Chapter 83 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   83 / 101

246K to 249K   out of 300.2K words

menene yayanta zai bawa wannan matar mai kama da karuwai,
amma kuma dakin dara fito daga ciki nan ya shiga ya dauko rigarsa, ma'ana daga nan ya fito babu riga
kenan, ma'ana..........



"Wallahi ba zan cika ka ba na gaya maka sai kabani kudina, ba Mama zaka kira ba ko Baba ne sai ka
sallame ni ko kuma su wadanda kake kira din su sallame ni tunda su suka haife ka bani ba ballantana in
dauki asara"
Ya juyo a zuciye da niyyar itama ya daki ya daki banza amma kuma har ya daga hannun sa sai kuma ya
sauke a ransa yana tambayar kansa menene laifin ta? Me tayi masa da zai dake ta? Tabbas duk da
kasancewar ta karuwa in ya dake ta yana da alhakin ta kuma Allah ba zai yafe masa ba harcsai ya nemi
gafarar ta ita kuma ta yafe masa, shi kuma a yanzu baya fatan abinda zai sake sakawa su hada hanya shi
da ita ma ballantana suyi magana.



Ya fara kokarin controlling kansa sannan ya dauko wayarsa yace "fado account number" ta sake cakumar
rigarsa. "Kutumar uba, ni zaka yiwa bura uba? Wallahi dama limcy tace min ranar nan da ka dauke ta
kace babu cash sai dai kayi mata transfer, har yau transfer din bata zo ba, to wallahi in ita ta kyale ni ba
zan kyale ba, wallahi sai na ............"



Murya suka ji daga bayan su.. muryar Mufida..,



"Nawa ne kudin naki?"



Ya rufe idonsa yana jin tamkar rufin dakin ne ya fado masa aka, yana jin ta tana gayawa Mufida sannan
yaji alamar lissafin kudi sannan kuma yaji ta saki rigarsa, bai juya ya kalle ta ba ballantana Mufida ya fita
yana jin cewa ita ma mufidan ba zai kuma iya kallon idonta ba.



Ya shiga cikin motar tare da juya wa baya inda ya kwantar da Mama yayi checking pulse dinta da yake jin
sa can ciki, ya dauke idonsa daga kanta yana tunanin duk duniya babu uwar da bata yi dacen da ba
kamar ta, duk duniya babu dan da ya ci mutuncin uwarsa kamar shi. Duk duniya babu wanda yayi asarar
rayuwa kamar yadda yayi asarar ta sa.



Ta dauko key din motar yana kokarin kunna ta amma karkarwar da hannun sa yake yi ya saka key din
faduwarsa biyu kafin ya samu ya shiga jikin motar. Sai kuma yaji an bude bayan motar an shiga, ya juya
suka hada ido da Mufida sai yayi sauri ya juyar da kansa tare da tayar da motar.



Mufida ta jawo Mama ta rungume ta tana sheshshekar kuka, shima Umar din kukan yake so yayi amma
ya kasa, burinsa a lokacin shine ya kai mahaifiyarsa asibiti mafi kusa wanda za'a bata taimakon gaggawa.
A haka suka fita daga gidan, fitar da Umar ya tabbatar har cikin zuciyarsa ita ce fitar sa ta karshe daga
gidan gonar, baya jin zai kuma bin koda hanyar gidan gonar ne ballantana ya kuma shiga ciki, sai dai ya
sani cewa ba zai taba goge memories din mummunar rayuwar sa a gidan ba.
Ya gyara mirror din motar yana kallon Mama ta ciki, a ransa yana fatan zata samu wani problem da zai
goge mata abinda ta gani daga kwakwalwar ta dan ya tabbatar bayan abinda ta gani rayuwarta ba zata
taba dawowa dai dai ba, kuma duk a dalilin sa.



Asibitin da ya kai Baba yau ma nan suka je, yayi packing sannan ya fita da sauri, ko minti biyu ba'a yi ba
suka dawo tare da nurses da kuma kujerar tura marar lafiya, suka fito da Mama da alokacin ta fara
dawowa hayyacin ta suka tura ta zuwa ciki, Mufida ta bisu a baya hesitantly tana waigen Umar tana
fatan shima zai taho tare da su amma sai taga ya tsaya a jikin motar sa yana bin su da kallo har suka
shige ciki, ya runtse idonsa tare da dafe kansa da hannu biyu, a ransa yana jin wannan shine gani na
karshe da zai yiwa mahaifiyarsa da kuma yaruwarsa, baya jin zai iya sake hada ido da su ko kuma duk
wani wanda ya shafe su.



Ya bude mota ya shiga sannan ya sake kokarin tayar da motar amma ya kasa, abinda ya faru ne kawai
yake ta replaying kansa a cikin kwakwalwar sa, ya girgiza kansa yafi sau a kirga amma kuma ya kasa
kawar da hoton abin a zuciyarsa. Gashi nan a kwance a saman mace, Maman sa kuma a tsaye a gabansu
idonta a kansu. Anya kuwa akwai wanda ya taba shiga irin halin sa ya ke ciki? Anya kuwa akwai masifar
da tafi wannan muni?



Da yasan abinda zai faru kenan da baiyi ba, to wai ma me ya saka shi yi ne? Shi da ya gama
sakankancewa cewa ya daina? Rabon sa da yi fa tun Jidda tana gidan sa, ya dauka da gaske ya daina, me
ya kai shi ya sake yi ne wai? Me ya kai shi?



Ya tuna sakon da Jidda ta tura masa yau da assuba cewa tana so ta ganshi, ya tuna da irin farin cikin da
sakon nata ya saka shi a ciki dan dama ya dade yana saia rai tare da zuba idon ganin sako kamar sa, ya
san cewa Jidda tana son sa, kuma soyayya tana tafiya tare da tausayi, wannan yasa yake zuwa unguwar
su kullum tare da fatan zata ganshi kuma taji tausayinshi.



Dan haka sanda ya samu sakonta, sanda ya kira ta ta dauka, ya dauka burinsa ne ya cika, ya daukar
soyayyar da take yi masa ce ta rinjayi fushin da take yi da shi, ya dauka tana son su sasanta ne ta dawo
gidan ta. Wannan yasa maganganun da tayi masa suka zama tamkar mari a fuskarsa ne ga zuciyarsa.
Sai dai kuma yanzu da yayi bitar maganganun na ta sai ya fahimci cewa gabakidaya gaskiya ne a cikin su,
amma sanda tana fada bai fahimta ba, lokacin kawai jin su yake tamkar bakaken maganganun ne ta ware
take gaya masa, cewa tafi karfin sa cewa shi mazinaci ne ita kuma mumina, cewa zata iya auren wani
bayan shi kuma ta zauna cikin farin ciki.



Wannan ya ingiza zuciyarsa zuwa ga aikata abinda a lokacin yake ganin idan yayi zai tabbatar wa kansa
da cewa shi ma zai iya rayuwa babu ita.



But now that everything is lost saboda abinda yayi sai ya fahimci cewa it is not worth it. Now that all his
life is lost sai ya fahimci cewa gabakidayan barikin ma is not worth it.



Ya lissafo dukkan rayuwar sa da mummunar harkar sa, all the forbidden pleasures da ya samu a cikin
harkar, just few minutes of pleasures, and now they have completely destroyed his life.



Kuma shi kansa ya san wannan abin da ya faru is just the beginning, the beginning of his torment a
duniya ka dai sannan ga eternal turture a lahira. Yace ba zai iya sake kallon mahaifiyar sa da yan'uwansa
ba, but what of Ubangijin sa? Mai zai ce masa ranar da ya tsayar da shi a gabansa ta tuhume shi da
laifuffukan sa? Bayan kuma ba rage shi da komai ba sannan ya bashi mata ta ke ce raina wadda ba kowa
ya bawa irinta ba.



Yanzu daya duba rayuwar barikin sa da kuma matan da zai iya tunowa wadanda yayi mu'amala dasu a
barikin sai yaga babu wadda za'a ita jera ta tare da matarsa a matsayi daya na kyawun halitta ballantana
kyawun zuciya, yanzu da yake duba abin sai ya fahimci he have never been truly satisfied sexually idan
ba da matarsa din ba, amma still yake komawa ya bita kudibsa ya sake yi, duk da cikin zuciyarsa ya sani
cewa masifa ce da bala'i yake siyawa kansa da kudin sa.



Gashi nan masifar ta fara saukowa kansa a yanzu, sai dai tashin hankalin sa shine ba wai kansa kadai
masifar zata sauko ba, har kan ahalinsa. Lallai Annabi yayi gaskiya.



Ya tuna da ganin da yayi wa Mufida yau.......

Ya tuna da ganin da Mama tayi masa yau ......
What is next.



Kuma wannan a duniya ne kadai.....



Duniyar da yaji ta fita daga kansa baki daya, so yake ya barta a yau, mutuwa yake so yayi ya huta da
wannan abin kunyar.



Amma in ya mutum mai zai tarar a lahira?



Ya tuna da ayar da take bayani akan azabar da ubangiji ya tanadarwa mazinaci a lahira.



Take wanj tsoro, mugun tsoro ya shige shi, ya dunkule a kan kujerar motar tare da fara wani kuka wanda
yaje cike da tsantsar nadama da dana sani mai tsanani.



"Astagfirullah!!!"



Ya fada daga can cikin zuciyarsa. Kalmar da tasa yaji wani sabon tsoron ubangijin sa ya sake shigarsa.



"Astagfirullah!!!" Ya cigaba da maimaitawa cikin kukan da yake jin sa yana tahowa daga zuciyarsa yana
vibrating a dukkan jikinsa.



Yafi awa daya a wajen a cikin wannan halin sannan ya tuna da sallolin da yake wasa da su, ya tuna cewa
bai ma yi sallar azahar ba gashi har ana kiran laasar, ya tuna sanda ake tafiya masallacin sallar juma'a a
lokacin ne shi kuma yake yake tafiya gurin aikata alfashar sa, sai yaji kunyar ubangijin sa ta kama shi, ya
tuna cewa yana kallon sa a lokacin da yake tafiya kuma yana kallon sa a lokacin da yake aikatawa, yana
kallon sa a duk lokutan da yake aikatawa. Wanne uzuri zai bayar idan ya tambaye shi? Yanzu da zai mutu
a yanzu wanne uzuri zai bayar na dalilin da yasa bai yi sallar azahar ba?
Ya bude motar da niyyar zuwa masallaci yayi azahar sannan ayi laasar din tare da shi sai kuma ya tuna
cewa sai yayi wankan tsarki. Ya koma ya zauna yana jin kunyar duniya gabakidaya ta kama shi. Kunyar
ubangijin sa yake ji kamar zai nutse a gurin.



Yanzu mai zai ce da Allah idan ya mutu kafin yayi sallar?



Ya kunna motar sannan ya share hawayen idonsa ya taka ta a hankali ya fita daga harabar asibitin. A
hankali yake tuka motar, a lokacin babu abinda yake tsoro irin mutuwa, gani yake zai iya mutuwa ko
wanne second kuma shi kansa yasan makomarsa idan ya mutu a halin da yake ciki. A hanyar ya yanke
wani hukunci a ransa cewa idan ya shiga cikin gidan sa ba zai kuma fitowa ba, ba zai kuma hada ido da
wani ba, zai yi dedicating sauran rayuwarsa ne zuwa neman gafarar Ubangijin sa har sai ya karbi ransa.



Yana zuwa gidan mai gadi ya tare shi "yallabai dazu Hajiya tazo tare da baki baka nan" gabansa ya fadi,
"wacce Hajiya?" Yace "Hajiya karama ta babban gida" ya fahimci Aunty yake nufi, sai kawai ya rabu dashi
ya shige ciki.



Yana shiga toilet ya wuce yayi wanka, wankan da ya dauki lokaci yana yi yana ji kamar yanaso ne ya
kankare fatar jikinsa ya zubar, maybe ko zai rage dattin najasar da take tare da shi, sai da ya fahimci
lokacin sallah yana cigaba da wucewa sannan ya fito ya chanja kaya ya saka wadu sababbi wadanda bai
taba sakawa ba, ji yake kamar sauran kayan nasa duk najasa ce a jikin su.



Yayi sallah, azahar da laasar, amma sai ya kasa yin addu'a, ya rasa abinda zai roka a gurin ubangiji, ya
rasa da bakin da xai nemi gafara a gurin ubangiji dan tabbas a lokacin gani yake yi babu wanda ya kai shi
munanan aiyuka. Maimakon ya daga hannun yayi addu'a sai ya mayar da goshinsa kasa yayi kuka, kuka
mai yawan da yake jin bai taba yin irinsa ba a duniya, kukan kuma da yake jin yana fitowa da ga cikin
zuciyarsa.



Sai da ya zama exhausted babu wani sauran karfi a tare da shi sannan ya kwanta a gurin ya rufe idonsa
yana cigaba da sake bitar laifuffukan sa. Mai yasa ya kasa dainawa ne? Ya jima yana cewa zai daina
amma kuma ya kasa dainawa, tun kafin yayi aure yake cewa zai daina idan yayi aure, da yayi auren
kumaya dauka ya daina din sai da wannan shegiyar zuwairan ta bishi Lagos ta hillace shi, daga nan ya
kuma cewa ba zai kara daga kanta ba amma kuma sai gashi ya cigaba, duk sanda yayi saibya gayawa
kansa na karshe ne amma wani opportunity din yana sake zuwa masa zai sake yi ya kuma cewa na
karshe ne.
Sai yanzu ya gano dalilin kasa dainawar tasa.......



Saboda ba dan Allah yake so ya daina ba... .



Amma yanzu ya gane kuskuren sa, he has learned the hard way but he is greatful for learning, ya gode
Allah ya ya nuna masa ayar sa tun a duniya har kuma ya juyo da hankalin sa zuwa tuba na gaskiya, ya
gode Allah dabai dauki ransa ba tare da ya tuba ba. Yanxu abinda ya rage masa shine neman yafiyar
Ubangijin sa, amma gani yake yi kamar sauran kwanakin sa a duniya sunyi masa kadan yayi
concentrating for his sins.



Karar wayarsa ce take ta breaking into his thoughts, ko kallon inda take baiyi ba dan yasan ba zai wuce
yan gidan su bane ba suke nemansa, maybe duk sunji abinda ya faru, shi kuwa ba zai taba zuwa inda
suke ba ballantana ya iya hada ido da su baya shi din ya zamanto tamkar annoba ne a gare su.



Sai kuma ya jawo rigarsa ya ciro wayar daga aljihunsa yana duba missed calls din sa, yawancin su daga
Aunty ne sai kuma wasu daga yaya Mubaraka. Sai kuma message daga Aunty tun da rana



"Umar kana ina? Muna neman key din gidan ka dan iyayen amaryar nan sun ce gobe zasu kawo ta"



Ya ajiye wayar kusa da shi ya cigaba da sauraron kidan ta as they kept calling.



Sai dai daga baya ne kuma yaji wayar tayi kida na daban wanda ya saka shi saurin dago kansa ya kalli
inda wayar take. Kidan daya saka wa number din Jidda. Rabon da yaji wayarsa tayi kara da wannan kidan
tun Jidda tana gidansa, sai lokacin da Yasmin ta kira shi.



Ya dauke kansa daga inda wayar take, me take nema? Ko itama taji labarin abinda ya faru ta kira shi tace
masa "I told you so?" In ba haka ba baya jin bayan rabuwar da suka yi dazu akwai dalilin da zai saka ta
kira shi. Yana ji kiran ya katse wani ya sake shigowa still daga gare ta. Sai da tayi masa kira biyar sannan
ya tashi ya dauki wayar jikinsa yana bashi babu lafiya, ko dai Mama ce ta rasu? Ko dai mahaifiyarsa ce ta
mutu da bakin cikin sa?
Ya dauki kiran ya saka a kunnen sa amma yakasa cewa komai sai yaji muryarta, but she sounded as if she
is crying.



"Umar! Kana ina?" Ya mike zaune. "Jidda? Lafiya kike kuka?" Ta kara sautin kukan ta "Umar babu lafiya,
yanzu aka kira ni wai daga police station ta gwauran dutse, wai sun tsinci Yasmin, wai sun kaita asibiti,
wai in tafi asibitin yanzu"



Ya mike tsaye, hankalin sa a matukar tashe "Yasmin? Me ya samu Yasmin Jidda? Me ya samu ƴata?"



Cikin kuka tace " wai wani ne ya tsince ta ya kaita gurin su, wai sun kaita asibiti, ka taho dan Allah Umar"



Yaji jiri yana neman daukar sa "kina ina? Wane asibiti suka ce?" Ta gaya masa sunan asibitin sannan tace
"ina hanya na tafi can, dan Allah Umar kazo, tsoron abinda zan tarar a can nake ji, dan Allah kazo"



Bai karasa jin magiyar ta ba ya katse kiran ya dauki key din mota ya fita daga gidan a guje, gidan da yace
ba zai kuma fita ba sai dau a fitar da gawar shi.



A guje yaje asibitin, a rikice, yana packing ko rufe kofar motar baiyi ba ya fita ya shiga cikin asibitin, a
reception ya hango ta, ta taho da sauri itama fuskar ta kacha kacha da hawaye, direct ta wuce kirjinsa
tana kara sautin kukanta, ya dago tada sauri "ina Yasmin din? Me ya same ta?"



Ta nuna masa wani daki a gefe "tana ciki....." Ya sake ta da sauri ya wuce ta ya shiga dakin da ta nuna.



Tun daga bakin kofa ya lura da fuskar yarinyar tasa, a kunbure kamar an dake ta a fuska, goshinta anyi
mata dinki. Ya karaso gabanta ya tsaya sannan a hankali ya saka hannunsa ya dauki hannunta daya ya
rike yana kallon dan karamin wrist din ta. Zagayen wrists din sunyi jajawur da wani zane mai kama da na
igiyar shanya. Kana ganin hannayen kasan daure ta akayi da igiyar shanya.
Ya juya da sauri a lokacin da Jidda take shigowa dakin itama, cikin budewar murya yace "me ya faru da
ƴata!?"



Kafin tayi magana doctor ya shigo tare da police a bayansa, police din ya na magana ya nuna Yasmin
yace



"yauwa wannan itace rape victim din"




Wadannan sune kawai kalmomin da suka daki kunnen Umar, kalmomin da yaji su tamkar saukar tsawa a
lokacin damina, suka kuma tarwatsa zuciyarsa kamar yadda tsawa taje tarwatsa bishiya idan ta sauka a
kanta.



Sune kuma kalmomi na karshe da Umar yaji, kafin ya fadi kasa sumamme.




*Jidda*



Tun bayan tafiyar Umar nake zaune a sitting room din cikin halin rashin jin dadi, banji dadin yadda
maganar mu da Umar ta kasance ba, ban kuma ji dadin yadda ya fita daga gidan mu ba, ina jin tsoron kar
ya yi wani abu, kar yaje yayi hatsari a yanayin da ya fita.



Ina nan zaune har aka sauko daga masallacin juma'a, a lokacin ne yaya Tahir ya shigo mukayi maganganu
akan shirin tafiya ta Ethiopia, daga nan ya tafi ni kuma na koma cikin gida nayi sallar sannan na kwanta
da niyyar inyi bacci zuwa laasar amma na kasa yin baccin, zuciyata duk babu dadi nake jin ta.



Na mike na dauko wayata na kira Diyam muka danyi hira na bata labarin latest abubuwan da suka faru
da kuma yadda muka yi da Umar yau, ta bani shawarwari tare da kara min karfin guiwa kamar yadda
saba. Mukayi sallama na tashi na ci abinci sannan nayi sallar laasar na kunna tv na zauna ina jiran
dawowar Asma'u daga makaranta dan ta dan ɗebe min kewar su Yasmin da nake jin ta dame ni.
Sai dai ban jima ina kallon ba kira ya shigo waya ta daga number din da ban sani ba. Sai dai true caller ta
nuna min "DPO Gwauron Dutse" na yi mamaki tare da jin tsoron mai police suke nema a gurina, abu na
farko da ya fara zuwa raina shine Umar yayi accident. Na dauka da sallama cikin tsoro da fargaba.



Yace "yauwa, dan Allah ina magana ne da babar yarinya mai suna Maryam wadda ake cewa Yasmin?"



Na mike tsaye cikin firgici, ina jin kamar zanyi fitsari a tsaye "eh ni ce, Yasmin yata ce. Me ya faru? Me ya
samu Yasmin?"



Yace "ki kwantar da hankalin ki Madam, yarinyar ki tana lafiya tana hannun mu amma yanzu zamu tafi
da ita asibiti sai dai ki same mu a can"



Na fara kuka "me ya samu Yasmin? Me take yi a hannun ku? Me yasa zaku kaita asibiti?"



Yace "farko zan yaba wa kokarin ki na saka yarinyar ki ta haddace

83 / 101