Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
dawo gidan miji
na. What would I do then?
Nayi sauri na girgiza kaina a hankali nace "Allah kar ka kawo min wannan rana ya Rabbi" amma sai nayi
tunanin maybe fa akwai wadda ta taba samun kanta a irin wannan situation din ko? Ko yaya tayi?
Kusan duk bayan awa daya sai Umar ya kira ni. "You know I love you right?" Nasan duk kamun kafar kar
in tafi gida ne. Da wuri ya dawo ranar na tare shi tamkar yadda na saba yi kullum, shi kuma ya taho min
da sabuwar waya yayi replacing wadda na fasa ranar nan, daga ranar muka saka wannan maganar
behind us muka cigaba da acting as if nothing really happened. Sai ma wani sabon babin soyayya da
muka bude.
A haka har cikina ya shiga watan haihuwa. Yaya Mubaraka ya hada ni da ita muka je siyayyar kayan
haihuwa tunda ni ban san abubuwan da ake bukata ba ita kuma ta san komai na kan haihuwa. Muna can
ma ta kira Mama take gaya mata abinda muke yi, kafin mu gama Baba ya kira ta yace duk abinda aka
siya shi zai biya.
Umar yana jin haka ya saka muka yi ta lodar kaya tunda ba kudinsa ne zasu motsa ba. Yaya Mubaraka
kuma ta taya ni muka zabi kayan fitar suna masu kyau da tsada har set uku, kayan Baby kuwa babu
abinda bamu siya ba har da abinda ni kaina ban san amfanin sa ba sai dai in na karanta. Bamu iya gama
siyayyar a rana daya ba sai da muka yi kwana uku a jere muna fita sannan muka kammala. Amma bata
bar min kayan a hannuna ba sai ta ajiye min wadansu wadanda zan bukatar immediately idan na haihu
sauran kuma ta tafi dasu gida tace sai na haihu za'a kawo su a matsayin kayan barka kamar yadda yake a
al'adance. Nawa kayan kuma ta kaini gurin tailor dinta zaiyi min dinkuna a jikin su.
Kwana biyu bayan nan sai Umma ta kira ni a waya take yi min zancen zuwa gida in haihu a can kuma inyi
wanka kafin in dawo gidana. "Ki tambaye shi, in ya amince sai Afia tazo ta dauko ki . Ni bana jin dadi in
na tuna ke kadai ce a gida ga haihuwa ba'a san sanda zata zo da yadda zata zo ba"
Nayi murmushi kawai na amsa mata da to, amma a raina nasan Umar ba zai taba yarda ba. Amma dai
banyi kasa a guiwa ba sai na shigar masa da maganar lokacin da muke dinner.
Ya yamutsa fuska "menene haka din?" Nace "au kai baka san ana zuwa gida in ciki ya tsufa ba. Chafdi. Ai
kuwa tafiya zanyi" yace "kwana nawa zakiyi a can?" Nace "kwana? Wata nawa zaka ce dai. Kamar wata
uku haka dan sai na haihu na yi arba'in yarinya tayi kwari sannan zan dawo"
Ya fara girgiza kansa. "Ina, ina, kina so in mutu kenan" na daga hannu na nace "bani na fada ba. Umma
ce ta fada" ya rike hannuna kamar zaiyi kuka "Jidda ba zan iya ba kin sani. Kiyi mata bayani yadda zata
fahimta" na juya ido na. "Ni ba zanyi mata bayanin komai ba, sai dai kai kayi mata. Ai dama cewa tayi in
tambaye ka in ka bari in tafi in kuma baka bari ba shikenan" ya sake marairaice wa "yanzu in nace ba zaki
je ba zata ji babu dadi, ni kuma....ni kuma"
Nayi murmushi, yana ta struggling da kansa yana so ya farantawa Umma kuma baya son rabuwa da ni.
Sai naji dadin hakan da yayi dan nasan da wani mijin ne da direct kawai zai fada yace ba zanje ba. Ya
cigaba da bayani. "Ki gaya mata ni doctor ne, kuma so nake in dauki annual leave da zarar cikin ya cika
38 weeks yadda zan zauna a gida in kula dake irin kulawar da ko a gidan ne ba lallai ki samu wadda ta fita
ba. Ko haihuwar yazo a gida zan iya karba, ko tazo da wata matsala zan sani tun kafin matsalar ta zama
matsala, dan Allah Baby kiyi mata bayani yadda zata fahimta sosai" na gyada kai ina murmushi "da gaske
zakaiya karbar haihuwa ta? I want to see you in action" yayi dariya "zaki sha mamakin how smartly zan
karba kuwa. Ni zan fara daukan babyn mu,a hannuna zata zo duniya" ya fada dreamly. And I instantly
know mai raba shi da yarinyar nan in tazo duniya sai Allah.
Tare muka je gida dashi, ya ajiye ni tare da jaddada min in yi wa Umma bayani yadda ba zata ga rashin
kyautawar sa ba. Sai ya tafi ya barni yace da dare zai dawo ya dauke ni. Ina shiga tun daga tsakar gida na
jiyo Abba yana fada a falon Umma "ku mata wata irin karamar kwakwalwa ce daku kuma kuce lallai sai
kun yi amfani da ita kun yanke hukunci. Ta yaya zaki ce zaki dauko yarinya daga gidan mijinta ki kawo ta
nan ta zauna? Mai zata yi miki anan din in ta zauna?"
Sallama ta ya saka suka juyo a tare, ya nuna ni da dan yatsa "koma inda kika fito. Kar ki sake ki karaso
dakin nan" na tsaya a inda nake ban motsa ba, kawai naji hawaye ya taho min. Na farko gashi na shigo
na tarar ana yiwa uwata fada duk yan gidan suna ji,na biyu kuma daga shigowa ta zai kora ni in koma. To
shikenan ita mace dama bata da gidan iyaye sai gidan miji?
"Ba zaki wuce ki tafi ba?" Nace "Abba ya tafi fa, ajiye ni dama yayi ya tafi yace sai dare zai zo ya dauke ni
mu koma" yace "au ho, na dauka zaman goyon cikin kika taho already. Allah ya rufa miki asiri da yanzu
zaki juya ki koma" sai kuma ya fito ya bani guri na shiga shi kuma ya fice,sai daya fita sannan na tuna ko
gaisheshi ban samu nayi ba"
Na zauna a kusa da Umma ina share hawaye, har yanzu ban daina wannan saurin kukan nawa ba kuma
bana jin zan daina. Ta kirkiro murmushi "kar kiyi kuka, tunda babanku bai bari ba shikenan kar ma kiyi
wa Umar din maganar. Kiyi zamanki kawai Allah ya sauke ki lafiya" na gyada kai na, "ameen. Kuma yace
ma zai dauki annual leave dan ya zauna dani a gida, kuma kinga likita ne shi sannan bangaren daya
karanta kenan dan haka zan samu kulawa sosai daga gurinsa ko da kuwa haihuwar tazo da gaggawa ne
zai iya karba ko da a gidan ne".
Ta gyada kai tana fahimta, naga alamar hankalin ta ya kwanta sosai, a raina sai naji tausayinta nace Allah
sarki uwa, ita duk dan ni take yi tana nema min sauki ne. Mun danyi hira da ita, na bata labarin kayan da
muka siya na haihuwa ita kuma ta bani labarin admittion din da mijin Aunty Afia ya samarwa Abbah a
state university wudil. Nayi mamakin da Abbah bai gaya min ba duk da muna waya kusan kullum sai tace
ai basu gama musu screening ba shi yasa yaki fadawa kowa.
Muna cikin hira Farhan ta shigo gidan, tana jin muryata ta shigo dakin a guje zata fado jikina Umma tayi
saurin riketa "baki ganin yadda take? In kuma kina so kiyi muku asarar ɗa ne to bismillah" na zauna a
gefe na tana dariya "chaf ai kuwa da yaya Doctor ya tsire ni a kasuwa. Wannan cikin yana tabuwa ne?"
Nayi shiru ban bata amsa ba tunda Umma tana gurin. Sai ta jani muka tafi dakin mu inda yanzu ita kadai
ce a ciki muka fara hira.
Na lura duk ta rame, na tambayeta dalilin ramar ta tace "hmmm. Har ma zaki tambayi dalili Jidda? Kamar
baki san yadda nake zaune a gidan nan ba? Yadda kika san akan kaya nake wallahi haka nake ji" nace "ke
Farhan, gidan ku ne fa, in baki sake a nan ba a ina zaki sake?" Ta daga kafada "oho. Nima ban sani ba.
Amma ni dai ba'a nuna min cewa anan ya kamata in sake, kullum zancen in fito da miji in fito da miji
kamar akan mutane nake a zaune. Dazu ma fa sai da Abba yace wai gab yake da yin shela a masallaci
akan wanda yake so na ya fito"
Na bude baki zan yi kwakwazo sai naga ta fara hawaye, sai na kwantar da murya "ke da wasa yake yi
miki, Abba ba zai taba yi miki haka ba. Kawai dai yana nufin ki mayarda hankalin ki wajen samun miji" ta
harare ni "dama mijin samo shi ake yi? Gaya min inda ake samu inje in samo a can"
Nayi ajjiyar zuciya "ba haka nake nufi ba sister, hausar ce banyi dai dai ba. Babu inda ake samun miji kina
gida rabon ki zai tarar dake. Dan dai na yi aure da wuri ne shi yasa Abba ya saka miki ido, dan kuma
dama can ya saba aurar da ƴaƴan sa da wuri. Dududu shekarar mu biyu fa da yan watanni da gama
secondary school. Idan a wani gidan ne sai yanzu za'a barmu yin samari, idan a wani ne ma har yanzu
bamu isa yin samarin ba"
Sai na bata labarin gidan su Umar, Mufida har yau bana jin tana da wani saurayi. Ita kanta muhibbat sai
last week naji ana maganar anzo neman aurenta bayan ta gama jami'a tayi service ta samu aiki sannan
aka fiyo neman aurenta. Kuma ban taba jin wani yayi mata maganar ta dade bata yi aure ba.
Muhsina kuwa anyi posting dinta service bayelsa, na dauka za'a nemi a dawo da ita kusa amma sai naji
ana shirye shiryen tafiyar ta can din, da nayi complain sai Umar yace "idan mutum bai fita duniya ba ta
yaya zaiyi yasan me duniya take ciki? Ki barta kawai ta tafi, experience ne ai"
Ina gama bawa Farhan labarin tace "chafdi. Wallahi Abba ko Kaduna ba zai barni inje ba in dai ba gidan
miji na ne a can din ba" nayi dariya "to ko kadunan zamu kai ki ne?" Tace "kinga kuwa yaya Hudallah ta
kawo min wani Alhaji dan kaduna" muka yi dariyar yaya Hudallah da alhazawan da take kawo wa Farhan.
Ranar wuni nayi sur a gida. Dan sai wajan karfe tara na dare sannan yazo ya dauka ta sai kuma a lokacin
ya shigo ya gaishe da Umma da Hajiya. Na hau sama na yiwa Abba sallama sai yace in na sauko in ce wa
Amira ta shirya mu tafi tare tunda tana hutu. Na sauko na gaya wa Umma mukayi ta mamakin halin
Abba idan da yana so in tafi da Amira ai da sai ya fada tun wuri ta shirya ba wai sai da muka zo tafiya ba.
Amma ko babu komai naji dadi dan zata taimak min sosai da ayyukan gida...
Bayan mun he gida ya fara tambayata yadda muka yi da Umma, wai taji haushi da bai barni ba? Sai na
nuna masa kawai cewa bata ji haushi ba amma ban gaya masa already kafin inje Abba ya hana ba.
Ya karbi leave din kamar yadda ya fada, kuma ya kula dani kamar yadda yayi alkawari. Edd na saura one
week na fara labor kuma ina fara wa ya gaya min cewa labor ne, haka muka yi ta yin kayan mu a gida
tare har sai da yayi nisa sannan ya dauke ni da Amira rike da jakar kayan haihuwata muka tafi asibitin Dr
Bashir.
Muna zuwa kamar da gaske, ya saka kayan doctors ya saka aka kawo masa duk abubuwan da zai iya
bukata aka bar mu daga ni sai shi a dakin, amma haihuwar tana zuwa sai ya rikice, yadda nake karkarwa
shima haka yake yi, ya ma kasa gane ina ne saman allura ina ne kuma kasanta. Dole ya kira wata midwife
a gurin ta taimaka masa. Sai dai babyn tana fitowa ya saka hannu ya karbe abarsa ya rungume tun kafin
a yanke cibiya balle a goge jiki.
"Welcome to the world Baby girl. You look just like your mother Yasmin"
*Wannan littafin na amana ne, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi sharing, in kika
yi kinci amana kuma ke da Allah*
*The Pictures*
Ya sunkuyo dai-dai fuskata ya nuna min babyn, "kin gan ta. Kamar ku daya ko? Ai dama na gaya miki" na
dan juya na kalle ta kadan, sannan na mayar da idona na rufe. Sai dai hakan bai hana ni yin murmushi ba
kadan duk kuwa da azabar da nake ciki. Fuskar yarinyar kadai ta goge min duk wahalar da nasha wajen
kawo ta duniya and I was already deeply in love with her.
Yace da ni take kama, amma ni a dan kallon da nayi mata na few seconds sai naga da yan gidan su take
kama dan ta fini fari sosai kuma dan siririn dogon hancin ta ma ba irin nawa bane ba.
Midwife din ce ta yanke mata cibiya sannan ta nannadeta a cikin towel yake jijjiga ta duk da cewa ba
kuka take yi ba, yayin da ni kuma midwife din take kokarin gyara ni. Sai naji tana gaya masa cewa na
samu tear dan yarinyar ba karama bace ba. Sai ya mika mata yaririyar yace ta gyara ta, shi zai min dinki
da kansa.
Yayi kira masu allura suka yi min epidural, sai daya tabbatar ta zauna sannan yayi min dinki, taking his
time har sai da ya gama sannan ya dago yana kallona yana murmushi yace "there you go. As good as
new" na bata rai na harare shi sannan na juya kaina gefe ina cewa a raina da nasan haka haihuwar ta ke
da ban bashi fuska ba ma ballantana yayi min ciki.
Sai yayi dariyar bata ran da yaga nayi sannan naga ya daura min drip, sannan ya gyara min kwanciya ta
ya lullube ni, a take bacci ya dauke ni.
Sanda na farka Aunty Afia na gani da auntyn su Umar suna zaune suna hira da new babyn a hannun
Aunty. Ina farkawa suka taso kusan a tare suna jera min sannu, sannan Aunty ta fita, jimawa kadan suka
dawo tare da Umar, ya duba bp dina ya yi min yan tambayoyi sannan ya ce da aunty ta bani tea insha
sannan in sha drugs din da ya kawo min. Sai kuma ya tsaya babu kunya ya dan shafa fuskar babyn sa
sannan ya fita.
Suka bani tea mai zafi na sha kamar yadda yace sannan suka bani magani shima na sha, sannan suka
miko min babyn suka ce in gwada feeding dinta, na karbe ta da bismillah sannan na rungume ta a kirjina
side din dama na, sai kuma na fito da abincin ta na goga mata a bakinta, ta dan motsa kadan amma bata
karba ba, sai na saka yatsu na biyu na dan bude dan karamin bakin ta na saka mata a ciki, ta saka
harshen ta kamar zata turo shi sai kuma ta kama ta ja da karfi.
Na dan zabura kadan saboda zafin da naji, amma sai ta bude ido tana kallona kuriiii kamar ta sanni, sai
naji zafin duk ya tafi murmushi ya zo fuskata. Na saka dan yatsa na ina shafa cheeks din ta ina jin wata
irin soyayya da ban taba jin irin ta ba, tabbas wannan ita ake kira soyayyar uwa da ya, wadda babu irin ta
kaf duniya. Lokaci daya naji a raina cewa zan iya yin komai saboda wannan yar karamar halittar da take
rungume a jikina.
An gyara ta tas an saka mata kayanta da na taho mata dasu, overall mai strips pink and white, sai white
hula da pink tutoci guda biyu a saman ta. Na cire hular ina kallon cikakken gashin kanta wanda ya zo tun
daga keyarta har kusan rabin goshinta, tsahonsa kuma da ace za'a kama da tsaf za'a kitsa shi. A raina
nace yarinya dole kiyi dashi tunda kinyo gado side biyu.
Ni gani nake kamar babu abinda take sha, dan banji alamar wani abu yana fita daga jikina ba amma
tunda ta kama din sai na barta tayi ta tsotsa. A haka har ta rufe idonta ta koma baccinta. Umar ya sake
dawowa, ya tsaya yana kallon mu fuskarsa kamar gonar auduga. "Aunty kinga sha take yi. Wannan
yarinyar da wayon ta aka haife ta. Aunty kinga yadda take sha kuwa?"
Naja dankwali na na rufe fuska ta ina jin kamar kasa ta tsage in shige ciki, Aunty ta harare shi "to
shugaban marasa kunya, in baka ji kunya ta ai kaji ta in-law din ka ko?" Sai ya dan shafa keya kadan ya
fita yana murmushi. Bai jima ba ya sake dawowa lokacin na cire ta da wayarsa a hannunsa ya dauke mu
hoto, sai kuma ya shiga shima ya dauke mu tare. Sannan ya dauki babyn yayi musu tare kala kala.
Su Aunty da Aunty da suka saki baki suna kallon sa, tace "da fatan dai kayi mata huduba ko sai dauke
dauken hoto ka iya?" Yace "nayi mata. Sunan ta Maryam" sunan Mama. Ya ajiye ta yana shafa fuskarta.
"Yasmin za'a ke kiran ta dashi"
Zuwan Umma, Hajiya da Farhan ne ya saka ya rabu da Yasmin ya mika musu ita sannan ya fita. Tun daga
nan kuma dakin ya cika da hayaniya, ba'a jima ba sai ga su Mufida suma sun zo sun taho da abinci, a
lokacin ne Mama ta kira ni itama daga Lagos ta duba ni sannan ta bawa Baba shima ya duba ni yana ta
murna wai yayi amarya kuma ance masa tafi Mama da Aunty kyau.
Da yake haihuwar safe nayi, zuwa dare Umar da kansa ya rubuta min sallama muka taho gida gabaki
daya. Bayan mun je gidan ne Abba yazo, the first time da Abba yazo gida na ya karbi Yasmin yayi mata
addu'a ni ma ya duba ni sannan yace su Hajiya su zo su tafi, sai dai ya bar Farhan da Amira yace su
kwana.
Washegari kuma da sassafe sai gashi ya dawo da Hajiya har da kayanta wai zata zauna tayi min wankan
jego, nayi mamakin hakan dan na dauka ko yace ta zo zata ce ba zata zo ba amma sai gashi ta zo din,
Amira ta gyara mata guest room din mu ta kai mata kayan ta can, kuma sai naga kamar da gaske take
gurin kula da ni din, ita take yi kin wanka duk da Umar ya hana yin na ganye amma ita zata gasa min
jikina sosai sannan ta saka ni in shiga cikin wani ruwan zafin in gasa kasana. Ita kuma take yiwa Yasmin
wanka sai biyu a rana ta shirya ta sannan ta taimaka wa Amira gurin girkin gidan duk da dai tunda na
haihu su Mufida da muhibbat kullum sai su zo gidan, kwana ne kadai basa yi amma suma suna taimaka
min sosai gurin karbar baki wadanda nake ta yi ta ko'ina.
Ba ga yanuwan mu ba ba kuma ga na su Umar ba, daga ko'ina yan barka bullowa