Chapter 65 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   65 / 101

192K to 195K   out of 300.2K words

mijinki ba da sunan wai kinyi yaji. Marar godiyar Allah. Ki goge
wannan hawayen na fuskarki ki zauna ki saurari nasihar da uwarki zata yi miki kafin mijinki yazo, na kira
shi yanzu yana kan hanya ma, yana zuwa ki dauki kayan ki kamar yadda kika dauko su daga can ki dauka
ku koma. Wannan kuma ya zamanto na karshe, ehe"



Ya juya ya fita. Hajiya ta bishi a baya tana cewa "sai hakuri Alhaji, ka haifi da ne baka haifi halinsa ba.
Yaran zamani sai hakuri. Allah dai yasa yazo ya dauke ta su koma din kar yace yayi fushi"



Na runtse ido na, hawayena yana zuba akan hijab dina, shikenan? Duk kuri da cika bakin da nayi wa
Umar akan cewa na gama aurensa amma shikenan abinda Abba zaiyi akan maganar? Few minutes after
na bar gidan sa sai a kira shi yazo ya dauke ni mu koma? Babu ko bincike babu ko fada babu ko bani
damar in fadi abinda yake cikin zuciyata? A matsayi na na wadda na dauki shekara shida a gidan miji ba
tare da nayi yaji ba ai ina ganin yau din da nayi I deserve to be heard ko? Wannan abin da Abba yayi
tamkar yana gaya wa Umar ne ya cigaba daga inda ya tsaya.



Na dago kai ina kallon Umma, hawaye yana zuba daga idona, nayi kokarin magana amma muryata taki
fitowa saboda bakin ciki daya tokare makogwarona. "Kiyi hakuri Hauwa'u" Umma ta fada, "ni nasan kina
hakuri amma ina kara gaya miki kiyi hakuri. Saboda mai hakuri baya taba tabewa kuma hakuri baya taba
kai mutum ga halaka sai dai ya kaishi ga tsira, idan ba'a duniya ba to a lahira. Hakuri baya taba yawa,
kuma yanzu ma shi zan kara baki. Shi bin miji bin Allah ne, dole ki bi mijinki in dai kina son samun tsira a
lahira. Ko wacce mace in kika ganta a gidan mijinta to hakuri take yi, mazan duk haka suke kowanne da
aibun sa, dole muyi hakuri da su mu kuma tayi musu addu'a......"



Nace "Umma hatta mazinaci? Dole muyi hakuri mu zauna da miji mazinaci? Umma ji nake yi annabi da
kansa yace haramun ne zama da miji ko mata mazinaci" Umma tayi saurin ta katse ni "subhanallah Jidda,
ya zaki ke jifan mijinki da wannan mummunar maganar? Ya zaki ke kiran mijinki da wannan sunan a
gaban ƴaƴan ki? Kar ki sake, kar ki bari kowa yaji maganar nan daga bakin ki. Kar ki bari maganar nan ta
fada kunnen makiyanmu Jidda. Kin san kuwa mata nawa ne suke fatan samun kansu a matsayin ki? Mata
nawa ne har a cikin dangi suke fatan ki fito su su shiga gidan ki? Har a cikin yanuwan ki ma da yawa bakin
ciki suke miki da samun miji irin Umar"



Na sunkuyar da kai, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, anya kuwa Umma ta jini sosai? Ko kuma dama ta
sani amma take yin shiru? Tabbas biri yayi kama da mutum, tabbas Aunty Afia ta gaya mata, wannan shi
yasa duk ramewar da nake yi nake kuma bushewa bata taba tambaya ta abinda yake damuna ba, saboda
ta riga ta sani. Yanzu kuma shine take ce min inje in cigaba da hakuri in cigaba da zaman aure da
mazinaci? Dan kar makiya suyi min dariya? Shine reason dinta?



Ta sauko gaba na ta rike hannuna. "Ki daina kukan nan Jidda, kinga, in kuka tafi gobe zan aikawa Afia taje
gidan ta same ki ku sake maganar, daga nan sai ku tafi gurin Malam Murtala ayi masa bayanin komai,
babu abinda ya gagari Allah, da Allah zamu hada shi, in aka yi mana addu'a a kansa ba zai kara kallon
wani gurin ba"



Na karbe hannuna daga cikin nata na goge hawayena ina gyada kai. Na cire hannun Yasmin daga jikina
na mike ina daukan handbag dina, ta bini da kallo "ina zaki je?" Nace "waya zanyi masa" ta danyi
murmushi "yauwa. Ki gaya masa ya dan bari sai an jima kadan dan yan zaman majalisar nan su gama
watsewa kar su ganku kuna fita da kaya su samu abin magana. Allah ma ya saka sanda kuka shigo suna
masallaci da yanzu magana ta zagaye unguwa" na gyada kai kawai ina jin numfashi na yana rike wa a
kirjina baya karasa wa cikina.



Na fita tsakar gida sannan na wuce soro na kifa kaina a jikin katanga ina jujjuya kaina zuciyata tana kuna
kamar ana gasa masara a kirjina. "Am done" na fada a hankali. Na gama auren Umar. Na lissafo sanda
sukayi waya da Abba nasan yanzu already yana kan hanya, maybe ma ya kusa karasowa. Na yi gyaran
murya sannan na daga murya na kira Yasmin "ku zo kuyi magana da Daddy a waya" nayi shiru ina
saurare, sai naji su sun fito tare, na lallaba na debo takalman su da sauri da dawo soro na saka musu na
kinkimi Asad na kuma ja hannun Yasmin muka fita daga gidan da sauri.



"Mommy ina zamuje" Yasmin ta tambaya " Mommy mun fasa zama a gidan Umma? Yaushe su Muhsin
din zasu zo muyi wasan?" Asad ya tambaya



Ban basu amsa ba, sai sauri nake zubawa ina waige. Muna fita bakin layi na tari Napep, yana tsayawa na
saka yarana a ciki nima na shiga nace masa "muje"
Muna hawa kan titi naga motar Umar ta wuce mu, na leka naga ya saka signal ya shiga layin mu. Na
dawo da kaina ciki na jingina a jikin karfen Napep din hawaye masu zafi, kwatankwacin zafin da zuciyata
take yi min yana zuba daga ido na. Ban san cewa sheshsheka nake ba sai da naji muryar mai Napep yace
"kiyi hakuri Hajiya. Komai yayi zafi maganin sa Allah. Ki daina kuka kinga kin saka ƴaƴan ki suna kuka
suma" na kalle su, sun hada kai a guri daya suna rusa kukan da basu san dalilin yin sa ba. So innocent.



"Ina zan kai ku Hajiya?" Ya tambaya. Nayi shiru ina kallon yayana ina tunanin if I was wrong to bring
them with me. Yasmin cikin kuka tace "mommy ina zamuje?" Na mayar da idona kan yatsun hannuna ina
kallon su.



Ina za mu je???????



Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din



0779484494

Nafisa Tafida Usman

Access Bank



Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp

08067081020



Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020



Please banda kira, WhatsApp only



*From the Readers*
Wadannan matan suna cikin groups din mu, dan Allah idan kinsan ba zaki fadi alkhairi a kan su ba to kiyi
shiru. In kuma kina da shawara mai kyau da zaki basu to bismillah.



*1*

Assalama Alaikum

Gaskiya jidda is going thru a lot I can also feel her pain wallahi....Am also in a this kinda marriage but
mine is also a Drug Abuser .... The mistake was from me daga farko gaskiya saboda tun kafin munyi aure
ya gaya min cewa he was into drugs bfr and now alhamdulillahi bayayi kuma I believe SBD ban taba
kamashi da abu makamancin haka ba lokacin courtship dinmu gashi antakura min nayi aure just like
gidansu jidda.Haka na tsarkake zuciyata akan ya daina n yadda mukayi aure. First week was
alhamdulillahi but daga second week komi ya canza ya started seeing his tru face ya ajemin abokinsa a
gida for almost 3days muna just scnd week da aure and then all sort of drugs fa suna shamin a cikin gida
nayi kuka nagode Allah har abokin y tafi. And that keep going ya fara shigomin d kayan maye cikin gida ,
ina ta masa addua da nasiha amma babu canji.haka rayuwa ta cigaba har muka sami matsala parents
suka shigo ciki and that was the time dana fada cewa he's into drugs both my family became aware of
that.Da farko his mum ta dauki abun so serious and tayi bani hakuri sosai wallahi (knowing she knws he's
into it since dama).haka dai akayi bani hakuri aka masa fada komi ya wuce but bai fa canza ba .Ga gida ,
ga mota, g sutura amma wallahi basa burgeni sbd auren drug addict masifa ne wallahi nayi duk iya yina
nakasa nasha cewa y sakeni just like jidda amma wallahi yace bazai taba iyawa ba koda hauka yake I
shud just knw auren mu mutu ka rabane. That's how life keeps going anytime his mum ask me if akwai
matsala nace mata is only drug habit ensa but bata taba daukan mataki akai wallahi, bcs sometimes tana
ganinsa ya dawo a buge amma bata iya wani masa fada sai dai tayi ta fadan wai ita tama gaji yana
samata ciwon kai nasan yadda zanyi da mijina n gyara shi ita bazai kasheta ba can you imagine as if nice
na haife shi. Haka nake ta rayuwa cikin kunci da rashin kwanciyar hankali domin dai yanzu freely a
parlour yake shan kayan mayen sa amma bani da say ...ya taba cemin dama na hakura na kyaleshi tunda
mamansa ma babu yadda ta iya dashi ae. To cut it short nayi realising abun ya fara taba masa brain
wallahi saboda wasu habits da naga yakeyi, the worst part am pregnant ya min duka kamar zai kasheni
telling me shifa tsohon mahaukacine i should know that idan ban sani ba bfr I was so scared wannan
shine karo na farko daya taba saka hannunsa a jikina and pray ya zama last..one funny thing ya gama
dukana nace nikam tafiya zanyi ya biyo ni daki yana ta bani hakuri shi baisan yayi bama wallahi a tsorace
nake dashi bani da wanda zan gayawa matsala ta kamar jidda ko frnds I don't trust wallahi ....ina zaune
har ynz a gidansa amma cikin fargaba, tsoro da bacin rai na rasa yadda zanyi wallahi a bani
shawara ...Allah ya kawo manah mafita nida jidda da duk sauran yan uwa da suke cikin irin wannan halin
namu .



*2*
Wallahi ga munan for good 21yrs but still the same

My first born is 20yrs she's in the university ***l

And her brother is 18yrs he's in ***l university

See me thinking andpraying

Still

😭😭😭😭😭




*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar ki
sharing, in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*



*The Savoir*



Kafin mu dora, let me say this.

Littafin Jidda an gina shine akan matsalolin zinace zinacen da al'ummar mu ta samu kanta a ciki, da kuma
yadda wannan matsalar take rusa happy families, like jidda's family.



Wannan dalilin ne ya saka characters din cikin littafin kamar, Umar, Bashir, baban su Aira, da sauransu
suka zama mazinata, saboda ma'anar labarin ta fito sosai, amma kuma hakan ba yana nufin cewa maza
haka suke ba, ko kadan halin Umar baya representing halayen sauran maza.



Yes, dole in mun karanta labarin wata wadda ta samu kanta a hali kamar yadda Jidda ta samu dole
zamuji babu dadi kuma zamu ji haushin miji kamar Umar, amma ba yana nufin cewa mune Jidda ba
kuma mazajen mu sune Umar ba. Please we should cool down and start taking things easy. Don't start
digging something that isn't there please!



Akwai maza na gari kamar yadda yake akwai bata gari, ni a gurina ma zan iya cewa nagarin sun fi yawa.
Saboda nafi ganin nagarin akan bata garin, ke ma kuma in kika duba surrounding dinki zaki fahimci haka.
Haka mata ma, muma akwai mazinatan a cikin mu kamar yadda yake akwai su a cikin maza, akwai
yammata, zawarawa, har ma da matan aure da suke mazinata, matsalar ba tamaxa bace ba tamu ce
gabaki daya.



Dan haka don't judge maza da halin Umar please. Don't judge mijinki uban yayanki da ya aure ki yake
kuma iyakacin kokarin sa gurin kyautata miki da halin Umar please.



Ba wai maza ne mazinata ba please, zamani muka zo da har matan ma ba'a barsu a baya ba. Dan in kuka
duba ko a littafin Jidda mazinatan maza da mata ne ba wai maza ne kadai ba.



Don't go digging! Even if you dug and find out cewa mijinki yana chatting da yammata ko yana da
budurwa ko yana zuwa zance that doesn't mean mazinaci ne. That means shi namiji ne and maza are
polygamist in nature, ba kuma hakan yana nufin baya son ki bane ba. Soyayya daban zina daban please.
Don't start imagining things that are not real! You are not Jidda please and your husband is not Umar!



Ga yammatan cikin mu kuma, there are very good men out there, just be a good girl and pray hard,
addu'a tana da karfin da ta kan iya chanja kaddara. Insha Allah, you will find one.



I repeat, our husbands are not Umar! Lol.



Allah yasa mu dace.



But seriously, lets all calm down and send out positive vibes. Let love reign ❤️



Back to Jidda........



Na mike zaune straight sannan na dauki Asad na dora shi akan cinyata na kuma jawo Yasmin jikina ina
rarrashin su. "It is okay. We are going to be okay" na fada a hankali, more to myself than to them. "Ina
zamuje Hajiya?" Mai adaidaita sahu ya tambaya, na dan girgiza kai na cikin kokarin tsayar da kukana, ina
zamuje? Na sake tambayar kaina. Guri daya ne ya fado min, gidan yaya Tahir, saboda tunawa da nayi da
alkawarin da yayi min na shige min gaba a duk lokacin da Umar ya sake maimaita laifin sa, duk da cewa
bai san menene laifin ba.



But ........



The first place da za'a neme ni in aka rasa ni shine gidan yaya Tahir, daga nan kuma sai gidan Aunty Afia,
sai kuma gidajen sauran yan'uwa. Abu na biyu kuma shine ko da naje gidan yaya Tahir din ko da kuma ya
goyi bayana yayi niyyar tsaya min akan maganar a single word from Abba zaifi over powering dinsa,
kamar yadda nake yar Abba haka shima yake dan Abba dan haka duk a karkashin ikonsa muke.



Na girgiza kaina "ba zanje gidan Yaya Tahir ba" nayi magana ni kadai



Gidan Aunty Afia kuwa bana jin akwai abinda zata iya yi min bayan bani hakuri, tunda ita ma bata iya
solving nata problem din ba ballantana tayi solving nawa.



Amma to ina zanje da wadannan innocent yaran? Na fada ina shafa kawunan su. Na jima da yin
alkawarin cewa zan rabu da Umar ko da kuww zan zauna a gefen titi ne, it was easier to say, sai yanzu da
abin yazo sannan na fahimci yana da wahalar aikatawa musamman saboda yaran da nake dasu. Amma
kuma na tabbatar da ace nabar su agida da Umar yana zuwa za'a damka masa su ba tare da jan magana
ba, a yadda Umar yake kuwa zai iya kawo mace ma ya kwanta da ita a gidan a kan idon yayansa. Waya
sani ma ko samda ya nemi Asaben suna cikin gidan?



Tabbas tahowata dasu shine mafi alkhairi a gare su amma kuma ina zan saka su......



A thought came to me, ko in tafi airport ne in sayi ticket in tafi Lagos gurin Baba? Watakila shi zai iya
yadda dani ba kamar Mama ba, nayi saurin girgiza kai na, zai iya yarda kuma zai iya yiwa Umar fada,
amma kuma zai dawo dani gidan Umar tare da bani hakuri da kuma nemar wa Umar wata damar, abinda
kuma ba zan iya ba kenan dan damammakin Umar sun kare a guri na.



But ina zani......
Gwoggo Habibah babu abinda zata iya yi min, daga ita har mijinta Abba ba sauraren su yake yi ba.



In nace zan tafi Ethiopia gurin auncle Muhammad bana jin kudin da suke account dina zasu ishe ni
tafiyar, kuma ko da ace zasu ishe ni dole ina bukatar gurin da zan zauna kafin in yi tafiyar tunda ba wai
zan tafi airport bane kawai in sai tickets in shiga jirgi in tafi ba.



Ina zanje?



"Ya Allah" na rufe idona tare da ambata



"Ya Allah bani da kowa sai kai. Allah kasan halin da nake ciki Allah ka kawo dauki"



Na fada a fili.



Mai adaidaitan was patient, yana tafiya a hankali kuma baiyi mita ba, na sake rufe idona ita ta zurfafa
tunani na mutanen dana sani, yan uwa da abokan arziki, amma banga inda zanje wanda za'a goya min
baya ba kuma a tsaya min in karbo yancina daga hannun Umar.



Wayata naji tayi kara, na dauko ta daga jaka. "Umarul Faruq" na gani.

"Ya karasa gida" na fada a raina "sun fara nema na" tana katsewa kiran Abba ya shigo. Sunan sa kawai in
na kalla kara min tsoro da faduwar gaba yake yi, wannan guduwar da nayi idan Abba ya kamani bana jin
zai barni ba tare da ya nada min na jaki ba.



I let the phone rang har ta katse dan kanta sannan kiran Umma ya shigo, yana katsewa na yaya Tahir ya
shigo, wato har sun kira shi suna nemana, gwara da Allah yasa ban doshi gidan sa ba, yana katsewa na
Abba ya kuma shigowa sai na Umar.



Haka sukayi ta kira na ina kallon wayar akan cinyata amma ko taba ta banyi ba, in dai suka san inda nake
abinda zai faru shine Abba zai ci mutumci na fiye da kima sannan kuma a mayar da ni gidan Umar. A
karshe sai na yanke shawarar kashe wayar gabaki daya ko dan inyi reserving charge dina dan bansan
yadda zata kasance dani ba.



Ina daukan ta da niyar danna power dan in kashe ta sai ga kira ya shigo da number din da ko kadan banyi
tunanin gani ba a lokacin.



"Halima Kollere"



Na ma manta ina da number din, nayi saving dinta tun shekaru biyu da suka wuce lokacin da mukayi
reunion a makaranta, lokacin da Ramla ta saka min number din a wayata. Bayan na dawo gida nayi ta
kiran number din bata shiga, kamar yadda Ramla dama already ta riga ta gayamin cewa haliman bata
kasar dan haka number din bata shiga, sai kawai na bar ta a waya ta tare da fatan wata rana zan gwada
kuma zata shiga. But I never called her again.



Sai yanzu, ita take kira na.........

Sai yanzu lokacin da nake tsakiyar halin ƙaƙanikayi..........

Sai yanzu lokacin da ba zan iya daukan wayarta ba...........



Ban katse ba sai na bari har sai da ta katse da kanta sannan na kuma sake kokarin kashe wayar amma sai
wani kiran ya kuma shigowa daga gare ta.



Shekaru fiye da goma kenan rabona da ita ......

Shekaru fiye da goma kenan ina fatan Allah ya sake sadani da ita....

Amma bamu hadu ba har yau, sai yanzu da take kirana...

Anya in naki dauka ai kamar ban kyauta ba ko? But bana cikin mood din daukan waya gaskiya.
Musamman daga wadda bana son wulakantawa. Amma kuma rashin daukan wayar shima wani form of
wulakancin ne ko?



Nayi sliding wajen daukan kira sannan na saka a kunne na.
"Hello"



Naji muryar ta, cike da accent din fulani.



"Jidda? Dan Allah ina magana ne da Hauwa'u Mahmud?"



Na danyi gyaran murya kadan nace "eh Jidda ce. Halima?"



Tayi dariya



"Kai! Amma naji dadin samunki wallahi, dazu na je har gidan su Ramla na karbo

65 / 101