Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
juya ina kallon
Farhan, itama ni take kallo tace "me kika yi?" Na bude hannu "nima ban sani ba" Amira tace "an kira ki a
court dole kinyi wani abu da sanin ki ko ba da sanin ki ba ko kuma wani yayi wani abu a gabanki zaki
bayar da shaida" na hadiye abincin bakina mukut cikin tsoro sannan na wanke hannu na na hau saman
ina karanto duk adduoin da suke cikin kaina, na tarar dashi yana cin abinci, Hajiya tana gefen sa tana yi
masa fifita.
Na zauna nesa dasu kadan nace "Abba gani" sai da ya jima yana kallona, jin Hajiya bata ce komai ba na
san cewa bata san dalilin kiran ba dan da ta sani da tuni ta fara fada tun kafin Abba ya fara, sai daya
gama kallona sannan yace "waye Umar?" na dago kai da sauri, jikina ya fara rawa kamar marar gaskiya
nace "na'am?" Ya maimaita "waye Umar nace, wanda kika tura office dina" na sunkuyar da kai na fara
wasa da band din hannuna ina murmushi cikin jin kunyar su, this is serious, wato har yaje kenan, lallai da
gaske yake kuma wannan ya kuma samar masa space mai kyau a zuciyata.
Jin nayi shiru ya saka Hajiya tace "saurayin ta ne ko?" Yace "eh haka yace min, amma so nake in san a
inda suka hadu dashi, yace min a gadon kaya gidan su yake, ita kuma bata da kowa a can, a ina ya
ganta?" Hajiya tace "zai wuce a waya?" Ya ajiye chokalin hannunsa yace "waya? Yaushe Jidda tayi waya
ban sani ba, waye ya siya mata?" Tace "a'a ba waya ce da ita ba, amma ai suna ɗaukar wayoyin mu suna
amfani dasu, zata iya yiyuwa wayar Umman ta ta dauka tayi wannan chatting din nasu na zamani anan
suka hadu, kasan yaran yanzu sai addu'a"
Na bude ido ina mamakin yadda za'a yi min sharri ina zaune da raina, nace "a'a Abba ba haka bane ba,
yayan Mufida ne fa, yayan kawata ne" ya mayar da hankalinsa kaina yace "yayan kawarki? Yaushe kika je
gidan su kawar taki har ya ganki? Ni dai ban san lokacin da kika tambaye ni cewa zaki je gidan su kawarki
ba" na sunkuyar da kai na, "a makaranta ne, ranar da muka gama makaranta yaje daukan ta ni kuma na
raka ta mota, shine .......shine......kuma sai yazo nan shekaran jiya sai nace yaje ya same ka"
Ya gyada kai yace "haka ya gaya min. Inaso ne in tabbatar. Malamin ku ne Abdulrashid ya raka shi gurina
kuma naga kamar da gaske yake, ba yaro bane ba dan cikakken likita ne ma a yanzu, na kuma ya ba da
hankalin sa da kuma asalin sa, nace ya cigaba da zuwa gurin ki, in Allah ya hada kan ku kuma kin zabe shi
shikenan. Tashi ki je"
Na mike da sauri a raina ina tunanin godiya ya kamata inji masa ko kuma godiyar zata zama kamar rashin
kunya? Ban dai gode ba na fita baki har kunne cikin farin cikin da yasa ban damu da maganar da naji
Hajiya tana yi ba "likita? Anya kuwa likita bai yi mata girma ba?" Abba yace "a ina kika taba ganin namiji
yayi wa mace girma?"
Ban ji sauran maganar ba na sauka da sauri, nasan halin Abba in dai yace abu to ba Hajiya ba ko wacece
ba zata chanja shi ba. Ganin fuskata yasa Farhan ta fara murna ita ma duk da bata san abinda ya saka ni
murna ba muka rungume juna muna dariya sannan tace "what are we celebrating?" Nace "Umar yaje
gurin Abba kuma Abba ya amince" ta kama kumatu na "inye, mun samu lisence sai soyewa kenan" na
kama nata kumatun "harda soye soye ma kuwa"
Umma data fito daga dakinta ta bimu da kallo "me za'a soya?" Amira da take jin mu tace "wai wani Umar
ne zasu soya shi" muka kwashe da dariya sannan na shige dakinmu da gudu ina jin Farhan tana yiwa
Umma bayanin saurayi na ne Umar din "yayan Mufida ne" banji amsar da Umma ta bayar ba saboda na
toshe kunnena ina murmushi mai hade da dariya.
A ranar, bai jira sai washegari ba a ranar yazo da dare. Umma tana daure tuwo a leda a tsakar gida ni
kuma ina karasa mata miya a cikin kitchen a ka shigo ana sallama dani. Yaron yace "wai ana kiran Jidda
inji Umar" nayi kamar banji ba amma na kasa faking murmushin daya sauka akan fuskata. Umma tace
"tana zuwa"
Sai kuma ta kira Abbah da ya shiga dakin ta yana kallo tace "kaje waje akwai bako a waje ka gyara sitting
room kace masa ya shiga" yace "waye yazo Umma?" Bata ce komai ba sai ta kalle ni, yace "au ho Musa
ne ashe, mun hadu jiya ai yana ta jin kunya ta" na juyo na harare shi a raina ina cewa "ba Musa ba sai dai
kakan Musa" yayi dariyar ganin yadda na bata rai yace "Allah ya baki hakuri yar malamin makaranta
matar malamin makaranta kuma kanwar malamin makaranta, kina tafiya chalk yana zuba"
Duk muka yi dariya har Umma, na dauko ludayin miya na bishi da sauri ya bude kofar sitting room ya
shiga, na koma kitchen Umma tace "miko kananan flask a zuba masa tuwo" na mika mata, Amira da take
kwance akan sallaya tana game da wayar Umma tace "Umma ni zan kai masa, sai in ganshi in ga ko ya
dace da yayata"
Aka zuba masa tuwon semo miyar zogale ta fita zata kai masa ni kuma na fito na wanke jikina a bakin
pampo na shiga dakin mu na cire doguwar rigar jikina na saka riga da skirt din atampa nayi daurin
dankwali na mai kyau na shafa powder na saka kwalli sannan na saka turare kadan yadda ba zai yi yawa
ba na kuma yafa mayafi na na fito, ina fitowa Umma ta harare ni, sum sum na koma na cire mayafin na
saka hijab na sake fitowa.
A lokacin Amira ta dawo daga kai abinci bakin ta har kunne "Umma baki ganshi ba wallahi ya hadu sosai.
Yace min nima ina da kyau kamar Jidda amma ita tafi ni kyau wai. Ya tambaye ni mu wane yare ne na
gaya masa" Umma ta kai mata duka, "to mai bakin aku, waye ya tambaye ki" ta matsa gefe tana dariya
sannan ta fito da kudi daga cikin hijab dinta yan dari dari sababbi bansan ko guda nawa bane ba, a daidai
lokacin da Farhan ta fito daga dakin Hajiya, ganin kudin ya sa tayi kan Amira da gudu suka shiga dakin
Umma, nayi musu dariya kawai na tafi sitting room.
Ina shiga na mayar da kofar shiga cikin gida na rufe, a raina ina fatan bai ji maganar da Amira tayi yanzu
a ciki ba, na juyo a kalleshi. Yana zaune akan kujerar da take bakin kofar fita waje, kananan kaya ne yau a
jikin sa rigar mai gajeren hannu wadda ta fito da damatsen sa tare da bayyana siffarsa ta cikakken namiji,
kansa babu hula sai gyararren gashin kansa.
Ya mike tsaye yana kallona kamar yadda nima nake kallon sa. Na zauna a kujerar karshe nace "sannu da
zuwa Yaya Doctor" yayi murmushi bai amsa ba sannan ya taho zuwa inda nake kamar yadda yayi ranar
nan amma maimakon ya zauna a kan kujerar kusa dani kamar yadda yayi ranar nan sai ya zauna a
gabana a kasa kusa da kafafuwa na yana kallona.
"Gani na dawo Jidda. Naje na karbo license din ganin ki a gurin Abba kuma ya amince min. Saura kuma
menene kike bukata? Say it, whatever it is, and it will be done"
Na girgiza kai na a hankali nace "nothing, for now" yace "sai nan gaba? Har yanzu ba'a gama yi min
jarabawar ba?" Nace "ba fa exam bace ba..." Yace "it felt like exam, sanda ina gaban Abba I felt like ina
cikin exam hall ne banbanci kawai shine babu question paper babu kuma answer sheet" ya danyi dariya
"kamar oral exams, nine student Abba shine supervisor" nace "tunda kace kana son ƴar malamin
makaranta dole yayi maka exam" yace "da gaske? Sake fada inji?" Nace "me?" Yace "ina sonki" ba tare
da tunanin komai ba nace "kana so na" ya lumshe ido ya bude yace "ke kuma me kika ce?"
Sai na fahimci trap yake neman hada min, na rufe ido na cikin kunya na kasa magana, yace "ki fada
mana, ina son ki Jidda, ke kuma fa?" Na girgiza kai na, yace "ba zaki fada ba?" Na gyada kai, yace
"saboda me?" A hankali nace "kunya nake ji" yayi dariya "in baki shawara? Tunda kunya kike ji ki toshe
kunnen ki zaki daina ji" na bude idon ina kallon sa cikin rashin fahimta nace "kunne kuma?" Yace "eh, ba
'jin' kunya kike ba? Ai da kunne ake ji ko? Ki toshe kunnen sai ki daina ji" nayi murmushi "ba wani nan,
ba haka bane ba" yace "baki yarda ba? Ki gwada ki gani. Ki toshe kunnen sai ki fada shikenan ni kadai
zanji abina"
Na makale wuya, "wayo zaka yi min, naki wayon" yayi dariya "to ki fada min dan Allah" nace "ba yau ba"
yace "sai yaushe?" Na juya idona Nace "sai nayi shawara" yayi ajjiyar zuciya yace "duk jan ajin ne haka?
Naji na dauka, duk sanda kika zama ready my ears my heart and my every other thing will be ready"
Nayi shiru ban ce komai ba, shima yayi shiru amma ina jin idonsa a kaina sai dai ni na kasa dago kai duk
da zuciya ta tana son hakan. Zuwa can naji yace "kafarki tana da kyau Jidda" nayi sauri na kalli kafar da
take a ajjiye a gabansa, tsirarar ta babu ko safa balle takalmi, nayi saurin dauke ta na mayar kan kujerar
da nake zaune tare da lullube ta da hijab din jiki na.
Yayi dariya "gabaki dayan ki kina da kyau, komai naki mai kyau ne kuma ina son komai naki sosai, yadda
kike magana, yadda kike tafiya, yadda kike murmushi da yadda kika yi wannan zaman komai burgeni
yake yi, komai yayi min yadda nake so. Ina son ki sosai Jidda, ina jinki a zuciyata irin yadda ban taba jin
kowacce mace ba, saboda ban taba ganin irin ki ba and I have seen a lot, have been in a couple of
relatonships even, amma tun daga lokacin dana dora idona akanki nasan cewa this is it, kamar irin
feeling din da mutum yake ji a lokacin da yazo gida bayan yayi doguwar tafiya"
"A dan lokacin dana sanki Jidda sai nake jin ki a raina kamar ba yanzu ne na sanki ba, kamar dama can
muna tare, kamar you have been there with me every step of my life kawai dai bana ganin ki ne, kamar
ke ce other side of me din da nake missing, sai yanzu dana ganki sannan na zama complete"
"Auren ki nake so inyi Jidda, that's idan kin amince kuma idan su Abba da Umma sun yarje min. Tun
ganin ki na farko na yanke hakan a zuciyata duk da ban san halayyar ki ba a lokacin, kuma a ganin da nayi
miki guda uku bayan nan na fara fahimtar wasu daga cikin halayyar ki kuma suma duk sunyi min. Amma
na sani cewa ke yarinya ce, yanzu kika gama secondary school kuma bansan lissafin ki da burinki ba. Dan
haka dole zan baki lokaci iyakacin yadda kike so ki shirya ki kuma zama ready"
"Daga gobe zuwa nan da shekaru biyar, ni zan jira, duk sanda kike so" na dago ina kallon sa nace "har
shekara biyar zaka jira?" Ya dan shafa sumar kansa yace "zan so kar ya kai haka, zanso with all my heart
amma sai abinda kike ce, ban sani ba ko kina son ki cigaba da karatu ne kafin aure ko kuma kina so sai
kin gama karatun ma gabaki daya kafin kiyi auren ko Abba yana so sai kin fi haka girma da wayo kafin
yayi miki aure ban san tsarin ba shi yasa nace shekara biyar din, maximum"
Nayi murmushin jin dadi, yadda yake saka damuwata a cikin lissafin sa yana burge ni sosai "ina son yin
karatu gaskiya, ko ban kammala ba ina son zan fara" "angama" yace, "inyi lissafin shekara biyu kenan,
kamar level two kenan ko?" Nayi murmushi bance komai ba. Yace "kinyi jamb ne?" Na girgiza kai na, na
tuno lokacin da aka yi jamb iyaye suka yi ta zuwa daukan yayansu daga makaranta suna kaisu gida suyi
kwana biyu suyi jamb, a ciki har da Mufida, ni kuwa dama ko saka rai banyi ba kuma ko mai kama da
Abba ban gani ba.
Ya shafa fuska, "ya salam, sai wata shekarar kenan. Amma wanne course kike so ki karanta" na danyi
tunani "ni ban san me zan karanta ba" ya bude baki cikin mamaki "kin gama secondary school baki san
me zakiyi a jami'a ba?" Na danji kunyar abin sai nace "uhmm, na dai ji ranar nan a school Abba yana
maganar nursing" yace "okay, na fahimta, abinda yasa bai dauko ki kinyi jamb din ba kenan. Amma Allah
yasa shi ma bamu makara ba, dan form dinsu da wuri yake karewa"
Ban ce komai ba sai ya dauko wayarsa yayi dialing ya saka a kunne "kai ya? Ya garin? Kana can kana jin
dadin ka ko?" Yayi dariya, dariyar sa tana kara masa kyau kuma tana yi min kyau sosai, ya cigaba "ka
shiga daga ciki ka bar ni da shafa kai. Ya maganar daliban ku ne? Form nake so dan Allah. Kai haba?
Gaskiya pull some strings ka samo min. Guda daya kawai nake so but it is very important, kayi min
wannan kokarin and I will forever be grateful. Okay. Thanks. Bye bye"
Ya ajiye wayar yace "har anyi an gama, next zuwa zan taho miki da form din school of nursing, sai ki
kaiwa abba mu ji abinda zai ce akai"
Naji wani irin dadi a raina, dadin da ba zan iya misalta shi ba irin wanda ban taba jin irinsa ba, kuma
wannan abin da Umar yayi min zan iya cewa yana daya daga cikin abubuwan da ba zan taba manta wa
dashi ba, daya daga cikin abinda har abada zan zama forever grateful for.
Na fara kokarin yi masa godiya sai ya dakatar dani, shi a ganinsa it was nothing, ni kuma a gurina it was
everything.
A kokarin sa na ganin banyi masa godiya ba sai ya fara dauko min labarin brief tarihin sa.
"Sunana Umar Muhammad Gidado Fata, kamar yadda nasan kin sani. Asalina bafulatani ne ta bangaren
uwa da uba gabaki daya, mahaifina dan kasuwa ne da yake safarar fatu daga Nigeria zuwa kasashen
ketare, mu bakwai ne a gidan mu, Yaya Mubaraka sai ni, sai Muhibbat, sai Muhsina, sai Mufida sannan
twins din aunty Aarif da Arfat. An haife ni a garin Lagos, a can kuma muka yi karatu ni da Yaya Mubaraka
tun daga primary har secondary, amma farkon shigar mu secondary school ne family suka dawo kano
saboda lokacin kannena mata sun fara girma kuma iyayen mu suna tsoron yi musu tarbiyya a can, sai
suka taho dasu nan ni kuma aka barni a can tare da Baba, su kuma matan gidan sai suke shifting na wata
ɗai ɗai a tsakanin su"
Na fahimci bayanin sa sosai, amma sai na samu kaina da tambayar kaina "shin akwai banbanci a tsakanin
tarbiyyar yaya maza da kuma mata? Shin duk abinda yake ba dai dai ba a gurin mace yana chanja suna in
ya koma gurin namiji? Me yasa iyayen mu suke ware tarbiyyar maza da ta mata? Me yasa ake takurawa
mata da tsoron kar su lalace amma kuma sai a sakarwa maza? Me yasa?
A cikin tunani na naji yana cewa "bayan na gama secondary ne nima na dawo Kano, anan buk nayi mbbs
sannan naje India inda nayi specialising a bangaren gynecology. A yanzu shekara ta daya da dawowa
kuma ina aiki a AKTH, ina kuma zuwa asibitin Murtala sometimes, sannan akwai wani private clinic na
friend dina da nake zuwa shima, mostly weekends. I am twenty eight years old, and very ready for
marriage but sai matata ta shirya tukunna"
Briefly nima na dan bashi nawa labarin da kuma siblings dina, sannan nayi masa tayin abincin da ya riga
ni zuwa gurin "baka ci abinci ba fa, Umma ce da kanta ta zuba maka tace a kawo maka" ya juya yana
kallon tray din yace "dole in ci abinci kuwa ko dan in samu albarkar Umma ta" nayi murmushi ina jin
dadin yadda komai nawa yake mayar dashi nasa. "Ki zo ki zuba min mana to.....ko baki san haka mata
take yiwa mijinta ba?" Na danji kunya amma na sauko na dauko tray din na dawo dashi kusa dashi
sannan na zuba masa tuwon leda daya na zuba masa miya a gefe na tabbatar na zuba masa nama a cikin
miyar sannan na ajiye masa a gabansa tare da plate din da aka sako pure water guda uku.
Ya dauki chokalin ya fara chi, loma daya sai ya dago yana kallona "wannan miyar tayi dadi da yawa, ban
sani ba kuma ko hakan yana da alaka da hannun daya zuba min?"
Kafin na bashi amsa aka bude kofar aka shigo, yaya Tahir, ya kalle ni sannan ya kalli Umar wanda ya
cigaba da cin abincin sa hankali kwance. "Sannu da zuwa yayana" na fada ina jin kunyar sa, yace "yauwa
jiddo, sai kuma ya mayar da hankalinsa kan Umar, na kalli Umar nace "ga yaya Tahir nan" sai ya ajiye
cokalin hannunsa ya mike tsaye ya mika wa Tahir hannu "sannu da zuwa yayana" ya fada yana
kwaikwayon yadda nake magana ta.
Duk suka yi dariya sai kuma suka gaisa, abin mamaki yaya Tahir din da ba mai yawan magana ba sai gashi
har da zama suna hirar ball saboda shirt din jikin yaya Tahir akwai hoton dan ball a jiki, ni bam ma san ko
waye ba amma dai na fahimci hoton nasa ne ya kawo hirar, suna hirar har Umar ya cinye tuwon sa
sannan Tahir ya shiga gida, nayi masa tayin in kara masa sai yace dama rowa ce ta saka na zuba masa
guda daya kawai "duk girman nan nawa ace malmala daya kawai za'a bani?"
Naji kunya, "to ai bansan zaka ci ba. Yanzu na sani, in ka dawo guda uku zan saka maka" ya mike yana
cewa "to yaushe zan dawo?" Na daga kafada "ko yaushe ma, ni ina gida babu inda nake zuwa" yace
"okay gobe in na fita office zan karbo miki form din ki. In an samu goben to a goben zan kawo miki da
yamma saboda da daddare ina da wani aiki da zanyi asibiti, in kuma ba'a samu gobe ba sai jibi zan dawo"
na gyada kai amma ina jin kamar jibi tayi min nisa, dan a yanzu ma bana son tafiyar da zaiyi dan dai ba
zan iya ce masa ya zauna bane