Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
na hakura da kallon na sunkuyar da kaina ina kallon
kafafuwana da suke cikin safa a kuma cikin sandals, ba wai dan kafafuwan suna birgeni ba sai dan bani
da wani zabi.
"Jidda" ya sake fada, zuciyata ta motsa a cikin kirjina. Mufida ta taba ni "ki gaida yaya Doctor yana yi miki
magana" "ina ruwanki" ya fada. "In bata gaishe ni ba ina ruwan ki. Chakwaikwaiwa!" Tayi dariya "kai
Yaya, kawai dai ranta a bace yake tun safe, abbanta ne yazo ba ummanta ba shine take ta fushi" ya gyara
tsayuwar sa yace "haka ne? I see. Wato ba kwa son maza suyi visiting dinku kunfi son mata ko? Shi yasa
ni ma tunda nazo baki ko kalle ni ba sai kika barni da leke ta window ko? Yayi kyau"
Ta kama hannunsa, nabi hannun da kallo ina lura da zobban azurfa guda biyu dasuke jere a middle finger
dinsa da manuni, "ha! Yaya, wallahi ban san kana cikin mota ba" ya karbe hannunsa "inafa zaki sani?
Kina can kina daddanne min uwa. Kina can kina introducing friend dinki to all but me"
Ta dawo kusa dani ta dafa ni "Jidda kenan. My very best friend" ta nuna shi "Jidda ga yaya Faruq, my
favorite brother. One in million" ya sake yin murmushi mai sauti. "Dadin baki ko? To ko kwandala ba zan
baki ba" na dan russuna, still kaina yana kasa "ina wuni?" Yayi shiru amma ina jin idonsa a kaina, "bana
amsa gaisuwa sai an kalle ni" Mufida tayi dariya "ba ka san Jidda ba, zaka bushe a gurin kafin ta daga kai
ta kalle ka" yace "baki san ni bane ba, bayan kallo i bet she is going to smile back at me kafin ta bar gurin
nan" ta daga kafada "okay, amma ni nasan kawata ba zata bani kunya ba"
Sai ta zagaya bayan motar ta dauka jakar ghana must go da kuma bagko guda dai dai, da kyar ta fito dasu
daga booth din sannan tace "Jidda zo mu dauka mu tafi" yayi saurin cewa "what? Wannan uban kayan
zata dauka?" Tace "zamu dauka, da ni da ita" ta fada tana nuna kanta sannan ta nuna ni, na tafi inda
take still kaina a kasa na fara kokarin kama jakar sai yazo ya janye hannun jakar daga hannuna. "ba zata
dauka ba" ya fada yana kallon Mufida" ta tabe taki ta fara yi masa shagwaba. "Ni baka damu dani ba
Yaya Doctor, ni zan dauka ni kadai kenan"
Ya danyi dariya yace "haba sweety kema kinsan kece favorite sister dina duk duniya amma ki duba
yanayin jikinki da nata ba daya bane, in ta dauki wannan kayan kafin taje hostel din ku ai ta karya kafa ko
hannu" sai naji haushin yadda yayi min kallon karama, duk da nasan Mufida ta fini ki ba amma ni ma ai
ba karamar da har za'a yi kwatance dani ba ce ba nace "zan iya fa, dazu ma mun dauki wasu kayan,
kullum ai muna daukan kaya" Mufida tace "da daukan ruwa, bucket din penti muke dauka kullum" nace
"dazu ma shi muka dauka. Am stronger than I look"
Yayi murmushi "show me" na bude ido "what?" Yace "ƙarfin" na cigaba da kallon sa cikin rashin fahimta
sai ya daga hannunsa ya nuna min kwanjin sa, ai kuwa na gani duk da ta cikin riga ne, nayi saurin dauke
kaina ina jin tsigar jikina tana tashi, yayi dariya. "Ga nawa, show me yours" Mufida tace "wow, Yaya
Doctor tsara kaga nawa nima" ta tattare hijab din ta tayi yadda yayi da hannun sa tare da daddagewa
lallai wai sai kwanji ya fito, yayi dariya yana dan dukan hannunta kadan "ji wani kwanji kamar na
kadangare" ta turo baki yace "ai kina dashi ma, kawarki ita irin na sauro ne da ita" na bata rai "sauro?
Sauro ai bashi dashi" yace "that's exactly what am saying, baki dashi" nace da sauri "ina da shi mana" ya
gyara hannunsa tare da jingina da jikin mota yace "then show me"
Muryar Mama muka ji "wai baku tafi kai kayan ba har yanzu?" Mufida ta daga murya, "Mama Yaya
Doctor ne ya hana mu dauka" ya bude ido "Mama sharri take yi min" ta murguda masa baki shi kuma
yayi mata alamar zai zaneta da hannunsa. Muka kuma yin kokarin dauka sai ya janye jakar yana kallona
yace "am serious fa, in dai ina gurin nan ba zaki dauki kayan nan ba. Baku da laborers haka da zasu
shigar muku dasu?" Mufida tace "akwai su amma sai an basu kudi" ya zaro kudi a aljihunsa idonsa a
kaina ba tare daya kirga ba ya mika mata, tayi saurin karba tana dan tsallen murna sannan ta fara waige
waigen neman mai daukan kaya.
Ya rankwafo da kansa yana kallon cikin fuska ta, muka hada ido nayi saurin kallon gefe, sai ya zagaya da
fuskar sa ta gefen da nake kallo, muka sake hada ido sai na rufe idona, ya danyi murmushi mai sauti
yace, muryarsa can kasa yadda na tabbatar ko da hankalin mufida yana kan mu ba zata ji abinda yace ba
"smile, please". na sake rintse idona ina jin muryar sa a jikina tana zuwa har inda banyi tunanin murya
tana iya zuwa ba, ina jin yakin da ake yi a tsakanin ƙwaƙwalwa ta da kuma zuciyata, zuciyata which
already belongs to him tana son yin obeying din umarninsa, yayinda ƙwaƙwalwa ta take kokarin cigaba
da maintening dignity dina. "Smile, ko da dan kadan ne, ko da iyakacin lips dinki ne, ko da bai gama
zagaya kyakykyawar fuskar ki ba"
Na sake juya fuskata gefe, zuciyata tana so ta cigaba da zama a wajen tana sauraron muryar sa yayin da
ƙwaƙwalwa ta take gayamin "run!" Yace "bude idonki ki kalle ni, ko ba zakiyi murmushi ba ki kalle ni
kawai kafin ki tafi, dan Allah" na juya masa bayana sannan na bude ido na naga Mufida tana bawa masu
shigar da kaya sako, sannan na kuma jin alamar ana kallona daga side din da yan gidan su suke, na kalli
gurin and I saw Mama, idonta a kaina da kuma wani irin yanayi a fuskarta. Daga bayana naji yace "in baki
kalle ni kinyi min murmushi ba, zan iya kwana a asibiti a yau"
Ba tare da na sake magana ko na waiwaya na kalle shi ba na bi bayan mai daukar kaya, duk da cewa
zuciyata tana kokawa, tana so ta sake kallon cikin idanunsa, Mufida ta biyo bayana da bakaken ledoji
biyu a hannunta, ta miko min daya "ai dai wannan ba zaki karye ba in kika dauka ko?" Duk mukayi dariya
a tare, duk da ni tawa dariyar bata kai ciki ba, all I wanted a lokacin is to look into his eyes again. Ina jinta
tana min hira, bansan ma me take cewa ba har muka danyi nisa kadan sannan kuma ina jin idanuwan sa
still a kaina, I can even swear cewa magana yake yi da zuciyarsa, addu'a yake yi in sake waigawa. And I
did.
Na dan dakata da takuna, ina jin kamar ba zan iya kara taku daya ba har sai na kalle shi, sannan na juya
na kalli inda yake tsaye har yanzu a jikin mota, kuma kamar yadda nayi tsammani, idanuwan sa a kaina.
Yayi murmushi sannan ya daga min hannu, and I smiled back and wave back. And then my life begins
and ended.
*💔 Jidda 💔*
*By*
*Maman Maama*
*Episode Two : Matters of the Hearts*
Free Episode
Ita zuciya, annabi yace wata tsoka ce a jikin mutum wadda idan ta gyaru to dukkan sauran jiki ya gyaru
idan kuma ta baci to dukkan sassan jiki ya baci kenan. Idan muka yi amfani da wannan maganar zamu iya
nada zuciya a matsayin sarauniyar gabaki dayan jikin mutum, wadda kuma a lokuta da dama tana
gudanar da mulkinta ne bisa son kai da son zuciya (lol) musamman in aka samu cewa shi mamallakin
zuciyar baya iya juyata ya sakar mata ragama tana yin abinda ta ke so, to ina kuma ga ni? Ni da zuciyar
tawa gabaki daya na riga na danka wa wanda bai ma nemi in bashi din ba, bai ma kuma san cewa na
bashi din ba.
Tun ranar dana fara ganin sa, ranar visiting day, ban kuma jin cewa na dawo dai dai Jidda ta yadda nake
kafin idanuna su shiga cikin nasa ba. Sau da yawa nakan samu kaina ido biyu bayan karfe biyun dare ta
wuce, kuma ba wai akan sallaya ina sallah ba ba kuma wai da littafi a gaba na ina karatun jarabawar da
aka kawo ni makaranta dan in karanta ba, a'a, na kan samu kaina ne a zaune akan gado na na jingina
baya na da pillow staring into nothing and smiling.
In kuma nayi yaki da zuciyar tawa na samu na dauki littafi na kunna fitila da niyyar karatu to bayan wasu
mintuna kadan zan iya samun kaina ina zana abinda zan iya tunawa na daga fuskarsa a bayan littafin da
ya kamata ace karantawa nake yi. Idan kuwa class muka tafi da niyyar sauraron extra lessons din da
coppers din makarantar sukan shirya mana kusan kullum dan shirin taryar jarabawar waec din da take
gaban mu, to na kan samu kaina da rafka tagumi da hannu bibbiyu, idanuna tsaf a kan malamin, faffadan
murmushi akan fuskata amma kuma sam babu abinda nake ji ko gani a abinda yake yi kuma yake fada,
sau da yawa fuskar yayan kawata na kan gani a fuskar mai koya mana karatun, da kuma muryarsa yana
cewa "smile, please".
Those were the good days....
On the bad days kuma ji nakan yi duniya tayi min zafi, in ji na tsani kaina for feeling what I was feeling,
inyi kokarin tursasawa kaina daina jin abinda nake ji din amma sai inji kamar kara hura wutar abin nake
yi a zuciyata. Nakan zauna inyi kuka a bayan idon kowa. Dama ni kuka babban abokina ne. Babu abinda
nake so illa in sake ganin sa, ko in sake jin muryar sa, ko kuma at least in ji ko da labarin sa ne, ko da hirar
sa ne ayi min. Sai dai kuma duk da halin da zuciya ta take ciki ba zan iya karya kambu na na yarinyar da
tafi duk sauran yammata aji a set din mu ba, ba zan iya gayawa Mufida feelings dina a kan yayanta ba.
Wannan zub da class ne right?
Wannan tunanin ya sa na tafi gurinta da niyyar in bugi cikinta ko zam samu abinda nake so, sai dai kuma
matsalar daya ita ce tun ranar da na ganshi din sai ya zamanto tamkar anyi min chanjin babbar kawa ta
Mufida ne da wata mai kama da ita amma ba mai halinta ba. Mufida yarinya ce mai shegen surutu, fadi
ba'a tambaye ka ba, da son iyawa. Yana daya daga cikin abinda take so shine ta tara mutane tayi ta basu
labarin gidan su da yan gidan su, kusan kaf set din mu babu wanda bai san yan gidan su Mufida ba, babu
wanda bai san Yaya Doctor ba, amma tun ranar da yazo din sai ya zamana kamar ta saka sealtape ta like
bakinta.
Na jawo kujera ta kusa da tata, nayi gyaran murya, ta dago daga karatun da take yi tayi min murmushi,
nace "na gaji da karatu wallahi, kaina ya toshe" ta dafa goshinta tace "same here, kawai yi nake yi kar
kuce bana yi" ta karashe maganar tana dariya. Nace "ni kaina ma ciwo yake yi" tace "ke ce fa health
prefect, nasan ba zaki rasa magani a jakarki ba" nace "haka ne. Daga naji ciwo nake shan abina" na danyi
shiru sai kuma nace "kuma a gida ai kunji dadin ku, gaku da Dr a gida, daga kun fara ciwo ba sai kunje
asibiti ba sai kawai ya duba ku" ta dan yamutsa fuska "eh fa. Haka ne" Sai ta ja kujerar ta baya ta mike,
"bara in dan zagaya insha fresh air ko kaina zai dan bude" na bi bayanta da kallo. She has been acting
like that tun ranar visiting, what's up?
Haka na cigaba da jinyar zuciyata ni kadai, telling my self that the feelings will go away, but they never
did, har yara suka dawo daga hutu muka kuma fara WAEC. Paper din mu ta farko bayan mun gama
practicals ita ce geography, muka shiga muka fito ba tare dana tabuka komai na kirki a ciki ba, ni kaina
nasan ko ni za'a bawa marking din paper ta ba xan bawa kaina credit ba indai ina so inga annabi. A cikin
hall din na yanke shawarar cewa in dai ina son kaina da arziki kuma ina son inga abin kirki a result dina
har in samu tafiya nursing school din da naji Abba ya ambata to kuwa dole in tattara Dr Umar Faruq
dashi da idanuwan sa da murmushin sa in ajiye su a gefe. But how ......
Ina yin sallar na tafi gurin wata yar ajin mu Ramlah. Ramlah yar soyayya ce, dan tun muna jss take da
samari kuma take zaunar damu ta bamu labaran su, dan haka sai nake ganin kamar duk ta fi mu
experience akan wannan harkar kuma maybe tana da shawarar da zata bani. But still I was not ready to
open up in yarda cewa ina son wanda bai san ina yi ba.
A dakin su na same ta a kwanar ta tana kwadon kanzo da yaji manja da yaji da albasa sai kamshi yake yi.
Na kwanta akan gadon ta ita kuma tana karasa hadawa nace "malamar soyayya nazo daukan darasi" ta
bude baki "kar dai ki gaya min finally wani yayi awon gaba da zuciyar beauty queen din mu" da haka
yawanci suke tsokana ta. Na bata fuska "neva, sai dai inyi awon gaba da zuciyar wani" na fada a raina ina
hoping ina ma dai haka ne, ina ma dai nice na tafi da zuciyarsa ba shine ya tafi da tawa ba?
Ta hawo kan gadon tana ajiye kwanon kanzon a tsakanin mu da cup din ruwa a gefe. To bani labari,
waye shi kuma me ya faru tsakanin ku? Ina so in san komai" na sake gyara fuska ta, ba zan zubar da ajina
ba fa. Nace "babu kowa fa na gaya miki. Kawai dai kinga mun kusa gama school, ina son in san yadda zan
facing rayuwa outside these walls" ta gyada kai cikin gamsuwa. "A Beauty queen like you will have a
swarm of flies after her kina fita daga school din nan"
Nayi dariya muka fara cin abincin tare sannan nace "flies kuma?" Tace "yeah, mostly flies ne, few of
them will be honey bees, amma ke kadai zaki iya tantancewa kuma kiyi filtering out flies din" na sake
cewa "okay, ta yaya zan danne zuciyata ko da naga wanda naji ina so" ta kalle ni da alamar tambaya,
"ban gane ba" nace "ta yaya zanyi unloving wanda already nake loving" ta bude ido sannan tayi dariya "I
knew it, yadda kika rame yadda kika kara yin silent akwai wani a kasa, ko kuma a sama zance ne?" Ta
sake dariya. Na bata rai "babu kowa fa na gaya miki"
Ta daga hannu, "tunda kin ce haka mu bar shi a hakan. No, bana jin zaki iya unloving wanda kike loving,
sai dai ko idan lokaci ya ja sosai kun rabu ba kwa tare to zaki iya rage son sa kiji cewa it doesn't matter
that much. Ko kuma idan yayi miki wani abu mai tsananin ciwo a zuciya, bacin rai zai iya danne soyayyar
sa amma shima bance zaki daina son sa ba" ta cigaba da cin abincin ta, yayin da ni kuma nake ta juya
spoon din data bani a hannuna, sannan tace "yadda kike ji a ranki zai ragu, with time zaki saba da feeling
din kuma zaki koyi controlling din sa, kar ki damu"
Bance mata komai ba, amma tunani na ya tafi kan cewa ban samu amsa ta ba. Kamar ta san tunanin da
nake yi sai tace "in the mean time, dole ki ajiye komai a gefe kiyi facing karatun ki" na ajiye cokalin nace
"ta yaya zanyi hakan?" Ta ajiye itama nata cokalin tana kallo na tace "ta hanyar concentrating on abinda
zai faru idan baki yi hakan ba" nace "me zai faru?" Tace "zaki fadi exams of cause, in ba ki da result mai
kyau baki da damar cigaba da karatu, in baki cigaba da karatu ba kuwa babu abinda zaki yi a rayuwa.
Worst case scenario Abba zai samar miki miji, dan abokinsa ko kuma abokin nasa ya aura miki. Wanda
kika ki karatu a akan nasa ko labarin sa ba zaki sake ji ba. That will be the end of your love story"
Na gyada kai ina relating, yayata Hudallah da akayi bikinta last year kusan abinda ya faru da ita kenan,
wanda take so ya gudu yaki auren ta, Abba ya saka ta fitar da miji ta rasa yadda zata yi shi kuma baya
barin ƴaƴan sa su dade a gida rana daya yazo yace ya samo mata miji, dan tsohon abokinsa, five months
later tana dakin mijinta, shekara ta zagayo da baby a kan cinyarta. Naji cikina yayi karar tsoro.
Ta cigaba da magana "idan kika yi karatu kuma kika ci exams dinki, kina da chance da zaki tafi school kiyi
ilimi, ki kara warewa ki kara class ki kara kyau ki kara shekaru. Add these to your beauty, wannan wanda
kike so din zai iya lasar takalmin ki dan ki bashi minti daya yayi magana da ke" na gyada kai, already ina
hango Dr Umar yana bina a baya kamar jela ni kuma ina ja masa aji son raina, yes, wannan tunanin kadai
ya isa ya saka in maida hankali na kan karatu na.
And it did.....
Ban ce na daina tunanin Umar ba amma tunanin nasa sai ya zama shi yake kara min kaimi wajen ganin
naci exams dina dan in same shi.
Farhan bata zo ba kamar yadda tayi min alkawari a letter din da ta rubuto min, haka zalika su umma
basu zo ba kamar yadda Abba yayi min alkawari, sai dai da muka yi waya a wayar wani copper da ya kan
bamu waya a boye mu kira gida, sun bani hakuri cewa basu samu dama bane ba, ni kuma nasan ba wai
dama ce basu samu ba tunda dai babu abinda suke yi a gidan, babu aiki babu sana'a, nasan dai Abba ne
bai bar su suzo ba, zai ce ne bashi da kudi ko kuma yace za'a shagwaba ni ko kuma wani excuse din da
shi kadai zai fahimci ma'anar sa.
Farhan kuma da yaya Mukhtar da Aunty Halima, nasan Hajiya ce zata hana su zuwa. Wannan bani da ko
shakka akai.
Lafiya lau muka cigaba da exams din mu, na cigaba da rike kambu na, na cigaba da tabbatar wa cewa
Mufida bata san cewa akwai wani abu a zuciya ta a dangane da yayan ta ba. A haka har muka zana final
paper din