Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
ba.
Tare muka fita na raka shi har gaban motarsa, cikin tsokana yace "ko in sace ki ne mu tafi gida na? Kinga
babu kowa a layin nan babu wanda yake ganin mu" sai na ja da baya duk da nasan wasa yake ina
murmushi, yayi dariya, "wata rana anan za'a zo da motoci a daukar min ke zuwa gidana" sai na juya da
sauri na koma ciki, amma sai na kasa shiga na labe a corridor ina leken sa sai da ya shiga mota ya bar
layin sannan na shiga ciki.
*Kar ku ce ban gaya muku ba, duk wadda bata sayi littafin nan ba tabbas ta bar dadi*
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*Episode Seven: The Ladies' Doctor*
Kamar yadda yayi alƙawari haka ya dawo washegari da yamma ya kawo min form din, sai dai cikin sauri
yazo ina karba ya juya ko godiya bai tsaya nayi masa ba. Na shiga gida da takardar a hannuna jikina a
sanyaye dan bansan abinda zai biyo baya ba. A cikin daki na samu Umma tana sorting kayan da aka kawo
daga gidan wanki, na zauna a bakin gado tare da mika mata takardar. Fuskar ta da alamar tambaya ta
karba tana dubawa tare da tambayar "takardar menene?"
Nayi shiru ban amsa ba sai da ta karanta heading din sannan tace "wannan ai kamar form ne na school
of nursing" na gyada kai "eh Umma, Umar ne muka yi magana da shi nace ina son nursing sai kawai ya
siyo ya kawo min, kuma yace in cike kafin ya dawo zai karba" ta fara girgiza kanta "kinsan babanku ba zai
yarda ba, babanku ba zai bari ba, me yasa kika karba?" Naji hawaye ya taho min,
"Umma kawai na gaya mishi ina son karatu ne, kawai na gaya mishi ina son nursing ne, shine ya siyo min.
Umma yanzu in ban cike ba in yazo karba me zance masa kuma?" Ta ajiye takardar tare da cigaba da jera
kayan da take yi amma daga ganin fuskarta kasan a cikin tunani take, sai ta juyo tana kallo na sannan
tace "idan baban ku ya dawo in an jima, in yana zaune shi kadai kije ki same shi ki kai masa takardar ki
gaya masa yadda kuka yi da Umar din, sai kiji abinda zai ce, in Allah ya dora mu a kansa sai ki ga ya bari
tunda naga kamar yana son Umar din, in kuma bai bari ba sai ki hakura ki gaya wa Umar din gaskiya ba'a
barin ku kuyi karatu a gida sai in kunyi aure, in yaso in da gaske yake maganar auren da kuma maganar
karatun sai ya bari in kinje gidan sa sai ya saka ki a can".
Na share hawayena tare da gyada kaina, already har na fara karanto adduoin da zaku dora ni akan Abba
dan ban san yadda zanyi wa Umar bayanin bama karatu sai a gidan miji ba, it will sound like ina gaya
masa aure za'a yi min yayi gaggawar fitowa, ni kuma pride dina bazai barni in fadi haka ba.
Ina daki naji shigowar Abba bayan Sallar magrib, ina ji kuma Hajiya ta hau saman ta kai masa abinci,
amma nasan zai sauko yaje masallacin isha itama kuma zata sauko kuma in ya koma sama zai ji labarai
ita kuma zata yi kallo a kasa ba zata koma ba kuma sai goma da rabi zuwa sha daya. Wannan lokacin
shine target dina.
Sama sama naci abinci, Farhan kuma tana waje tana zance da Sulaiman, ina jin Abba ya dawo ya koma
sama sannan naji ya kunna radio, na tashi na shiga daki na dauko form din na saka hijab dina na fita, na
jima a tsaye ina karanto adduoi sannan na hau. Yana baranda yana kwance akan karamar katifar da ake
shimfida masa anan musamman idan babu nepa, nayi sallama ya amsa sannan na durkusa daga dan nesa
da shi kadan.
Ya rage radion sa kadan sannan yace "Hauwa'u? Ya akayi?" Na fara inina "Abba dama.......uhm dama
zuwa nayi.....uhm takarda ce dama.....? Ya mike zaune "ki gaya min abinda kike so ki fada, ko kuma ki
tashi ki koma in kin shirya sai ki dawo. Wacce takarda kike magana akai?" Nayi sauri na mika masa Form
din hannuna inajin hawaye already yana tahowa, na tsani wannan saurin kukan nawa amma hali na ne a
jikin rai na yake.
Ya karba yana haska touchlight dinsa a kai, nayi saurin cewa "Umar ne ya kawo min dazu, nima ban san
zai kawo ba kawai dai nace masa naji kace kana so inyi nursing shine ya kawo min form" ya dago ya kalle
ni sannan ya mayar da kansa ya na karanta takardar, jin yayi shiru kuma bai wurgo min takardar ba ya
saka na samu courage din cigaba. "Shine na kawo maka dama in gaya maka, sai in ka yarda kuma kace in
cike sannan sai in cike, in kuma kace a'a sai in mayar masa" ya ajiye takardar yace "wannan takardar
wahalar samu ne da ita, ya akayi ya samu cikin sauki?"
Nace "akwai abokin sa a gurin, kuma shima kaga kusan duk harkar su ce" ya sake yin shiru yayin da
zuciya ta take bugawa. Sai kuma ya gyara zama yace "naga kamar da gaske yake, tunda har sai daya bi ta
gurin aboki na sannan yazo gare ni. In har aurenki zai yi da gaske to zabin sa ne kiyi karatu ko a'a, amma
ni inaso kiyi din, sai dai nafi son kiyi a gidan mijinki" ya miko min takardar "ki je ki cike ki bashi, sannan in
har yayi kokari ya samo miki admission din to ki karba, amma duk sanda nayi niyyar aurar dake kuma aka
ce masa ya fito yaki sannan wanda yazo da gaske zai aure ki yace baya so to zaki ajiye karatun duk da ina
so kuma kema kina so amma aure yafiye miki komai".
Tunda kunne na ya jiye min cewa ya amince sai ya toshe saboda murna, sauran sharadin ma duk ban ji
su ba na fara zuba godiya cikin murna sannan na karbi takardar na sauko da sauri ina hada stairs bibbiyu,
ina saukowa Farhan tana shigowa ta dawo daga zance, na rungume ta ina tsalle, Umma da take dakin ta
take jiran saukowa ta ta fito da sauri, tana gani na tasan nayi nasara sai ta fara tayani murna
"alhamdulillah, Allah na gode maka" Farhan ta rike ni "ke lafiya?" Na dan tsaya da murna ta nace
"Farhan, Abba ya amince za'a nema min admission a school of nursing"
Ta karbi takardar da sauri "what?" Nace "da gaske wallahi, Umar ne ya siyo min" Umma ta karba a
hannun ta "kawo nan kar ku yaga" Farhan ta mika mata sannan ta fara tayani rawar da nake yi muna
zagaye tsakar gida, Hajiya ta fito hannunta rike da charbi "menene naji ana cewa? Hayaniyar menene
kuke yi haka?" Farhan tace "Hajiya kinga Jidda saurayinta ya samo mata makarantar karatun nursing,
kuma Abba ya barta zata yi"
Sai Hajiya ta saki charbin hannun ta tana karasa fitowa daga dakin ta zuwa kan baranda. "Menene?
Karatu? A gidan nan? To wallahi ba'a isa ba, chafdi, wato ni yayana an tauye su an hana su karatu sai da
abin yazo kan ƴaƴan shafaffiya da mai sannan za'a bari ayi? To wallahi yadda suma ba suyi ba itama ba
zata yi ba. Uban kuturu ma yayi kadan"
Umma wadda kamar jira take yi tayi farat ta bayar da amsa "yana sama, wanda ya bari ayi din yana sama
sai kije ki gaya masa uban kuturu ma yayi kadan" Hajiya tace "ai yana jina daga nan ma, ba zai yiwu ba
wallahi, na gaji da rashin adalcin da ake nuna min a gidan nan ni da yayana wallahi. In kuwa za'a bar
Jidda tayi karatu to kuwa dole ne a samo wa Farhan itama su tafi tare"
Sai muka ja da baya ni da Farhan muna kallon su, dama haka muke yi kullum in suna maganganu irin
wadannan kuma ko sun gama ba zamu mayar da baasi a tsakanin mu ba, Abba ya leko ta saman sa yace
"nine mai gidan kuma ni nace tayi, idan akwai wanda zai hana yazo ya hana, itama Farhan in wanda zai
aureta ya amince tayi to zata yi, amma ni ba zan nema mata ba kamar yadda itama Jidda bani na nema
mata ba" daga haka ya koma, muna jinsa ya shige dakinsa ya turo kofa.
Ni dai wannan bai hana min farin ciki na ba. Da safe kuwa da yaya Tahir ya shigo na saka shi a gaba sai da
ya taya ni muka cike form din tare, bani da passport photograph ma amma a ranar ya kai ni akayi min
two minutes nazo nayi attaching. Da dare da aka zo kirana sai naji dadi na dauko takarda ta na fara shiri,
sai da aka ce Musa ne sannan kuma raina ya baci na ajiye takardar na lallaba zuwa soro nace da yaron
yaje yace bana nan, na dan jima kadan a gurin sannan na koma nace da Umma har ya tafi wai sauri yake
yi.
Umar din da nake jira kuma vai zo ba a ranar sai washegari da yamma sannan aka sake aikowa ana
kirana amma this time around ma sai aka kuma cewa inji Musa. Na maze nayi kamar banji ba, niyya ta
yau ma inki fita, amma Umma ta matsa min sai naje "babu kyau wulakanta mutum. Ki je ko gaisawa ne
kuyi a hankali Allah zai raba ku lafiya. In kuma shine mijinki babu yadda zaki yi" sai naji raina ya kara baci
da maganar ta ta karshe duk da nasan cewa gaskiya ne. Amma ina rokon Allah kar ya kaddara min auren
wanda bana so, sai dai abinda ban sani ba a lokacin shine wata kaddarar tafi wata tashin hankali.
Ban ma bude masa sitting room ba dan kar ma ya zauna balle yayi tunanin yi min hira, a tsaye na gaishe
shi ya amsa yana kallon kofar sitting room din amma na dauke kaina nayi kamar bansan me yake yi ba.
"Gani ance kana kirana" ya dan yi jim sannan yace "kin san dalilin kiran naki ai ko?"
Nayi shiru. "Jidda me yasa kike rufe min duk wata kofa da zata sada ni da zuciyar ki ne? Me yasa ba zaki
bani dama ba?" Na dan kalle shi "to ba gani na fito ba? In bana so in baka dama ai ba zan fito ba ma ko?"
Yace "Kamar yadda baki fito ba ranar nan? Ki ka ce ace ba kya nan?" Nayi shiru ina jin nauyin sa, ashe
yasan ina gida a lokacin.
Ya cigaba "yanzu ma jikina yana bani cewa matsa miki aka yi kika fito, dan gashi ko gurin zama kin ƙi ki
bani" a raina nace wannan mutumin ko dai dan duba ne? Allah dai ya shiga tsakanin nagari da mugu. Sai
nace "ina wani abu ne a cikin gida shi yasa, bana so in dade sosai" ya danyi yar hirarsa shi kadai wadda in
za'a yanka ni bansan me yake cewa ba, a karshe ya hakura yayi min sallama ya tafi.
Washegari Umar ya dawo. Wannan karon bayan magrib yazo kuma tun a aiken farko yace ace inji Umar,
nayi kokari sosai wajen boye excitement dina, Amira harda riga ni shiryawa wai zata je ta gaishe shi sai
da Umma ta hana ta "bana son kwadayi, dan ya baki kudi ranar nan shine zaki koma masa?" Ta hakura ta
zauna amma ranta bai so hakan ba. Ni kuma na shirya na saka hijab dina na dauki takarda ta na fita.
Sai da na bude kofar sitting room din sannan na leka waje, yana tsaye a gaban motar sa idonsa yana
kallon kofar da yake saka ran zan fito. Muna hada ido yayi min murmushin da naji shi a ko'ina na jikina,
ban san sanda na mayar masa ba sannan ba tare da nace komai ba na koma ciki shi kuma ya biyo ni.
Ganin yana zama a kasa ya saka yau na riga shi zama a kasan. Shima ya zauna sannan na gaishe shi. "Ya
mutan gida? Ina Amira" "tana ciki" na amsa "ina Farhan? Ita ba zata zo mu gaisa ba?" Nace "zata zo
mana, ba ka neme ta bane ba" yace "ita ma Amira ai ban neme taba, dan tana da kirki ne ya saka tazo"
nace "wato Farhan bata da kirki kenan ko? To sai na gaya mata" ya daga hannu "kar ki hada ni da ita,
dan naga alama a gurinta ne zan kafa gwamnati na. Nayi murmushi "tabbas. Dan ita ce babbar aminiya
ta" yace "har Mufida? Sai na gaya mata"
Na danyi dariya "kar ka hada ni da ita, dan naga alama nima ta gurinta zan kafa tawa gwamnatin" yayi
dariya sosai sannan yace "tabbas, dan kaf sisters dina nafi ji da ita, but she is a little bit stubborn, abinda
na fahimci shine ya karfafa kawancen ku" na rike baki "ni yanzu stubborn ce?" Yace "sosai ma, gashi har
yanzu kin ki cewa I love you Umar" na jawo hijab zan rufe fuska yace "na daina tsokanar ki, dan Allah kar
ki hana min kallon kyakykyawar fuskar ki mana, dan Allah" ya fada murya kasa kasa yana hade
hannayensa alamar roko.
Na saukar da hannu na kasa amma na kasa daga ido na dan ina jin idanuwan sa akan fuskata. Na fara
wasa d band din hannuna, sai naji yace "ni fa kishi ne dani" na dago ido nace "kishin me fa?" Ya nuna
band din "wannan" nace "wannan kuma? Menene abin kishi a wannan?" Yace "ina kishin attention din
da kike ba shi, sai zuciyata take gaya min kamar wani ne ya baki shi" na bude ido "wani kuma? Wallahi
ba wani ne ya bani ba, yan sport club din makarantar mu ne suka bamu as soveniers, in baka yarda ba ka
tambayi Mufida"
Yace "ban yarda ba, ita ma kuma in ta gaya min ba zan yarda ba saboda duk bakin ku daya" nace
"gaskiyar kenan. Wallahi" yace "kina so in yarda?" Na gyada kai sai ya miko min hannun sa yace "ki bani.
Nasan in na wani ne ba zaki bani ba. In baki bani ba zan tabbatar saurayi ne ya baki" na fahimci wayo
yake son yi min amma babu yarda zanyi sai na cire na mika masa, sai kawai naga ya karba ya saka a
hannun sa.
Nace "yayi maka kadan ai" ya nuna min hannun, "yayi min dai-dai dai. Dama ai ke yayi miki yawa" na
kalla naga yadda yayi masa kyau sosai a kan farar fatarsa kuma ya dace da zobban azurfar da suke
yatsunsa. Ya karanto rubutun jiki "beauty Queen. Lallai ko waye ya bada wannan sunan da zan ganshi da
sai na bashi kyauta, ya bawa Baby na sunan daya dace da ita"
Nayi murmushi ina so in mayar masa da kalaman sa in gaya masa shima kyakykyawa ne amma kunya ta
hana ni, sai na wayance da zuwa kiran Farhan su gaisa, daga nan sai hirar ta koma mu uku a inda yayi ta
bamu labaran sanda yake makaranta da irin wahalhalun da yasha a wajen karatu. Sai bayan ishai sannan
yayi mana sallama na raka shi bakin mota ya shiga. "Bye Baby" ya fada yana murmushi sannan ya tafi.
Sai bayan ya tafi sannan na tuna da takardar dana fito da ita zan bashi amma tunda na dora ido na
akansa na manta batun takarda. Gashi bani da number din sa ballantana in kira shi kuma na san ba
karamin fada Umma zata yi min ba in taji ban bashi ba, Sai na koma na dauke ta na daga kujera na saka
ta a can ciki yadda babu wanda zai ganta da niyyar in ya dawo sai in bashi.
Zuciyata fes na koma cikin gida, muka ci abinci muka sha hirar mu a tsakar gida sannan muka je muka
kwanta, sai dai muna kwanciya Farhan ta dauko wata maganar data bata min farin ciki na "gyneacologis
ko?" Nace "eh, me yasa kika tambaya?" Ta danyi dariya "ni tunda ya fada kawai naji kunyar sa ta kama
ni" na mike zaune "saboda me?"
Ta mike itama "Jidda likitan mata fa kenan. Hakan yana nufin duk wani abu da kike dashi a jikinki har ma
wanda baki san kina da shi ba shi ya san da shi. Hakan kuma yana nufin duk sanda yace ya tafi gurin aiki
to y tafi duba mata ne, in nace duba mata ina nufin parts na mata, including the most private parts. Duk
patients dinsa fa mata ne"
Naji wani abu mai zafi ya taba zuciyata, na fara kokarin neman amsar dazan bata amma na rasa sai ta
koma ta kwanta cikin tsokana tace "daga yau ki saka a ranki yasan komai da kike boyewa a cikin hijab
dinki" na daka mata duka a baya "karya ne wallahi. Yasan dai na wasu marasa lafiya amma ba nawa ba"
ta tashi tana sosa inda na dake ta tace "da naki da nasu duk daya tunda duk mata ne" nace "a'a wallahi,
bai san nawa ba kuma nawa special ne ba irin na kowa bane ba" na kwanta ina kallon ceiling amma
zuciyata tana kuna, ita kuwa dariya take yi, da alama bata san irin ciwon da maganar ta ta ji wa zuciyata
ba.
Har sai da ta gama dariyar ta sannan nace "kuma ai aikin sane haka, aiki yake yi ba wai kalla yake yi dan
yana son ya kalla din ba, babu komai a zuciyarsa sai neman yadda zai warkar da patients dinsa" sai data
tashi ta matsa sannan tace "bayan kalla har tabawa yake yi" tayi tunanin zan kai mata duka ko wani abu
amma sai n juya baya na ina jin raina yana kara baci, sai na samu kaina da tambayar kaina me yasa Umar
ya zabi ya zama likitan mata?
Why not likitan yara? Ko likitan maza jinsin sa? Ko kuma likitan daya daga cikin manyan cututtukan da
suka addabi al'umma. Why likitan mata? Amma sai zuciyata wadda take a cike taf da soyayyar sa ta
bashi uzuri da cewa idan har maza basu karancin bangaren mata ba to za'a samu matsala a bangaren
tunda mata basu cika samun damar yin karatu kamar maza ba, he is just doing a job to earn a living and
save lives.
Washegari ya dawo, amma kamar ranar daya bani takarda yau ma mota ya tsaya "na manta ban karbi
form ba, I hope kin cike?" Na gyada kai "na fito dashi ma jiya zan baka kuma sai na manta" yace "nima
mantawar nayi, da maganar nazo a raina amma ina ganin ki na manta da komai sai ke" nayi murmushi
kawai dan nima hakan take, sai na koma n dauko masa na dawo