Allah ya tambaye ku a kanta"



Tace "to ya zanyi Jidda? Babu yadda zanyi ne" na sake girgiza kai na "there is always a way, kar mutum
yace babu yadda zaiyi, tabbas to every problem there is a solution. Na farko zaki iya yi mata addu'a, ki
dage babu dare babu rana. Na biyu zaki iya sakawa a taya ki yi mata addu'a, kiyi ta istigfari dan maganin
masifa ce, kiyi ta sadaka dan waraka ce. Abu na uku ina baki shawarar ki kawo ta gidan nan ki durkusa
kiyi wa abbay kuka ki gaya masa halin da ake ciki, shima jininsa ce tabbas ba zai so ta tabe ba. Kuma
kinsan halin tsaurin Abba, in tana gidan nan ba zai sassauta mata ba, damu family gabakidaya zamu yi
iyakacin kokarin mu a kanta. Hannunka baya taba rubewa ka yanke ka yar inji hausawa. Shima kuma
baban nata kar ki barshi, ki cigaba dayi masa maganar ta, da tuna masa nauyin ta da yake kansa, kafin
Allah ya sa ta samu miji ayi mata aure"
Ta gyada kai cikin amincewa. "Nagode sosai Jidda. Insha Allah I will not give up. Sai inda karfina ya kare"
nace "good"



Babu bata lokaci Mammy ta dawo gidan mu a karkashin kulawar Abba da yake kula da duk motsinta with
iron fist. Sai dai kuma, duk da nace na yafe amma kullum na ganta....kullum tayi min magana.....sai na
tuna....



And then time moves...........



Shekara daya ta wuce sannan ta biyu ma ta wuce........



A cikin shekaru biyun nan abubuwa da yawa sun faru a rayuwata. Abu na farko daya faru shine irin
cigaban da na samu a harkar kasuwanci na. Sosai Allah ya saka min albarka a ciki tare da taimakon Abba
karami wanda yayi dedicating rayuwarsa toward the success of the business har yayi out growing dakin
da muka karba, a lokacin ne muka yi shawarar fitar da business din bakin titi mu kama hayar babban guri
sannan kuma mu fara yin new furnitures da kan mu, tunda dama duk dan kano yasan unguwar gandu
akan harkar furnitures, tun daga farkon titin mu har karshen sa furnitures ake siyarwa, wannan ya saka
kusan dukkan samarin gidan mu sunsan one or two things akan carpentry including Abbah.



Babu bata lokaci muka karbi gurin, muka gyara shi tas muka tare. Sai muka muka dauki maaikata
kwararru masu experience da zasu ke aiki a karkashin Abbah da yake a matsayin manager. Na chanja wa
business din suna daga "used....to be reused" zuwa "Jidda's Signature" still muna siyan fairly used
second hand din muna siyarwa sannan kuma a hankali muna introducing newly made items din
wadanda muke captioning a social media accounts din mu as "made by Jidda. With love"



Kuma suma sun samu shiga alhamdulillah, saboda ina matuƙar kokarin ganin nayi research na samo
designs masu kyau na kamfani sai mu kwaikwaya kuma sai yayi kyau sosai ga kuma kwari. A hankali sai
naga hankalin mutane yafi karkata ga sababbin sai dai wadanda ba zasu iya affording ba. Bayan watanni
akan hakan sai kuma na fara dauko kayan kitchen ina siyarwa a gida, suma suna shiga sosai musamman
a gurin maaikata wadanda na kan bawa bashi su biya ni in anyi albashi. A yanxu haka zan iya cewa
albarkar da nake samu a kasuwanci na tafi wadda nake samu a aiki na dan in aka ce min in zaba zan zabi
kasuwancin ne duk da dai shima aikin ina son sa. Lol
Abu na biyu mai muhimmanci da ya faru shine bikin Farhan da akayi few months into the two years,
mun sha bikin ta da Sadiq din ta, munsha iyayi da soyayya, at last after the long wait ta hadu da soul
mate din ta sai dai muyi musu fatan alkhairi.



And months after that akayi bikin Amira da Aira a lokaci daya, bayan kin yarda da auren hadin da Amira
tayi a karshe an aura mata Souraj din ta, wannan ya sa ita kuma Aira da har yanzu take fama da takaicin
rabuwa da masoyin ta Musaddiq ta ce zata share wa iyayen mu hawaye zata auri daya daga cikin suitors
din, imday a karshe suka daidaita da Djimon. Sai aka hada bikin akayi a tare aka daura aure anan Nigeria
sannan muka kai amare Addis Ababa inda anan mazajen nasu suke da zama.



Abu na uku da ya faru wanda kuma ya kasance na bakin ciki sabanin abubuwan da suka gabace shi shine
rashin lafiyar da Aunty Afia ta kama yi gab da bikin su Amira. Zazzaɓi take ta fama da shi da wani mugun
tari da yaki tafiya, gashi ta kanyi complain na ciwon ciki da kuma yawan ziyara da take kai wa toilet. A
haka dai aka lallaba aka gama bikin, ko zuwa kai amare ma bata samu damar yi ba anan muka barta
Daddy ya turo likitansa ya duba ta ya bata magunguna. Sai dai bayan mun dawo din ma bamu tara da
cigaba ba a yanayin jikin nata, wannan yasa a lokacin na roki Abba ya bar ni naje na zauna jinyarta. A
yayin jinyar tata ne na lura da cewa bata iya cin abinci sosai saboda tana complain cewa da kyar take iya
hadiye abincin in ta saka a bakin ta ga kuma lost of appetite. Sai nayi checking bakin nata and I saw
rashes a kan harshen ta. Tun daga lokacin gaba na yake faduwa da lamarin ta, and I decided to observe
more. Cos something doesn't feel right, ina kuma having wani gut feeling marar dadi akan maganar. Ina
suspecting wani abu.



Rana daya sai na dauki wayarta na shiga facebook din ta na nemo account din Zuzu, and I realized kamar
ba'a using account din yanzu. I searched for gery friend wadda lokacin da Umar ya dake ta tayi posting
cewa bata da lafiya, i sent her a message cewa ina neman Zuzu din ne because I am her friend. And her
reply shocked me. Cewa Zuzu ta rasu few months ago.



A ranar na samu aunty in roke ta akan ina son in tafi da ita asibiti inyi running some tests akan rashin
lafiyar ta, amma sai daddyn su Aira yaki yarda yace ai already likita yana duba ta kuma yana bata
maganin duk da ya dace. Ni kuma na duba magungunan nata naga ana treating symptoms ne kawai ba
tare da ansan menene tushen ciwon nata ba. Na matsa mata tazo muje and she refuses. Sai na taho da
kayan aikina dauki blood sample dinta na tafi dashi asibiti na kai lab nayi requesting for test din ciwon da
nake suspecting. Sai da zan taho na koma lab na karbi result na gama addu'a sannan na bude. And it was
positive.
A ranar naga tashin hankali. Na rasa ta yadda zanyi breaking wannan mugun labarin ga Aunty. Aunty Afia
has been a good wife duk tsahon rayuwar ta, and it is true that she never lacks anything a gidan ta dan
tun kafin inyi aure ita ce role model dina ita nake fatan in samu irin rayuwar ta, and now I know better.



Now I understand cewa *ba kowacce matar auren da muke ganin cewa tayi dacen miji a zahiri ce tayi
dacen ba, wani auren a zahiri ne yake success, a badini kuwa is a woman's worst nightmare.*



I went to her room, tana zaune tana ta faman tari ta hada uban gumi, na tsaya ina kallon ta ina lura da
yadda ta rame ta lalace kamar ba ita ba, duk wannan kyawun ya yamushe sai ƙashi sai fata. Na zauna a
kusa da ita sannan na bude hannunta na saka mata takardar.



Ina kallon ta ta bude ta karanta. Sai takardar ta zame daga hannunta ta fadi kasa. And I started crying
tun kafin ita ta fara. I am not a very good comforter ni na sani dan in mutum yana cikin damuwa ma ni
sai na fishi zubar hawaye. Zai ta same ta sauka gaban gadon ta zauna a kasa sannan ta fara rera nata
kukan wanda jinsa kadai ya isa ya huda zuciyar mai saurare. Na sauko nima na rungume ta muka cigaba
da yi tare. Sai da muka yi muka koshi sannan tace "yayi min alkawarin ya daina fa" na share mata
hawayen ta da damkwali na nace "most of them never stop".



Bayan doguwar rigima wadda har sai da Abba ya shiga, bayan kuma dogon bincike ne aka gano cewa
ashe ya riga yasan yana da cutar kuma already yana shan magani abinsa, bai gaya mata ba ita ballantana
ta sha maganin ita, sannan kuma ya hana ta zuwa asibiti ballantana asan tana da shi a bata magani. Sai
ya bar ta a gida, maybe plan dinsa shine ta mutu a gida, shikenan asirin sa ya rufu. How cruel.........



(Wannan labarin ya faru a gaske. Nayi using dinsa dan nuna how bad it can be)



Cikin yardar Allah da dagewar mu yanuwanta da yayanta, muka kaita asibiti aka bata dukkan kulawa
sannan aka dora ta akan magani. I expect her daga asibiti ta taho gidan mu ko ta tabi Ethiopia but sai
tace in mayar da ita gidan ta. A can muka samu daddyn Aira babu kunya babu tsoron Allah yana cigaba
da rayuwarsa and She demanded ya sake ta, kuma ya tattara kayansa ya bar mata gidan ita da yayanta in
kuwa ba haka ba she will go to media and expose duk abinda yayi including kokarin kashe ta da yayi.
Babu kunya babu tsoron Allah kuwa sai ya zabi ya bar mata gidan. A lokacin sai na fahimci wani abu,
cewa yawancin su mazinatan nan sunfi tsoron tonon silili akan tsoron Allah.
Wannan kenan......



Abu na gaba daya faru a shekaru biyun nan shine yadda manema suka feso min ta kowacce kusurwa.
Family members, including Salem din Aunty Nuru wanda dagabaya na fahimci saboda ni yaki zurfafa
neman sa akan Amira, work colleagues, wadanda suka hada da likitoci har ma da patients, yan unguwa
wadanda suka san aurena ya mutu, customers da suke siyan kaya a guri na da kuma wadanda muke
haduwa a hanya.



Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din



0779484494

Nafisa Tafida Usman

Access Bank



Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp

08067081020



Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020



Please banda kira, WhatsApp only



*Wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar ki
sharing, in kika yi kinci amana kuma ke da Allah*



*The Empty Heart*
To those in Jidda's position, idan har Allah ya saka kin zo wannan junction din a rayuwa, kin zo wannan
stage din da Jidda take ciki, shawara ta a gare ki ita ce kiyi addu'a, ki nemi Allah ya zaba miki abinda yafi
alkhairi a gare ki. Ko

95 / 101