Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
mu. Hausa language. Ranar da ta zama ranar graduation din mu. Ranar kuma da nayi masa
gani na biyu a rayuwata. Ranar kuma da ya yi ban ruwa akan shukar daya riga yayi a cikin fadarsa dake
zuciyata.
Tun saura sati daya graduation din mu aka fara shirye-shirye, ana ta gabatar da programs na yin
bankwana da mu, kowanne club yana shirya wa members dinsa dinner da kuma dan entertainment haka
sannan kuma a bayar da gifts, a ciki nima na dan samu rabo na babu laifi. Kyautar da na samu ta farko ita
ce ta tsafta kuma dama kusan duk shekara ina samun wannan kyautar, ba wai nafi kowa tsafta bane a
set din mu ba, a'a, ni abinda nake ganin ya sa ake bani wannan kyautar bayan tsafta ta wadda na san ina
da ita to akwai gayu kuma. Gashi dai ni ba yar masu kudi sosai can ba amma ina da daukar wanka ko da
kuwa a cikin uniform ne ballantana a gida. Kuma sanyin jikina sai yake karawa gayun nawa kyau, komai a
nutse nake yinsa a tsare. Wannan ya saka aka bani health prefect, sannan kuma yanzu da zamu yi
graduation aka sake bani kyautar tsafta.
Bayan ita ma kuma na samu kyautar third overall student, sannan in-coming health prefect ita ma ta
bani kyauta kamar yadda yake al'ada ta makarantar. A harkar sports ma an raba kyaututtuka, amma ni
ban sami komai ba saboda hardly in yi sport ko ranar sport day ne, sai dai in an matsa min sai inje inyi
table tennis, dan ni duk abinda zai saka ni wahala bana son sa.
Amma duk da haka sai aka raba mana wani hand band wanda akayi customising dinsa kowa da sunansa
da kuma sunan makaranta da graduation year a jiki, an yi masa ado mai kyau haka kamar saƙa da
different colors masu daukan ido. Ana bani nawa na karba ina karantawa "JIDDA. Beauty Queen" sai
kuma sauran rubutu, nayi murmushi ina jin a raina ina son abin, na bare shi a ledar sa na saka a
hannuna, naga ya danyi min yawa kadan amma a raina nace in naje gida naci abincin gida na huta nasan
zanyi kiba kuma zaiyi min dai dai.
Ranar da za mu bar makarantar, paper din mu ta karshe ita ce hausa dan haka ba wani karatu mukayi
sosai ba, da daddare ana ta kitson candy da lalle masu hada kaya nayi masu kukan rabuwa da juna nayi
nasu kida da table da rawar murna nayi. Ni dai ranar na wuni dakin su Maryam kawata.
Maryam kawata ce, dan zan iya cewa a lokacin bayan Mufida sai ita a layin kawaye na, babban abinda ya
hada mu kawance da Maryam shine gayun mu da yake kusan iri daya, amma ita kasancewarta yar
talakawa futuk sai ya zama gayun nata ya zama kamar karya dan tana daukar wa kanta abinda yafi karfin
ta ne, wannan ya saka tamu tafi zama daya da Mufida, ita kuma yar masu kudi ce sosai amma kuma
down to earth, funny, and sweet, sannan kuma tana so na.
Tun safe ina kwance gadon Maryam ina ta cike slum books din da ban zauna na cike ba, masu su suna ta
bina suna hada ni da Allah da Annabi, sai a ranar na cike musu wasu kuma na bawa Maryam ta taya ni
cike wa dan sunyi min yawa, muna yi muna hirar mu da nishadi.
Bayan mun gama ta wanke min kaina, muna ta rigima dan ni babu abinda na tsana irin a taba min
gashina, sannan bayan tayi towel drying gashin tayi oiling sannan ta fara min kitso inata mita ina cewa
tayi min manya ita kuma tace kanana zata yi min, ai kuwa ita kanta sai da jikinta ya gaya mata saboda
gashina cika ne dashi in ina kitso kamar ba zai kare ba, jelar ma kuma in tayi rabi sai ta saka band ta
daure ta ta barta a haka dan in bata daure ba warwarewa zaiyi.
Haka muka zauna har bayan magrib, taje tayi sallah ta dawo muka cigaba, da yake ni ina off, har ishai
muna abu daya, sai ga Mufida tazo ta zauna a gurin mu ita ma sannan da kyar aka gama kitson. Yan
ƙanana, kitson da ina jin ban kuma yarda anyi min masu kankantar su ba.
Kusan kwanan zaune mukayi a ranar muna hira, muyi hira muyi kukan murna muyi kukan bakin cikin
rabuwa sannan kuma muyi dariyar jin dadi. Da assuba muka kammala hada duk wasu sauran kayayyakin
amfanin mu dan kusan komai mun bayar dashi sai few abubuwan da suke da muhimmanci muka dauka.
Da sassafe muka kai kayan mu bakin gate din makaranta muka koma ciki sannan muka yi wanka muka
shirya a tsanake muka fito daga hostel bayan munyi bankwana da metrons da sauran daliban da muka
bari a bayan mu, muka tafi exam hall muka zauna, sai a lokacin ne muka danyi karatu kadan kafin a shigo
mana, ana shigowa kuwa muka ajiye komai muka rubuta final paper din mu.
Kowa yana gamawa, daga mai ihu sai mai tsalle sai masu rungume juna suna kukan dadi da kuma na
rabuwa, amma ni sai na samu kaina da tunani.
Wannan fa shine kamar wata border a rayuwa ta, kamar with this final paper na ajiye duk wani
childhood dina kenan. Na zama cikakkiyar budurwa, kamar yadda nake kallon wadanda suka yi candy a
matsayin manyan yammata nima na shiga cikin su kenan yanzu.
And my battle begins......
Neman admission, samari, aure ko karatu, yaushe zaki yi aure, samari yan yaudara da yan iska......duk
yanzu zanyi facing dinsu in full scale. Am I ready?
Ni dama haka nake a rayuwata ina da tsoron chanji, na gammace in ta jure halin da nake ciki akan in
nemi chanji sai imta jin tsoron irin kalubalen da zan fuskanta a sabon babin da zan bude, but wannan
babi ne da dolen dole in bude shi, ba wai shawara ta bace ba, a'a dole ne.
Tunanin cewa aure yana daga cikin abinda wannan sabon babi na rayuwata ya kunsa sai ya dawo min da
tunanin sa, though dama ba wai tafiya tunanin yayi ba, but sai naji son ganinsa ya dawo min sabo, sai na
ji a raina ina addu'ar ina ma yazo daukan kanwarsa? At least nasan zan raka ta mota ko kadan ne sai in
samu damar satar kallon sa ko da kuwa bamuyi magana ba.
Mufida ce ta katse min tunani na ta hanyar zuwa ta dane min jikina tana ihun murna, daga nan komai ya
rike ce, muka fara bin malamai muna yi musu sallama su kuma suna yi mana nasiha akan rayuwa,
wadanda already aka zo dauka suka fara tafiya. Ana ta exchanging phone numbers musamman a gurin
wadanda suke da waya, mu kuma wadanda bamu da ita sai muke bayar da wayar wani da za'a same mu
tare, ni dai wayar Umma nake bayarwa.
Muna cikin haka aka zo kiran Mufida, nan take naji cikina ya murda sosai kamar zanje toilet, Muka kama
hannun juna muka fito daga hall din tare, a raina ina son in raka ta ko Allah zai saka shine yazo daukanta
sai in ganshi, har munyi nisa sai kuma na ja na tsaya ina tambayar kaina ina aji na yake? Ai ba dan Allah
nake da niyyar raka tan ba sai dan in ganshi, in dai har shine yazo daukan ta zan so ace shima yana son
ganina dan haka shi zai aiko a kira ni ba wai ni inje kafin ma ya neme ni ba.
Sai na saki hannunta ina girgiza kaina "kije kawai Mufida, na tuna nayi mantuwa a hostel kuma nasan an
kusa zuwa dauka na, ki je kawai zamuyi waya in na je gida" ta tsaya tana kallona, daga dukkan alama
bata ji dadin magana ta ba kuma na saka ran zata yi retaliating amma sai naga ta gyada kai tace
"shikenan. Allah ya kiyaye hanya. Ki kira ni fa kina zuwa gida. Ki gaida Umma da Amira" nace "zasu ji. Ki
gaida kowa" a raina ina son ko sakon gaisuwa ne in aika masa amma pride ya hana ni, na juya na koma
inda na fito.
Sai dai ban gama sauraron labarin da Maryam take bani ba, duk da ba fahimta nake yi ba, sai ganin
Mufida nayi a gaba na. Gaba na ya fadi, muka tsaya muna kallon juna sannan muryar ta can kasa tace "ki
zo wai.....inji Yaya Doctor" gaba na ya fadi, har wani gumi naji ya karyo min, kafin in bada amsa Sai ta
juya ta fita, wani side na zuciyata ya ce min inyi zamana kar inje, wani kuma, inda already dama yake
daukin ganin sa ya fara tsallen murnar ganinsa, nasan babu yadda zanyi in rarrashe shi ya hakura dan
haka na tashi na bita a baya.
Har tayi nisa saboda sauri take yi, ni kuma ban iya sauri ba kuma ba zanyi saurin zuwa saurayi ba dan
haka na cigaba da catwalking abina. Sai kuma naga ta tsaya can nesa kadan da inda naga mota irin
wadda rannan suka zo a cikinta. Na karasa kusa da ita na tsaya nima bance komai ba, a raina ina jin babu
dadi abinda tayi min, ta juyo tana kallona sannan tace "daga Abuja yake, suna can shida Daddy, yaji yau
zan yi graduating shine ya dauko hanya tun asuba ya taho dan yana so yazo ta ganki, ba wai dan ya
dauke ni ba" na bita da kallo, ina jin zakin maganar ta kamar suga a zuciyata, amma kuma bana jin dadin
yanayin da take yi min maganar da shi.
Ban ba ta amsa ba ya bude kofar motar ya fito, numfashina da bugun zuciya ta duk suka tsaya a tare, ya
saka shadda ruwan zuma kansa da hula ba kamar ranar nan ba, sai naji na kasa tantance yaushe ne yafi
kyau, ranar nan ko kuma yau?
Na taka a hankali na tafi inda yake, dan nasan ni yake jira kuma nasan in banje ba zai iya tahowa kuma
inda muke tsaye ana iya hango mutum tun daga exam hall din da sauran daliban suke ciki.
Kafin in karasa naga ya zagaya daya side din motar ya bude kofar gidan gaba sannan ya tsaya a bakin
kofar tare dayi min nunin cewa in shiga da dayan hannunsa, fuskar sa dauke da irresistable murmushi.
Naje gabansa na tsaya idanuna a cikin nasa, sannan a hankali na sauke idona kasa. Naga kofar motar
daya bude na kuma fahimci me yake nufi da hakan amma nayi ignoring. "Sannu da zuwa" na fada da
sassanyar muryata. "Yauwa nagode" ya amsa, "bismillah" ya fada yana sake nuna cikin motar da hannun
sa, na daga kai ina kallon fuskarsa amma ban shiga ba sai yace "ba cinye ki zanyi ba fa, I promise, ina so
muyi magana ne amma bana son muyi a nan saboda........" Ya nuna jama'ar da suke ta zirga zirga a
wajen.
Na gyada kai na. Zan so inji abinda yake so muyi magana akai amma ba zanso Abba ya shigo ya ganni a
tsaye tare da wani wanda bai sani ba. Ƙwaƙwalwa ta tayi kokarin tuna min da cewa gwara ya ganni a
tsaye tare da wani akan ya ganni a cikin motar wani, amma sai zuciyata tayi saurin kawar da warning din,
dan tana so ta farantawa abin son ta.
Na sunkuya na shiga motar na zauna tare da dora yar karamar jakar hannuna a kan cinyata, idanuna
akan hannayena, ina jin sa ya rufe kofar sannan ya zagayo seat din driver ya bude ya shigo tare da
rufewa.
Na rike numfashi na ina jin rashin dacewar zaman mu har cikin zuciya ta, I had never been so close to
namijin da ba muharrami na ba kamar haka. Na kasa dago ido in kalleshi amma ina jin idan sa a kaina, na
dan ja hijabi na ina kara rufe cinyoyi na da suka bayyana kasancewar wandon uniform ne a jiki na kuma
hijabin mu bashi da girma sosai. Sai kuma na tuna cewa ban gaishe shi ba. "Ina kwana?" Na fada da
muryar da naji kamar ba tawa ba. Bai amsa ba sai kallo na daya cigaba da yi, na fara tunanin in bude
motar in fita sai naji yace "wai dan Allah in tambaye ki Jidda, ke wacce tribe ce?" Na dago da sauri muka
hada ido, sai dai banyi mamakin tambayar tasa ba saboda na sha jin irinta a gurin mutanen da basu san
ni ba.
Yace "ina ganinki ranar nan sai nayi tunanin bafulatana ce, sai dana kalla sosai naga cewa ba ita bace ba
and definitely not Hausa and not kanuri, nooooo bayin nan basu da wannan kyan, and I thought about
shuwa but idanunki ba irin nasu bane ba, idan ma sune to an samu mix, ba dan kalar fatar ba kuma zan
iya cewa Arab but skin din ba tasu bace ba" ya dan rage ido yana kara kallon fuskata, sai na kama kasan
hijab dina zan rufe fuskar sai kuma na tuna hakan yana nufin bude cinyoyi na, sai na saki hijab din na
rufe da hannu na.
Ina jin shi yayi dariya kadan. "Please ki gaya min mana, it kept me awake at night, inyi ta tunani, har
pictures din girls from different tribes nake browsing ina comparing da taki fuskar dana riga na dauki
hotonta na kuma yi saving anan...." Ya fada yana nuna kirjinsa. Na bude fuskata inajin maganganun sa
kamar busar sarewa a kunne na saboda dadin su, amma na dage wajen kin nuna hakan a fuska ta.
Nace "kace zamuyi magana, ina dan sauri ne kar azo daukana ayi ta nemana. Wacce maganar zamuyi?"
Ya dan gyara zama da serious murya yace "taimako nazo nema gurin ki Jidda" naji gaba na ya fadi nace
"taimako kuma? Wanne irin taimako?" A take zuciya ta ta fara lissafo irin abubuwan da zan iyayi
dominsa, sai ya dan langwabe kai "bani da lafiya, magani nazo ki bani" na kalleshi da sauri, a idona sai
naga yayi kamar mara lafiyan gaske, kamar ya dan rame akan wancan ganin da nayi masa, nace "me
yake damunka? Ni bani da magani ai, kai ba Doctor bane ba ka duba kan ka mana?"
Ya danyi murmushi still idonsa cikin nawa yace "nayi kokarin treating kaina na kasa, har allura nayi wa
kaina duk da bana son allura amma ban warke ba" na danyi shiru ina assessing maganar "to ka fada
mana a gida sai a kaika gurin wani likitan ya duba ka? Ni ai ban iya duba marasa lafiya ba, me yasa zaka
taho guri na?" Ya sake fadada murmushin sa, idanuwan sa suna sake yi min kyau, na kasa dauke idona
daga kansa a hankali kamar mai rada yace "saboda kina da nasaba da abinda yake damuna" nima nayi
magana a hankali "zazzabi ne yake damun ka ko mura? In zazzabi ne zan baka paracetamol in mura ce
kuma...." "Nan ne yake min ciwo" ya fada yana nuna kirjinsa, ɓangaren da zuciyarsa take, "kuma bana
iya bacci, in na rufe ido na sai inyi ta ganin ki kina yi min murmushi, irin wanda kika yi min ranar nan da
kuna tafiya ke da Mufida, shine na dawo in roke ki Allah da Annabi ki sake yi min wani irinsa, ko wanda
ya fishi"
"Wannan shine maganin ciwo na, shine abinda zai warkar dani, shine abinda ya saka yau nayi driving
seven hours straight dan in ganki, ina fatan ba zaki hana min ba" na cire idona daga cikin nasa na mayar
dasu kan hannayena da absentmindedly suke wasa da strings din jakata, a raina ina tunanin ko dai
mafarki nake yi? A cikin ire ire-iren mafarkan da nake yi nasa, amma it felt sooo real, kalaman sa felt as
real as kamannin sa.
"Please......" Ya kuma roka, "please kar kice nayi zuwan banza, ko fake smile ne a bani ina so a haka,
amma nafi son real din, in son samu ne a hada min harda dariya ko yar karama ce"
Ban san yaya akayi ba sai kawai jin murmushi nayi akan fuskata, bansan sanda nayi ba dan zuciyata bata
yi shawara dani ba kawai ta bi umarnin sa. Ajjiyar zuciya naji ya sauke mai karfi "alhamdulillah. Masha
Allah. Tsarki ya tabbata ga ubangijin da ya halicci wannan kyakykyawar sura. Jidda Allah yayi miki kyau, ki
gode masa, fuskar ki da suffar ki mai kyau ce sosai. Kuma yanayin yadda kike ta faman gyaran hijab dinki
da yadda kika makale a jikin kofar kadai ya saka naji a raina cewa kyawun ki ba'a physical kadai ya tsaya
ba, har cikin zuciyarki ke kyakykyawa ce. Ni Umar Faruq naga Hauwa'u Maijidda kuma ina sonta, har
cikin ruhina ina son ki. Na yaba da komai da idanuwa na suka gani, ina kuma neman alfarmar ki bani
dama in gama sanin abinda ban sani ba kema kuma ki san duk abinda kike bukatar sani daga gare ni,
that's in abinda kika gani physical yayi miki....."
Ya fada yana nuna kansa, na kalle shi briefly na kuma mayar da idanuna kan band dina da nake ta jujjuya
wa a hannuna, ina jina kamar ina yawo a cikin gajimare.
Yace "Maijidda.......kiyi magana mana..... please zaki bani dama? Zaki bamu dama mu karanci juna sai
kuma muga inda Allah zai kaimu. Me kika ce?"
Na motsa bakina amma sai na kasa magana, to me ma zance ne? Ina sonsa, kuma abinda na gani na
daga suffarsa yayi min, sannan nima ina fama da irin ciwon da yake fama dashi kuma nima fuskarsa da
murmushin sa sune suke ratsa cikin baccina a duk lokacin dana kwanta, wannan shine amsar dana bashi
amma ba zan iya gaya masa ba, kunya da kuma pride ba zasu barni in gaya masa ba, at least not now. Na
bude bakin sai kuma na mayar na rufe.
Ya rankwafo yana leka fuskata "ba zaki yi magana ba ko? Ni kadai zanyi kida na kuma inyi rawa ta ko?
Shikenan to, in dai zaki saurara kuma zaki kalla I will gladly sing and dance for you, indai har hakan zai
saka ki cigaba da yi min kyakykyawan murmushin ki" na sake yin murmushin, sai kuma na kama hannun
motar ina kokarin budewa, naji ta a rufe, na juyo ina kallon sa "am I a prisoner?" Ya daga hannu "nooo,
never. But at least say something mana, anything........ please" nace "abbana zai iya shigowa makarantar
nan a kowanne lokaci, and do you know abinda zaiyi min in ya ganni a cikin motar nan?"
Ya girgiza kai, his face looking concern. Ni kaina bansan abinda zaiyi min din ba amma ba karamin aikinsa
bane gobe inji an daura min aure, zaice zan dauko masa abin kunya ne, but ba zan gaya masa haka ba sai
nace "zai shiga staffroom ne ya aro bulala ya fito nan ya zane ni a gaban kowa sannan ya saka ni a booth
din motar sa ya tafi dani gida" ya danyi dariya, sannan yayi unlocking kofar, yace "that means akwai
good upbringing. Masha Allah" na bude kofar na fita