Chapter 76 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   76 / 101

225K to 228K   out of 300.2K words

kasa gane karkarwar sanyi take yi ko kuma magana take yi a hankali? Tazo dai-dai shi kunnen
sa ya jiyo masa........... ".,............subhanaka inni kuntu minaz zalimin"



Mamaki ya kama shi, wato addu'a take yi da neman tsarin Allah daga abinda zai yi mata. Dama tsoron sa
da suke ji har ya kai haka? Ya shiga falo ta biyo bayansa ta rakube a gefe



"Abba dan Allah kayi hakuri. Wallahi ba nisa nayi ba nan makota na shiga gurin kawata na karbo aron
phone charger din ta"



Ya zauna yana kallon ta, ya tuna yadda Jidda ma ta kanyi karkarwa idan yayi mata irin wannan kiran.
Sai yace "tambayar ki zanyi. Maganar Jidda, tsakanin ki da Allah kin san inda take ko baki sani ba" ta
bude ido "wallahi Abba ban sani ba. Jiya dai Umar ya ce yana tunanin tana gidan wata kawarta Diyam,
yace yau zai je ya bincika, amma wallahi ni ban sani ba"



Ya gyada kai, sannan ya danyi shiru kafin ya kara da "dalilin tafiyar ta fa? Kin sani?" Tayi saurin girgiza
kai, amma sai yaga alamar rashin gaskiya a tare da ita dan haka ya sake tambaya "kin san wata matsala
da take samu da mijinta? Ke ce aminiyarta kuma na tabbatar ta gaya miki suna samun matsala da
mijinta, kin sani?"



Ta dago kai, gabakidayan ta a tsorace take amma bata ce komai ba sai da ya sake tambaya "da gaske
Jidda tana da hawan jini?" Sai yaga alamar damuwa a fuskarta sannan tace "da gaske ne Abba, nima ba
gaya min tayi ba magungunan hawan jini na gani a jakarta shine na tambaye ta, sannan ne ta gaya min"
ya gyara zama yace "me tace miki?" Ta danyi shiru, da alama maganar tayi mata nauyi a bakinta, sai ya
taimaka mata "tace miki mijinta yana neman mata ko?" Ta gyada kai da sauri tana kara dunkule wa a
gurin, ya rufe idonsa yana jin zafin maganar sai kuma ya sake yi mata tambayar "da wa da wa tace miki
ya nema?"



Ta dago tana kallon sa sannan sai ta lissafa da yatsun hannunta "da yaya Jamila, da kawarta Maryam, da
kuma wadansu da ban san su ba" yaji kansa ya sara yace "tashi ki tafi" ta mike da sauri tana Allah Allah
ta bar gurin kar yayi mata fadan yawo sai kuma taji ya kira sunan ta "Aisha" ta juyo taga ya dafe kansa da
hannunsa "kar ki gaya wa babarki" ta gyada kai da sauri sannan ta fita. Yana jin ta tana sauka stairs a
guje.



Ya dan jima a zaune sai kuma ya mike ya dauki wayarsa da hularsa ya fita. A daidaita sahu ya hau ya
bashi kwatancen gidan su Umar Mintuna kadan suka je gidan, ya biya ya fita ya shiga gidan sannan ya
gayawa mai gadi ya sanar wa da alhajin zuwan sa, jim kadan Alhaji Muhammad Gidado ya fito da kansa
ya tare shi suka shiga falon sa na waje suka zauna tare da sake gaisawa. Sai dai kowannen su yana lura
da yadda yanayin fuskar dan'uwan sa take babu dadi. Sai kuma suka yi shiru. Sai daga baya Abba ya
dauko wayarsa ya bude sakon Jidda sannan ya mika wa Baba. Yana lura da yadda hannun Baba yake
rawa sanda ya karba, yana gama karanta wa kuwa wayar ta zame daga hannunsa ta fadi kasa sai kuma
ya sunkuya ya dauka ya mika Abba yana ambaton innalillahi wa inna ilaihir rajiun, daga nan kuma sai ya
dafe kansa ya kasa cewa komai, ya jima a haka sannan ya dago kai yana kallon Abba yace "tana ina
yanzu?" Abba ya daga kafada "ban sani ba gaskiya, amma yaruwarta ta gaya min cewa Umar ya san inda
take"
"Umar" Baba ya fada cikin kunan zuciya, "Umar" ya sake ambata

"Alhaji dan Allah kayi hakuri, wallahi sam bani da masaniya akan wannan mummunar halayyar ta Umar,
da ace jiya wani ga gaya min ma da ba lallai ne in yarda ba amma dazu na tabbatar, dazu na tabbatar da
dalilin da yasa Jidda tabar gidan sa" Abba ya juyo yana kallon sa yace "wanne dalili ne?"



Baba ya dan tauna maganar yana kara jin ciwon ta, amma Abba a matsayin sa na baban Jidda ya kamata
ya sani dan sai sun zama frank to each other kafin su kamo bakin zaren. Yace "akan yar aikin ta ne, akan
irin wannan maganar" Abba yaji kansa ya kara sarawa "yar aiki?" Sai yaji zuciyarsa tana kara yarda da
maganar Mammy ma, tabbas Mammyn da ya sani ce.



Baba yace "su waye wadannan da ta ambata a cikin sakonta? Yadda tayi maganar kamar ka san su"



Abba ya jingina kansa da jikin kujera yace "Jamila yayar ta ce, da ni da babar Jamila uwa daya uba daya
ne suka haife mu"



Baba yace "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" Abba ya dora da cewa "Mammy kuma yarta ce, yar yayar ta
ce, da Jidda da mahaifiyar Mammy duk ni na haife su"



Sai ya mike da sauri yana jin zafin abin yana shiga can cikin zuciyarsa, Umar ya ci mutuncinsa fiye da
tunanin sa, ya wulakanta matarsa iyakacin wulakanci.



Yace cikin sarkewar murya "Mammy ta kan je gidan Jidda ta zauna dan ta taya ta ayyukan gida a
matsayin ta na uwarta, na kan ji dadi in hakata faru dan ina ganin hakan zai kara hada kai tsakanin
yayana da suke ba uwa daya ba. Ban san abinda yake faruwa ba kenan ban san........." Sai kuma yayi
shiru, sannan ya kara da cewa "I thought I was protecting them from sharrin mazan da suke waje, ban
san wanda na hada ta dashi yafi na wajen guba ba"



Baba ya mike "kayi hakuri Alhaji, duk da nasan ko harshe dubu ne da ni ba lallai ne su ishe ni in baka
hakuri ba" Abba yace "ba sai ka bani hakuri ba Alhaji, mai laifi daban mai bayar da hakuri daban?"
Baba yace "a yanzu na fahimci cewa laifin duk nawa ne, da ace na bawa tarbiyyar yayana muhimmanci
fiye da yadda na bawa kasuwanci na maybe da yaro na bai zama haka ba, I didn't know because I wasn't
looking. Na tattara tarbiyyar gabakidaya na barta a hannun iyayen su mata ni kuma na rungumi neman
kudi tunani na dashi zan basu rayuwa mai kyau. Na manta cewa ita tarbiyya ta uwa da uba ce
gabakidaya dan ita uwa ba zata ga abinda da yake yi a waje ba, kuma a wajen ne ake aikata mafiya
munin laifuffuka. Dan haka laifi nane, nine ban rike amanar da Allah ya bani da kyau ba" ya karasa kamar
zai fashe da kuka.



Abba yayi hanyar waje yana cewa "idan yazo a gaya masa ya sanar dani inda yata take, zan je in dauko ta
in dawo da ita gidan su, sannan kuma a gaya masa ya rubuta mata takardar ta ko kuma in kai alkali ya
rubuta mata"



Baba ya biyo bayan sa yana magiya amma bai kula shi ba dan yana jin nauyinsa sosai, baya son ya karya
masa zuciya ya ya kasa yin abinda yayi niyya.



Yana fita daga falon Umar yana shigowa gidan, kuma ya ganshi, gabansa yayi wata irin faduwa, ya bude
mota ya fito sannan yabi bayan Abba ba tare da ya rufe kofar motar ba.



"Abba Abba Abba" amma ko kallon sa baiyi ba har ya fita gate shi kuma ya bi bayansa, ya ga yana
kokarin tsayar da adaidaita sahu sai yace " Abba ga mota, gida za'a kai ka?" Bai amsa ba ya shiga sannan
ya juyo yace "na bar maka sako a gurin babanka, kaje ya gaya maka".



Umar yaji ya kasa motsa wa daga inda yake har adaidaitan tayi nisa, sai kuma ya juya zuwa gida da sauri
ya kuma zarce falon Baba.



A kofar falon yaga Asabe da iyayenta a zaune, ya wuce su without a single look.



A tsaye ya tarar da Baban a tsakiyar falon nasa, fuskarsa da wani yanayi mai wuyar fassara. Suka tsaya
suna kallon juna sai Baba yayi masa tambaya



"ka san wata yarinya Mammy?"
Umar bai san sanda ya kai kasa ba sai ganinsa yayi a kasan, numfashin sa a rike a kirjinsa.



Baba ya danyi murmushin da yafi kuka ciwo yace "ba dan ta jiki na ka fito duniya ba, da tabbas yau zan
ce babu ni babu kai. Kuma ka rubuta takardar yarsa ka kai masa"



Sai ya juya zai shiga dakinsa amma sai wani jiri ya kwashe shi yayi baya straight, Umar yayi sufa ya rike
kansa kafin ya kai kasa amma duk da hakan Baba bai karasa hannun Umar din cikin hayyacinsa ba.



"Baba!" Umar ya fada da muryar da tafi kama da ba tasa ba.



Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din



0779484494

Nafisa Tafida Usman

Access Bank



Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp

08067081020



Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020



Please banda kira, WhatsApp only
*Wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta idan kuma kin siya kar kiyi
sharing in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*




*Pushed away*



Cikin tashin hankali Umar ya kai hannun sa wuyan Baba ya taba pulse dinsa, sannan ya mike da sauri ya
daga shi duk kuwa da cewa ba wai karami bane Baban amma gani yake in ya barshi anan ya tafi neman
taimako wani abun zai iya samunsa kafin ya dawo, yana fita waje ya fara kwalla kiran driver yana neman
taimako, da gaggawa drivers din gidan su uku suka taso kusan a tare kowa yana laluben key din motar da
take hannunsa amma sai Umar ya doshi tashi motar ya saka Baba a baya driver daya ya shiga ya ja suka
bar gidan.



Nearest hospital suka je, nan da nan aka karbe su aka shiga dashi inda za'a bashi taimakon gaggawa aka
bar Umar a tsaye yana jin kamar bai taba shiga aji ya zauna da niyyar koyon karatun likita ba, ga kujeru a
gurin amma sai ya zauna a kasa dirshan yana magana da kansa kamar tababbe. "Am sorry Baba, please
don't leave me, stay with me. Oh Allah. Allah na tuba Allah. Not my father please" sai ya rufe fuskar sa
da hannayensa yana fitar da numfashi mai zafi yana jin kansa yana tsananin juyawa kwakwalwar sa ta
toshe babu abinda yake iya tunawa sai the fact that Baba ya yanke jiki a fadi a saboda bakin cikin sa. The
fact that a Dalilin sa ne baban ya fadi hurt him so much, cewa daga safe zuwa yanzu har ya saka wa
Baban sa bakin cikin da har zai fadi unconscious, probably ace jininsa ne ya hau, abinda duk shekarun
Baba a duniya bai taba haduwa da shi ba sai yau sai a kansa, sai a dalilin bakin cikin sa, a rana daya.



Wannan wacce irin rana ce? Wacce irin bak'ar doguwar rana ce wadda ba zata kare ba haka nan?
Abubuwan da suka faru a ranar suna da yawan da Umar yake ganin su kamar a shekara guda ne suka
faru. Gashi kuma har yanzu dare ba wani yi yayi sosai ba. Ya duba agogon hannunsaya ga it is just 7: 30,
sai ya tuna bai yi sallar magrib ba sai ya fita zuwa masallacin da yake cikin asibitin yayi alwala ya tayar da
sallah, amma cikin sallar yayi sallama ta kai sau uku yana sakewa, gabakidayan sa a rikice yake bai san
me yake karantawa ba, bai taba tunanin akwai tashin hankali irin wannan a duniya ba, shi sanda yana
yaron sa zuwa zamanin samartakar sa bai san menene tashin hankali ba, shi a lokacin tashin hankalin sa
shine ya ji aljihunsa babu kuɗin da za'a yi wa mata burga da su, bayan yayi aure kuma tashin hankalin sa
shine Jidda ta kama shi da laifi, yanzu kuma tashin hankali have a totally entirely different meaning.
It means not seeing your family hearing from them for over a month, it means getting rejected by the
one you love the most, it means admitting a gaban Mama da Baba da maigadi da iyalin sa cewa ya nemi
lalata da yarinyar su, it means makala maka laifin da ba kayi ba and getting punished for it, punishment
din ma kuma wai shine auren lalatacciyar yar aikin matarsa, it also means admitting to Baba cewa
wannan bashi ne karo na farko daya aikata laifin zina ba, sannan kuma tashin hankali yanzu yana nufin
surukinka da yake ganin girmanka fiye da sauran maza ya gane cewa kai din mazinaci ne kuma har ma da
jikarsa, ƴar yar matarka kayi lalata da ita, sannan kuma babban tashin hankali shine babanka ya yanke
jiki ya fadi rai a hannun Allah saboda bakin cikin ka.



Duk wannan kuma ya faru dashi ne a yau, duk wannan ya faru da shine sanadiyyar kaifi guda daya, zina.



Da ba yayi, da hakan duk ba zai same shi ba, da ba zasuyi rigima da Jidda har ta kai ta ga guduwa ba, in
ma zasuyi rigima sai dai akan kananan abubuwan da dole ba zasu iya avoiding ba a matsayi su na
mutane, amma ba'a kan zina ba.



Shi kalmar ma wani iri yake jinta ko da kuwa a bakin sa ne ballantana a bakin wani. Shi duk sanda yake
yin abarsa ba da wannan kalmar su ke kiran abin ba, basu taba kiran abin da wannan kalmar ba.



Amma abin tambayar shine, ta yaya Abba ya san maganar Mammy har yazo ya gayawa Baba? Ta yaya?
Ko dai yarinyar ce ta bude wannan mummunan bakin nata ta gaya wa mutane? Har maganar ta je
kunnen Abba, da wa da wa ta gayawa so far? Da wa da waye suka sani so far? Amma tabbas sai yaci
ubanta wallahi, shi bakin cikinsa shine bama shi da tabbas din ya neme ta dan bai san sanda ya neme tan
ba kamar yadda bai san ya aikata abubuwa da yawa da suka faru a lokacin da aka ce ya neme tan ba,
well akace zai ce, dan shi a bakin Jidda yaji da bakin Bashir da bakin mai gadin gidan gonar su Bashir da
kuma a cikin wayarsa. Damn it, wai me yasa laifuffukan da ake kama shi dasu ba wai ainahin wadanda ya
aikata ba ne ba?? Me yasa?



Sai zuciyarsa ta raya masa cewa saboda ba Jidda, da Abba da Baba ne suke kama shi ba, ba sune suke
hukunta shi ba, Allah ne yake kama shi kuma shi yake hukunta shi kuma shi yasan dukkan laifuffukan sa
hatta wadanda ko babban amininsa Bashir bai sani ba, hukuncin su yake yi masa ba wai hukuncin
wadanda aka gane yayi ba.



Sai yaji tsoro ya kamashi, tabbas indai laifuka irin wadannan ne suna da yawan da shi kansa ba zai iya
lissafa su ba, dan haka shi kansa ya sani cewa wannan hukuncin yayi kadan, tabbas wannan sharar fage
ne yake gani, tabbas something big is coming. Sai yaji jikinsa ya kama karkarwa saboda tsoron abinda zai
zo next, menene? Baba ne zai mutu? Sai kuma ya tuna da maganar Baba kafin ya fadi



"kuma ka rubuta masa takardar yarsa ka kai masa"



Ya mike da sauri ya fita daga masallacin, kokari yake yi ya tura maganar zuwa can bayan kwakwalwar sa
inda ba ma zai ke tunawa da ita ba. Amma sai taki tafiya, ta baro kwakwalwar ta dawo cikin zuciyarsa ta
share guri ta zauna.



"Wacce 'yar Baba yake nufi? Ko dai a labarin da suka ji na Mammy munafukar yarinyar ce musu tayi ya
aure ta ne shine suke maganar ya sake ta. Ko kuma har sun daura auren da suka ce zasu daura na Asabe
shine Baba yake maganar ya kaiwa maigadi takardar sakin yarsa an fasa auren.



But what if duk ba wadannan impossible imaginary abubuwan suke magana akai ba, what if suna
magana ne akan reality, suna magana ne akan matarsa ta sunna? What if Abba ne bayan ya gano abinda
ya faru tsakanin sa da jikarsa shine yazo yayi demanding a sakar masa yarsa? Shi kansa Umar yasan
wannan ita ce maganar gaskiya amma ba ma yaso ya kawo wannan tunanin a ransa dan zuciyarsa zata yi
collapsing ne ya fadi kasa ya tarwatse.



Amma what if wannan shine next punishment din da zai fuskanta a duniya, punishment na rabuwa da
abinda yafi so fiye da komai, matarsa Jidda.



Ya girgiza kai sannan ya danyi murmushin tabbatar wa kansa cewa wannan wani mugun wasa ne ma
iyayen nasu suke yi masa, abu daya da zai raba shi da Jidda shine mutuwa, ko tashi ko tata. Sunyi fushi
ne ya sani, amma zasu sauko dan kansu tunda dai sakin nan a hannunsa yake shi kadai kuma ko gigin
mutuwa yake yi ba zai sake ta ba sai dai in ya mutu tayi takaba.



Yana fita waje yaga shigowar motar gidan su, a ciki ya ga Mama da Aunty da Mufida da twins,
gabakidaya gidan ma kenan, suna hangoshi duk suka yo inda yake dukkan su hankalin su a tashe amma
sai ya fara aiyanawa a ransa ko suma sun sani? Ya san Mama ta san wasu abubuwan amma Aunty da
kannensa fa? Kannensa fa? Idan suka san abinda yake aikatawa zasu kuma ganin girmansa har su saurari
maganar sa idan yayi musu ko kuma suji fadansa idan yayi musu, a matsayin sa na babban wa ta yaya zai
iya rike kannensa idan babu ran mahaifinsu.
Sai ya hango anzo nema auren afnan gurinsa sai kuma aka binciko halinsa aka ce an fasa "shi marikin
nata ai tsohon mazinaci ne, yaran mutane yake lalatawa" and they will be gone, never to return again.



Wato punishment din ma ba zai zamanto nashi bane shi kadai, zai shafi har wadanda suke kusa da shi,
wadanda yake holding very dear to his heart, iyayensa (tunda ga Baba already a gadon asibiti),
yanuwansa, matarsada yayansa. Yaji gabansa ya fadi, matarsa da yayansa, indai har za'a iya fasa aure
Afnan saboda laifinsa Yasmin kuma fa? Asad kuma fa? Za'a bashi aure in yaje nema? Ko kuma za'a bashi
damar tsayawa takara idan ya kasance yana son yin siyasa?



Sai ya hango abinda zai faru da Asad idan ya girma ya shiga cikin abokai musamman if he tries to play
holy, one of the abokai might just say "dalla can ku rabu da shi, ai mun san komai an bamu labarin
komai, har labarin yadda ubale ya danne yar aiki"



Ashe dai abin kunyar ba'a kansa kadai zai tsaya ba, ashe dai da gaske ne da Jidda tace masa sharrin zina
yana naso ne daga wanda yayi zuwa dukkan wadanda suka shafe shi. Yayansa da matarsa kuma sune
farko tunda sunfi kowa kusanci da shi.



Maganganun su Mama ne suka dawo dashi hayyacinsa "Umar ina Baban naku" "yaya Doctor are you
okay" "Faruq mai ya samu Alhaji? Mai ya faru da shi?" "Yaya ina Baba?"



Ya girgiza kai yana so ya dawo da tunaninsa zuwa gare shi. "Uhmmm. Yana ciki. Ku taho. Bara inje in
duba"



"Da tahowa kai waje ka

76 / 101