Chapter 5 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   5 / 101

12K to 15K   out of 300.2K words

ita.



Yayansa Bakwai, Yaya Mubaraka itace babba, sai Umar Faruq, sai Muhibbat, Muhsina, sannan Mufida
auta a gurin mahaifiyarsu Hajiya Maimunatu da suke kira da Mama, sai kuma twins din amaryar Alhaji
Afnan da Affan.
Umar Faruq kyakykyawan saurayi ne da yake ji da kansa a fannin kudi, ilimi, gata, asali, background mai
kyau da kuma uwa uba kyau. Bafulatani ne shi ta bangaren uwa da uba baki daya, kuma matsayin da
yake dashi na babban da na Alhaji Mahmud ya saka iyayen suka dage wajen ganin sun bashi ilimi mai
kyau har xuwa matsayin cikakken likita, wanda ya samu a cikin wannan shekarar, sannan kuma suka
dora shi akan son kannensa tare da fatan ko babu ransu shi din zai zama mai rike yanuwansa ya zame
musu uwa da uba.



Sun kuma yi nasara, dan Umar ya samu duk abinda suke so ya samu, sannan kuma yana tsananin son
yanuwan nasa kamar yadda suka yi fata. Dan tun yanzu da yake a matsayin matashi kuma suke still da
ransu da lafiyar su a duniya ya riga ya karbe kuma ya tsaya akan dukkan al'amuran da suka shafi
yanuwan sa, dasu kansu ma, wannan abin shi ne ya sake polishing tauraruwar sa a idon mahaifan sa tare
da dukkan sauran wadanda suka san shi.



Ba iyayen Umar ba hatta yan'uwa, makota, da abokan arziki suna yabawa da halayyar sa musamman
yadda yake faran faran da mutane da kuma yadda yake girmama manya. Sukan yiwa ƴaƴansu fada da
cewa "me yasa ba zaka zama kamar Umar Fata ba? Yaron kirki mai ganin girman mutane, shi ko yar
sigarin nan ma ta matasa shi baya sha"



Abu daya ya rage wa Umar yazama perfect son, shine aure.....




******************************************




Ina ta tunanin mafita a kan sabuwar rayuwa da zan fuskanta a haka har muka je gida



Gidan mu yana nan a unguwar gandun albasa dake garin Kano. Gaban gidan railer ne doguwa tun daga
farkon gidan har karshe. A cikin ta ne Abba yake ajiye motar sa tunda bashi da garage. Idan ka shiga cikin
ta akwai kofa biyu, daya double door ce wadda zata shiga da kai cikin sitting room din Abba, a nan ne
yake zama da bakin sa anan ne kuma duk wani bako namiji yake sauka, a cikin sitting room din akwai
dakuna guda biyu da kuma toilet, a dakunan samarin gidan suke zaune duk da dai yanzu tun bayan bikin
yaya Muntari saura su uku, Tahir, Muslim, da Abbah.



Sannan a cikin railer da akwai karamar kofa wadda zata shiga da kai cikin corridor shi kuma zai shiga da
kai tsakar gida, tsakar gidan bashi da girma sosai, kana shiga dakuna biyu ne suke facing dinka, ɗakunan
Hajiya da Umma, kowacce ciki da falo madaidaita, sai kuma dogon filin da muke cewa ventilation a
bayan dakunan nasu inda anan ne muke shanya kayan wankin mu. Kowacce tana da toilet a cikin falon
ta.



Sai kuma daki daya daga barin hagu wanda shine dakin yammata, Farhan ce kadai a ciki yanzu sai ni da
nake da niyyar zama tare da ita. A barin dama kuma kitchen ne, sai kuma toilet din tsakar gida a kusa da
kofar shigowa.



A gaban toilet din benen Abba ne wanda ya hau zuwa saman dakunan su Umma. Shima ciki da falo neda
kuma katuwar baranda da yake zama mostly da yamma har zuwa dare, lokacin zafi ma anan yake kwana.
Da azumi ma anan yake shan ruwa.......



Da damuwa a raina na shiga gidan mu, sai dai ina shiga ganin ummata ya wanke duk wasu traces na
bacin rai da suke cikin rai na, naji zuciyata tayi fari kal, naji cewa kowanne problem ma mai sauki ne ashe
in dai har kana da uwa a duniya, ko bata yi maka maganin sa ba ganin ta kawai ya isa ya warkar da
dukkan damuwa.



Abinci mai rai da lafiya na tarar an shirya min, shinkafa da miyar kifi da salad kamar yadda nake so,
Farhan tayi min dan malele da manja da yaji da tumatir da albasa. Ga kuma sobo mai sanyi an hada min.
Sai ma na rasa wanda zanci ina ganin kamar sunyi min yawa amma dana faraci sai na lura ashe akwai
yunwa sosai a tare da ni, musamman da Farhan da Amira suka saka hannu sai mukayi ta zurawa muna
hira har bamu san mun cinye ba.



Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din



0779484494

Nafisa Tafida Usman
Access Bank



Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp

08067081020



Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020



Please banda kira, WhatsApp only




*💔 Jidda 💔*



*By*



*Maman Maama*



*Episode Four : Musa*



Bayan mun gama ne naje nayi wanka na chanja kaya zuwa atamfa riga da skirt da dankwali, suna ta
yabawa da sabon kitsona ni kuma ina complain din zafi yake min, sai Umma ta ce inje in gaishe da Hajiya
sannan in shiga makota duk in gaishe su kafin Abba ya dawo.



A dakin Hajiya na tarar da ita tare da Mammy babbar yar mama Sa'a, lokacin sunyi Junior candy shine
tazo zata kwana biyu a gidan.
Na gaishe da Hajiya, ta amsa babu yabo babu fallasa "an gama jarabawa ko? Allah ya bada sa'a. Saura
aure kuma ko? Sai dai ke naga kamar har yanzu babu wani tsayayye, to Allah yayi zabin alkhairi"



Farhan da take zaune a kan hannun kujerar da nake kai tace "ameen" tana kallo na da dariya, ni kuma
na harare ta cikin wasa. Hajiya ta kalle ta tace "ke kam dai ai na roki baban ku ya bar min ke kiyi
makarantar nan dai kema, kuma insha Allahu Allah zai dora ni a kansa tunda dai ke ce auta ai ba zai hana
ba, ballantana yadda kike da kokarin nan dan Alhaji Kabiru ya gaya min ana saka ran zaki ci jarabawa
sosai".



Farhan tace "insha Allah zan ci Hajiya. Kuyi tayi mana addu'a ni da Jidda mu tafi jami'a tare" Hajiya ta
rike baki "Jidda kuma? Ke ma kinsan Jidda aure za'a yi mata musamman yadda tayi girman nan haka. Ita
ma umman ta ai zata so taga nata jikokin tunda a kanta zata fara samu, su zo suyi ta danne ta itama" ta
karasa tana ture Mammy da ta dora kanta akan cinyarta tana danne danne a yar karamar wayar da take
hannunta.



Muka yi dariya gabaki daya, ta mike zaune tana bata rai sannan ta kalle ni sama sama tace "sannu da
zuwa. An gama school. Congratulations" "thank you" nima na bata amsa a takaice. In da sabo na saba da
rashin kunyar Mammy amma bana taba kulata saboda gudun karin raini a tsakanin mu.



Farhan ta karbe wayar hannun Mammy "marar kunya. Bani inga abinda kike aikatawa a wayar. Haka
kawai mu manyan yammata ba'a bamu waya ba sai ke yar ficiciya da ke, wani in ya gani sai ya dauka
ubanki wani abu ne a Kano" ta fada tana duba screen din yar karamar wayar data karba daga hannun
Mammy. Ina kallon Hajiya tana hararar Farhan a fakaice, dan babu abinda ta tsana irin a fadi aibun wani
nata a gaban mu ko wani wanda ya shafe mu, kullum nunawa take yi tamkar yayanta sunfi kowa komai
bayan mun san ba haka bane ba.



Dariyar da Farhan tayi ce ta dawo da hankalin mu kanta, ta nuna min wayar "kinga, wai facebook take yi,
dan Allah ji wani hoto da ta saka ita a dole yammata ce" na karba ina kallo, taci kwalliya an sha jambaki
da uban gilashi, ga maza nan sun dage sai comment suke yi mata "WOW" "wow" "wow" sai kace wata
jiniyar motar asibiti. Na rike baki nima ina dariya. Ta taso ta warce wayarta daga hannuna tana kunkuni
ta shige cikin daki.



Farhan tace "kar dai ki zage mu, marar kunya, kin san ni yanzu sai in fasa miki baki wallahi, kuma wannan
hoton kamar a kunnen uwarki, gwara tasan me kike yi da wayar". Ganin Hajiya har yanzu tana ta harare
harare yasa na mike tare da cewa "bara inje in gaishe da Abba naji kamar ya shigo" tace "okay, wannan
maganar sai kin tashi mayi" nayi murmushi, tatsuniyar gizo dai bata wuce ta koki, ba zai wuce zancen
wani sabon saurayi ba ko something like that. Tun muna yra Farhan ce yar soyayyar cikin mu, kullum
zancen ta baya wuce na samari ko aure ko wani abu mai kama da haka.



Ina fita na tsaya ina kallon saman Abba, kofar falon sa a bude take nasan yana ciki amma gabana
faduwa kawai yake yi dan ban san da wadda zai tarye ni ba. Haka muke ni da Farhan kullum fargabar
zuwa gaishe shi da safe muke yi, in mun tafi a hanya kuwa munyi ta tunani ko akwai wani laifi da mukayi
wanda ba'a yi mana fada a kansa ba. In kuwa dama mun san munyi laifi har kirkirar ciwon karya muke yi
mu kwanta a daki mu ki zuwa gaishe shi amma har dakin ya kan biyo mu yayi mana fadan ko da kuwa
muna karkarwar zazzabi ne.



Nayi bismillah sannan na hau benen a hankali cikin nutsuwa naje kofar falon nayi sallama sannan na
saurara, daga can ciki naji ya amsa min. Na daga labule na shiga na ganshi a zaune akan kujera da table a
gabansa da takardu a kan table din, da alama aikin makaranta ne ya taho da shi gida. Na dan karasa
gabansa kadan na durkusa na gaishe shi. Ya dago kai yana kallona yace "Hauwa'u an dawo gida ko? Ya
jarabawar taku?" Na danyi murmushi "alhamdulillah Abba" yace "good, Allah ya bada sa'a. Kuka ya kare
ko?" Na sake murmushi bance komai ba sai ya kuma mayar da hankalinsa kan takardun gabansa.



Hakan yasa nayi yunkurin mikewa ina jin dadin ba'a yi min fadan komai ba, sai naji yace "dakata tukuna"
gaba na ya fadi amma automatically na koma na zauna ina jiran me zai ce sai ya fara magana.



"To alhamdulillah. Kin kammala secondary school dinki. Allah yayi miki albarka"



Nace "ameen"



Ya cigaba "zan so ace kin cigaba da karatun ki har ki zama wata aba a rayuwa, amma kuma zan so ace
kinyi hakan ne a gidan mijinki ba'a gidan nan ba. Saboda haka nayi wa yanuwanki kuma kema haka zanyi
miki. Kai ko da ba haka nayi musu ba ke hakan zanyi miki saboda idanuwan mutane sunfi yawa a kanki a
kan akan su. Wannan idon na jama'a shine dalilin da yasa ban matsa akan sai na samo miki makarantar
day kamar yaruwarki ba, saboda na fahimci cewa tafiyar ki makarantar kwana shi zaifi kwantar min da
hankali a kanki,ba ruwa na da tunanin ina kike ko tare da wa kike me kuma yake gaya miki. Abinda yasa
nafi damuwa da ke akan yaruwar ki saboda banbancin halitta da yake tsakanin ke da sauran mutanen
mu, zaki fi jan hankalin mutane musamman maza saboda suna ganin ki daban da sauran mata."
To yanzu kuma gashi kin gama kin dawo, kin kara komai da zai ja hankali kanki ɗin, amma kuma ina
tunanin kin kara hankali. Wannan yasa nake miki wannan maganar. Ba wai ina gaya miki ki fito da miji
inyi miki aure ne ba a'a ina gaya miki na baki iznin yin samari, kuma hakan da na fada ba wai yana nufin
na baki izni kiyi ta kula ko waye yayi miki magana a hanya ba, duk wanda yayi miki magana cewa yana so
ya nemi auren ki to ki turo min shi gurina first in fara ganin sa in san ko shi waye sannan in bashi iznin
fara neman ki ko kuma in naga bashi da nagarta in hana shi, kar ki yarda in ganki tare da wani wanda ban
san da zamansa ba, kar ki yarda in ganki tare da wanda na hana ki ganin sa. Idan lokacin da nake son yi
miki aure yayi zan gaya miki ki fitar a cikin wadanda suke zuwa gurin ki. In kin bi abinda nace zamu dai
dai ta in kuma baki bi ba to zamu bata ni da ke"



Na gyada kai da sauri a raina ina lissafin abinda yake nufi da batawar, na dauka ya gama sai kuma naji
yace "kinsan yaron nan Musa?" Na daga kai ina kallon sa, sannan nace cikin rashin fahimta "wanne?"
Yace "dan gidan Malam Magaji na bakin layin nan" na fahimci wanne Musa yake nufi, yayan kawar mu
Sakina, tabbas na san shi ina ganin sa a hanya ko kuma in mun shiga gidan su ni da Farhan mun biya wa
Sakina zuwa islamiyya.



Na gyada kai kirjina yana bugawa nace "na san shi Abba" yace "good, yaron kirki ne mai girmama
mutane da addini, wani lokacin ma shi yake kiran sallah a masallacin mu idan ladan baya kusa. Satin
daya gabata Malam Magaji ya same ni ya gaya min cewa Musa ya aiko shi ya gaya min yana son a bashi
iznin neman auren ki"



Na dago kai da sauri ina girgiza kai, yace "ba cewa nayi na bashi ba, duk yayana mata babu wadda nayi
wa auren dole kuma kema ba zanyi miki ba, na bashi izni zai ke zuwa wajen ki, idan kun daidaita to
shikenan idan kuma baku daidaita ba kuma Allah ya kawo wani nagari sai muyi masa fatan alkhairi"



Nayi ajjiyar zuciya ina jin sanyi a raina, lallai ma wannan musan, ko a fuska bai taba nuna min wani abu
ba, babu abinda yake hada mu sai gaisuwa a hanya in mun hadu ko a gidan su, gaisuwar ma wani lokacin
Farhan ce take yi ni sai inyi kamar ban gan shi ba.



Daga haka Abba ya sallame ni na taso ina jin wani iri a raina har na fara saukowa daga stairs sai kuma na
tsaya ina murmushi ni kadai, tabbas na samu hanyar gane gaskiyar magana akan Umar, in dai har ya
kuma dawowa gurina zan gaya masa yaje yaga Abba, in dai ba da gaske yake ba nasan zai gudu, in kuma
da gaske yake to shikenan ni na huta da neman wasu samari kuma, dan na riga na gani na yaba kuma na
gamsu.



Sai dai kuma da dare bayan mun kammala komai munyi shirin kwanciya sannan na zayyanawa Farhan
labarin Umar, yadda muka hadu da yadda nake ji a zuciya ta game da shi, abinda ya gaya min shima da
kuma yadda mukayi da Mufida. Sai kuma na bata labarin abinda Abba yace min da shawarar dana yanke
akan Umar. "Kinga in ba da gaske yake ba sai yayi tafiyar sa kawai"



Sai kawai naga tayi dariya, na tsaya ina kallon ta dan ni banga abin dariya a cikin magana ta ba, sai da ta
gama dariyar ta sannan tace "lallai Jidda kin tabbata yar boarding school wadda bata san abinda yake
faruwa a cikin gari ba. Ai in dai dan yaudarar ne kamar yadda kanwarsa uwa daya uba daya ta fada to
kuwa zuwa gurin Abba ba zai hana shi yaudarar ki ba. Rikakkun yan yaudara su kan kawo kudin aure ma
kuma har zuciyarsu ba da gaske suke ba. Ke dai kawai muyi ta addu'a muna neman zabin Allah tare da
neman tsari daga hatsabibai kuma mugayen samari"



Nayi tagumi da hannu daya ina kallon ta, ina jin duk farin ciki na na samun solution yana tafiya. Ta dan
baya rai "ke ni har cikin raina ma sai naji bai yi min ba duk da ban ganshi ba. Yadda kike tsara shi sai nake
ganin kamar kinyi masa kankanta, irin su manyan yammata suke so wayayyu yan jami'a"



I was so into my problem har na manta da maganar da tun ina makaranta take cewa zata gaya min. Sai
da ta tuna min "baki tambaye ni labarin da zan baki ba?" Na juya barin da take ina kallon ta, sai naji
kunyar mantawar da nayi, nace "okay, ina ji. Bani labarin new catch din" tayi murmushi mai sautin da ya
saka nan take na fahimci cewa ita ma duk a cikin jirgin da nake a nan take ita ma, jirgin soyayya.



"Kinga, sunan sa Sulaiman, lokacin da muna waec shine yake mana invigilation, to shine fa ranar nan
mun taso na fito neman mota zan taho gida sai gashi yazo wucewa shine ya dauko ni"



Na bude ido "a motarsa? Baki ji tsoro ba? Da Abba ya gan ku fa?" Tayi murmushi "nima naji tsoro ai, but
kawai na daure, kuma dai rabon zamu dai dai ta ne. That was how it started" na dan dake ta kadan ina
dariya "to a ina zata yi ending?" Ta juya ido "a inda zaku yi ending ke da Umar din ki" na dauki pillow na
na doke ta ita ma ta dauki nata ta rama, muka yi tayi sai da muka gaji dan kanmu sannan muka kwanta
muna haki, sai kuma muka cigaba da hira, planning our lives, but Allah shine the greatest of planners duk
namu tatsuniya ne.
Kwana na biyar a gida, a cikin kwana biyar din nan Sulaiman yazo, dama already ya samu amincewar
Abba, kuma naje mun gaisa da shi ya kuma kwanta min a rai, mutum ne mai faran faran da wasa da
dariya.



Malamin makaranta ne shima kamar Abba, sai dai bai kai Abba dadewa a system din ba kuma bai kai
Abba matsayi ba. Kuma daga ganinsa ba karami bane ba sai dai yana da karamin jiki kuma yana da kyau
dai dai gwargwado da saurin shiga zuciya and I didn't blame Farhan for falling for him.



A daya bangaren kuma tunda na dawo gida kullum idan wayar Umma tayi kara sai inyi sauri in duba, a
raina ina tunanin ko Umar ne, dan nasan a gurin Mufida zai nemi hanyar samuna kuma nasan number
din Umma take da ita. Sai dai the call never came through.



Haka zalika a duk lokacin da naji yaro yayi sallama sai inyi tunanin ko za'a ce ana sallama da Jidda ne
amma shiru. Sai a ranar da nayi five days a gida ne aka aiko kira na



"Salamu alaikum, wai ana sallama da Jidda" na dago kai daga karatun littafin hausan da nake yi ina kallon
Umma, ita ma ni take kalla, sai muka ji Hajiya ta amsa wa yaron tare da cewa yaje ya tambayo waye mai
sallamar. Na mike zaune ina wasa da band din hannuna. Zuciya ta tana bugawa da tsananin karfi a kirjina
har naji motsin yaron ya dawo yace "wai inji Musa" naji zuciyarta tsaya da bugawar da take yi sai kuma
hawaye ya taho zuwa idona. Nayi saurin tsayar dasu tare da sunkuyar da kaina kasa dan kar Umma ta ga
kuka na.



Bata ce min komai ba sai ga Hajiya ta zo ta daga labule, Jidda ana kira a waje, ko ace masa ba zaki zo ba?
In ba kya son zuwa sai ace masa ba kya nan shikenan"



Umma tace "tana zuwa, mai zai hana ta zuwa?" Hajiya ta saki labulen tare da cewa "wai da" na mike na
shiga cikin daki na zauna a bakin gado, ni dai har ga Allah bana

5 / 101