Chapter 52 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   52 / 101

153K to 156K   out of 300.2K words

and still have it. He is sooo selfish. Ki fita ki bar masa gidan sa ai ba anan
ne kadai zaki cigaba da rayuwa ba, idan kin bar gidan sa ba mutuwa zaki yi ba. Idan kin zauna ne ma zaki
mutu dan na tabbatar in dai baki bar gidan nan ba wannan mutumin sai ya kashe ki an fitar da gawarki"



Nace "Farhan ina zan je in na fita? Ina zanje Farhan? Kin fi kowa sanin halin Abba kin san babu yadda
zanyi in je gidan mu da sunan yaji, Abba kora ta zaiyi, ko kuma ma yayi min mugun baki, ba zai tsaya ya
saurare ni ba, Umma ba zata iya yi min komai ba sai dai ta dora damuwa ita ma a ranta har ta samu
hawan jinin da za'a bata gado a kusa da nawa. Bayan gidan mu kuma ina zanje?"



Tace "try. At least try. Ki gwada zuwa gidan ki gwada yi wa Abba bayani watakila ya fahimta, with Abba
you can't really tell, sai kin gwada tukunna" na goge hawaye na nace "abinda zanyi kenan Farhan. Na
riga nayi wa kaina alkawarin the next time da zan kama Umar da irin wannan laifin to zanje gidan, zuwa
gidan mu shine next step dina kuma zanyi. Bana fatan zuwan ranar saboda bana fatan sake kama Umar
da laifi mai kama da wannan, amma in ya sake, in na saka kamashi tabbas zan je gida Farhan. Ban san
me zan tarar a gidan ba amma nasan zanje insha Allah"



Ta gyada kai tana share nata hawayen "yanzu Jidda in dai har Umar duk da son da yake miki da kuma
son da kike masa, duk da kyan da Allah ya baki, duk da yadda kike kokarin kula dashi shima yake kula da
ke, duk da yayan da kika haifa masa, in dai har zai iya yi miki haka then who is safe kuma a wannan
zamani?"



Nace "ba haka bane ba Farhan, abin ba'a soyayya bane ba ko kyau ko wani abu, abin a hali yake, sai ki ga
kuma wadda mijin baya sonta kuma baya bata kulawa kuma bata da wani kyau amma mijinta baya
neman mata. Haline kuma kaddara ce, ba gazawa bace ba daga matar"



Ina ma ace matan waje na banza zasu fahimci cewa wannan namijin da yake zuwa gurin su suna alfasha,
watakila yana da matar da ta fi su komai, kuma tana iyakacin kokarin ta ba wai ta gaza bane ba, kuma
yana sonta fiye da tunanin su, maybe da sun daina daukan kansu da wani muhimmanci



Farhan bata yi kwana biyun da tayi min alkawari ba sai ta hada kayanta tace tafiya zata yi "bayan abinda
na sani, bana jin zan iya budewa Umar baki inyi masa dariya in yazo gidan nan, zan iya ambaton sunan
Mama in zaga, gwara in tafi tun kafin in kunno miki wuta a gidan ki" ta cigaba da hada kayan ta tana
mita. "Ni dama tun asalin Umar din nan ba son shi nake yi ba, ni dama tun farko bai yi min ba, he is just
too much, tun farkon gani na da shi yayi min kama da playboy, ashe ya wuce duk inda nayi tunani" ta
juyo tana kallona "ita kuma wannan mokadaddiyar Maryam din sai na karya wannan karkatacciyar kafar
tata duk ranar dana kuma ganin ta a kusa da ke"



Ni dai ban ce mata komai ba har ta gama hada kayanta sai na kira Umar na tambayeshi zanje in kaita
gida, yayi ta tambayar dalilin da yasa ta fasa kwana sai kawai nace masa Abba ne ya fasa barin ta, da
yake yasan halin Abba sai kawai ya bar maganar.
Bakuwa ta biyu da nayi kwana biyu bayan zuwan Farhan ita ce Surayya, matar Bashir. Rabon ta da tazo
gidana tun sanda nayi wa Bashir iyaka da gidan mu kuma nasan shine yake hanata zuwa, ni ma kuma tun
daga lokacin dama ban kuma zuwa gidan su ba sai dai mukan yi waya mu gaisa ko kuma mu gaisa ta
WhatsApp.



Ranar sai gata tirtsi tirtsi da ciki. Na tarye ta da fara'a da komai muka gaisa tace wai tazo sada zumuncin
da na tsinke a tsakanin mu. "Ko menene dalili?" Nayi dariya "kinji ki da wata magana, kawai dai yanzu ne
bana samun lokacin fita unguwa wallahi gabakidaya. Kafin mutum ya tashi ma ya gama aikin gida ga
yara, nan da nan sai kaga lokaci har ya tafi. Unguwa yanzu ai sai ku amare" na fada da sigar tsokana sai
naga bata wani yi dariya ba ta tabe baki "wa yaga amare, ke ma dai da tsokana kike wallahi" nace "as
long as baki haihu ba, amarya ce ke. Ni kuwa fa? Na gama zama cus"



Sai tayi shiru kawai. Muna tare Umar ya fito daga daki, da yake ranar bai fita ba tun safe yana daki shi da
Asad, suka gaisa sama sama, yana acting kamar ma bai gane ta ba sai ya dauki Asad yace zasu je unguwa,
na raka shi bakin kofa yace "cook something delicious kafin mu dawo, in akwai abinda kuke bukata sai ki
kira ni ki gaya min in taho dashi, zan biya in dauko Yasmin daga school ba sai kin fita ba. Ki huta sosai kiyi
bacci. I love you, bye" sai yayi kissing cheek dina daya.



Naji kunya saboda bakuwar da take gurin kuma nasan in dai tana kallon mu ta gani, sai nayi kissing Asad
ni kuma sannan nace "a dawo lfy" suka fita ni kuma na dawo gurin bakuwa ta na zauna sai tace "Jidda
kinji dadin ki ke kam" nayi murmushi "dadin me naji?" Ta sunkuyar da kanta yana yin ta yana nuna
zuciyarta babu dadi "ni har mamaki nake yi in naga maza suna yiwa matansu magana irin haka. Sai inyi ta
sha'awa ince ko yaushe ni ma turn dina zai zo? Ko yaushe Bashir zai kalle ni irin yadda naga Umar yana
kallon ki?"



Na girgiza mata kai nace "wannan fa duk ba shine zaman lafiya ba Surayya. Halayyar kowa daban. Zaki ga
wani mijin vaya sakar wa matarsa fuska irin haka amma hakan ba yana nufin wai baya sonta bane ba ko
kuma basa jin dadin zama da juna ba, a'a halayyar sa ce haka"



Ta dago kai tana kallona kamar mai shirya maganar ta sannan tace "akwai kuma wadanda basa sakin
fuskar, basa sakin aljihu, sannan kuma ga mummunar halayya mai cike da cutarwa ga iyalin su" na danyi
shiru nima ina jera tawa maganar sannan nace "hakan kuma ba yana nufin su wadanda ake sakarwa
fuskar suna cikin jin dadi bane ba. Za'a iya yin mamaki sosai idan aka san halin da suke ciki a sirrance.
Watakila akwai abinda yake cin su ta ciki wanda ko da zasu furta ba lallai ne a fahimta ba" ta kama
hannuna a natada naji shi da zafi "kin sani kenan Jidda? Kin san halayyar mazajen mu?" Na dago ina
kallon ta, sai naji sanyi a raina, at least na samu wadda take fuskantar the same kalubale irin nawa,
wadda na tabbatar zata fi kowa fahimta ta.



Na gyada kai "na sani Surayya, na sani tun ina amarya, tun kafin in haifi Yasmin" ta rufe baki da hannun
ta, idonta yana kawo kwalla, "amma kullum kallon ki nake yi kamar hankalin ki a kwance yake, kamar
vaki da wata matsala shi yasa ban taba ko da yunkurin gaya miki ba dan kar in tarwatsa farin cikin ki"
nace "wani lokacin ba lallai ne abinda idon mu yake gane mana ya kasance shine gaskiya ba. Kowa da
akwai battle din da yake fighting a rayuwarsa, ni na saka a raina wannan shine nawa kaddarar"



Ta girgiza kai "amma taki kaddarar da sauki Jidda, taki rayuwar da sauki sosai dan zan iya cewa ke a
aljanna kike idan nayi comparing da kaina. Bansan yadda yanayin muamalar auratayyar ku take ba amma
na tabbatar Umar yana baki kulawa kuma yana baki lokacin sa, ni kuwa fa? Jidda ko kallo ban ishi Bashir
ba. Bashir ya kanyi sati biyu zuwa uku ba tare da ya bukace ni ba. Tsakani na dashi shine ya ajiye min
kayan abinci ni kuma in zauna a gida in kuma amsa sunan matarsa"



"Jidda ban san ya kuke da Umar ba amma nasan yana gudun bacin ranki, yana kokarin boye miki
halayyar sa, amma Bashir a fili yake abinsa babu ruwan sa da in gani ko kar in gani, babu ruwan sa da me
zanyi in na gani, in ma zuciya zan hadiya in mutu shi babu ruwansa shi dai rayuwarsa kawai yake yi
tamkar wanda bai yarda cewa akwai mutuwa kuma akwai hisabi ba"



"Babu irin chats dinsa da bana gani tare da mata, su tura masa hotunan tsiraicin su ya tura musu nasa,
wayarsa da laptop dinsa a cike suke tap da pornography, kuma babu ruwansa da wai zan dauka in gani
babu abinda ya dame shi. In na bishi daki ma na nuna ina bukatar sa zai iya tashi ya fito falo yayi
kwanciyar sa yana sexting mata har yayi releasing kuma ya ajiye min wandon sa in wanke"



Na toshe kunne na ina taya ta kukan da take yi "ya isa Surayya ya isa, wannan wanne irin tashin hankali
ne muke ciki? Ya zamu yi da rayuwar mu ne wai?" Tace "na gaya wa iyaye na, har shaida na dauka daga
wayarsa na nuna musu cewa ga abinda yake yi amma sai suka ce me yasa na taba wayarsa? Ina ruwa na
da abinda yake yi a wayarsa ai ni na jawo wa kaina bakin ciki tunda na duba masa waya. Wai ai kazantar
da baka gani ba tsafta ce. Suka kuma kara da cewa zan bata zumunci, auren da aka yi dan a karfafa
zumunci ni kuma zan bata shi. Sun dai ce sun kira shi sunyi masa fada amma ni banga chanjin komai ba,
sai ma masifa da yayi min wai zan hada shi da mutane zan zubar masa da mutuncinsa. Daga nan kuma ya
cigaba da kara daure min fuska. Yanzu nace gurin iyayensa zanje kuma in gwada can in gani"
Nayi saurin girgiza mata kai "don't try that. Ni ta can na fara kuma hanyar bata bille da ni ba sai ma kuma
afkawa cikin matsala da nayi" tace "to ya zamuyi kenan? Wacce hanya zamu bi? Wacce ce mai bullewar?
And the society and our families expects us to be good and obedient wives to such husbands. Abinda
ake so muyi shine muyi ta hakuri, muyi musu ladabi da biyayya, sannan muyi ta addu'a. Mu daina bincike
akan su ballantana muga kazantar da bamu san da ita ba, sannan kuma in mun sani ma kar mu nuna
musu bacin ran mu mu danne zuciyar mu, wata rana zasu daina. What a selfish society! Amma kuma a
tsakanin iyayen mu ko nasu ko kuma a cikin society din da wahala a samu wanda zai zaunar dasu ya
nuna musu cewa abinda suke yi ba dai dai bane ba sannan kuma ya gaya musu su zama good husbands
to us"



What a selfish life!



Mun jima muna wannan hirar da ita, a cikin hirar ne take sanar min da cewa farkon samda ta fara gane
halayyar mijinta sai ya nuna mata laifin Umar ne, yace Umar ne ya koya masa kuma shi yake gada shi da
mata tun a jami'a. Sai ni kuma nace mata "ba zan ce Umar ne yake koyawa Bashir ba, kamar yadda ba
zan ce Bashir ne ya koya wa Umar ba, abinda kawai nasani shine kowa a cikin su halinsa ne sai kuma
suka hadu suke abota. Ni a bangare na abinda nayi shine nace wa Umar ya rabu da Bashir, though ban
tabbatar ya rabu da shi ko bai rabu da shi ba amma ni da shi bamu kuma yin hirar Bashir ba har yau. Ke
ma a naki bangaren kiyi mana kokarin ganin kin matsawa Bashir ya rabu da Umar"



Ta rike baki "rufa min asiri, ni na isa ince da Bashir ga abokin da zai kula ga wanda ba zai kula ba? Kamar
yadda na gaya miki, ba kowanne miji ne irin naki ba dan haka you should cherish what you have".



Tana gidan har su Umar suka dawo tare da yara gabakidaya, sai kuma tace zata tafi ni kuma naji tausayin
ta ga tsohon ciki kuma nasan wannan mijin nata ba zuwa zaiyi ya dauke ta ba, sai na roki Umar ya barni
na kai ta har gida a mota ta. A motar ma sai da tayi comment "ki duba kiga motar ki Jidda, amma ni in
samu arzikin da zai dauke ni a tasa motar ma abu ya gagara"



A hanya ina dawowa sai na fara lissafa rayuwar Surayya da tawa, sai na fara tunanin tabbas kamar yadda
ta fada a gurinta ni kamar a aljanna nake, in ana jin irin nata complain din bama za'a saurari nawa ba.
Kuma at least ni na zaba wa kaina Umar, ita kuwa zaba mata Bashir aka yi, maybe ma da akwai wanda
take so aka hana shi aka bawa dan uwa dan a karfafa zumunci.
I felt blessed for some days bayan zuwanta, sai kuma bakuwa ta uku ta zo min ta kwance min dukkan
lissafi na.



Bakuwar itace Aira. Ta shigo min gida a firgice kamar wadda aka koro ta. Na tashi da sauri na rike ta ina
tambayarta abinda ya faru "Aira wani ne ya mutu? Wani abin ne ya faru?" Sai ta rungume ni ta saka
kuka. Nima na rungume ta ina jin kamar zanyi kukan duk da cewa ban san abinda take wa kukan ba.



Sai data gama ta dago sannan na zaunar da ita akan kujera na bata ruwa ta sha na kuma tambayar ta
"me ya faru Aira? Ke da waye? Waya sauke ki a mota?" Ta goge hawayen ta tace "Musaddiq ne" (wanda
aka saka ranar auren su) nace "fada kuka yi da Musaddiq din?" Ta girgiza kai "na raka shi kasuwa ne,
muna hada kayan lefe, shine......shine.....shine..... " Ta cigaba da kukan ta, gaba na ya fadi, kar dai wani
abin banza yayi mata a hanya, na shiga uku.



Nace "ki gaya min Aira mai Musaddiq din yayi miki?" Ta dakata da kukan ta "babu abinda yayi min Jidda,
mun shiga Well Care ne muna siyayya sai kawai na ga yana dariya, sai ya nuna min wasu wai ga wani
gara nan wata kilaki tana wanke shi, Jidda kin sa wa na gani?"



Ban amsa mata ba saboda yawun bakina da ya tsaya chak. "Jidda Daddy na na gani tare da wata da
kallon farko na tabbatar wa kaina da cewa karuwa ce. Ta sha attachment da muguwar shiga, tana kuma
makale da jikinsa suna ta raha da dariya" ta karasa tana cigaba da kukan ta



Naji kaina yayi wata irin sarawa. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Aira kin tabbatar da abinda kike fada?
Daddyn ki fa kika ce?" Tace "Jidda Daddy na ne wallahi. Musaddiq bai san fuskarsa ba tunda ba gurinsa
suka je neman aure na ba gurin auncle din mu suka je"



Ta dauko wayarta tana budewa tace "na daki idon Musaddiq na dauki hoton su. Wallahi sai na nuna wa
mommy ta ga abinda yake yi. Yanzu ni yaya zanyi da raina, yaya zan kalli Musaddiq idan ya fahimci
tsohon da ya gani da karuwa shine mahaifina? Jidda na shiga uku. Jidda fasa auren nan zanyi gabakidaya
dan na tabbatar wata rana sai ya goranta min. Kuma wallahi ina sonsa" ta karasa tana sake fashewa da
kuka.
Na karbi wayar daga hannun ta, wayar da kuka ya hana ta karasa budewa ballantana ta miko min, na
bude sannan na shiga gallery na nemo pictures din da tayi yanzu. Daddyn na dafa ganewa dan fuskarsa
ta fito fes yana ta washe baki, sai kuma na gane matar da take makale a jikinsa, Zuwaira.



Bazan taba mantawa da fuskar ta ba kamar yadda bazan taba mantawa da murmushin da yake kan
fuskarta ba, irin wanda take yi a cikin hotunan su data aiko min ita da Umar a Lagos. "Innalillahi wa inna
ilaihir rajiun" na sake ambata tare da ajjiye wayar.



"Kin gan su ko?" Aira ta fada "wallahi sai na nuna wa mommy" sai na mike batare da na ce mata komai
ba na shiga daki na zauna tare da rufe fuskata da hannu na. Na tuno maganganun Aunty Afia.



"Nima na taba shiga irin matsalar da kike ciki a yanzu Jidda, amma da nayi hakuri na kuma dage da
addu'a yanzu ba gashi komai ya wuce ba?"



Sai kuma na tuno da maganar daddyn Aira "ki bani sunan yarinyar, ni zanyi bincike akanta daga dabi'un
ta zan gane gaskiyar lamarin, sai mu san yadda za'a shawo kan maganar"



Binciken da har yanzu ba'a kammala ba.



Ashe ba bincike yake yi ba, ashe kansa ya samarwa sabuwar kamu......



Ashe bai daina ba kamar yadda Aunty Afia tayi tunani, ashe ya kara kwarewa ne kawai wajen boye mata
halin sa.......



Ashe role model din da nake bi har yanzu a cikin ruwa take tsundum bata sami fita ba ballantana ni da
nabi hanyar ta in samu fita ni ma.



Na tashi na koma falo na tsaya ina kallon Aira, ina tunanin abinda zan ce mata, sai kawai naga a idona ta
koma min Yasmin, Yasmin ta girma ta kama babanta in the act, me zance mata? Kiyi hakuri nima hakurin
nake tayi? Sai naji a raina tabbas wannan ranar tana nan zuwa indai abubuwa basu chanja ba.
Forgive the typos please..........

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din



0779484494

Nafisa Tafida Usman

Access Bank



Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp

08067081020



Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020



Please banda kira, WhatsApp only




*Wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar ki
sharing, in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*



*Mammy*



Na koma na zauna a kusa da ita sannan na dago kanta ina share mata hawayen ta. "Kiyi hakuri Aira. Kiyi
hakuri ki daina kuka dan Allah" tace "ni yanzu yaya zanyi? Yanzu Jidda ashe wai Daddy na ne yake da
wannan mummunar dabi'ar?" Na girgiza mata kai "kar ki ce haka Aira, Daddy ne fa, maybe ma ba abinda
kike tunani bane a tsakanin su da wannan matar maybe abokiyar aikinsa ce ko something like that" ta
girgiza kai da sauri, "baki gansu bane ba Jidda, baki ga matar nan ba kina ganin ta zaki san ko ita wacece
daga yanayin shigarta, kina ganin yadda suke yi zaki fahimci abinda yake tsakanin su" sai ta sake wani
sabon kukan. "wai babana. Jidda babana ne. Mutumin da duk mazan duniya babu wanda ya kai shi kima
da mutunci a idona, mutumin da har addu'a nake Allah ya bani miji kamarsa saboda yadda yake kula da
mu da mahaifiyar mu amma ashe da akwai abinda yake aikatawa a boye bamu sani ba. Shin anya ma
kuwa

52 / 101
Connection failed: SQLSTATE[HY000] [2002] Operation not permitted