Chapter 6 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   6 / 101

15K to 18K   out of 300.2K words

son zuwa, mai zan je inyi? Ni akwai
wanda nake jira..



Umma ta shigo tana kallona, "yana jiran ki fa" bance komai ba na mike ina neman hijab dina, ta cigaba
da magana "baban ku yayi min maganar sa dama, Musa ne dan gidan Malam Magaji na bakin layi, yaron
kirki ne ya gama karatun sa har ya samu aiki koyarwa a makarantar su Amira" na saka hijab dina still
bance komai ba, tace "ki bude muku sitting room din baban ku, baya son ake tsayawa da samari a titi" na
tsaya a gabanta nace "to Umma na tafi" tace "a dawo lafiya Allah ya bada sa'a" bance ameen ba dan
bana jin akwai sa'a a fitar tawa.



Ta kofar cikin gida na shiga sannan na bude kofar waje, yana tsaye a cikin railer ya juya bayansa, bude
kofar da nayi ya saka ya juyo, na sunkuyar da kaina ban yarda mun hada ido ba nace "bismillah" sannan
na koma ciki na zauna a kan kujerar da take ta can karshe wadda daga ita sai kofar da za'a koma cikin
gida. Ya shigo da sallama, ya ajiye ledar hannunsa a kasa sannan ya zauna shima, bance komai ba duk da
nasan ya kamata in gaishe shi.



Yace "ina wuni Jidda?" Sai naji babu dadi, ko babu komai ya girme ni nesa ba kusa ba. Na dan russuna
nace "sannu da zuwa. Ina wuni?" Yace "lafiya lau. Ya bakunta?" Bance komai ba, ya cigaba "ke yanzu kin
zama bakuwa anan ko?" Still no answer



Ya zauna yana ta shafa kai sannan yace "nasan zaki yi mamakin ganina a gidan ku, musamman da kika ji
gurin ki nazo, amma hakan ba abin mamaki bane ba musanman in kika yi la'akari da ke din wacece......."



"Ban yi mamaki ba, Abba ya gayamin zaka zo, ya kuma gayamin abinda zai kawo ka"



Ya danyi shiru, sai kuma ya yi murmushi mai sauti yace "Allah sarki Abban mu, ya kyauta min sosai kuma
ya taimaka min ya hutacce da ni daga dogon bayani, yanzu abinda ya rage mana shine....."



Na dago kai da sauri nace "ba cewa yayi ya baka ni ba ai" ya daga hannu "ni ma bance ya bani ke ba,
amma at least na taka wani stage mai kyau a maganar mu ko?" Na girgiza kai, "kawai dai kaidar sa ce
hakan, ba wai yana nufin wani abu bane ba" yayi shiru yana kallona yayin da ni kuma nake kallon gefe na
hade girar sama da ta kasa, yayi ajjiyar zuciya "okay. Maybe na yi raising expectations dina sosai, maybe
nayi wa maganar shigar sauri, maybe Jidda zata fi so ace ita na fara samu da maganar kafin Abba. Amma
har yanzu ma bata baci ba, ki gaya min abinda kike so inyi, kiyi min magana ki saki jikinki mu fahimci juna
ni kuma zanyi duk abinda kike so"



Na juyo da idona ina kallon sa, sai naji zuciyata tana comparing dinsa da Umar, nayi saurin kawar da
tunanin daga raina sannan nace "daga farko ina son inyi karatu" ya danyi shiru, ina jin a jikina kamar
kallo na yake yi, sai naji yace da alamar mamaki a muryarsa "karatu kuma?" Na daga kai kawai, yace "I
thought Abba baya bari" nace "Abba baya bari ba yana nufin mu bama so ba, dan Abba bai bar yayye na
ba ba yana nufin ni ba zai barni ba"



Yace "duk na fahimci wannan kuma na amince, zan kuma so hakan ta kasance, ni malamin makaranta ne
dan haka na san darajar karatu ba kuma zan so ace matata bata da ilimi ba, amma ina tuna mana cewa
biyayya ga iyaye wani babban abu ce a rayuwa, idan Abba bai bari ba ina so mu dauka a haka, ba sai
lallai kinyi karatu a waje ba, zaki iya yi daga ciki hankalin ki a kwance" na dago ina kallon sa a raina ina
tunanin ko wannan shine maganar da mazajen sisters dina suke yi musu kafin aure.



Jin nayi shiru yace "look Jidda daga kallon da kike min da kuma yadda kike amsa min magana na fahimci
cewa banyi miki ba, and I understand that, amma ba wai na hakura bane ba yanzu ma na fara insha
Allah, abinda nake bukata daga gareki kawai shine dan Allah kar ki rufe zuciyarki ki bar min ita a bude ni
kuma xanyi iyakacin kokarin ganin na shiga cikin ta a hankali. Ki daure, ba dan ni ba kinji Hauwa'u?"



Na gyada kai na a hankali ina jin a raina babu dadi saboda yadda nayi masa, amma kuma sai zuciyata ta ji
haushina akan damar dana amince zan ba shi, yayi murmushi, "Nagode. Insha Allahu ba za kiyi nadamar
yin hakan ba" ya fada yana gyara zama, sai na mike tsaye da sauri nace "am sorry zan koma cikin gida,
dama ina yin wani abu ne aka yi kirana" fuskarsa ta nuna rashin jin dadin hakan amma baiki ba sai ya
mike tare da miko min ledojin daya shigo dasu a hannunsa yace "shikenan, Nagode sosai da kika fito
kuma kika saurare ni, ga wannan a bawa Amira" na girgiza kai na, "ka barshi kawai" ya matso "ai ba ke
na bawa ba, Amira nace ki bawa" na sake girgiza kai "ka barshi kawai" sannan na juya na koma cikin gida.



A falon Umma na same ta tare da Abbah da Amira suna hira, Umma tace "ya akayi? Ya tafi?" Na gyada
kai kawai ina jin kamar zanyi kuka, na kwanta akan kujera na juya musu baya duk da ina jin Abbah yana
tsokana ta wai na fita zancen farko a rayuwata "ya kamata in dauke ki a hoto in ajiye miki tarihi, sai kin
haihu in nuna wa yayanki"



Amira tayi dariya "na ganshi ai a sitting room, Yaya Musa ne yayan kawata Saddika, dama kullum muka
hadu sai ya bani wani abu ashe yayata yake so" suka sake yin dariya tare da Umma, Umma tace "ni ma
muna haduwa da babarsa a islamiyya, ranar nan ma har take bayar da labarin cewa ya samu aiki ta bada
sadaka tace ayi masa addu'a" naji kamar zan tashi in bar musu gurin sai mukaji yaro yayi sallama a tsakar
gida
Amira ta mike tana amsawa a lokacin da Hajiya itama ta fito daga nata dakin tana amsawa, banji me
yaron yace sosai ba sai da Amira ta dawo hannun ta da ledojin da naki karba daga hannun Musa tana
murna, suka zauna suna budawa, daya kayan kwalliya ne da turare a ciki dayar kuma fruits, na tashi na
shiga ciki dan haushin su nake ji kuma babu yadda zanyi dasu, su kuma duk sai suka dauka wai kunya
nake ji, ina ciki naji yaya Tahir ya shigo shima amma naki komawa duk da cewa inaso ayi hirar dani nayi
kwanciya ta a daki.



Sai dare bayan mun kwanta ni da Farhan sannan na samu na bude abinda yake zuciyata. "Bana sonsa" na
fada mata. Bata nuna mamaki ba tace "saboda me?" Na gyara kwanciya ta ina neman dalili, ba zan hada
shi da Umar a kyau ba amma kuma ba zan kira shi da mummuna ba, yana kuma da hali mai kyau dan
kowa a unguwa ya shaida, babansa abokin Abba ne, maman sa kawar Umma ce, kanwarsa kawata ce,
daya kanwar tasa kuma kawar Amira, yana da ilimi na addini dana boko dai dai gwargwado. What else
nake bukata kuma?



Na yamutsa fuska nace "yayi min gajarta da yawa, da kadan fa ya fini tsaho, sannan sunan sa babu dadi"
Farhan ta kwashe da dariya har da rike ciki sannan tace "Allah da gaske? Wannan dalili ne? Ki fadi
gaskiya, ko dai kina nufin ki ce Umar ya cika ko'ina babu gurin da Musa zai zauna?"



Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din



0779484494

Nafisa Tafida Usman

Access Bank



Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp

08067081020



Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020



Please banda kira, WhatsApp only
Episode Five : The Visit



Free Episode



Ranar dana kwana goma a gida ne na gaji da jiran kiran wayarsa nayi deciding zan kira Mufida watakila
ko zan samu wani labari a kansa a gurinta, duk da dai nasan cewa pride dina ba zai barni in tambaye ta
shi ba. Na dauko slum book dina na nemo number din ta na kira a wayar Umma, bugu biyu ta dauka
"Hello?" Nace "hey Mufida" sai tayi dariya cikin murna tace "Jidda? Wow. Ko da yake nayi fushi, ke da
mukayi da ke cewa kina zuwa gida zaki kira ni amma sai da muka kwana goma sannan zaki kira?" Nayi
murmushi "kiyi hakuri yammata, ko da yake ai bai kamata in baki hakuri ba tunda kema ai kina da
number din Umma mai yasa baki kira ni ba? Dan haka laifin ba nawa bane ba ni kadai" sai tayi dariya
kawai.



Muka yi ta hirar mu, kowa yana bayar da labarin abinda ya faru bayan zuwan mu gida, a lokacin ne take
bani labarin zasu tafi Lagos suyi hutu gabaki dayan yan gidan su "banda yaya doctor tunda shi yana aiki"
a wannan statement din ne kawai ta ambaci sunan sa, ban nemi karin bayani ba kuma nima ban ambace
shi ba har muka yi sallama. At least dai naji cewa he is fine, sai dai wannan ya saka na sake shiga wani
tunanin, tunanin dalilin da yasa bai neme ni ba har yanzu.



A ranar ne kuma da yamma muna cin abinci tare da Umma da Amira, sai ga Abba ya shigo falon, ya zaro
kudi daga aljihunsa ya ajiye akan kujera yana kallona yace "ki shirya gobe da safe ki tafi ki zagaya gidajen
yan uwanki, mazan kowa kiyi masa kwana biyu matan kuma kwana daya, sannan ki je gidan Aunties
dinki Habiba da Afia suma kiyi musu kwana dai dai. Na amsa da "to" kaina yana kasa ina jin babu dadi a
raina, duk yayyen nawa ba wani jin dadin juna muke yi ba dan haka ba dadin ziyarar zanji ba, Umma ta
gyara zama tace "amma da an barta tayi wa Afia kwanaki da yawa, yaushe rabonta da ita? Ba ka taba
barinsu suje su kwanar mata ita kuma nata yayan duk hutu sunanan gidan. Dan Allah ka barsu suyi sati
ita da Amira. Ita kadai su ke da ita a matsayin dangin uwa" direct yace "kwana daya nace, kuma ita kadai,
idan kwana dayan bai yi ba to tayi zaman ta" ya juya ya fita. Duk muka yi shiru kowa ransa babu dadi sai
kuma muka ji shi ya dawo yana kwalla wa Farhan kira yace "ki shirya ki bi Jidda zaku zagaya yan'uwa" sai
kuma ya sake fita.
Umma tayi dan karamin tsaki. Wato ya hada ni da Farhan dan kar in ki yin yadda yace. Amma ni sai naji
dadin hada ni da Farhan din da yayi, at least zan fi jin dadin tafiyar akan ace ni kadai ce.



Umma ta dauki kudin daya ajiye tana kirgawa sai ta sake wani tsakin "wannan ai ba zai ishe ku ba, tunda
ku biyu ne yanzu, sai dai inya dawo ita sai ta je ta karbi nata tunda wannan ke kadai ya bawa" Amira tace
"gashi inda zasu je babu mai basu kudin mota, sai dai ko gidan Aunty Habiba da gidan Mami" Umma ta
tabe baki tace "su samu abinda zasu saka a cikin su first kafin suyi tunanin a basu kudin mota. Su kansu
nema suke ballantana su bawa wani".



Ban kuma tabbatar da maganganun Umma ba sai da muka je, gidan Mama Sa'a muka fara zuwa, ƴaƴan
ta shida, Mammy ce babba kuma tana jss3 a lokacin, amma sai da muka kirga yaya sunfi ashirin a gidan,
duk yayan kishiyoyi da mijin yake aura yana saka ana tarawa Mama Sa'a su, ita ma kuma abinda muke
tunanin ya saka take gidan har yanzu shine saboda yadda take daukan duk wani wulakancin sa dan tasan
in ta mayar masa ya sake ta to bata da gurin zama a gidan mu ita kanta ballantana ƴaƴan ta, ita kuma
yadda take sane da yanayin gidan ba zata iya tafiya ta bar yayanta a cikin wannan halin ba.



Mugu ne na karshe, daga matan har yayan tsoronsa suke ji kamar wani dodo, sai dai jin dadin su daya
shine basu rasa ci ba ba kuma su rasa sha ba, ba dai za'a ce suna da komai ba amma basu da yunwa. Sai
dai yawan yayan da kuma rashin kulawa daga uban ya saka rasa tarbiyya. Idan kaji yaran suna zabga
ashar zaka dauka yayan maguzawa ne, basu kyale kowa ba har matan uban zagi suke yi uban ne kadai
basa zaga shima kuma dan sun san jikin su ne zai gaya musu.



Kallo daya zaka yi wa Mama Sa'a ka fahimci cewa ba jin dadin zaman take yi ba, bakin ciki ne fal a
zuciyarta babu wanda zata iya budewa zuciyarta.



Da safe cikin bacci muka ji shi ya shigo ya balbaleta da masifar bata gama sallamar yara da wuri sun tafi
makaranta ba har sun makara. "Kina cen kina shegen bacci sai kace kasa, babu abinda kika iya sai dai ki ci
ki koshi ki kwanta kiyi ta bacci kina munshari, common abinci ba zaki iya tashi ki dafa wa yara ba bayan
na fita na nemo duk abinda kuke bukata babu abinda na rage ku dashi. Ke dai Allah wadaran halinki
wallahi" haka ya kare mata tatas bai kodamu da idon mu mu baki ba ballantana kishiyar ta ta lokacin
balle kananan yaran da basu fara zuwa makaranta ba. Har ya gama bata ce masa komai ba ya fita sannan
ta tashi ta shiga daki, na tabbatar kuka taje tayi, ni kaina da ba ni akayi wa fadan ba saboda raguwar
zuciya ce da ni sai naji hawaye yana bin fuska ta.
Bayan mun shiga dakin ne muka tarar da ita ta zabga tagumi, absentmindedly tace "wallahi, ganin idon
Abba ne kawai yake zaune dani a cikin gidan nan, wallahi duk ranar daya fadi ya mutu in na tafi gida na
tafi kenan sai dai a raba gidan a bani rabona ko daki daya ne in zauna ni da yarana, in yaso ko kosai in
ringa soyawa a bakin layi ina ciyar dasu" sai muka kalli juna ni da Farhan, duk da cewa ba zamu iya
kwatanta halin da take ciki ba amma munsan abin ya munana.



A gidan Mama Hadiza kuma matsalar abinci ne, duk sun rame sun kanjame ita da ƴaƴanta kamar wasu
kajin mayu. Maigidan kullum zai yi awo na shinkafa ko hatsi ya kawo daga nan kuma babu abinda zai
kara akai, tun daga coal din da take girki da shi har zuwa kan maggi ita zata nema ta siya, kuma yana
sane da cewa bata aikin fari balle na ja. Yawan bani banin ta ne ya saka Abba ya siya mata keken dinki
duk a kokarin sa na ganin cewa ta zauna a gidan mijinta bata fito ba, to wannan ne ya taimaka mata take
dan samun na biyan bukatu, ƙafafuwan ta har sun kumbura saboda zaman kan keke.



Muna zuwa bayan mun gaishe ta ta miko wa Farhan hannu "autar Hajiya ina sakon da Hajiya tace zaki
kawo min?" Farhan ta dauko kudi a jakarta ta mika mata yan dubu dubu guda biyu. Ta karba tana leka
hanya dan kar mijin ya gani, "yanzu idan da ace Allah ya kiyaye zai ga wadannan kudin da sai munyi sati
bai bamu komai ba yace ai ya gan ni da yan dubu dubu, wannan kudin kuwa yanzu da kyar zai ishe mu
siyan mai da barkonon da zamu kwana biyu muna amfani dasu, ga sabulun wankan mu ma ya kare"



Farhan tace "kai Mama Hadiza, yanzu har sabulun wanka ma baku dashi? Duk ina kudin dinkin naki?"
Tace "hmmm, dinkin dai ba ina yi ne kawai ba? Duk fa a bashi yake karewa. Wani lokacin sai in hana
idona bacci inyi dinki da fatan da safe in an zo karba zamu samu abin karyawa amma in an zo karba sai
ace bashi, daga nan kuma shikenan sai dai ayi ta bayar da kudin kadan kadan wata ma sai dai in bita da
Allah ya isa".



Gidan yaya Hudallah ne mai dan dama dama, gidan ta fes fes, ita da yarta ma haka, ga abinci nan a
wadace, kuma ita kadai ce ta samu nasarar ci gaba da karatu duk da dai itama iyakacin ta diploma, sai
dai kadaici. Muna zuwa ta rungume mu tana ta murna "amma dai sati biyu zakuyi ko?" Duk muka
kwashe da dariya "kwana daya zamuyi" na fada ina kokarin tsayar da dariya ta amma sai na cigaba ganin
yadda tayi da fuska kamar zata yi kuka "haba dai kwana daya. Ni da nake saka ran idan kunzo zan rike ku
ku cigaba da zama anan tunda babu abinda kuke yi a gidan? Ni kuma gani kadaici yana neman zautani?"
Mijinta a Abuja yake aiki kuma baya zuwa kano sai bayan sati bibbiyu, shtayi tayi kuma ya mayar da su
can yaki yace rayuwar Abuja akwai tsada.
Ta cigaba da mita "na gaji da zama ni kadai wallahi, kuma nayi nayi dashi ya barni in nemi aiki ko private
school ne in ringa teaching ina samun yar 10-15k dina amma yaki, wai private basa biyan kudi da yawa
sai dai in bari ya nemar min government, aikin gwamnati kuwa a zamanin nan masu degree da masters
ma nema suke yi sun rasa ballantana mu masu diploma".



A gidan tane muka fi samun sakewa mukayi hira sosai dan da kyar mukayi bacci da daddare tana ta dora
mana darasi.



"Allah dai ya taimake ku ya dora ku akan Abba ya barku kuyi karatun nan na zamani kuma, dan wallahi
yawancin mazan nan masu alkawarin zasu bar matan su suyi karatu karya suke yi" sai na tuno da
maganar mu da Musa, ta cigaba "kuma bara in baku shawara, in kun tashi zaben miji ku zabi mai dan
maiko maiko, dan shegu duk halinsu daya, amma da kiyi kuka a gaban murhun itace gwara kiyi a gaban
gas cooker ko?" Duk muka yi dariya ta bata rai tace "am serious fa, ku daina dariya, duk ba kirki ne dasu
ba, wani talakan ma yafi mai kudin iya shege dan idan talaucin sa ya dame shi sai ya dawo kan matar ya
huce. Dan haka duk ranar da Abba ya kirawo ku yace ku fito da miji to ku duba a cikin samarin ku ku ga
wanda yafi maiko sai ku zabe shi, musamman ke Jidda, dan wallahi fuskarki da jikin ki ba irin na matan
talakawa bane ba, na matan manya ne" ta jawo ni na zauna kusa da ita tace "kinga, akwai wani aboki ko
kuma in ce ogan Abban Sudais da suke tare a Abuja, ranar nan Abban Sudais ya gaya min wai yana
neman mata yana so yayi ta biyu ya tafi da ita can dan matarsa tayi girma ta tara iyali

6 / 101