Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
mu mun amince cewa laifi na Umar ne, shima kuma da nayi magana
dashi ya karbi laifin sa, amma ni kuma sai nake ganin kamar laifin iyayensa yafi yawa akan nasa, amma
hakan ba yana nufin cewa bashi da laifi ba dan laifin su a gurin Allah sam bai kai yawan nasa laifin ba dan
duk abinda ya aikata da hankalinsa ya aikata shi. Sai dai abinda nake nuna mana shine da ace iyayen sa
sun kyautata gurin tarbiyyar sa da bamu samu kan mu a inda muke a yanzu ba. Kuma a ganina laifin
mahaifin sa yafi yawa akan na mahaifiyar sa tunda ita mahaifiyar sa at least zamu ce tayi iyakacin kokarin
ta shi kuma mahaifin sa shine ya saki tarbiyyar gabaki daya ya mayar da hankalinsa kan kasuwancin sa"
Daga nan kuma a laifi sai shi mahaifin Jidda, wanda maybe da ya tsaurara bincike a lokacin aurar da
yarsa da ya bankado halin Umar da bamu sani ba, watakila da yayi haka da ya ankarar da iyayen Umar
halin dansu kuma da sun dauki mataki tun a lokacin, laifin sa ma biyu kuma shine rashin jan yayansa a
jiki yadda zasu iya gaya masa abinda yake damun su, da ace da akwai kyakykyawar dangantaka a
tsakaninsu da tun farko da ta fahimci halin mijinta da gurin iyayenta zata zo, maybe da tun lokacin za'a yi
maganin matsalar. Sai ita kuma kuma Jidda, she should have try ta samu hanyar gayawa magabata ba
wai ta rike abin a ranta tana tunanin zai wuce ba, abinda addini ya tsara shine irin wannan maganar sai a
gaya wa magabata su kuma sai su bi tsarin shari'ar wajen ganin an samu dai dai to"
Mama tayi gyaran murya tace "akwai laifina a nan" duk suka juyo suna kallon ta ban da ni da Umar sai
tace "Jidda ta gaya min. Ta aiko babbar yar mu ta gaya min. Amma sai zuciyata ta ki yarda da maganar a
karshe ma sai nayi kokarin dora laifi a kanta dan ina ganin kamar zuciyata ba zata dauki kasancewar
maganar gaskiya ba, dana binciki maganar tun a lokacin watakila da na samo gaskiya, wata kila da bamu
zo inda muke a yanzu ba, da abubuwan da suka faru ba su faru ba, watakila da ban ga abinda na gani ba"
Ta karasa maganar tana kuka, Baba ya yunkuro da bacin rai kamar zaiyi mata fada akan cewa na gaya
mata amma bata dauki mataki ba kuma bata gaya masa ba sai Baffa ya dakatar da shi. "Kamar yadda na
fada tun farko, ba mu zo gurin nan dan mayar da magana ba. Nazo ne dan in fada wa kowa laifinsa sai
kuma mu san matakin da zamu dauka"
"Yanzu na gama fadar laifi, sai kuma abinda nake ganin shine a kamata muyi. Abu na farko shine dole mu
gyara tushen matsalar, ma'ana Umar, abinda bamu bashi a da ba wato tarbiyya dole ita zamu bashi a
yanzu, bashi tarbiyya kuwa ba yana nufin ignoring dinsa ba kamar yadda iyayensa suke yi a yanzu, ba shi
tarbiyya ba yana nufin aura masa mai aikin matarsa wadda ake zargin sa da cewa ya lalata ba, bashi
tarbiyya a gani na yana nufin jan shi a jiki, keeping him busy with something good, samar masa aikin yi,
dora shi akan tafarkin Allah da kuma tunatar da shi girman laifin da yake yi"
"A ganina wannan auren da kuka yi masa bashi da wata ma'ana, ta yaya mutumin da yake auren
kamilalliyar mace, kyakykyawa mai tarbiyya da ilimin addini da kuma na zamani dadin dadawa kuma
wadda yake so amma bai daina halin sa ba sai kuma a aura masa wadda take totally opposite sannan ayi
tunanin zai daina? Ta yaya? Tabbas Umar ba yaro bane ba yasan dai dai ya san ba dai dai na amma a
ganina there is no harm in guiding him, making it easier for him to do the right thing"
Baba yace "ni ban yiwa Umar aure dan wai ya daina halinsa ba, nayi aura masa yarinyar can ne dan in
koya masa darasi kuma dan in cika alkawarin da na dauka wa iyayen yarinyar wanda a ganina idan ba'a yi
haka ba tamkar an zalinci yarinyar ne. Daina halin shi ko rashin daina wa is all up to him, shi kadai zaiyi
deciding zai daina kuma ya daina din"
Baffa yace "but we can still help him ai, with prayers, nasiha and guidance. A ganina ita case din yar aikin
ba dai iyayenta suna gudun abin kunya bane ba shi yasa suka dage akan ya aure ta? To an daura auren.
Zama da ita ko rashin zama da ita ku barshi a matsayin choice din Umar. In yaga zai zauna da ita a
matsayin mata fine in kuma ba zai zauna da ita ba kar ku takura masa a bisa hakan dan takura masan will
do more harm than good a ganina. Idan ana maganar aure ana maganar zuri'a ne, idan kuwa ana neman
kyakykyawar zuri'a to ana neman tsatso ne mai kyau. A shawarce Iyayenta su kawo ta nan gidan ku a
bata daki ta zauna, sai shi kuma ku bashi lokaci idan a cikin lokacin ya ga zai zauna da ita fine, idan kuma
ba zai zauna da ita ba sai ya sauwake mata ta koma gidan iyayenta a matsayin bazawara kunga an yi
musu maganin wannan abin kunyar da suka ce suna tsoro. Shi kuma ba'a sake tura shi ga halaka ba"
"Abu na gaba kuma shine a shawarce gabaki dayan ku kuna bukatar break from each other, Umar kansa
yana bukatar break daga gare ku ku iyayen sa kuma kuma haka, idan har kuna tare maganar ba lallai ta
mutu a zuciyoyin ku ba amma ku bashi space yaje yayi tunani akan girman laifuffukan sa sannan ya
fahimci inda ya tsaya da kuma inda zai dora a rayuwa. Ku ma kuma ku huce ku daina ganinsa for
sometimes, duk da nasan abubuwan ba zasu wuce a zukatan ku ba amma zaku huce kadan"
Baba yace "ina zai je kenan a ganinka?" Baffa yace "Lagos" ba Mama ba har ni sai da muka dago kai
muka kalle shi. Mama tace "Lagos? Ji nake zaman Lagos din yana daya daga cikin abinda ya kai shi inda
yake a yanzu? Sai kuma ya sake komawa a yanzu da ya kamata ya kara nisa da garin?"
Baffa yace "ita shiriya ai ba a gari take ko a cikin mutanen garin take ba, ita shiriya a zuciya ta ke. Idan
har Umar da gaske yake abinda ya fada cewa yayi tuba na gaskiya then zaman Lagos ba zai saka ya dawo
ba. Eh tabbas gari yana da tasiri a wajen bayar da tarbiyya amma Umar already yana da tarbiyya, already
tasan right and wrong ba wai yaro bane ba shi. Kuma ina so mu sani cewa akwai shiryayyun mutane a
Lagos kamar wadda yake da akwai lalatattun mutane a Saudiyya. Abinda ya sa nake son ka tura shi Lagos
din dan a can ne zaiyi fighting temptations din sa sosai, kuma a can ne zai samu abin yi. Tunda anan ba
aiki yake yi ba kawai zaman kashe wando yake yi. Mahaifin sa kuma ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba.
Dukkan harkokin kasuwancin sa na can sai ya damka masa a hannunsa ya barshi ya cigaba shi kuma ya
zauna a gefe ya saka masa ido akai. In ya ga dama ma zai iya komawa makarantar addini a can din dan
akwai su da yawa, in bai ga dama ba ya bari, wannan a zuciya yake in an tilasta masa yaje din ma in babu
abin a zuciyarsa karatun da wa'azin duk ba zasu ke shigar sa ba. Amma in akwai abin a zuciyarsa ko bai
koma makaranta ba zai gyara rayuwarsa, ko sallah ya tsayar yake yi akan lokaci zata gyara masa rayuwar
sa".
"Sai maganar data kawo mu nan baki daya, maganar auren Umar da Jidda. Duk abubuwan da suka faru a
gidan auren su mu waliyansu bamu sani ba sai yanzu. Dan haka ni a matsayina na waliyyin Umar ina
nema masa alfarma a gurin iyayen Hauwa'u da suyi hakuri. Su sake bamu wata damar. Mu zasu bawa
dama ba Umar ba. Idan har Umar yayi wasa da damarsa ko ince damar mu dan tamu ce ba tasa ba, ni da
kaina zan karbi takardarta a hannunsa in bata"
Abba ya girgiza kai "gyara muke kokarin yi. Gyaran dan ku kuke kokarin yi. Gyaran kuskuren ku kuke
kokarin yi kamar yadda ni ma nake kokarin gyaran nawa kuskuren" Baba yayi saurin cewa "Dan Allah
Alhaji kar ka ce ba zata koma ba. Nauyin ka da girman laifin yaron nan ya saka na kasa zuwa tunda abin
nan ya faru ballantana in baka hakuri, amma yanzu ka duba darajar mu......"
Abba yace "ita na duba a lokacin da na bada auren Jidda, darajar taku ce ta rufe min ido har na kasa
bincike mai kyau a kansa kamar yadda ya dace. Wannan shine kuskure na. Wannan shine abinda nake so
in gyara. Ba zan hana Jidda komawa gidan mijinta ba indai har hakan shine abinda take so kamar yadda
ba zan tursasa mata ta koma ba in hakan shine abinda bata so. Gatanan ga ku. Idan zata koma yanzu ma
zata iya dauko kayanta ku tafi. Amma idan tace bata so ina son kuma kuyi respecting din decision dinta
ku barta"
Na yi shiru kaina a sunkuye duk ina jin maganganun su. Baffa Halilu ya kira sunana na amsa ba tare da na
dago kai na kalle shi ba sai yayi min straight tambaya "kina son Umar kina kuma son ki koma gidan sa?"
Na dago kai na kalli Umar wanda yake opposite dina, zuciya ta ta buga saboda tsoron da yanayin sa ya
bani. Ya koma kamar skeleton mai fata. Farar Fatarsa tay duhu sosai lips dinsa duk sun bushe, kayan
jikinsa a hargitse.
Na mayar da kaina kasa sannan a hankali nace "ina son Umar Baffa. Amma kuyi hakuri. Allah shine
shaidata bana son cigaba da auren sa, aurensa ya fita daga raina gabaki daya"
Duk gurin yayi shiru. Sai Mama ta sauko kusa da ni ta dafa ni "Jidda. Ki duba darajar yayan da suke
tsakanin ku. Dan Allah kiyi hakuri ki koma gidan mijinki. Kiyi hakuri da duk abinda yayi miki da wanda ni
nayi miki ki yafe mana ki....."
Na dago kai ina kallon ta nace "na yafe masa Mama, na yafe miki ke ma. Amma aurensa na gama"
Zata sake magana sai Baba ya sauko ya kama ta ya mayar da ita kan kujera, ina jin sheshshekar kukan ta
daga baya but for the first time in my life naji babu hawaye a nawa idon. My mind was already set. Na
san abinda nake so and I am standing by it.
Naji Baffa yace "to Umar kaji. Cikin mu kuma babu wanda zai matsa mata. Decision dinta ne kuma ta riga
ta yanke"
Sai naji Umar yayi maganar sa ta farko tunda yazo gurin.
"Babu komai Baffa, na gode da dukkan kulawa"
Sai ya mike ya fita waje. Duk mutanen gurin suka bi shi da kallo. I thought ya bar unguwar ne ma. Sai
kuma gashi ya sake dawowa falon ya zo gabana ya durkusa, ban dago ido na na kalle shi ba sai ya mika
min wata farar takarda sannan yace "gashi. Thank you for everything".
Na saka hannu na a hankali na karbi kar karamar takardar da tafi kama da wadda aka yago daga jikin
jotter. Sannan cikin dabara yadda babu wanda zai gani na zira hannu na cikin nasa sannan naja tsohon
band dina da har yau yake makale a hannunsa. Ya tsinke ya tarwatse akan cinyata, sannan without
looking at his eyes na karbi takardar nace "nima na gode".
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana idan baki siya ba kar ki karanta idan kuma kin siya kar ki
sharing in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*
*The Next Page*
*Rayuwa feji feji ce, kamar pages na littafi, kowanne page idan ka bude yana da farko kuma yana da
karshe, in ka gama wannan fejin kuma ba zaka san menene a cikin next page ba har sai ka bude shi
tukunna*
*We all have the right to open the next page in the book of life, what most of us lack is the courage*
Umar
Wadannan kwanakin, wadannan unfortunate kwanakin are the worst days of his life. Gabakidaya duniya
ta juya masa baya. Ba zai iya tuna ranar da ya zauna yaci abinci a tsanake ba, ko ya saka abincin ma a
bakinsa baya iya wucewa ta makwogwaron sa saboda wani abu mai daci daya tokare masa a
makogwaron, ba zai kuma iya tuna ranar da ya kwanta yayi bacci for five hours straight ba. Some nights
yana yin su ne a zaune akan gadonsa hannun sa dafe da goshin sa idonsaa kafe a guri daya duk da ba wai
kallon abinda yake gurin yake ba.
Babu abinda yake yawo a kwakwalwar sa irin daci da takaicin irin mummunar rayuwarsa. Babu abinda
yake yawo a zuciyarsa irin tsantsar nadama da kyamar irin abubuwan da ya aikata a baya.
Ba zai iya nuna abu guda daya da ya karu da shi a bariki ba, amma a yanxu zai iya nuna abubuwa fiye da
lissafin sa wadanda ya rasa a sanadiyyar bariki. Bayan his relationship with God, babban abinda yafi
damunsa a cikin abubuwan da ya rasa shine iyayensa. They have been the light of his life tun sanda ya
bude idon sa ya ganshi a duniya amma yanzu ba zai iya daga ido ya kalle su ba, ba zai iya zama a kusa da
su ba, ba zai iya yi musu magana ba, ya tabbatar da ace ana musanyan ɗa to da tabbas zasu chanja shi
suyi disowning dinsa, gwara ma su bada shi a basu shinkafa yar hausa, ko babu komai sa dafa su ci su
kuma bayar sadaka su samu lada, shi kuwa fa? Menene zasu iya nunawa nashi wanda ya amfane su da
shi? In banda takaici da bakin ciki da tozarci da ...da ....da ....da?
Musamman Mama. Anya kuwa akwai uwar da ta taba nuna wa danta soyayya kamar yadda Mama ta
nuna masa? Anya kuwa akwai uwar da danta ya taba nuna mata mugun gani kamar wanda ya nuna
mata?
Duk sanda ya tuno last time da ya hada ido da mamansa sai yaji kamar ya makala igiya a jikin fanka ya
rataye kansa. Yo in ma ya zauna a duniyar menene amfanin sa? In kuma ya mutum wanene zaiyi kewar
sa? Iyayensa kam ya san mutuwar sa will be a good riddance to them, matarsa ma haka, watakila
yayansa zasu yi kewarsa a yanzu tunda basu da hankali basu san ko waye shi ba amma ya tabbatar idan
suka girma suka ji irin halinsa da abubuwan kunyar daya aikata zadu gode Allah daya mutu da wuri.
Musamman Yasmin. Idan Yasmin ta fahimci abinda ya faru da ita kuma ta san halinsa tabbas zata jingina
abinda ya faru da itan da cewa laifin sa ne, and she will never forgive him kamar yadda her life will never
be the same again.
Ya runtse idonsa hawaye masu zafi suka zubo kan kuncinsa. He had a good life, good parents, excellent
wife, excellent everything, amma ya tattara a zuba ruwa a kansu ya watsar a rariya. And now he is
paying for his sins na duniya kadai. Na lahira kuma yana can yana jiransa. All for a few minutes pleasure.
Forbidden pleasures.
Ya juya kansa yana kallon wayar sa da take kara a gefensa, through the blurry vision na idonsa ya karanta
sunan Baffa Halilu. Waliyyin sa. Ya matsa fatar idon hawayen cikin su ya zubo, vision dinsa ya zama clear
ya dauki wayar yana jin zuciyarsa tana gitsitstsirewa a kirjin sa, ya san kwanan zancen, last thing da ya
rage masa najin dadi a rayuwarsa za'a karba. Aurensa.
Sai da kiran ya kusa katsewa sannan ya dauka ya saka a kunnensa ya danyi gyaran murya sannan yayi
sallama. Ba tare da baffan ya amsa sallamar sa ba yace "Faruq ka zo ina neman ka. Yanzu" bai jira ya
amsa ba kuma ya katse kiran.
Umar ya ajiye wayar sannan ya sake jingina kansa a jikin bangon dayake bayansa "innalillahi wa inna
ilaihir rajiun" na ambata a hankali. "Ya Allah!" Sai kuma ya kasa addu'ar, to mai zai ce? Shi kam yana da
bakin yiwa Ubangijin sa magana ne? Ya tuno da maganar Jidda ranar dazata bar gidan sa.
"Wanne Allahn kake rantsewa dashi? Allahn da kake sabawa a duk lokacin daka samu dama?"
Sai yaji wata irin kunya ta rufe shi, kunyar Ubangijin sa, ya tono da munanan abubuwan da ya yi ta
aikatawa ya kuma tuna da cewa duk lokacin da yake aikatawar ubangiji yana kallon sa. Ya tuno da
maganar Jidda
"Ka manta cewa akwai ranar da za'a saka maka rayuwar ka a gaban kowa kamar a TV kowa ya gani?"
Ya tuna cewa Mama ta riga ta ga wani bangare na cikin rayuwar ta sa and ganin da tayi masa is the worst
thing that has ever happened to him. To Ubangijin sa fa da yake gani kullum? Da yasan komai?
Ya dafa bango ya mike tsaye tare da dafe kirjinsa ɓangaren hagu da hannunsa na dama. Ya rufe idonsa
yana jin yadda zuciyarsa take yi kamar zata fito daga ma'ajiyar ta. Sai da ta lafa masa sannan ya mike
straight ya fara neman key din motarsa, bai taba tunanin Jidda zata yi irin wannan taurin kan akan
wannan maganar ba, they have been through worst cases than wannan na karshen kuma duk tayi hakuri
soyayyar da take masa tayi prevailing amma wannan ta rikide ta koma wata halitta ta daban ba jiddan da
ya sani ba and the last time he saw her, the last time they talked, ranar da ya aikata abin da ya aikata har
Mama ta ganshi, a ranar ya gani a idon Jidda cewa da gaske take maganar da take fada. She is done with
him.
Sai dai baiji haushinta ba. Tabbas tayi masa kokarin da baya jin zai samu matar da zata yi masa irin sa,
tayiasa soyayyar da baya jin zai samu wadda zata yi masa irin ta, tabbas yayi asarar da ba zai taba
mayarwa ba. And that's what hurt him the most a cikin maganar su.
Direct gidan baffansa ya nufa not minding kayan da suke jikin sa da kuma the fact that jikinsa bai ga
ruwa da sunan wanka ba ballantana turare, ya riga ya san maganar da zai tarar a can din, ya san Abba ne
ya kira baffan ya gaya masa halin da ake ciki kuma ya nemi ya karbar