Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
ta kawo me tona mata asiri haka baban **** made
it to d dailies....
I left the house ba a zo anji why ba cz when I concluded cewa yana yi just as jidda did, na daya na biyu d
next one I was ready to give up d marriage and I did, So nayi parking babu Wanda yazo yace me ya faru,
muka ta saka ido tunda sun san maybe asirinsu zai tonu sai basuzo b and the mum said duk Wanda yazo
Allah ya isa😊. Baba na ya bi elder brother dinshi yace me ya faru me ake ciki? he's a step bro so I think
he backed out.
So d baba ya tashi he went to a sharia court yace gashi yarshi na gida 6months baya son ta koma gidan
wani ya za ayi? Sai akace sai dai yayi min khulki(na mayar d sadakin d na karba lokacin aure) sai baba
yace toh, but still an tura mashi sammaci akan yazo aji ta bakinshi sai basu zo b
Ran d akace mu koma naje ni kadai he didn't show up, aka Kara tura mashi still be zo b sai alkali ya ce mu
dawo rana kaza sai baba yaje yazo d waliyanshi, toh tunda an bada date d za ayi finilizing sai ga waliyy
yazo min da takarda wai ya rubuto min saki daya in na samu miji nayi aure and ya yafe sadakin ba sai na
biya b
So sai alkali yace dole sai an bani certificate of divorce akan shi alkalin ne ya raba auren bisa khulki, alkali
ya raba aure ya bani certificate showing khulki akayi yace in ba'a bani ba he can say gobe ya mayar d ni
Kuma na maidu
So khulki is refunding d sadakin to the husband sai ya bama alkali ikon raba aure ama idan ya yafe it's ok
in bai yafe b sai an mayar. In akayi khulki miji bashi da ikon cewa ya mayar da matarsa ko da kuwa tana
idda ne, sai dai in ta gama in an daidaita sai a sake sabon daurin aure ya sake biyan wani sadakin.
Shi abun da a ke cewa sharri nayi mashi shi abun sai gashi an dora shi a goggle, ko yanxu kukayi yanzu zai
fito, banji Dadi ba Don na haifi yara har biyu MAZA❤️❤️ama sai nace toh ga sharri d akace nayi mashi shi
duniyace ta wankeni😊...
D ace za a zauna d ƴa ko matar ɗa a saurari maganar su d za a shawo kan matsalan, kaman nawa tun
baiyi nisa b d mahaifan sa sun dage d dua d yazo d sauki amma aka ce wace ni?😰 karku manta shine
uban 'ya'ya na to an extent ai mu mata munfi iyayensu son gyaruwarsu ko akasin haka Don tsatson su d
suka biyo ta mu... To cut d lonnnnnnng story short ko last week an kirani akace ai Naga wane a youtube
ashe haka ya faru nace walhi mun rabu yanzu 4 years+ amma d aka tashi one random person haka ni ya
Kira, I felt bad for his kids Don suma Kila a samu me kiransu yace ashe kaine Dan wane kenan😭😭
bamuzo ma wurin neman auren su ba...ko neman aiki/takara lokacin za a tuno maka d abun d ba kai kayi
b😊
Nayi aure na yanzu alhamdulillah to the husband da a guri na is the best in the world, ba shi da problem
sai ajizanci irin na dan adam. An I am over wancan case din. Kuma yayana suna hannuna.
Jidda Allah ya Baki saa ya zaba maki abun d yafi alheri
Ki rufe kunenki Don Zaki sha zagi zaki sha magana ki dauki na dauka ki bar musu sauran,nima nasan sai
nasha amma babu komai
Kuyi hakuri d dogon sharhi na💪🏼💪🏼💪🏼
Writing this got me a lot relieved even though I'm over it. But ai jiki d Jini and seeing my boy sometimes
reminds me of it. And d call na last week 😊 sai naji tausayinshi dana ya kamani.
If jidda is still in this mess she needs to b strong for her kids coz d hustle out here is real 😰
*2*
Jidda touched me sosai da sosai ina karantawa ina dariyar takaici saboda tunawa da abubuwan da suka
faru Dani, nikam sam ban samu mafita ba, September na gudo gida nace na gaji, karshe sai babana ne ya
karba min takarda da kyar a November yanzu har na gama idda ta na fara kiba abuna
*Wannan littafin na siyarwa bisa amana ne, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi
sharing, in kika yi kinci amana kuma ke da Allah*
*The fourth Step*
Na saki kwalar rigar Asabe daga hannuna, ko kuma ince rigar ta zame daga hannuna dan ban ma san
cewa na sake ta ba sai da naga asaben ta yi baya da sauri tana neman hanyar barin kitchen din. Jiri nake
ji yana dibana, yawun baki na gabakidaya yayi hijira sai bile mai daci da yayi replacing dinsa. Duhu nake
gani a idona, na fara lalube ina neman abinda zan dafa dan kar in fadi, hannuna ya sauka akan cabinet
din kitchen din, na dafa da hannu daya daya hannun kuma na dafe kaina dashi ina ambaton "innalillahi
wa inna ilaihir rajiun" Allah nake kira ina neman daukin sa dan shi kadai ne zai taimaka min a lokacin
saboda shi kadai ya san halin da nake ciki, shi kaɗai yasan abinda nake ji a zuciyata sai kuma wadda ta
samu kanta a cikin yanayi irin wadda na samu kaina a ciki a lokacin.
Wani irin bacin rai nake ji yana tasowa daga zuciyata yana zarce wa har cikin kwakwalwa ta, a tare da
bacin rai akwai tsantsar tsanar wanda da nake ji kamar nafi sonsa a duk cikin mazan duniya bayan
mahaifina. Mutumin dana kwashe shekara shida ina kiran sa da mijina shi kuma yana kirana da matarsa,
mutumin da a yanzu yake a matsayin uban yayana guda biyu kuma mutumin da bayan ni yayana suka fi
so fiye da kowa a duniya.
Hawayena ya sauka akan hannayena da suke kan cabinet din, na kalli hawayen ina ayyanawa a raina
cewa sune na karshe da zan zubar a kansa. Na zubar da hawaye sunyi cikin jarka a kansa amma
wadannan sune na karshe. Na gama. Am done.
Dariyar Asad najiyo ta shigo kitchen din daga window tana ratsa cikin zurfin tunani na kamar kibiya on
fire, kamar tunatarwa cewa I can't say that, I can't make that decision, kamar tunatarwa cewa ba
rayuwata kadai wannan hukuncin zai taba ba har da rayuwar innocent yayana. Are they ready to face
that?
Na juya ina kallon window din, a lokaci daya muka hada ido dashi shima yana kallon na da Asad a
hannun sa gefensa kuma Yasmin tana rike da skipping rope a hannunta, na tsaya kawai ina kallon sa ina
jin wutar kiyayyar sa tana kara ruruwa kamar ana zuba mata fetur a cikin zuciyata.
Fuskarsa da murmushi ya rada wa Asad wata magana a kunne sai Asad ya dago min hannu alamar kira
"mommy come and join us, ki zo muyi wasa, Daddy zaiyi wasa tare da mu" ya karasa maganar tare da
mannawa Umar kiss a goshinsa.
Nayi saurin dauke kaina tare da juya baya na na daina kallon su "in time zasu koyi rayuwa ba tare da
daddyn su ba" wata zuciyar ta gaya min "Baby Dove. Come out and show us if you still have it in you"
naji muryarsa ya fada da alamar dariya a muryarsa da kuma tsokana. Idona ya sauka a kan set din
wukake na da suke ajjiye a maadanar su, wata zuciyar tana gaya min "dauki babbar ciki kije ki soka masa
a zuciyarsa, kamar yadda ya soka miki time and time again"
Hannuna ya sauka kan wukar na dauko ta na juya ina kallon inda suke, suna iya hango ni amma ba zasu
iya karanta emotions dina daga can ba. "Mommy daddy yana tsokanar ki wai ba zaki iya skipping ba"
Yasmin ta sake fada da karfi. Na juya na sake kallon su, duk su ukun dariya suke and they look so happy
together, na kalli hannuna rike da wuka, wukar dana dauka amma ban ma san na dauka din ba, wukar da
zuciyata take gaya min in je in chakawa mijina a gaban yayan mu. Na sake ta ta fadi kasa ina jin kamar
nima in bita mu fadi tare, har yanzu dariya suke yi suna cigaba da kiran sunana.
And I knew wannan daukan wukar da nayi shine na farko amma ba lallai ya zama na karshe ba in dai har
na cigaba da zama da Faruq, nasan cewa there will be only two ways out of our marriage in dai na cigaba
da hakurin da kullum ake gaya min a kunnuwa na, ko dai in kashe Umar ko kuma shi ya kashe ni da bakin
cikin sa, either way yayan mu zasu taso da tabon cewa daya daga cikin mahaifan su ne ya kashe dayan.
"I must get out, now" zuciyata ta kuma gaya min. A hankali na ce "am sorry Yasmin, am sorry Asad" sai
kuma na juya da sauri mai hade da gudu na bar kitchen din na wuce falo na tafi bedroom dina, niyya ta
ina shiga in fada gado inyi kuka kamar yadda na saba a duk lokacin da Umar yayi aika aikar sa, amma
wannan karon sai na ji na kasa karasawa kan gadon nawa, naji kafafuwa na sunyi giving up a tsakiyar
dakin, na durkusa a gurin hannayena duk biyun a dafe da kirjina kamar mai kokarin rike zuciyata da hana
ta fadowa kan cinyata, dan irin bugun da take yi da ace ba rike take da jijiyoyi ba da tabbas zan ganta a
gabana and that will be the end of me. "In baki bar Faruq ba tabbas Faruq zai kashe ki wata rana, zai
kashe ki da bakin cikin sa" na tuno kalaman Farhan. "In kin mutu karkarinta ayi sadakar arba'in dinki,
wata zai kawo dakin ki, ya debi yayanki ya bata dan kin san babu mai hana shi karbar yaya, ita kuma ta
gana musu azaba son ranta". Inji wani sashe na zuciyata
Na dauke hannayena daga kan kirjina ina girgiza kaina ina magana a hankali kamar tababbiya "ba zaka
kashe ni ba Umar, I won't let you" na mike sai kuma jiri ya debe ni na sake zubewa a gurin. Wai Asabe,
Umarul Faruq wai Asabe, tabbas idan bai kashe ni da bakin ciki ba zai kashe ni da cutar da zai kwaso a
wani gurin ya shafa min, in yaso in mun mutu duka a rabawa dangi yayan mu.
Motsin kofa naji, ban dago kai na daga kan carpet ba amma kamshin sa da rashin sallama ya saka na
fahimci shine. "Baby, muna jiran ki fa, ko kinyi giving up ne?" Ya fada cikin raha. Ban dago kai ba amma ji
nake kamar wani mala'ikan mutuwa ne ya shigo dakin, tabbas in bai fita ba, in ya bari na kama shi tabbas
sai na nakasa shi, in ya sake yi min magana da wannan muryar tashi tabbas zan iya fasa bedside lamp a
tsakiyar kansa.
Hannunsa da naji a bayana ne ya saka na zabura da sauri kamar wadda aka dorawa garwashin wuta a
jiki. Tsaye na mike ina nuna shi da hannu amma maganar ta kasa fitowa daga bakina sai hawaye da yake
bin kuncina. Ido ya zaro waje yana kallon fuskata. "Jidda? Lafiya? Are You sick?" Ya jero min tambayoyin
guda uku da bani da niyyar amsa ko daya daga cikin su.
"Kar ka sake" na samu harshe na ya furta, "kar ka sake ambaton sunana daga yau, kar ka sake tunanin ka
sanni, in ka sake yi min magana Allah ya isa" mamaki ya bayyana a fuskarsa. "Jidda?" Ya fada da sauri
cikin mamaki, da alama bai ji warning dina ba.
Bansan lokacin dana karasa gabansa ba, ban kuma san sanda na aikata ba sai dana ji karar mari a
kunnena sannan na fahimci marin sa nayi. Sai a lokacin na samu kukan da yaki zuwa gabaki daya ya taho.
Ya juya da sauri, a tunani na marin da nayi masa ne ya saka zai fita amma sai naga ya rufe kofar dakin da
sauri ya juyo yana kallo na. Of cause, babban tashin hankalin sa shine yayansa, babban abinda zai tayar
masa da hankali shine yayansa su fahimci akwai problem a cikin their lovely painted happy family.
Ya dawo da sauri yana kokarin kama hannuna. "Jidda lafiya? Mai kuma nayi? Talk to me" idan da wani
zai gan mu a lokacin zai yi tunanin babu wadda tayi dacen miji iri na, mijin da zai tashi hankalin sa idan
yaga kukan matarsa, mijinda matarsa zata daga hannu ta mare shi amma ko gezau bai nuna ba.
Na ture hannun sa daga jikina, har abada jikina ya haramta a gare shi kuma. An gama. Na dago ido ina
kallon sa, zuciyata tana kara kuna a lokacin da idona ya sauka akan fuskarsa. It hurts so much idan
mutumin da ka tattara soyayyar ka akansa ya kuma kasance wanda yafi kowa hurting dinka. Am done.
But still ya kamata inji his side of the story right? Albarkacin yayan mu ya kamata in bashi damar yi min
bayani right? Albarkacin soyayya, soyayya da nake masa, soyayya da yake min.
"Asabe?" Na furta a tsakiyar kuka, "me ya faru tsakanin ka da Asabe?"
Irin yadda jini ya dauke daga farar fuskarsa ta koma kamar takarda, da yadda idonsa ya tsaya tsak a kaina
shock a rubuce a duk angle na fuskarsa ya saka na gama fahimtar amsarsa. It did happen. Na rufe bakina
da hannuna, kukan ma ya tsaya. Muka tsaya chirko chirko muna kallon juna lallai ta bahaushe da yace
wargi ma guri shikai.
Ina kallon sa yana kokarin harhada kalamansa sannan ya tattaro duk wani bravo da yake ganin yana da
shi yace "nothing happened" but I know he is lying, yanayin fuskarsa kadai ya tabbatar min da cewa he is
lying. Shi abinda bai sani ba shine sam sam bai iya karya ba, duk sanda yayi min karya sai na gane saboda
sam bai iya pretending ba, ko da zaiyi karyar da baki amma abinda fuskarsa zata nuna daban. And right
now, he is lying.
Na juya da sauri na daina kallon sa dan zuciyata ba zata iya cigaba da kallon sa ba, in kuwa na cigaba to
tabbas abinda nake gudu zai faru, zan fadi in mutu da bakin cikin sa. Da sauri na karasa gaban wardrobe
dina na bude na fara watso kayana zuwa kan gado na. Ya taho yana kokarin rufewa, na juyo a fusace "ka
matsa ka bani guri tun kafin inyi maka rauni" ya kama hannuna yana dukan fuskarsa dashi "hit me, hit
me all you want but listen to me. Nothing happened. Na rantse miki da Allah nothing happened. Babu
abinda ya faru karya take yi"
Na kwace hannuna tare da goge su a jikin zani na kamar wadda aka shafa wa datti, nace "nothing
happened? Kamar yadda nothing happened a tsakanin ka da Mammy, tsakanin ka da Maryam, tsakanin
ka da Zahra ko kuma kamar yadda nothing happened tsakanin ka da zuwaira? Ko tsakanin ka da sauran
wadanda na manta da sunansu ko kuma tsakanin ka da wadanda ban ma sani ba? Wanne daga cikin
nothing happened din kake so in dauka?" Na fada cikin karajin da na tabbatar mai gadi ma ya jiyo.
Yayi kokarin toshe min baki yana zaro ido cike da tsoro, idanunsa kamar zasu fado, nasan tsoron me
yake ji, nasan babban abinda yafi tsoro sama da komai shine kar yayansa suji, kar yayansa su gani.
"Shshsh" yace yana doya yatsansa akan lebensa "the kids! Kiyi magana a hankali" nayi murmushin takaici
ina girgiza kaina. "The kids" na maimaita. "Your kids. Shin ko ka manta ni ma yar wani ce? Ko ka manta
Wadannan matan da na lissafa maka duk yayan wasu ne? Ko ka manta yarinyar can Asabe yar wani ce
ita ma?"
Ya sake kokarin toshe min baki yana kallon kofa sannan ya kalli taga hankalinsa a matukar tashe, yana
girgiza kansa. "I didn't. Na gaya miki karya take yi. Haba Jidda, believe me, Asabe fa muke magana akai,
wannan kazamar yarinyar, this is so insulting to even think about haba Jidda. Na rantse miki, wallahi, na
rantse da Allah......." Na ture hannunsa daga bakina na koma gaban wardrobe na cigaba da watso kayana
zuwa kan gado "ka rantse kace, as if rantsuwar ka is worth anything to me. Ka rantse da Allah kace,
Allahn da kake sabawa at the slightest chance da ka samu? Ta yaya kake tunanin rantsuwar da zaka yi
min dashi zata ba da wata ma'ana a gurina"
Ya biyo ni ya rike hannuna da hannu daya yana rufe kofar wardrobe din da daya hannun. "Jidda! Ya fada
yana girgiza ni kamar mai kokarin dawo dani hayyacina. "Think with your head, not your heart please.
Asabe fa kike zargina da ita" na tsaya ina kallon sa cikin ido, ina kallon yadda yake struggling with his
inner self yana son yayi maintening innocent look dinsa. A hankali kuma a nutse nace
"ba Asabe ba umarul faruq, ko akuya ce aka daura mata zani aka kuma shafa mata jan baki to in ka ganta
sai ka bita ballantana mace, yarinya karama mai jini a jika kamar Asabe"
Ya sake ni a hankali, ina lura da yadda kamannin fuskarsa suka juya daga innocent zuwa bacin rai, tabbas
magana ta ta bata masa rai ni kuma hakan ya faranta min, and I am looking forward to fada masa
wadansu masu zafin da zasu cigaba da bata masa rai kamar haka. Yayi taku biyu baya yana kallona
sannan ya juya da sauri ya fita daga dakin.
Akwati na na cika da kayana, sannan na dauko babbar jaka na fara zuba kayan yayana a ciki, ina yi ina
magana ni kadai kamar tababbiya, "na gama, na gama aurenka Faruq. Ko da duniyar nan zasu taru a
kaina ba zan dawo gidan ka ba. Kuma ba zan bar maka yayana ba ko da kuwa bara zanyi in ciyar dasu"
babu ko ninki haka nake watsa kayan a cikin jakar.
Kofa naji an turo da karfi an shigo still ba tare da sallama ba, na dago da niyyar in sauke masa kwandon
bala'i sai naga Yasmin tana kallo na fuskar ta cike da tsoro. "Mommy yanzu naga Daddy ya shiga dakin
Asabe da belt a hannunsa, dukanta zai yi?" Na yar da kayan da suke hannuna ina kallon yarinyar da take
tsaye gaba na.
Umar bai taba daga hannunsa ya dake ni ba ballantana yayan mu, ni ko tsawa ma zance ban taba jin yayi
mana ba. Ihun Asabe ne ya saka na kalli kofa da sauri "wayyo mommy ki taimake ni" ban jira komai ba
na fita da sauri, na shiga uku, kar ya kashe yar mutane, wannan cin zali har ina? Ga mari ga kuma tsinka
jaka?
Ai kuwa abinda na tarar kenan. Ya rike