Chapter 21 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   21 / 101

60K to 63K   out of 300.2K words

sha, bara in hada miki ki shanye kafin ku tafi dan in nace in kunje ki sha ba lallai ne ki sha ba"
ta fita sannan sai gata ta dawo da cup a hannun ta ta bani ta ce in shanye, ina cikin sha ya shigo dakin
yana duba agogon hannun sa, Aunty tace "gata nan zuwa sarkin gaggawa, wannan kai da maye ne in ka
kama mutum sai ka kai shi lahira zaka rabu dashi" sai yayi murmushi kawai bai ce komai ba ya fita.



Muka fito palo nayi wa Mama sallama, sai ta bani wata leda ita ma ta gaya min spices ne a ciki na girki,
"in akwai wani abun da kuke bukata a gidan ki kira auntyn ku ki gaya mata, kar ki kira gida, shi kuma in
kin gaya masa ba lallai ya san inda zai samo muku wani abun ba, a hankali kema zaki san inda zaki samu
komai. Na bayar ma za'a yi muku garin kunu tunda yana so, za'a aiko muku da shi" na durkusa nayi mata
godiya na kuma yi mata fatan Allah ya kiyaye hanya.
Afnan tazo ta zauna a kusa dani tana yi min rada "Aunty zan biki kinji?" Na shafa kanta nace "maza
dauko kayanki mu tafi" sai ta mike da sauri tana murna "mommy ki hada min kayana aunty Jidda ta
yarda zan bita" Affan ya mike "wallahi nima sai naje mommy" Aunty ta girgiza kai "kuna da school gobe,
ku bari sai da weekend sai kuje kuyi musu two days" Mama tace "da weekend din ma suna da islamiyya,
sai dai in anyi hutu" suka fara rikici, sai na rarrashe su da cewa ai an yi hutun sai suje suyi min two
weeks.



Sai dana fadi haka sannan suka fara murna, a lokacin ne kuma naji ana maganar Ummi ita ma bata nan
akayi bikin sai anyi hutu zamu hadu, ban gane wacce Ummi suke nufi ba kuma ban tambaya ba.



Umar ya sake lekowa. Ya tsaya kawai a bakin kofa ya saka hannu a aljihu yana kallon mu. Hajiya ta taba
ni "tashi maza ku tafi yana jiran ki, kinsan unguwar ku da nisa" ina mikewa ta kwalla wa Mufida kira tace
tazo ta karbi kayan hannuna sannan ta dauko mana abinci a kitchen mu tafi dashi tunda bamu yi dinner
ba. Mufida ta fara buga kafa tana shagwaba, "Mama ita ta dauko mana da kanta" Aunty tayi dariya
"yayarki ce dai yanzu ko kin ki ko kinso" ta juyo tana harara ta ni kuma na yi mata gwalo sannan na sake
yiwa su Mama sallama na fita.



Yana cikin mota a zaune, sai na tsaya a jikin motar ban shiga ba, na sauke glass yana kallona amma bai yi
magana ba, nace "Mufida nake jira, zata kawo min kaya inji Mama" sai ya dage glass din. Sai naji ni bana
son wannan shirun nasa, fushi yake yi dani na sani. Na hadiye yawun tsoro.



Mufida ta fito tare da Muhsina, suka saka mana kayan a mota sannan mukayi sallama na bude gaba na
shiga na rufe.



Bai ce min komai ba ya tayar da motar muka fita muka hau titi, na juya ina kallon sa ta hasken street
light ina jujjuya hannuna nace "kayi hakuri" ya juyo yana kallo na "hakurin me fa?" Na mayar da kaina
kasa, "naga kamar kayi fushi ne" yace "fushin me zanyi?" Nace "akan abinda nayi" yace "me kika yi" na ji
kamar zanyi kuka "dana boye maka gaskiya" yace "gaskiyar me fa?" Na fara yarfa hannu na "aika san
maganar da nake yi wallahi kawai so kake ka nuna baka sani ba"



Yace "so nake inji kin fadi laifin ki da bakin ki. Kin kuma amsa cewa kin yi laifi kin yarda kuma cewa baki
kyauta min ba" nace "to ai na yarda ban kyauta din ba shi yasa na baka hakuri ai, kuma ina sake baka
hakuri. Allah ya baka hakuri" yayi shiru yana kallon gabansa.
Na fara share hawaye na "sau nawa zan baka hakuri ne to wai ba zaka hakura ba?" Ya juyo yana kallona
yana jin sautin kuka a muryata. Sai ya danyi murmushi yace "cry cry Baby. Zan hakura mana, amma ba
yanzu ba. Ask me again tomorrow morning zaki ji nace miki na hakura"



Na gane abinda yake fada, sai kuma naji damuwar rashin yin hakurin sa ya tafi tsoro kuma ya dawo min.
Na jawo kafafuwa na kan kujera na nannade su a cikin skirt dina na kwanta a jikin kofar mota na rufe ido
na.



Ina jin motar ta tsaya, na bude ido na na gan mu a kofar wani guri da ban gane ba, sai kuma na lura
kamar gurin sayar da gasassun kaji ne, ya bude ya fita bayan mintuna kadan ya dawo da leda ya saka a
seat din baya. Kamshi ya cika motar gabakidaya amma ni sai naji kamar hawa min kai kamshin yake, sam
banji ina son cin kazar ba, dan gabakidaya bani da appetite.



Ya tayar da motar muka dauki hanyar gida, yayi horn mai gadi ya bude muka shiga yayi packing ya kashe
motar. Na dago kai ina kallon sa, ina jin alamar kamar zazzaɓi yana neman rufe ni nace "in na roke ka
nace ka hakura da wannan abin zaka hakura?" Sai naga yayi dariya har yana dafe kansa, na bata rai ina
jin haushin dariyar sa yace "my dear sweet Jidda. No. Ko kin bani hakuri ba zan hakura ba saboda babu
laifin da kika yi min. Ni wannan abin da kike yi ma in baki sani ba shi yake kara min son abin"



Na harare shi ina magana kasa kasa "kayi dariyar ka ka gama, tunda bai kashe kowa ba nima ba zai kashe
ni ba" ya juyo sosai sannan ya kama hannayena biyu ya damke a cikin nasa yace



"look at me Jidda. Trust me, ina neman alfarmar kamar yadda kika danka min zuciyarta ki daure ki danka
min kijinki shima and I will not hurt either of them. I will not hurt you Jidda. I promise I will never hurt
you"



Na lumshe idona na bude. Ya dawo da hannayenmu a tare zuwa fuskata yana goge dan guntun hawaye
daya fito a kasan idona.
Ya na kallona cikin ido yace "I can't do it in ranki baya so, in hawaye yana fita daga idonki. Duk matsuwar
da nayi da ke Jidda in baki ce kin amince ba ba zan miki komai ba. Zan cigaba da kallon ki ina lallabaki har
sai kin ce min kin amince. That's how much I love you"



Na cire idona daga nasa na sauke su kasa, sannan a hankali naji tsoron dake raina ya ragu, gyada kai na
"na amince"



Yayi alƙawarin cewa he will not hurt me, but he did, it hurts alot at first har sai da nayi tunanin ajali na
ne yazo and then he took away the pain with the pleasures ta yadda har sai da nayi tunanin babu wani
sauran pain a duniya. Nayi tunanin babu sauran komai a duniya sai abinda muke yi, na kuma yi tunanin
babu sauran kowa a duniya sai shi.



A ranar ya mallaki jikina ya mayar da shi nasa, kamar yadda ya mallaki zuciyata ya mayar da ita tasa.



Wannan dare ne da bazan taba mantawa dashi ba a tsahon rayuwata.....



Ban san sanda muka yi bacci ba, amma nasan nayi dogon bacci dan ban farka ba sai da rana ta fito sosai.
Shima kuma feeling din cewa rana ta fito ne da kuma feeling din ana kallona ne ya tashe ni.



Na bude idona a hankali, sannan na sauke su a cikin nasa. Yana kwance a kusa dani, kansa a kan pillow
na, fuskarsa kusa da tawa, sannan idonsa akai na. Ina bude ido na yayi min murmushi. Zan iya rantsewa
ban taba ganin murmushi akan fuskar sa mai kyawun da yakai na ranar ba.



Na jawo hannayena da sauri na rufe fuskata nima ina murmushi, sai ya rankafo yayi kissing goshina
sannan ya saka hannu yana gyara min gashina daya baje akan pillow yace "tun dazu nake ta so in gyara
gashin nan, hannuna har kaikayi yake yi amma bana son in tashe ki because you looked so beautiful
when sleeping and I love you so much. Maybe a little bit too much. Ina so ki sani cewa daren jiya is the
best night of my life so far, ban sani ba ko akwai wani daren da zanfi so fiye dashi nan gaba, in ma akwai
inajin daren da zaki haifa min kyakykyawar baby irin ki ne" ya fada yana shafa karan hanci na sannan ya
goga nasa akan nawa.
"Na gode Jidda. You gave my everything that I have ever dreamt of. Duk abinda nake so kuma nake da
burin samu na samu anan wajen. Ina fatan Allah ya biya ki da aljanna ni kuma ya bani ikon faranta miki
kamar yadda kika faranta min. Nagode"



Ya dauke hannayena dana rufe idona dasu sannan yayi kissing idanuwan da suke a rufe. Na bude su ina
kallon sa, ina jin sonsa yana kokarin yiwa zuciyata yawa nace "godiyar me kake yi ne wai? Me na baka da
zaka gode min? Dama ai naka ne. Abin ka ne da nake ajjiye maka kuma kazo ka karbi abinka. My heart
and my body are yours, na Umar ne shi kadai"



Ya dora goshinsa akan nawa, hancinsa akan nawa ya rufe idonsa sannan a hankali shima yace "my heart
and my body are yours. Na Jidda ne ita kadai"



And then he kissed me.



Hasken ranar daya matso kan fuskokin mu ne yasa na janye fuskata daga tasa tare da kare hasken da
hannuna. "Rana ta fito ba muyi sallah ba" na fara kokarin mikewa sai dai wani suka da naji a kasana ce ta
sakani komawa in kwanta tare da yin yar karamar kara. Sai yanzu na tuna da pain din da naji jiya, har
yanzu yana nan sai ma tsami da gurin yayi yanzu. Ga karin cinyoyi na da suke ciwo kamar wadda nayi
tsallen kwado, sannan ga cikina kamar anyi min yasa, bayan abinci ma kamar harda hanjina aka hada aka
kwashe.



"Oops, sorry baby"



Sai kuma yayi dariya. Na juya na harare shi "dariya ma kake yi min ko?" Ya daina dariyar sannan yayi
fuskar tausayi "sorry dear, ni ne ko? Ki bar ni da ni zan yi maganin ni. Bulala nawa kike so nayi wa ni?" Na
fara matso hawaye duk da bana gaskiya bane ba. Ya mike "sorry sorry, don't start with the crying please.
I am going to take care of you" ya sauka daga kan gadon, nayi sauri na rufe idona saboda lura da nayi
ashe babu komai a jikinsa, amma na kasa cire image din daga raina.



Ya shiga toilet sai kuma ya fito "babu ruwan zafi a toilet din nan ashe. Bara in duba toilet dinki" na dan
bude idona kadan sai kuma na sake mayarwa na rufe. "Please ka saka wani abun a jikin ka" ina jin shi
yana dariya sannan ya fadi wani abu da banji sosai ba sannan naji ya bude kofa ya fita.
Na sauke ajjiyar zuciya na bude ido na ina kallon hotonsa da yake dakin, sanye da kayan su na doctors da
stretescope a wuyan sa, fuskarsa dauke da murmushi. Nima nayi murmushin ina ji kamar babu wadda ta
kaini dace da miji a duniya.



Ina jin motsin sa na mayar da idona na rufe, yace "can din ma babu, but na kunna yanzu. Bara in kunna
anan ma. Let me get you something to eat kafin ruwan yayi" na dan bude ido naga ya saka jallabiya, sai
ya kunna heater sannan ya sake fita. Few minutes ya dawo da tray a hannunsa ya ajiye sannan ya fara
kokarin tashina zaune ni kuma nayi ta zuba masa shagwaba, sai da ya hada min pillows da kuma jikinsa
na jingina sannan na tashi ya bani cup din tea daya hada min mai kauri na karba na shanye tas, ya daga
hannu "to kin shanye tea din da me zaki ci bread din kuma?" Na langwabe "wani zaka hada min".



Ya dauki cup din "an gama ranki ya dade" sai ya koma ya hado wani ya dawo, sannan ya dauki bread ya
shafa min butter na kuma cinye na sake shanye tea din. Ya dauke tray din ya fita dashi sai gashi da apple
ya kawo min,shima nace ba zanci ba sai ya yayyanka min, ya koma ya dauko wuka da plate ya zauna
yana yanka min ina ci har na cinye.



Sai da na gama sannan nace "banyi brush ba fa" yace "kar ki damu, nayi miki already"



Toilet ya koma ya hada min ruwa sannan ya dawo yana tattare hannun rigarsa da murmushi a fuskarsa.
"Yauwa, lokacin yiwa baby wanka yayi" na bude ido "wa za'a yi wa wankan?" Ya kashe min ido, "wai da"
kafin in sake magana ya yaye bargon, nayi kokarin tashi da sauri sai kuma nayi kara ina rike waist dina da
naji shima ashe ciwon yake yi.



Dole na hakura ina ji ina gani ya dauke ni zuwa toilet, ya saka ni a cikin ruwan zafin da naji kamar ya zuba
jajjagaggen attaruhu a ciki, na rike shi kam ina jin ruwan yana shiga kofar da da take a rufe sai jiya aka
bude ta, jikina har karkarwa yake yi shi kuma yana ta jera min sannu, a hankali kuma sai na fara jin dadin
ruwan sai na sake shi na koma na kwanta. Ina jinsa ya fita.



Ban jima sosai ba saboda sallah da nake ta tunanin banyi ba. Na tsarkake jiki na sannan nayi wanka na
tsarki dana sabulu. Na dauko toothbrush dinsa, a raina ina tuna ranar da yace zamu yi sharing
toothbrush da toilet, nayi murmushi sannan na saka paste nayi brush sannan na daura towel dinsa na
dafa bango na fita.
Baya dakin amma naga alamar ya gyara bed din, duk da dai kana gani zaka fahimci cewa wanda yayi
gyaran gadon bai iya ba, bani da kaya a dakinsa dan haka na tafi dakina na lallaba na saka riga da hijab
nayi sallah ina jin guilty feeling a raina na rashin sallah da wuri.



Bayan na idar na tashi na shirya cikin riga da wando masu fadi wadanda basu takura jikina ba amma
sunyi min kyau sosai kuma sun fitar da shape dina sosai. Na gyara gashina na daure shi a keyata sannan
na gyara fuskata lighly. Na bude kofa na fita palo duk da cewa da kyar nake daga kafata amma tunani na
Umar, ko ya ci abinci?



Ina shiga palon yana shigowa shima daga waje, da leda a hannunsa, yazo ya kamani "wa yace ki tashi ne
wai. Ke fa patient dina ce yanzu" ya zaunar dani akan kujera sannan ya dauko robar ruwa ya bude min ya
kuma dauko ledar daya shigo da ita ya ballo min magungunan da suke ciki. Ina gama sha ya kwantar dani
akan kujera tare da saka min pillow, shi kuma ya zauna a gabana yana shafa fuskata.



"Don't worry, zaki yi bacci idan kika farka kuma zaki ji ciwon duk ya tafi. Kar ki manta, you have a doctor
waiting on you dan haka baki da wani problem"



Na lumshe idona ina masa murmushi, realising cewa harda maganin bacci ya hada min ban sani ba. Ko
minti daya banyi ba kuwa baccin ya dauke ni



Cikin baccin naji kamar muryar Farhan tana magana da Umar, na dan bude idona kadan sai na ganta a
tsaye tare da Amira, nayi kokarin tashi amma kaina yayi min nauyi sai na mika mata hannu "Farhan" ta
karaso inda nake ta rike hannuna



"Amarya. Kar dai baki da lafiya ne, mu da muka zo ziyara" bance komai ba Umar yace "eh bata jin dadi.
But tasha magani kuma na bata maganin bacci dan ta huta sosai. Ku barta tayi baccin in ta tashi zata ji
dadi sosai" daga nan na koma bacci na.



Sanda na kuma farkawa wajen karfe biyu, naga Amira tana zaune da remote a hannunta tana kallo, na
dafe kaina tare da kokarin tashi zaune ina cije lebe da tunanin zanji ciwo a kasa na amma sai naji babu
kamar yadda nayi tsammani, sai dan ciwon jiki kadan da kuma wani feeling na yaji yaji a kasan.
Amira ta gaishe ni tayi min sannu sannan naga Farhan ta fito daga kitchen, ita ma tayi min sannu sai na
tashi na shiga toilet nayi alwala nazo nayi sallah ta. Ina idarwa Farhan ta zubo mana abinci muka hadu
muka ci, tana ta yi min labarin gida da abubuwan da suke latest a gidan "Abba ya bawa yaya shamsu da
yaya Aminu kudi zasu shiga kasuwanci da sunan sa, duk wata zasu ke kawo masa abinda aka samu na
riba" na gyada kai cikin fahimta. Sai dai ina fatan bai yi mistake ba, saboda su din masu iyali ne kuma naji
ance ba'a trusting namiji mai iyali da kudi, amma bance komai akan hakan ba dan bana son Farhan tayi
min mummunar fassara.



Ni kuma na bata labarin yanuwan Umar da suka zo min ziyara da kuma zuwan mu gidan su. Ta matso
kusa dani tana yi min rada "to wannan rashin lafiyar fa? Anya kuwa ta gaskiya ce?" Ta karasa tana kashe
min ido, na dake ta a kafada ina dariya sai tace "dan Allah bani labari, ya kika ji? Da ciwo sosai" she
looked concern sai na tuna da nima nawa tsoron.



Sai na girgiza mata kai, "ba irin ciwon da muke tunani bane ba fa, da ciwo dai amma ba sosai can ba. Ba
irin wanda muke karantawa a novels bane ba, ba'a suma kuma ba'a wani fitar da jini kamar an yanka
rago" mukayi dariya tare sannan ta kara matsowa "bani labari mana" na harare ta "ke zancen manya ne
fa. Duk abinda kike so kiji zaki sani ne wata rana, duk kuma bayanin da zan miki ba zaki fahimta ba sai
yazo kanki"



Ta tabe baki sai ta fara bani labarin irin damuwar da take ciki yan kwanakin nan da bana gida, kowa ya
saka mata ido, dangi kowa zai tafi sai yace "ke yaushe ne naki bikin?" Ko kuma "saura ke, ai da an sani
ma hada ku akayi aka huta" Abba kuma yakan ce "hada sun naso inyi ai, ita kuma taki fito da mijin"



Ta juya hannu, "ni makaranta ma nake so ya barni in shiga wallahi. Ga result dina yana da kyau, gashi
bana komai a gida, ban san me yasa ba zai barni in yi karatu ba kafin Allah ya kawo mijin".



Sai nayi ta lalashinta da bata shawarar da nake ganin zata bulle mata "hakuri". Muka tashi muka gyara
gurin muka tafi kitchen, tare da ita mukayi ta duba kitchen appliances din wadansu ma bamu san yadda
ake amfani da su ba sai mu karanta manual, muna fitowa ta tambaye ni "amma dining table din nan ba
Abba ne ya siya ba ko?" Nace "eh. Daddyn su Aira ne ya siya min a matsayin gudummawa" ta shafa shi
"yayi kyau

21 / 101