Chapter 50 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   50 / 101

147K to 150K   out of 300.2K words

irin fadi tashin da
bamuyi akan sa ba babu irin ilimi da tarbiyyar da mu bashi ba, kuma idan baki sani ba bara in sanar da
ke, babu irin yammatan da basu so shi ba, wadanda kuma suka fiki komai da komai amma shi ya nace ya
dage sai ke, mu kuma muka bi son da muka ga yana yi miki muma muka so ki sosai muka dauke ki daya
da dukkan yayan mu, ashe ke din ba yar goyo bace ba"



"Kullum na ganki sai nayi tunanin menene yake hana ki kiba, ke ba rashin ci ba ba rashin sha ba, ke ba
kishiya ba kuma ke babu abinda kika nema kika rasa amma sai bushewa kike yi a tsaye, ashe shegen kishi
kika dauka kika saka a ranki."



"Shikenan kuma dan ya aure ki sai aka ce mikin a zai kula kowacce mace ba kenan? Shi kenan sai aka ce
miki duk macen da kika ganshi da ita neman ta yake yi? Ita wannan yarinyar da kika yi magana akanta ba
Mufida ta gaya min cewa kawarki bace kuka yi fada, sai ta shirya masa sharri to gate back at you? A
tsakanin ku waye ya kamata yaji haushi? Shi da akayi kokarin batawa suna akan ki ko kuma ke da idan da
zaki saka kishi aside zaki fahimci cewa sharri ne?"
Naji hannayen Yasmin a bayana ta zagaye ni da su tana dan jijjiga ni kamar mai rarrashina. Naji Umar ya
sake magana "Mama dan Allah ki bar maganar nan haka. Rashin fahimta ne muka samu a tsakanin mu
kuma zamu warware matsalar a tsakanin mu insha Allah. Ki bar mu mu tafi gida kawai, ki manta ma da
cewa hakan ya faru"



Tace "ai ni bani na shigar da kaina maganar ku ba ita ta shigar dani tunda ita ta aiko takanas azo a gaya
min, maganganun fa su a da yawa data shishshirya wadanda ni ina ji na fahimta cewa shiri ne, raina ya
baci ne kawai saboda banyi tsammanin haka daga gareta ba, shi yasa na nuna mata bacin raina dan ta
kiyayi gaba kuma ya zama warning a gareta cewa ni ba zan bar dana guda daya a duniya ya zama bawan
mace ba, tunda duk abinda ake mata bata gode Allah ba yanzu kam sai mu saka kafar wando daya ni da
ita mu gani, dan halak ka fasa"



Ya sake cewa "Mama please" tace "kasan Allah in ka kara yi min magana sai na fasa bakin ka, banza
shanyayye. Ni bansan yadda akayi ka koma solobiyo ba wallahi, ina zafin ka yake ina zuciyar ka take da
har mace zata samu uwarka ta gaya mata wadannan maganganun amma ka zauna kana kare ta kuma"



Haka ta cigaba da fada sai da ta wanke ni tas a gaban Umar, wai Umar ni ma mai bada hakuri, karshe sai
ta hada dashi tayi masa fadan me yasa yake kare ni. Sai da tayi ta gama dan kanta sannan tace mu tashi
mu tafi. Yazo ya kama hannuna ya mikar dani tsaye, ban musa mishi ba dan na tabbatar in na tashi
faduwa zanyi dan jiri kawai ne yake dibana, sai daya kai ni mota na shiga sannan ya saka yara a baya ya
tashi motar muka tafi.



Muna fita daga gate din gidan na juyo ina kallon sa nace "gidan mu zaka kaini" yayi banza dani kamar bai
jini ba, na sake maimaita wa ganin ya dauki hanyar gida, "Umar ka kaini gidan mu na gaya maka, wallahi
ko ka kaini gidan ka sai na fito, yau a gidan mu zan kwana"



Ya juyo ya kalle ni, fuskar sa da alamar bacin rai yace "da iznin waye zaki je gidan? The last time I
checked ni mijinki ne kuma sai na baki izni sannan zaki je ko kofar gida ne" nayi shiru na kwantar da
kaina a jikin kujerar mota amma a raina ina lissafa ko sama da kasa zasu hade sai naje gida gida sai dai
ayi wacce za'a yi. Ai nima ina da iyayen kuma nima iyayena suna sona.



Sai dai su suna da kawaici da sanin ya kamata. Ko kuma ince suna ganin suna da sanin ya kamata bayan
ba wai kamatar yayi ba.
Sai naji ya cigaba da magana



"Why Jidda why? For God's sake what were you thinking? Ta yaya zaki samu mahaifiya ta wadda ta kawo
ni duniya ki fada mata wannan maganar" na juyo ina kallon sa nace "kasan dalilin da yasa na gaya mata?
Saboda ita ta kawo ka duniya kuma ita ya kamata kake kunsawa bakin cikin ka bani ba, na gaya mata ne
dan zuciyarta ta buga maybe in bakin cikin ka yayi ajalinta sai kasan cewa ba daidai kake yi ba"



Yayi saurin yin packing a gefen titi ya juyo "what????" Na dauke kaina "in kaji haushin abinda nace ka
kaini gidan mu, ka hada min da takarda ta" yayi shiru yana kallona sannan yace "okay, ranki a bace yake I
get it. Ni kuma ba zan kula ki ba, sannan kuma gida nace ba zaki je ba" ya sake tayar da motar ya cigaba
da tafiya.



"Maybe sanda kika gaya wa yaya Mubaraka maganar nan you though you were doing the right thing, but
yanzu na tabbatar kin fahimci cewa it was not the right thing. Gashi kin jawo wa kanki fada a gurin
Mama, na tabbatar baki san halin fadan Mama ba amma yanzu kin sani. But ni abinda ba gane ba shine;
na dauka mun gama maganar nan tuntuni, just because I confessed to you cewa da ina neman mata
doesn't mean yanzu ina yi, ba na gaya miki na daina ba? Sau nawa ina gaya miki na daina wai? Me yasa
ba zaki yarda dani ba wai Jidda? Abinda yafi komai kona min rai shine rashin yarda dani da kika yi kuma
har zaki nuna min kin yarda da abinda nace sannan ki zagaye ki gaya wa Mama. Kina tunanin Mama zata
yarda......"



Nace "zata yarda, da ace ka gaya mata gaskiya da zata yarda. Zata yi bakin ciki tabbas amma ba zatayi
disowning dinka ba kuma zata yi maka abinda nake yi maka kwadayin samu wanda dalilin sane ya saka
na gaya mata din, zata yi maka addu'a. Za ta kuma iya sakawa shima Baba yake yi maka addu'a. Tare da
support din su da addu'ar su zamu ga karshen matsalar nan. Wannan shine dalilin da yasa na gaya mata"



Sai kuma ya saukar da murya kasa "Jidda wai addu'ar menene Mama zata yi min ne? Me yasa wai ke
baki yarda cewa na daina din ba?" Na girgiza kaina "saboda baka daina ba. Saboda karya kayi min da
kace baka nemi Maryam ba. Na sani ka neme ta"
"What?....... How...... Ta yaya ma zaki ce haka? Bayan ga bayani nayi miki kuma har police sun kama
yarinyar nan ta kuma yi accepting laifin ta shiga office dina tayi min sata kuma na gaya miki a lokacin ne
ta chanja band din bansan kuma me kike so in ce miki ba. Ban san me yasa baki yarda ba"



Nace "guilty look din daya ke kan fuskarka a lokacin da kayi min wannan bayanin shine dalilin da yasa
ban yarda ba, kuma look din shine yanzu ma akan fuskarka. Abinda baka sani ba Umar shine karya a baki
kawai ka iya yin ta amma baka iya controlling emotions dinka. Abinda bakinka yake fada daban abinda
fuskarka take nunawa daban. Farkon auren mu bana ganewa sai daga baya na kara fahimtar ka.A duk
lokacin da kayi min karya ina ganewa sai dai nakanyi shiru dan a zauna lafiya. Ka nemi Maryam, that's a
fact, kuma in har yanzu baka yarda ba to kayi rantsuwa da Allah cewa baka neme ta ba"



Nayi shiru ina kallon sa amma bai ce komai ba kuma bai kalle ni ba. Sai na cigaba "sanin ka nemi Maryam
shi ya sa nayi tunanin sanar da iyayenka ina yi maka kwadayin addu'ar su, dan na fahimci tunda har ka
iya neman kawata to Allah ne kadai yasan yawan wadanda kake nema, maybe har a cikin yan'uwa ma,
natan ne dai ya fito tunda tayi niyyar tona maka asiri a guri na"



A lokacin muka shiga gida yayi packing ya juyo "Jidda" na daga masa hannu "please ka rike maganganun
ka bana son ji, not now please"



Muka yi shiru muna kallon juna, sai a lokacin muka ji sheshshekar kukan Yasmin. A tare muka bude kofa
muka fita muka kuma bude kofar baya a tare, na riga shi daukan ta na rungume ta ina shafa bayanta
"Yasmin? Menene kike kuka?"



Ta dago kai tana kallona "ba Mama bace tayi miki fada kuma shine kuke fada ke da Daddy"



Na sake rungume ta ina jijjiga ta kadan, a raina ina mamakin wayon yarinyar "ba fada muke yi ba Yasmin,
magana kawai muke yi kinji" ya zagayo ya miko hannu zai karbe ta sai na wuce shi na tafi cikin gida shi
kuma ya dauko Asad da yake ta baccin sa hankalinsa a kwance.



Ya wuce dashi daki ya kwantar dashi, ni kuma na zauna a palo da Yasmin a jikina ina rarrashin ta. Sai
gashi ya dawo da magungunan da ya siyo min tun a asibiti a hannun sa da kuma robar ruwa, ya ajiye min
a gefe na sannan ya saka hannu ya dauki Yasmin "Yasmin, mu je daki ki kwanta kinji, ki bar mommy
kinga bata da lafiya, yanzu ma zanzo inyi mata allura, shi yasa dazu a mota take cewa bata so ni kuma
nake cewa sai nayi mata, wai ita tsoron allura take yi. Ba fada muke yi ba kinji mamana?"



Da haka suka shige ciki ni kuma na kwanta akan kujera na rufe ido na ina sauraron yadda kaina yake
tsananin sarawa, trying so hard not to think about maganganun Mama. Motsin sa naji ya dora hannun sa
akan nawa da yake kan goshina. "Ciwon kan ne ko? Ki tashi ki sha magani"



Na dan bude ido na kadan na kalle shi ina jin haushin yadda fuskarsa take nuna damuwa a kaina. Na ture
hannun sa daga kan nawa "ina ruwanka da shan magani na? Ina ruwanka da lafiya ta?" Ya zauna a gaba
na tare da bare maganin sannan ya bude robar ruwan "dan Allah ki sha, in kika samu lafiya zamu zauna
muyi maganar kinji?"



Nace "babu wata magana da zamuyi ni da kai, saboda mun gama magana tsakanin mu ya saka na kai
maganar gurin iyaye dan nayi tunanin zasu fahimta za kuma a samu maslaha, I was wrong, amma yanzu
ma ba zan hakura ba, gurin nawa iyayen zan kai maganar tunda Allah yasa nima ina da iyayen kuma suna
so na nima"



Yace "Jidda please, ki daina maganar zuwa gidan nan dan Allah. Ni bana so maganar nan ace ta kuma fita
daga tsakanin mu, we i solve this together, ni da ke" na jiya kaina "I thought we can, tunda nasana
halinka I kept thinking I can change you, yanzu na fahimci I can't, tunda har ka iya neman kawata nan
gaba ban san wadda zaka nema ba kuma, Amira? Ba zan jira gar sai hakan ya faru ba. wallahi Umar a
yanzu abinda yasa kawai nake cikin gidan ka gida daya ne, saboda bani da lafiya nasan ko bakin titi ba
zan iya zuwa ba, amma duk sanda naji sauki abu daya ne zai hanani tafiya gidan mu"



Yayi saurin rike hannuna tare da cewa "menene? Me kike so?" Nace "ka koma gida ka samu Mama ka
gaya mata cewa duk maganar da na fada gaskiya ce, kayi mata admitting mummunar dabiar ka kamar
yadda kayi min, sai kuma ka roke ta take maka addu'a ta kuma baka shawarwari"



Ya fara girgiza kai "Jidda Mama fa kike magana akai, mahaifiya ta ta yaya zan iya gaya mata maganar
nan. Dazun ma ba wai dan in bata ki naki karbar maganar ba sai dan ba zan iya ba. Mahaifiya ta ce fa
Jidda" na mike tsaye "saboda mahaifiyar ka ce shi yasa nake ganin ita ya kamata ta fara sanin halin da
kake ciki, ko ba komai nasan ba zata yi disowning dinka ba kuma ina tunanin sai tafi kowa damuwa da
kuma nema maka mafita. Amma ba zata yi hakan ba har sai ka amsa laifin ka"
Ya sake cewa "I can't, Jidda I can't" na fara tafiya "then I have nothing more to do with you, daga na
samu lafiya zan kama hanyar gidan mu tunda ni ma haifata akayi, nima kuma nawa iyayen suna so na
kamar yadda nake son su"



Ya riko hannu na ya mika min maganin, "to naji, ki sha magani amma, kinga in baki sha ba ai ba zaki
samu lafiyar ba" na karba na jefa a baki na kora da ruwan da ya miko min sannan na wuce shi na shiga
dakina na kwanta. Na fara tunanin yadda tafiya ta zata kasance zuwa gidan mu da zarar na farka naji
jikina yayi karfi kuma na daina jin jiri.



Sai dai sanda na farka maimakon inji jikin da sauki sai ma karuwa da naji ciwon yayi, lokacin tsakiyar dare
ne kuma zan iy cewa ba dan da sauran kwana na a gaba ba da a daren zan bar duniya, amma da
taimakon Allah da kuma kasancewar Umar Doctor na wayo gari, da assuba ya dauke mu ni da yara ya
ajiye yaran a gidan su sannan ya zarce da ni asibiti.



Muna zuwa aka bani gado, aka kuma fara bani taimakon gaggawa saboda bayan bp na da yayi sama ga
asthma ta data tashi ta rike min numfashi na, a very dangerous combination. A dole suka saka min
oxygen sannan suka yi min allurai, Umar duk ya wani rikice, ni kuma rikicewar tasa tana kara kona min
rai da kara saka min jin haushinsa, dan haka sai kawai na mayar da ido na na rufe, a haka bacci ya dauke
ni.



Kwana na daya a asibitin ya matsa lallai sai an sallame ni, yace shi zai cigaba da kula da ni a gida, ni kuma
na lura gani nake yi insecurities ne suke damunsa gani yake yi kamar zan fi saurin tafiya gidan ne daga
asibitin kamar yadda nake ta gaya masa a duk lokacin dana bude ido na. Sai dai muna shiga gidan na
jawo jaka na fara hada kaya na kuma nace yaje gidan su ya dauko min yayana dan ba zan tafi in barsu ba.



Ya karbe jakar yana mayar da kayan ni kuma ina sake debowa ina mayar wa cikin jakar, ina sakawa shi
kuma zai dauke ya mayar cikin wardrobe. A karshe dai ya zagaye ni da hannayensa ya kankame ni a jikin
sa "Jidda, Jidda. Ki tsaya hakanan please. Listen to me please"



Na fara kokarin kwace kaina shi kuma ya ki cikani a haka muka fada kan gado, da yake ba lafiya ce ta ishe
ni ba kuma karfi na ya kare sai na kwanta lakwas shi kuma ya samu yadda yake so "dan Allah ki tsaya ki
saurare ni Jidda. I know I have hurt you more than yadda nake tunani ma, kuma da kinsan nadamar da
nake ciki yanzu a zuciya ta da kin sassauta min Jidda. Wallahi Jidda yarinyar nan ta jima tana nemana ban
taba gaya miki bane ba saboda kar ranki ya baci, ta jima tana yinkuri bani kanta kyauta, kuma....... Jidda
ban san me yazo kaina ba a lokacin dan Allah kiyi hakuri..... I had no idea plan dinta kenan..... I didn't
know what I was doing or thinking...... Jidda dan Allah kiyi hakuri...."



Na lumshe idona hawaye yana zuba daga idon nawa, hawayen da nake jin su tamkar turiri ne da yake
tahowa daga zuciya ta. Finally yayi accepting cewa yayi.



Nace "aikin gama ai ya riga ya gama ai. Ka riga ka zubar min da mutunci na ka kuma ya shi a kasa. Ka
kuma zubar da duk wani sauran abu da yake tsakani na da kai accept for yayan da suke tsakanin mu da
kuma igiyar auren ka da take wuyana. Abu dayaya rage shine a kiyaye gaba. Abinda nake tsoro shine
ranar da zan ganka in the act a cikin gidan nan tare da wata shakikiya ta ko taka"



Yayi sauri ya rufe min baki "Jidda don't say that please. Wallahi, kinji na rantse miki wallahi ko? Hakan ba
zata taba faruwa ba. Insha Allah Jidda in kika kara min wata dama, nasan banyi deserving kowacce
dama ko alfarma a gurinki ba, amma in kika bani, bazan baki kunya ba Jidda nayi miki alkawari. We have
come sooo far Jidda. Kar mu bari duk kokarin mu ya zama for nothing. Ki sake gaya min wadansu
sharudan, ko menene zan bi kamar yadda nabi wadancan"



Nace "wadancan din ai baka bisu ba gabaki daya, da nace kayi auren ai baka yi ba" ya langwabe kai
kamar zaiyi kuka "Jidda aure fa kike magana akai, shi aure ai ba haka kawai ake yinsa ba sai da niyya
tunda ibada ne kuma sai na samu wadda nake so na kuma yarda cewa zan iya sakata cikin iyali na kuma
ta haifa min yaya. Bani da niyya Jidda kuma bani da wadda zan iya aure a yanzu. Ki fadi wani sharadin
please, in karamar wayar kike so in ajiye wallahi zan ajiye ta, in daya aikin kike so in bari in nemi wani
source of income din wallahi I will do it indai hakan sai faranta miki"



Na girgiza kaina "ni fa duk dadin bakinka na gama jinsa, na gaya maka ai abinda nake so Umarul Faruq,
kaje ka samu Mama ka gaya mata cewa duk abinda na fada gaskiya ne ba karya nake yi maka ba.
Wannan ne kadai zai nuna min you are willing to change, sannan kuma zai samar maka abinda kwadayin
sa ya saka na gaya mata in the first place, zai samar maka addu'ar ta data Baba, kuma za'a samu zaman
lafiya da fahimtar juna a tsakanin mu, dan a yanzu ka riga ka shafa min bakin fenti a idonta, fentin da
bana jin zai gogu anytime soon"
Yayi shiru yana kallon fuska ta, ina kallon adam's apple dinsa yana ta motsawa sannan ya rufe idonsa ya
bude "Okay. Okay. I will do that. Amma a matsayin alkawari cewa zaki ajiye maganar zuwa gida and it
will be karshen maganar nan tsakani na dake, we will never mention it again"



Na lumshe idona na bude sannan na gyada kai, "na yarda. And I really hope we will never mention it
again" ya danyi murmushi, fuskarsa tana nuna hankalin sa ya fara kwanciya, sai yayi kissing goshina da
cheeks dina yace "you are a very good wife Jidda, you don't deserve me, but insha Allah ba zan kuma
baki kunya ba. Allah yayi miki albarka"



He kept his own side of the bargain, ya je kuma yayi abinda mukayi dashi zaiyi din. Ban dai san ranar da
yaje ba amma nafi tunanin kwana biyu bayan munyi maganar ne ranar da yaje ya dauko yara. Na kuma
tabbatar da yaje din

50 / 101