Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
number din ki. Ina ta
neman ki. Ya kike? Ance kinyi aure har da yara ko? Ya yaran ya maigidan"
Na dan janye wayar daga fuskata saboda wani sabon kuka na naji ya taho min. Nayi kokarin rike shi
amma bai riku ba. Sai kawai na katse kiran na ja hijab dina na rufe fuskata dashi.
Wani kiran ya sake shigowa, still daga gurin ta. Ta riga ta same ni kuma har na dauka sannan na katse,
rashin daukata yana nufin ina sane da ita ce kuma bana son alaka da ita kenan. Abinda zata dauka
kenan.
Nayi kokarin tsayar da kukana sannan na kuma dauka
"Hello Halima. Ina kan hanya ne yanzu kuma kamar network bashi da kyau zan kira ki in naje gida"
Sai naji tayi shiru, na kalli screen na ga time yana reading, na mayar kunne na "Hello?"
Tace "Jidda? Are you crying?"
Wannan tambayar sai ta zama Mabudin kuka na, kawai ma saka mata kuka nayi tayin abina kamar
wadda ta shekara bata yi ba, bayan I have already cried enough. Sai da na tsagaita da kukan sannan tace
min "me ya faru Jidda? Kina ina?"
Na dan dago kaina na kalli inda muke, ni ban ma gane unguwar ba musamman saboda duhun da gari
yayi a lokacin, nace "ban sani ba ma ni, ina cikin adaidaita ni da yara. Ban san ma inda zanje ba"
Tace "subhanallah. Then something is definitely wrong kenan. Kin ga, in babu damuwa, come to my
house ki huta kiyi tunani kinji, zaki zo?" Na gyada kai kamar tana ji na sannan nace "eh, zan zo" tace
"okay, ki ce da mai adaidaita ya taho unguwa uku, I will send you the full address ta message. Please do
come kinji? We will sort it out together in kin zo"
kadan bayan nan muna kofar gidan da tayi min kwatance. Na sauko da Asad a hannuna wanda ya gama
kukan sa kuma yayi bacci a jikina, sannan na sauko da Yasmin da duk jikin ta ya saki ita ma, sai kuma na
biya mai adaidaita kudin da yafi karfin nasa saboda kyautatawar sa gare ni.
Na daga kai ina kallon kyakykyawan gidan da tun daga waje tsarin sa ya burgeni. Sai dai bana cikin mood
din kalle kalle.
Yana tafiya aka bude kofar gate din gidan aka fito, da alama mai gadin gidan ne yace "Jidda?" Na gyada
masa kai kawai sai ya bude min kofa muka shiga ya rufe sannan yayi gaba da sauri yana min alamar in
biyo bayan sa. Muka he zuwa wata kofa ya bude min sannan ya matsa tare da yi min alamar in shiga da
hannun sa.
Na shiga na tsaya hannuna daya riƙe dana Yasmin, dayan kuma dafe da Asad. Tana tsaye a tsakiyar falon,
fuskar ta cike da damuwa. Muka tsaya muna kallon juna.
"Jidda?" Ta kura sunana, na kasa amsa mata da farko saboda ban tabbatar ita ce wacce nake tunanin ita
din bace ba dan kusan komai nata zan iya cewa ya chanja, sai da na kalli fuskar ta sosai sannan na gane
kamannin ta, kyakykyawan dogon hancinta da dagaggen bakinta.
"Diyam?"
Na fada cikin doubt. Sai ta taho da sauri inda nake ta jawo ni jikinta tare da rungume mu ni da yara
gabaki daya.
Sai kuma ta ja mu zuwa kujera "seat please. You must be very cold, bara in kawo muku something warm
ku sha" ta danyi rubbing fuskar Yasmin sannan ta shafa kan Asad sai kuma ta kara karfin room heater din
da take falon sannan ta wuce bude wata kofa ta shiga da sauri.
Na dawo da dubana kan Yasmin da ita ma ni take kallo sannan tace "mommy wacece wannan? Ina ne
nan? Me zamuyi anan?" And for the first time tun da muka fito daga gida I answered
her "wannan sunanta Aunty Halima. Kawata ce. Mun zo ne zamu kawo mata ziyara". Ta juya tana kallon
kofar da Diyam ta shiga sannan tace "in mun gama kuma sai mu tafi gida ko?" Wannan tambayar ce
kuma ban amsa mata ba. Nima kaina ban sam amsar ba. Gamu nan dai a gidan a lost but found friend
dina, then what next?
Na dauko waya ta da har yanzu take ta ƙugi a cikin jakata, missed calls 30+ daga numbers din Umar,
Abba, Umma, yaya Tahir da Aunty Afia. Sai kuma messages daga Umar
"Don't do this Jidda please"
"Zan bar ki a gidan in abinda kike so kenan, zan ce da Abba ya bar ki a gidan in nan kika fi so"
"Just pick up the damn phone"
Ban karanta sauran ba na fita daga messages din sannan na kashe wayar a lokacin da Diyam take
shigowa wata yarinya a bayanta hannunta rike da tray. Ta jawo table gaban mu ta dora tray din sannan
ta koma ta kofar da suka shigo, Diyam ta matso tana yiwa Yasmin murmushi "ya sunan ki baby girl?"
Yasmin ta bata rai bata ce komai ba, na juya na harare ta sai tace "Yasmin" muryar ta can kasa.
Diyam tayi murmushi. "Ni kuma sunana Diyam" sai kuma ta jawo tray din da aka ajiye ta hada wa Yasmin
da Asad tea mai dumi ta basu duk suka sha Sannan ta kira yarinyar dazu tace ta shiga dasu ciki ta kula
dasu.
Asad bai wani damu ba ya tafi, amma Yasmin sai ta makale tana kallona sai da nace mata taje zamuyi
magana ne sannan ta tafi tana waige.
Bayan sun shiga Diyam ta hada min tea nima ta miko min, nayi saurin girgiza kai na dan in na karba ma
bana jin zai iya wucewa ta makogwarona dan a toshe nake jin sa sosai. Sai ta mayar ta ajiye sannan ta
rike hannuna a cikin nata tana murmushi. "You are still looking just like a remembered. Very beautiful"
na sunkuyar da kaina ina so inui murmushi in kuma amsa mata compliment dinta sannan ita ma in yaba
mata amma na kasa, sai naji ta kuma cewa "naji a waya kina kuka, yanzu ma kuma gashi naga idon ki duk
a kumbure suke Allah ne kadai yasan yawan kukan da kika yi. Kin ce min ba kya gida kuma baki san inda
zaki je ba right? Kuma ni banga alamar wahala a tare da ku ba ma'ana yanzun ne kuka bar gidan ba wai
dama can baku da gidan bane ba. And I can't help but wonder Jidda yaji kika yi? Fada kuka yi da mijin ki
kika yi yaji? Kin je gida kuma an koro ki ko?"
Na daga kai ina kallon ta ina wondering ko dai ta koma malamar duba ne? Sai kuma na gyada mata kai
da sauri "eh. Yaji nayi Diyam, kuma nayi alkawarin ba zan koma gidan Umar ba. Amma ina zuwa gida sai
Abba ba tare da ya saurari dalilin yaji na ba ballantana in saka ran zai bani hakuri ko kuma shi yayi masa
fada sai kawai ya dauki waya ya kira shi yace yazo mu tafi. Shine na gudu daga gidan dan ba zan koma
ba. Shine kuma ban san inda zan je ba. Duk gidajen yanuwana duk inda naje mayar da ni zasuyi. Duk son
shi suke yi. Duk ganin kimar sa suke yi. Saboda bashi da wani babban aibu sai abu daya. Sai abun da yayi
min nauyin da ba zan iya fitowa in gaya wa duniya ba. Sannan yayi munin da ba zan iya cigaba da zama
da shi ba" na fada cikin kuka.
Sai ta jawo kaina kan kafadar ta tana dan bubbuga baya na kadan kamar yadda ake yiwa yara in ana
rarrashin su. "Shshsh. Kiyi hakuri Jidda, kiyi hakuri but cry all you want, please let it all out in your tears
zaki ji sanyi a zuciyar ki"
Abinda bata sani ba shine kukan nayi shi nayi shi har na fara tsoron rasa idanuwa na a sanadiyyar kuka.
Sai da na tsagaita da kukan sannan ta dago kaina ta na dan murmushi tace "I was once in a position like
yours. Ba exactly ba amma something simila. Mijina ya kaini bango and I decided na gama zama dashi,
sai na debi kayana na dauki ya ta na shiga adaidaita na tafi gidan mu. Abba dama ya rasu already. Inna ta
tana gani na she was like "Diyam yaji kika yi?" And I was like "bazan koma ba ni Inna ba zan koma ba na
gama auren" and she was like "sai kin koma din, ja'ira, ina mijin naki?" But a lokacin shi mijin nawa da
take magana akai yana hannun yan sanda, ba dan haka ba dana tabbatar ita ma kiransa zata yi tace yazo
ya dauke ni mu tafi. But then she called wanda ya saka aka rufe shin and said "Diyam ta kawo kararka ka
saka an kama mijinta" shi kuma ya ji haushi ya kumbura kamar zai fashe "tayi hakuri za'a sako mata
mijinta" and I was like "oh noo Inna what have you done?"
Ta karasa maganar tana dariya, dariya sosai, and I couldn't help but smile duk da ko kadan ban gane kan
labarin nata ba but daga yadda take murmushi da dariya na tabbatar labarin wani sad memory ne take
bani wanda ya riga ya wuce ya zama abinda zata tuna tayi dariya yanzu.
And I thought.... maybe nima wata rana zan tuna all of these in yi dariya. Amma yadda zanyi in riski
wannan ranar ne ban sani ba, ko ma zan ganta din?
Ta gama dariyar ta sannan tace "but wannan shine asalin rabuwa ta da mijina. Daga ranar ban kuma
komawa gidan sa ba sai daukar kaya"
Na bude ido, sannan na kalli gidan da muke ciki, sai kuma nace ban gane ba. Tace "ina nufin na rabu da
mijina na fari wanda kuma shine uban yata ta fari, wanda kuma nayi shahon shekarun da na tabbatar
sunfi wadanda kika yi da mijinki a yanzu. But rabuwa dashi wasn't the end of me, it was rather just the
beginning"
Nace "Sadauki? Kina nufin kin iya rabuwa da Sadauki duk son da kike masa?"
Sai tayi murmushi "ashe kin tuna da Sadauki" nace "ina tuna sunansa kullum idan na tuna ki. Diyam
kowa ya sanki a school yasan sunan Sadauki attached to you. Ashe zaki iya rabuwa da shi?"
Ta girgiza kai "ai ba Sadauki ne mijina na farko ba Jidda"
Nace "but sanda aka ce mana anyi miki aure, lokacin muna jss3, duk mun dauka Sadauki aka aura miki
tunda munsan yayanki ne kuma saurayinki"
Ta girgiza kanta yanayin fuskar ta yana chanjawa, da alama ta tuna da wani memory marar dadi, tace
"ba sadauki aka aura min ba. Mijina na farko sunansa Saghir, cousin dina ne, yanzu ne nake auren
Sadauki" na kuma kallon ina so in fahimci kam labarin ta amma sai ta dakatar da ni "don't let me bore
you with labari na, just know that I went through a lot kafin in zo inda nake yanzu" na sunkuyar da kaina
ina tunanin nima ai ina going through a lot a yanzu, but will I reach where she is ko kuma nawa destiny
din ba irin nata bane ba.
Sai ta sake rike hannuna tace "look Jidda, you are my dear friend, nan kuma gidan mijina ne, in kina so
you can stay here for tonight kafin gobe sai ki yanke hukuncin abinda zaki yi, but I advice you to call your
parents ki gaya musu you are okay dan hankalin su ya kwanta. But choice din ki ne yin hakan. Ban ce
lallai ki gaya min matsalar ki ba ko dalilin da yasa kika baro gidan mijinki ba, amma in kina son gaya min
din I will listen, sannan kuma zan baki shawara dai dai da fahimtata. I won't judge you, because I am a
woman, and women are supposed to be each other's keepers"
Na gyada kai kawai, sai ta sake tambayata "kin yarda? Kin amince zaki kwana anan gidan kafin ki yanke
hukuncin abinda zaki yi?" Na sake gyada kai na tare da sauke ajjiyar zuciya "Nagode. Nagode sosai"
Ta mike tsaye tare da jan hannuna nima na mike "muje ciki to, ki samu kiyi sallah ki huta ki ci abinci. And
then think about it. Gobe in Allah ya kaimu sai mu zauna mu san inda muka tsaya da kuma inda zamu
tashi.
Na bita a baya, ina lura da kyau da tsarin gidan tun daga yanayin ginin sa har zuwa furnitures da
decorations, akwai taste mai kyau gaskiya kuma akwai kudi sosai.
Wani daki ta kaini, daga gani zaka gane guest room ne dan babu alamar akwai mutum a ciki, sai ta bude
wardrobe din ciki ta dauko min sallaya ta shimfida min sannan ta nuna min toilet na shiga, ina fitowa na
ga wata yarinya tana yin shimfidar gado, ta gaishe ni sannan ta cigaba da aikin ta, ina sallar ta gama
shimfida gadon ta kunna room heater sannan ta saka room freshener ta fita, bayan jimawa kadan ta
dawo da tray dauke da abinci ta ajiye a gaban dan karamin carpet son da yake gaban gado.
Na idar na zauna addu'a, sai na samu kaina da yin irin addu'ar da Surayya ta gaya min cewa tayi na Allah
ya ji min jagora akan abinda na saka a gaba yayi riko da hannu na kar ya barni ni kadai dan ni kadai ba
zan iya ba, ya kawo min dauki.
Ina cikin addu'ar Diyam ta dawo dakin, na kammala na shafa tare da share hawayen da ya zubo min
sanda ina addu'ar. Ta zauna a bakin gado tana kallona "kiyi hakuri Jidda. Insha Allah komai yayi farko zai
yi karshe, Allahn daya dora miki wannan matsalar shi zai yaye miki if you believe and trust him kinji?" Na
gyada kai sannan na mike tsaye ina kallon abin da ta shigo dashi a hannunta.
Duk da halin da zuciyata take ciki sai da nayi murmushi "babies!" Na fada "twins. Diyam twins kika
haifa?" Tayi murmushi tana miko min daya, na karbe ta na daga ta sama ina jin sha'awar jarirai tana
shiga zuciyata. "So cute wallahi kamar in sace ta. Dan Allah ki bani" tayi dariya "na baki. In dai wannan ce
na baki ita. Da dai wannan rigimammen ne da sai inji tsoron kar ya hana ki bacci" ta fada tana yiwa daya
jaririn da yake kan cinyarta wasa "ko ba haka ba abba na? Mai rigima irin ta babansa" na zauna a kusa
da ita ina kallon kyakykyawan dan da yake cinyarta yana yi mata toothless dariya, nayi murmushi a raina
ina fatan kar nawa yayan suyi halin nasu uban.
"Sannu Diyam!" Na fada "haihuwar twins ance da wahala ko?" Ta yi dariya "da wahala mana, ko wacce
haihuwa ai akwai wahala. Amma ni ba su ne twins dina na farko ba na taba haihuwar wasu, na fari na,
Allah yayi musu rasuwa amma a ranar dana haife su, ko kwana daya basu yi ba" ta fada tana murmushin
takaici, daga dukkan akama har yanzu tana jin zafin mutuwar yayan nata.
Na sunkuyar da kai na ina wasa da hannuna sannan nace "Allah sarki. Allah yasa masy ceto ne" tace
"ameen Nagode" sai kuma na kalli kofa ina tunanin nima nawa yayan amma bance komai ba, kamar ta
san me nake tunani sai tace "su Yasmin suna can suna cin abinci, ko a kawo miki su nan ku ci tare?" Nace
"eh" a raina nasan Asad zai iya cin abinci acan amma Yasmin ba zata ci ba, ko a gida bata cin abinci ita
kadai sai mum hadu gabakidaya, sai dai ko in tea ne ko kuma wani snacks haka.
Jimawa kadan da fitar Diyam yaran suka shigo tare duk suka fado jikina "mommy anan zamu kwana ne?"
"Mommy nan ne sabon gida mu? "Mommy daddy fa? Shima nan zai taho?" Na jawo tray din na fara
zuba musu abinci "ku zauna ku ci abinci" Asad yace "an bani na ci. Ni yoghout zan sha. Ki kira Daddy ki ce
in zai taho ya taho min da yoghout" nace "to babana, maza shiga toilet kayi fitsari kazo ka kwanta" ya
shiga toilet da sauri ni kuma na dawo da hankali na kan Yasmin "sauko ki ci abinci"
Ta sauko ta zauna tana kallona "mommy anan zamu kwana?" "Eh na amsa mata ina juya mata abincin.
"Mommy daddy shi kadai zai kwana?" Na dago kai ina kallonta "ban sani ba. Ki rufe min bakin nan naki
kuma ki ci abinci" ta dauki chokali tana ta jujjuya abincin har Asad ya fito ya kwanta yana ta surutan sa
shi kadai har bacci ya dauke shi. A lokacin Diyam ta kuma dawowa, wannan karon babu babies din a
hannunta sai kaya, "ga kayan bacci, amma na rasa wanda zan bawa Yasmin da Asad,na Subay'a sunyi
musu yawa," na karba ina murmushi, ina jin dadin kyautatawar ta "nagode, babu komai" Yasmin ta mike
"na koshi da abincin mommy" sai ta shiga toilet.
Ranar da kyar na samu Yasmin tayi bacci, amma ni kuma banyi baccin ba, tashi nayi na sake yin alwala
sannan na cigaba da kai kukana ga ubangiji, zuciyata a lokacin da hawayena duk sun kafe, addu'ar samun
mafita kawai nake yi duk da cewa har lokacin ban san menene mafitar a gare ni ba. Abinda na sani kawai
shine na gama auren Umar, abu na biyu kuma shine nasan indai na koma gida sai sun mayar da ni gidan
sa, dan haka yanzu gidan zama nake tunanin inda zan samu. Diyam ta bani gurin zama na tsakanin yau
da gobe, kawata ce ita amma rabon na da ita shekara da shekaru bazan zo rana daya kawai in zauna
mata a gida in dora mata responsibilities dina ba, dole in nemi mafita. Shin ko gurin yaya Tahir zan koma
in roke shi kar ya gaya wa Baba ina tare da shi? And then what? Ba zan cigaba da zama har abada da
auren Umar a kaina ba Umar kuma bana jin ko bindiga aka saka masa a ka zai sake ni.
But he must, dan na gama da shi.
Ranar yadda naga rana haka naga dare, na saka yayana a gaba ina ta sakawa ina warwarewa. Har gari ya
waye kuma ban saka abinda nake ganin shine mafita a gare ni ba.
Da assuba bayan nayi sallah ne na dauko wayata na kunna, ko gama kamawa batayi yi ba sai kiran ya
shigo "Umma" sai kawai naji hawaye ya taho min, Allah sarki uwa, yanzu haka itama yau kwana tayi bata
yi bacci ba tana kiran wayata, sai naji wani irin guilt, naji cewa bata chanchanci haka daga gare ni ba
amma duk da haka sai naki dauka. Messages ma suka yi ta shigo min yawanci duk daga Umar, wadansu
dogaye kamar mai rubuta labari wadansu yan kadan, babu wanda na tsaya na karanta a ciki sai naga
wani ya shigo daga yaya Tahir
"Jidda call me"
sai na shiga nayi masa reply.
"I am safe. Ka gaya wa Umma"
Message din yana tafiya na kuma kashe wayar, a lokacin ne na yanke wata shawara, ban san inda zanje
ba, ban