Chapter 32 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   32 / 101

93K to 96K   out of 300.2K words

sai
yai sauri ya bude min kofa ya miko hannu zai dauki Yasmin na janye ta na matsa na fita daga kofar da ba
ita ya bude ba, ya rufe kofar sannan ya bude booth ya dauko mana jakar kayan mu sannan ya biyo
bayana bakin kofa inda nake ta kokarin nemo key a cikin jakar hannuna, ya ajiye jakar hannun sa yace
"kawo Yasmin din sai kiji dadin daukowa" nayi banza na bawa iska ajjiyar sa, ya sake miko min hannu sai
na matsa na cigaba da abinda nake yi, sai ya koma mota da sauri sai gashi dawani key din ya dawo ya
bude gidan sannan ya matsa yace min "bismillah" na ja dogon tsakin danasan da ace zare ne da sai ya kai
bakin gate sannan na shiga. Ya biyo bayana da kayan mu a hannun sa.



Falon kacha kacha kamar anyi yakin badar a ciki. Yace "am sorry for the mess, yanzu zan gyara miki gidan
gabakidaya, kamar sabo zan mayar miki dashi. Kin san dai ai na fiki iya gyaran gida ma ko? Yanzun
ma....." Banji karshen maganar ba na wuce shi na tafi dakina, ina shiga na rufe kofa na murda key sannan
na kwantar da yarinya ta nima na kwanta.



Hawayen ya tsaya yanzu a idona, amm zuciyata tankar garwashin wuta haka nake jin ta acikin kirjina.
Wato Umar ya dauki wuka ya daba min a cikin zuciyata ta hanyar cheating on me, sannan kuma hakan
bai ishe shi ba sai ya debi gishiri ya barbada a kan yankakkiyar zuciyar ta wa ta hanyar rufe laifinsa da
kuma yi min sharri a gurin iyaye na.



Daya abin kuma daya kara rura wutar zuciyata shine yadda Aunty da Daddy suka tabbatar cewa Umar ne
marar gaskiya amma suka kasa yi masa fada sai ni da suka san ni ce mai gaskiya ni kuma suka yi wa fada.
Ni akayi wa laifi, babban laifi, sannan akayi min sharri, sannan kuma akayi min fada kuma aka bashi ni
yadawo dani gidan sa.



Saboda me??????
Saboda shi namiji ne ni mace? Saboda an haife shi da jela a tsakanin kafafuwan sa ni kuma babu???
Wannan shine dalilin????



Kuma ma wai dan gidan Aunty nae ba gidan mu ba. Maybe da gidan mu naje da bayan fada Abba sai ya
hada da duka.



It was a bitter experience but I learnt something, something din kuma shine ba zan sake fita daga gidan
Umar da niyyar yaji ba, duk kuwa ranar da na fita to tabbas na gama aurensaa ranar ba zan sake dawowa
ba har abada. Duk kuwa da tsananin son da nake masa.



Tunowa da soyayyar Umar da take kwance a cikin zuciyata shi ya taso min da bakin cikin abinda yayi, ya
dawo min da hotunan pictures dinsa shi da zuwaira cikin zuciyata, hotunan da duk da ya goge su a waya
ta ba zasu taba goguwaba daga cikin kaina ba for as long as akwai ƙwaƙwalwa a skull dina.



Na dauki Yasmin da ta fara rigima nayi feeding dinta ina kallon fuskarta, shin anya kuwa nayi mata zabin
uba na gari? Anya kuwa?



Bayan ta gama na kwantar da ita sannan nima na kwanta na jawo pillow kirjina na rungume ina jika shi
da hawaye, ina hango rayuwar da take facing dina, ina hango challenges dina wadanda a lokacin ma ban
san dukkan su ba dan babu wanda yasan abinda gobe zata kawo sai Allah.



Daga dakin nake jiyo shi yana ta butuntu a falo da kitchen, har da su karar blender najiyo daga kitchen
din, zuwa jimawa kadan kuma naji kamshin turaren wuta. Ni dai ina nan a kwance ban tashi ba kuma
bani da niyyar tashi in dai har yana gidan. Ni da shi mu zuba mu gani, dan halak ka fasa.



A haka bacci mai nauyi ya dauke ni, exhausted from my cries. Cikin baccin naji ana kwankwasa kofa, na yi
mika tare da salati dan baccin mai nauyi ne nayi sannan na kalli agogo naga around 3pm. Nayi sauri na
kalli Yasmin naga har yanzu bacci take yi dan su jarirai basa gajiya da bacci.



Aka sake knocking. "Jidda, ki bude ga abinci ki ci" Na sake tsaki ma koma na kwanta ina rufe idona da
kunne na, hoping zan daina jin muryar sa. "Jidda" ya sake kirana. "Nasan kina jina. Please don't punish
yourself da yunwa, ni nayi laifi ni za'a yiwa dukkan hukunci ba ke ba. Ki fito ki ci abinci. Ni na dafa miki da
kaina"



Takaici ya kama ni na taso da sauri nazo bakin kofar na rike kugu "go away please. Ko ba zaka tafi bama
please ka daina magana kana ambatar sunana, muryar ka tana saka ni jin amai" ya danyi shiru sannan
yace "naji, zan tafi. Amma ina zanje?"



Nayi tsaki "oho maka. Go and hang your self or something I don't care" yace "okay. Naji, you don't care.
You are angry I know kuma you have absolute right to be angry. Ki ce min komai kiyi min komai but
Please ki bude kici abinci"



Ban ce komai ba na koma na kwanta ina jin haushin kaina dana kula shi ma. Zuwa anjima kadan sai naji
motsinsa ya same dawowa naji kamar ya ajiye wani abu a bakin kofa sannan yace "ga abinci, ki bude ki
dauka"



Nayi sauri na mike na sauka daga kan gadon sannan na bude kofar, yana tsaye bai bar gurin ba, a kasa ga
tray nan da flasks guda biyu babba da karami da robar lemo data ruwa.



Ya dan fara murmushi nervously yana jujjuya hannun sa "Jidda" na durkusa na bude abincin, taliya ce da
miya, daga ganin miyar kasan ko gama dahuwa kayan miyan basuyi ba ballantana su fara soyuwa. Har da
nama zuku zuku a ciki.



Na daga kwanon taliyar na watsar a corridor din sannan na bishi dana miyar, miyar ta bata har jikin
Umar da kuma jikin bango, sannan na bude lemon na daga shi na tuttular a kasa na kuma jefe shi da
robar a fuskar sa, naja kofa ta na rufe.



And I was so happy with myself duk da dai banga irin bacin ran da nake fatan gani a fuskar sa ba.



Naji ya fita sannan ya sake dawowa, daga alama gurin yake gyarawa. Na koma na kwanta, a lokacin ita
kuma Yasmin ta farka ta fara tsanyara min kuka kamar zata shide, na gwada feeding dinta amma babu
komai a nonon, na chanza mata diaper na sake mata kaya amma bata yi shiru ba. Time din lokacin
around 5pm



Ya same dawowa. "Dan girman Allah Jidda ki bude kofar nan" nayi kamar ban ji shi ba sai kuma yace
"Okay. Ba kya son ganina I get it, zan fita daga gidan in dai har zaki fito ki ci abinci. Kinji?" Nan ma shiru
sai Yasmin da take ta kukan ta.



Jima wa kadan naji fitar sa sannan naji ya tayar da mota duk da dai bana iya hango shi amma naji ya fita
daga gate. Na bude kofa na fito da Yasmin a hannuna, ya gyara corridor din, sai jikin bangon daya baci da
maiko, na fita falo na ganshi fes, har da jona incense burner ya saka turaren wuta a ciki kamar yadda ya
ga inayi.



Na wuce falon na shiga kitchen shima a gyare, sai tukwanen da aka jera su duk sun bushe da indomie
sun ki fita. Na harare su na dauko wankakkiya na dora na dafa ruwan zafi na hada tea na koma falo na
zauna na sha sannan na dan huta nayi feeding Yasmin sannan na goya ta na koma na dafa taliyana
jajjaga attaruhu da albasa nayi sauce na zuba na dawo falo na ci sannan na juye sauran a flask na kai
dakina, na dafa ruwan zafi shima na hada da kayan tea na kai dakina. Sannan na shiga na gyara dakin na
wanke toilet na kwantar da Yasmin na rufe mana kofa na shiga wanka.



Sai bayan magrib naji dawowarsa. Straight nan ya taho ya gama babatunsa a kofar daki ya hakura ya tafi.
Zuwa bayan ishai naga an kira ni da new number kuma jikina ya bani shine dan haka naki dauka. Ya
cigaba da kira sai na saka wayar a flight mode na cigaba da game din da nake yi.



Zuwa jimawa ya sake dawowa. "At least ki bani Yasmin in dauke ta, kin san dai nima yata ce ko? Kin san
inada hakki a kanta ko?" Na mike zaune.



"Ka tafi gurin Zuwaira ta haifa maka wata yar sai ka dauke ta. Ni tawa yar babu datti a jikinta, kuma zan
nesanta ta da daddaudan mutum irin ka"



Daga nan bai kara cewa komai ba kuma bai kara yi min magana ba har nayi bacci.
Da safe ya kara dawowa, ni kaina lokacin zaman dakin ya ishe ni ji nake kamar zanyi dan karamin hauka,
ga Yasmin ta ishe ni da kuma. Yayi knocking yace "Jiddo kun tashi? Me kike so kiyi breakfast dashi in soya
miki irish ko in hada miki sandwich. Na siyo bread din nan da kike so na Grand Square"



Na juya ido na. Wannan mutumin me ya mayar da nine? Bayan wawiya ya kuma mayar da ni
kwadayayyiya? Zuwa jimawa ya sake dawowa. "Zan fita to. Zan zauna a bakin gate ki fito ki ci abinci kiyi
kallo ki mike kafar ki dan gidan ki ne kinji?"



Na sake juya ido na, ni mamaki yake bani pretending as abinda yayi is a minor mistake wanda kawai
zamuyi kiss and make up mu manta dashi. Tabbas zai sha mamaki na, Jiddan daya sani a da ba ita bace
ba a yanzu, wannan ta waye, wannan ya wayarda ita.



Sai bayan ya fita sannan na fito. Na dauko rocker din Yasmin na saka ta akai na bar ya a palo na tafi
kitchen, akan dining table na ga an ajiye sandwich a ciki guda biyu a orange juice a gefe, a kasan plate
din kuma ga takarda



Baby Dove,



"Please ki ci wannan, For I made it with all my love"



Umarul Faruq



Bansan me yasa ba kawai sai naji hawaye, na dauki takardar na gutsitstsira ta na barbada akan sandwich
din sannan na juye lemon akai na barsu a bude, ma wuce kitchen na hada golden morn na dawo falo na
zauna ina sha a raina ina tambayar kaina me yasa nake ta buya a daki? Shine yayi abin kunya shi ya
kamata ya buya bani ba.



Kamata yayi in fito fili in facing dinsa in nuna masa it really is over between us, in Allah yasa ya gani ya
fahimta to in kuma bai fahimta ba sai in saka microphone in sake gaya masa.
Ina zaune sai gashi ya shigo, nayi masa kallo daya na dauke kaina. Ya chanza kayan jiya but still ynaa
looking rough, ya zagaya da sauri ya dauki Yasmin da take baccin ta ya daga ta sama sannan yayi planting
kisses all over her small face "God! I miss you so much my cutie pie"



Ta fara mutsumutsun zata yi kuka sai yayi sauri ya ajiye ta ya fara jijjiga ta, "sorry sweetheart. Daddy ya
tashe ki ko? I just wanted to kiss your little face that's all"



Sai ya dawo ya zauna a kujerar datake kusa da wadda nake zaune, idonsa a kasa yana kallon hannun sa
yace "naji dadi da kika fito kika zauna gar kika kunna kallo, ina fatan kuma anytime soon zaki yardamu
zauna muyi magana"



Na ja kafafuwana saman kujerar sannan nace "ubana ne ya sayi kujerun da kuma kayan kallon, da kudin
fansho. Ohh sorry ashe fa ka sani tunda har ka iya bawa karuwa labari"



Ya mike tsaye yana dafe kansa, fuskarsa tayi ja yace "wallahi wallahi ba gaya mata haka ba, you have no
idea yadda raina yake baci in kika fadi maganar nan bayan ni nasan ban fada ba" na mike zaune "ohh
really? Ashe da ciwo? Ashe sharri da ciwo? Add that to seeing me naked and lying on someone"



Ya taho taku biyu zuwa gaba na, for a second I thought dukana zaiyi sai kuma ya dunkule hannunsa ya
rintse idonsa sannan ya juya da sauri ya bar falon ya shiga dakinsa. Na ja dogon tsakin da na tabbatar ya
tarar da shi har dakin nasa sannan na koma na kwanta tare da karo volume din tvn da babana ya siya.



Sai dai maimakon maganar da na gaya masa ta sa raina yayi sanyi sai naji kamar zafi na kara wa zuciyata.



Ina nan kwance har around 12, shi kuma yana daki bai fito ba sai jin sallama nayi, Umma da Farhan. Na
tashi da sauri na tafi na rungume Umma ina jin kamar zanyi kuka amma na rike shi, Farhan ta tsaya daga
gefe tana kallona sannan tace "tashin hankali. Kinga yadda kika rame kuwa? Skeleton!"



Na shaga wuyana, realising wadansu manya manyan kasusuwa da suka yi min sarka. Umma ta zauna
akan kujera tana cewa "ko dai tsoron tsotso ne da ke Jidda?" Na zauna a hannun kujerar da take kai nace
"menene tsoron tsotso kuma?" Tace "wadansu in suka haihu sai suyi ta rama, shine hausawa suke cewa
tsoron tsotso" na daga hannu "ni bana jin wani tsoro Umma" tayi dariya "ai ba tsoron ake ji ba, kawai dai
hausar ce haka".



Farhan ta dauki Yasmin tana yi mata rawa "ka ga uwar ubanta, ƴar fara yar dan balarabe" Ummu ta
harareta "in kuma yana gidan kuma fa, ke surutu ne da ke"



Nayi murmushi kawai na gaishe da Umma, tace "yayan ki ne jiya ya zo ya saka ni a gaba wai sai nazo na
ganki, nace masa lafiya ya ce wai dai kawai inzo in ganki" na sunkuyar da kaina ina iyakacin kokari na
akan kar inyi kuka nace "Allah sarki yaya na, ya damu dani ne kawai, yaga na haihu kuma duk kun watse
kun barni ni kadai shine ya damu da ni"



Na fada ina kara jaddada wa kaina cewa gaya matan bashi da amfani tunda ba zata iya yi min maganin
komai ba, sai ma damuwa da zata shiga ita ma. Tayi shiru tana kallona, da alama bata yarda da ni ba sai
na kirkiri murmushi "ko kuma mafarki yayi kura ta cinye ni"



Farhan tayi dariya, nima nayi ina jin stress dina yana raguwa. A lokacin ne Umar ya bude kofa ya fito da
murmushi a fuskar sa amma kana gani kasan iyakacin fuskar ya tsaya. Ya kalle ni sannan ya kalli Umma,
da akwai alamun damuwa a ransa. Na dauke kaina na tashi na tafi dauko musu ruwa.



Ya durkusa a gaban Umma ya gaishe ta ta amsa masa da fara'ar ta,and I saw his face relaxed, suka dan
tsokani juna shida Farhan sai ya tafi hanyar bakin kofa sannan ya juyo yayi kirana "Jidda, zo mana" naji
wani takaici ya kama ni, ban amsa ba amma dole na ajiye ruwan hannu na na tafi.



Na tsaya hannuna rike da labule ina kallon sa kamar yadda shima yake kallona. Ya motsa bakinsa ya kai
sau uku amma ya magana. Nace "in koma ciki ne? Important mutane suna jirana" ya sake yin kokarin
magana "Jidda. Umma ta zo" sai ya kuma yin shiru tare da shafa fuskarsa.



Na bata rai "kana da abin cewa ne? Akwai maganar da zakuyi da umman ne?" Ya girgiza kai. Na daga
kafada "then Allah ya kiyaye hanya" sannan na saki labulen na rufe kofa na koma ciki.
Ga mamaki na bayan tafiyar sa sai naji zuciyata tayi min dadi, muna ta hirarrakin mu da Umma da
Farhan, daga baya ma muma shiga bedroom suna ta taya ni sorting kayan barkan dana tara ana ware
wadanda ba yanzu Yasmin zata yi amfani da su ba ana adanawa, sannan Umma tana ajiye min wadanda
nima zan ke yin barka da su in anyi haihuwa, sannan kuma ta ware wa Farhan, Amira da kuma Hajiya
atampopi masu kyau tace in basu, amma ita sai taki dauka tace bata so, ni kuma sai na dauki wasu nace
ta kaiwa Aunty da Aira.



Farhan ce ta shiga kitchen tayi mana girki, tazo tana tsokana ta wai in nuna mata food warmer din da
zata zubawa Umar abinci, kar ta zuba a wani abun da ba zai ci a ciki ba. Ban kula ta ba har ta gama ta
fita. Sai Umma ta tambayeni. "Lafiya dai ko?"



Na kalle ta ina kirkirar murmushi "Lfy lau Umma, kinga wani abu ne?" Tace "duk kin rame Hauwa'u,
annurin fuskar ki duk ya kau" na daga kafada "kawai stress ne Umma, ga rigimar Yasmin ga hidimar gida
ga karatu da zan koma next week" tace "to a samo miki mai aiki mana? Yar dattijuwa haka da zata ke
kula da gidan tana kuma taya ki rainon Yasmin"



Na girgiza kai, ni a raina sam bani da sha'awar yar aiki ko dan ina da muguwar tsafta ne? Gani nake yan
aiki zasu yi min kazanta a gida ne ko suyi min wani abun ba dai dai ba. Nace "babu komai umma, zan
saba in na kwana biyu, babu komai" tq cigaba da kallo na sai na tashi na shiga toilet duk da babu abinda
zanyi a ciki.



Sanda na fito bata nan, sai na fita falo na tarar da ita ta goya Yasmin suna maganada Farhan. Nima na
zauna muka cigaba da hirar. A lokacin ya shigo falon da sallama, da ledo ji a hannun sa yana rarraba ido a
tsakanin mu sannan ya sake gaishe da umma sai ya tafi kitchen da ledojin.



Banyi niyyar binsa ba na cigaba da zamana sai naji Umma tace "Jidda....." Kafin ta karasa yakira ni "Jidda"
na mike ba tare da nace komai ba sai Umma ta kama fada "shashancin banza kenan. Mijinki ya shigo
baki bishi kinji me yake bukata ba kuma yayi kiranki ba zaki amsa ba?" Kafin inyi magana ya sake kirana
"Jidda"



Na amsa "gani nan na taho fa" na shiga na same shi da ledojin a hannunsa sai ya miko min, ban karba ba
ya ajiye a kasa "uhmm, dama naga bamu da kaji a freezer ne, shine na siyo wa Umma gasassu, irin
wadanda nake siyo mana din nan masu laushi, na ga kina son su maybe zata so su itama"
Na bata rai "shikenan abinda ya saka kake rafka min kira?" Yayi shiru bai ce komai ba. Na ja karamin
tsakin da nasan Umma ba zata ji ba na koma falon. Bai jima ba shima ya fito, sai ya sake yiwa Umma
sallama sannan yace min "Jidda zan dan fita, idan su Umma zasu tafi sai ki kira ni inzo in kai su gida"



Yana sane, yasan cewa nayi blocking number dinsa, wato so yake yi in bude shi in kira shi. Umma tayi
saurin cewa "a'a doctor, ina za'a taso ka daga gurin aikin ka saboda kai mu gida? Mun gode amma kayi
zaman ka wallahi zamu tafi ma da kan mu, muna zuwa bakin layi zamu samu abin hawa"



Ya sake cewa "ai ba office zan koma ba, nan bakin layi zan je, tana kira na zan dawo, menene amfanin
mota ta in ban kai ki gida

32 / 101
Connection failed: SQLSTATE[HY000] [2002] Operation not permitted