Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
ta da hannu daya dayan hannun kuma yana lafta mata belt din
hannunsa. Na rike hannun duk da nasan ba wai karfina ne ya rike shi ba, ya tsaya ne kawai saboda gani
na, fuskarsa murtuk idonsa yayi ja, Asabe ta koma bayana tana soshe soshen dukan da ta riga ta karba
kafin in zo. Na nuna shi da dan yatsa na nace "duk hannunka daka saka a jikin ta bai ishe ka ba sai ka
kuma sakawa da niyyar duka? To wallahi bar ganin Yasmin da Asad da suke tsakanin mu, idan ka kuma
dora hannun ka a jikinta sai na hada ka da hisba"
Ya bini da kallo, mamaki fal a cikin idonsa sannan ya mayar da dubansa kan Asabe yace "ki bar gidan nan,
kafin in shiga daki in fito"
Ya juya ya fita, na zare hannun Asabe daga jikina ba tare dana kalli fuskarta ba na fita. Haka kawai ganin
su a tare a dakin sai naji kwakwalwa ta tana painting scenes iri iri, irin wadanda zuciya ta ba zata iya
dauka ba. Na fita da sauri ina rufe bakina. Anan ne abin ya kasance ko a dakinsa? Kan gadon da muke
kwanciya ni da shi? Kukan da nayi rantsuwa na daina shine ya taso min, nayi saurin shiga daki har da
turo kofa amma ina juyawa da niyyar yin kuka na sai naga Yasmin a tsaye a gaban kayan da bake
hadawa. Asad tsaye a gefenta suna kallona.
"Mommy ina zamu je" Asad ya tambaya
"Mommy what's going on? Are you crying?" Yasmin ta tambaya
"Ko Daddy ne ya dake ki? Naji kukan Asabe Daddy yana dukan ta" Asad ya sake tambaya
"Mommy fada kuka yi da Daddy ko? Irin wanda kuka yi ranar nan ko? Ba kunyi min alkawarin kun daina
fada ba?" Yasmin ta sake tambaya.
Na hadiye kukana, na share hawayen da already ya fara gangarowa zuwa kuncina sannan na kirkiri
murmushi.
That's one of the hardest things dana taba yi a rayuwata but for my children I can do more than that. Na
durkusa a gaban su ina rarraba ido a tsakanin su. Zaman da nake yi a gidan nan after all that has been
happening saboda su ne, and yanzun ma tafiyar da zamuyi saboda su ne. Na shafa fuskokin su a tare
nace "tafiya zamuyi, zamuje gidan Umma" Asad yayi tsalle "su Muhsin (dan yaya Hudallah, sa'an Asad)
zasu je suma? Mommy zan iya tafiya da game dina muyi tare da su ko?" Na gyada masa kai, bai jira
sauran amsa ta ba ya yi hanyar waje da sauri yana cewa "bara inje in harhada kayan wasa na" ya juyo
yana nuna ni "mommy kar fa ku tafi ku barni, yanzu zan dawo".
Bayan ya fita na dawo da kallona kan Yasmin, har yanzu da kirkirar ren murmushi a fuskata. Amma
kallon da take min ne ya saka murmushin ya gudu ya barni. "Whats going on?" Ta sake tambaya ta.
Bance mata komai ba saboda bansan me zance mata ba. Mamakin ta kawai nake yi, kamar kullum she is
acting matured, tamkar kwakwalwar ta tafi shekarun ta girma. "Gidan Abba zamuje, na sake fada mata,
we are going to be living there for a while" "Daddy kuma fa?" Ta tambaya. Na mike tsaye ina cigaba da
hada kayan mu. "Mommy daddy kuma fa? Bin mu zaiyi ko shi kadai zamu bari a gida?"
Na juyo a fusace tare da nuna ta da yatsa "shut your mouth. Mai shegen iyayi. In kika sake min wata
tambayar sai na fasa bakin ki" ta tabe baki sannan ta samu bakin gado ta zauna tare da folding
hannayenta tana bina da kallo har na gama abinda nake na fito musu da kayan sanyi na mika mata "ki
saka sweater da hula da socks, sai ki kira Asad ya saka nasa" ta karba tana cewa "mommy yanzu zamu
tafi? Ba zamu bari sai gobe ba? Magrib ta kusa fa" na watsa mata harara sannan na jawo ta na fara saka
mata da kaina. She is right, magrib ta kusa sanyi kuma ya fara kadawa. Gari ya fara duhu, but am not
going to spend another night breathing the same air with Umar. I rather take my chances with the cold.
Shigowar sa ta saka muka dago a tare muka kalle shi. Yasmin tayi saurin matsawa daga kusa da ni ta tafi
gurinsa "Daddy wai gidan Abba zamuje inji mommy. Daddy ni bana son zuwa bana son tafiya in barka ni
nafi son zama a gurinka" ta karasa tana matsar hawaye. She has always been daddy's girl tun tana baby.
Ya durkusa a gaban ta. "Babu inda zaki je kinji baby girl? Kina tare da daddyn ki. Now go and watch TV a
falo zanyi magana da mommy" ta juya ta kalle ni sannan ta fita da sauri, I noticed tayi relaxing, maganar
sa ta kwantar mata da hankali.
Sai data rufe kofa sannan ya juyo kaina inda nake kokarin rufe windows "Jidda, please don't do this. In
ba kya son ganina I can leave the house for you har sai kin sauko zuciyarki tayi sanyi sai in dawo. Please
ba dan ni ba ko dan yaran nan kar ki raba musu hankalin su dan Allah. Kar kije ki tayar da hankalin su
Abba a kan maganar da bata taka kara ta karya ba. Karya ce yarinyar nan tayi miki, I told you koma me
tace nayi karya take banyi ba, I don't know me yasa zaki dauki maganar ta ki bar tawa ni a matsayina na
mijinki. I don't....."
Na daga masa hannu "ya ishe ka haka. Ganin ka ma a gabana bata min rai yake yi ballantana sauraron
muryarka. Please ni ba fahimtar ma me kake cewa nake yi ba dan yanxu am beyond reasoning. Go away
please, kaje dakinka ko kitchen ko dakin Asabe..... anywhere but inda bazan ganka ba har in gama abinda
zan yi in fita. Then you are free to do koma menene zakayi. You are free ka kawo mata har cikin gidan ka
ma ba zan cigaba da zama shamaki a gare ka ba. Do whatever you want, I don't care. Am done caring"
Yanayin fuskarsa zai iya saka mai saurin kuka ya fashe da kuka ba tare da yaji karin bayani ba. The same
look da yake using a duk lokacin da nayi mishi irin wannan kamun. "Jidda please, give me one more
chance. One more chance. In na kuma wasa da wannan damar na yarda kiyi min komai ma. One last
chance please......"
Nayi dan gajeren murmushi. "Last chances dinka guda nawa ne a duniya Faruq?........am done" na zuge
jakar kayan na fara kokarin dauka. Ya rike hannuna biyu na nasa guda biyu, "Dan Allah dan Allah fa nace
Jidda. Ni fa mijinki ne kuma nace miki ki duba Allah kiyi hakuri. Ki bani dama inyi miki bayani Jidda,
wallahi banyi abinda kike tunani ba, wallahi karya take yi, darajar yayan da suke tsakanin mu. In ci
darajar su please ko ban ci darajar soyayya ba, ko ban ci darajar son da nake miki ba. Kin sani Jidda, kin
san ba zan iya rayuwa babu ke ba Jidda, in kika bar no bansan yadda zanyi ba, ban san me zan zama ba,
kar ki yanke min hukuncin kisa ba tare da kinji nawa side of the story din ba"
Sai ya cika hannuna daya ya kamo bayan wuyana da hannunsa, hannun da naji ya dauki zafi kamar
gasashshen naman da aka sauke shi daga wuta yanzu. Na tabbatar da za'a auna temperature dinsa a
asibiti to kuwa tabbas za'a bashi gado, kamar yadda da za'a auna bp dina nima za'a bani gado, sannan ya
dora bakinsa da sauri akan nawa ya na kissing dina as heated as yadda jikinsa ya dauki zafi.
Da farko kiss dinsa ya shige ni, as usual, kamar yadda kalaman sa suka fara shigata as usual. But sai
ƙwaƙwalwa ta ta aiyano min bakin Asabe, musamman farkon zuwanta gidan lokacin da har sai dana
hanata magana a kusa dani saboda warin da bakinta yake yi. Sai dana takura mata da yin brush sau biyu
a rana sannan muka samu sa'ida, sannan bakin ta ya fara zama irin na mutane.
Wani amai naji ya taho min mai zafi, na fara kokarin ture shi amma yaki shikani, yunkurin aman da nayi
ne ya saka yayi saurin saki na, Allah ya taimake shi, badan haka ba da tabbas na juye masa taliyar da naci
da rana a cikin bakinsa, na shiga toilet da sauri na juye ta a can. Na wanke bakina da fuskata ina kokarin
kawar da hoton bakin Asabe daga zuciyata, in ba haka ba aman ba zai tsaya ba saboda ni mutun ce mai
tsananin tsantsani. I wonder yadda na iya zama da Faruq har tsahon shekara shida. Lallai ba karamin so
nake yi masa ba. But not anymore.
Na fito da face towel a hannuna ina goge fuskata da hannayena, yana tsaye a inda na barshi kamar
mutum mutumi fuskar sa cike da mamaki yace "did you just......." Na karasa masa "vomit, because you
kissed me. Yes. And that ought to assure you that it really is over between us" na dauki hijabi na na saka,
na rataya handbag dina sannan na kinkimi jakar kayan yarana na kuma ja hannun akwatin kayana nazo
na wuce shi na fita.
A falo naga Yasmin a zaune a kan kujera ta zubawa kofar dakin da muke ciki ido, hawaye a fuskar ta
wasu suna bin bayan wasu. Ina fitowa ta mike tsaye sannan ta kalli kayan da na fito dasu tace "mommy
fada kuke da Daddy ko?" Ban bata amsa ba. Asad ya fito daga dakin da yake matsayin nasu duk da dai ba
zama suke yi a ciki ba sai dai in zasu yi wasa , hannayensa cike da tarkacen kayan wasan sa fuskarsa cike
da annashuwa, na karbi kayan na zuzzuba a aljihun jakar kayansu shi kuma ya zuba wasu a pockets
dinsa. Na saka masa sweater da socks na hannu dana kafa, sannan na saka masa hula na rufe masa har
kunnuwan sa. "Oya muje"
Ina kallon Yasmin tana kallon kofar dakina, kuma jikina ya bani yana tsaye a gurin amma ban waiga ba
kuma bani da niyyar waigawa. Naji tace "Daddy!" Sai naji muryarsa yace "go, Yasmin, go with your
mother, zan zo anjima da daddare in taho daku gabakidaya" naji kamar in juya in gaya masa magana
amma na daure saboda idon yara. Bama taba musayar magana a gaban yara.
Na tisa keyar yarana har waje, a lokacin ne na lura kofar dakin Asabe a bude kuma bata ciki, ko a jikina
ban damu ba, ban dau da inda ta tafi ba ko kuma abinda zai faru da ita ba, alhakin ta yana yuwan wadda
ta kawo ta gidan.
Muna fita compound automatically muka tafi inda mota ta take fake kusa da tasa, sai kuma zuciyata ta
ayyana min wani abu, shi ya sayi motar, in dai har zan rabu dashi ya kamata in fara koyan rayuwa ba tare
da shi ba. Sai na juya nayi hanyar gate, ina jin Yasmin tana jero min tambaya, Asad yace "mommy a
motar haya zamu tafi?" Nace masa "eh" yayi tsalle "cool! This is amazing!"
Na jiyo takunsa da sauri ya biyo bayanmu. "Jidda Jidda Jidda. Jidda please don't punish these kids. Kar ki
fita dasu a cikin sanyin nan, ina zaku samu mota yanzu a nan? Dan Allah ki shiga motar ki, ni ki bani inyi
driving din in driving din ne ba kya son yi. Dan Allah" na watsa masa wani mugun kallo ina kankance
idona a kansa, maganganu da dama suna forming a zuciyata amma ina danne su saboda yara, kamar
yadda nake komai saboda yara.
Yayi kokarin rike hannu na not minding kallon da nayi masa "kin san baki da lafiyar numfashi Jidda, idan
ciwonki ya tashi a hanya me kike tunanin zai faru? Ya kike so inyi da raina?"
Nayi gaba na barshi ina hada hannun akwati da hannun Yasmin ina ja a tare. Sai ya sunkuya ya dauki
Asad ya dora shi a kafadar sa yana gyara masa hularsa, sannan ya biyo bayana ya zare jakar kayan daga
hannuna. Na bar masa saboda mun fito bakin layi bana son creating scene musamman saboda mutane
da suke tafiya masjid dan har amfara kiraye kirayen sallah. Na ja hijab dina na rufe rabin fuskata na
sunkuyar da kaina kasa ina zabga sauri. Ina jinsa suna gaisawa da mutane a duk inda muka wuce, few
suna tambayarsa dalilin da suka ganmu a kasa da kaya haka, shi kuma yana bada amsa da mota ta lalace.
A ciki harda wanda yayi offering zai dauko tasa motar ya kaimu.
Muna fita titi ya sauke Asad sannan ya fara kokarin tare mana Napep, wani ya tsara ya bashi address din
gidan Abba sannan ya dauko kudi ya bashi yayin da ni kuma na saka yayana a ciki ina kokarin daukan
kaya yazo da sauri ya dauka ya saka a ciki sannan ya bani guri na shiga, ya durkusa ya ja min skirt dina ya
rufe min kafafuwana, yana kallon Yasmin yace "share hawayen ki kinji sweetheart. Zanzo an jima in taho
daku gabaki dayan ku" ya karasa maganar yana kallona, Sannan ya kai hannunsa da niyyar gyara min
hijab ya rufe min hanci da shi, na dauke kaina gefe, ya sauke hannunsa yace "akwai hazo jidda, kar
ciwonki ya tashi" bance komai ba kuma ban kalle shi ba sai yayi taku biyu baya ya bawa mai Napep
damar tayarwa muka tafi.
A hanya Asad ne yake ta hirarsa shi kadai, yana ta lissafa abokan sa da zasu yi wasa har da yayan
makotan da ni ban ma san su ba. Lokaci zuwa lokaci ina bashi amsa with hope cewa zaiyi shiru ya bar ni
da tunani na amma baiyi ba kamar wanda aka sakawa batir.
This is my step four, abinda na jima ina lissafin zanyi indai har abubuwa suka cigaba da tafiya a yadda
suke. Amma yanzu da lokacin yazo, yanzu da na riga na dauki niyyar yin abin, sai naji dukkan confidence
dina babu shi, ban san me zan ce a gida ba, ban san me zance da Abba ba, ta ina zan fara? Kuma a ina
zan tsaya? Komai da komai zan fada ko kuma akwai abinda ya kamata in cire?
Ban sani ba, abinda na sani kawai shine na gama auren Umar. Ko za'a daka ni a turmi kuma a tankade ba
zan koma gidan sa ba.
A haka har muka je gida. Na sauka, na sauke yaran sannan mai Napep ya sauke min kayana ya tafi. Na
tsaya na seconds ina kallon gidan da anan aka haife ni anan na girma anan ne kuma iyayena suke har
yanzu. Am I really ready for the life ahead of me? Are my children ready? Can I? Can they?
A tsakar gida na samu Hajiya tana alwala, na gaishe ta ina kallon dakinta tare da expecting Farhan zata
leko, ko sallah take yi? Ta amsa tana tsokanar Asad shi kuma ya fara yi mata surutu, na lura da yadda
take bin kayanmu da kallo fuskarta da wani yanayi da na kasa tantance wa. Na wuce zuwa dakin Umma
da kayan, na tarar tana sallah a falo, Amira tana kwance akan kujera da littafin hausa a hannunta. Ta
mike da sauri tana yi min sannu da zuwa sannan ta fita ta dauko Asad ta shigo dashi tana dungure masa
kai "mai shegen surutun nan. Yaje sai zuba yake kamar fanfon daya lalace" ya turo baki zaiyi kuka na fita
na barsu. Toilet na shiga a tsakar gida na fito nayi alwala nima na shiga na tayar da sallah. Ina cikin yi naji
sallamar Abba ya shigo.
Ina idarwa ko addu'a banyi ba naji ya shigo falon. "Hauwa'u? Ina Hauwa'un take? Ke Jidda?" Umma tace
"sallah take yi, bata idar ba" nayi saurin shafa addu'a na juyo. "Abba ina....." Ya daga min hannu
"menene naji ance kin shigo gidan nan da kaya? Wanki za'a yi muku ko kuma kayan bayarwa ne kuka
kawo?"
Na sunkuyar da kaina, hawayen nan da basa jin magana ta suka fara bin fuskata. "Kuka?" Umma ta
tambaya. "Jidda me ya faru? Yaji kika yi?" "Yaji?" Naji muryar Hajiya a bakin kofa "kash! Amma wannan
abu baiyi dadi ba. Yaji kika yi ko kuma sakin ki yayi? Allah dai yasa ba sakin bane ba?" Na dago kai na
kalle ta ina jin wani irin zafi a zuciyata, fuskarta cike da farin ciki. Umma ta mike tana rike kugu "sai dai
kiga saki akan yayanki ba dai akan Jidda ba wallahi. Aniyarki ta koma kanki"
Abba ya kama fada "to sarakan masifa, an girma ba'a san an girma ba. Kun gama yin fada a gaban
yayanku kun koma yi a gaban jikoki dan abin kunya" duk suka dauke kai gefe suka yi shiru. Amira ta faki
idonsa ta murguda wa Hajiya baki a hankali tace "haka kawai ba a kasa da mutum ba yazo yana diba"
Yasmin ta taso ta dawo kusa dani ta zagaye ni da hannayenta ta saka fuskarta a wuyana, ina jinta tana
sheshshekar kuka.
Abba ya kuma nuna ni da hannu "magana nake miki fa? Ko kin zama kurma ne yau. Kayan me kika shigo
dasu? Me ya kawo ki gidan nan da magriba?" Ban amsa ba still, dan tun a hanya nake gada kalaman da
zan gaya masa amma basu hadu ba. Jin nayi shiru ya saka ya dauko wayarsa daga aljihunsa sa, gaba na
ya fadi, he is not going to call Umar is he? Maganar na naji yayi ta tabbatar min da fargaba ta.
"Doctor lafiya kuwa muka ga Jidda da kaya?"
"Babu abinda ta gaya mana kuma mu babu abinda muke so muji. Shi sirri na tsakanin mata da miji ai
boye shi ake yi ba bayyana shi ba"
"Babu komai. Sun iso lafiya, babu komai. Ka taho kawai yanzu kazo ka dauke su ku koma. Yarinta ce irin
ta Jidda, kayi hakuri"
"A'a, babu komai wallahi. Allah ya kiyaye gaba"
Ya mayar da wayar aljihu ya juyo yana kallo na "zancen banza zancen wofi. Ga iyayenki nan, shekarar mu
nawa a gidan nan kuma babu irin rigimar da bama yi dasu amma babu wadda ta taba daukan kaya ta tafi
gidan su da sunan yaji. Haka yayyenki duk sunsan doka ta ba'a yi min yaji a gida wallahi. Babu yarinyar da
zata kashe aurenta tazo ta zauna min a gida walahi, sai dai kuma idan wani uban zaki sake bani ba. Ke
banda sakarci irin naki duk dangi wacece tayi dacen miji irin naki? Duk yan uwanki wa kika ga tana
rayuwa irin taki? Duk cikin surukaina wa nake ji dashi kamar mijin ki? Ji nake kwana biyu da suka wuce
yazo nan ya lissafa kudin makarantar kanwarki chif ya dankamin a hannuna, shine kuma kike so ki debi
kasa ki watsa min a idona? To wallahi ahir dinki, kar in kuma ji kar kuma in kuma gani. Kar ki kara tako
kafarki zuwa gidan nan ba tare da izinin