Chapter 80 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   80 / 101

237K to 240K   out of 300.2K words

ina so ya fahimci cewa zan iya rayuwa babu shi, happily, ya
fahimci cewa zan iya rabuwa da shi. Ya fahimci cewa ina da gata na, iyayena da hukuma zasu tsaya min
su kwatar min yancina in har ya cigaba da abusing dina emotionally.



A haka na kwana hudu a gidan mu tun daga asabar har zuwa laraba, a ranar Alhamis din yaya Tahir ya
dawo shi kadai kamar yadda dama yace shi kadai zai dawo. Ban san wanne hali Umar yake ciki ba, naso
in je in duba Baba amma na kasa tambayar Abba shi kuma ya ki ce min komai, har yanzu yaki yi min
maganar komai. Suma kuma a bangaren su babu wanda yazo gidan mu, ban sani ba ko sun san na dawo
gida ko kuma basu sani ba Allah ne masani. A ranar Alhamis din ne Abba ya zo da yana tambayata "kina
da isassun kudi a hannun ki wadanda zasu kaiki inda mahaifiyarki take?" Nayi shiru ina lissafi sannan
nace "ba zasu ishe ni ni da yara ba" yace "ke kadai ai nace ba wai da yara ba. Yara ki hada musu kayansu
zan kira ubansu yazo ya dauke su, bana son yake samun uzurin yi min sintiri a gida, saboda ina da
yammata a cikin gidan nan" na sunkuyar da kaina ina fahimtar cewa Umar yana zuwa unguwar kenan
kuma lallai Abba yayi fushi sosai da Umar.



Amma kuma banason rabuwa da yayana, na sani a cikin zuciyata I will fight for my right to have their
custody amma sai komai ya lafa tukunna, kuma yanzu zuwa gidan nasu yai dai dai dan suma yaran suna
missing babansu kuma shima yana da right na ganin su da kuma zama da su. Kuma bani da matsala da
Mama dan na san tana son su, sosai, ba zata cutar da su ba, amma hakan ba yana nufin zan bar mata su
ba.



Sannan naji dadin shawarar Abba na tura ni Ethiopia, at least zan samu in huta sosai away from all these.
Kuma zan ga Umma.
Sai ya cigaba da magana "na nemi takardar ki a hannun sa har yanzu yayi shiru, ina ganin mutuncin
mahaifin sa shi yasa nayi shiru nima, amma zam ga iya kacin gudun ruwa sa" ya juya ya hau sama yana
sake maimaita min maganar hada kayan yara.



Sai naji ina mamakin yadda Abba ya sauko haka, wai har shine yau yake nemawa yarsa takarda a gurin
mijinta, amma kuma sai nayi tunanin maganar Mammy ce ta taba shi sosai, har yake gudun haduwar
Umar din da yammatan yayansa.



Na hada musu kayan nasu, suka saka ni a gaba da tambaya sai na gaya musu zasu je gidan Mama ne su
zauna acan tare da daddyn su. Nan da nan sai murna har suna rungume ni suna kissing dina, sai kuma
Yasmin ta fara tambayoyin nata "mommy ke kuma fa? Tare zamu tafi da ke?" Na jawo ta jikina ina shafa
kanta ina jin kamar zanyi kuka nace "a'a Yasmin, ba tare zamu je ba, ni zanyi tafiya ne shi yasa za'a kai ku
can din"



Tace "in kin dawo kuma fa? Zamu koma gidan mu tare da ke da Daddy?" Na sunkuyar da kaina kasa,
"ban sani ba Yasmin, ban sani ba, Allah ne kadai ya sani"



Har dare ba'a zo an dauke su ba. Na dauka Umar zai zo ya dauke su da gaggawa tunda na tabbatar ya
matsu da son ganin su. Da safe ranar Alhamis Abba ya sauko ya fita waje sai gashi ya dawo yana fadan
har yanzu Umar bai zo ya dauki yayansa ba, ya kira Farhan "ku dauki yaran nan ke da Amira ku je ku kai
su gidan kakan su"



A haka na rabu da yayana, su Farhan suka tafi dasu, basu dade sosai ba sai gasu sun dawo har sun kai su.
Na tambayesu ko sun ga Baba suka ce Aunty ta kaisu har dakin sa sun gaishe shi kuma sun duba shi. Sun
gaya min cewa jikinsa da sauki amma har yanzu ba shi da lafiya.



Sai kuma suka bani labarin Mama "ko tambayar inda kike ma bata yi ba, kawai ta karbi jikokin ta har da
cewa wai za'a duba musu school mai kyau, auntyn ce kawai ta tambaye mu ke tace kuma tana gaishe ki".
Farhan ta matso kusa dani tace "ashe gobe za'a daura wa Umar aure? Auntyn ce take gaya mana amma
kamar mamar ba ta so a gaya mana ba"



Sai kuma Amira tace "Yaya, ni dai ban san me ya hada ki da yaya Doctor ba amma ina tausayin sa Allah.
Kin san kullum sai na ganshi a layin nan? Yanzu ma fa yana bakin layi a cikin mota a zaune, jiya ma na
ganshi a gurin. Baki ga yadda ya zama ba. Kasumbar da ya tara ko? kamar za'a bashi loudspeaker ya fara
wa'azi"



Farhan ta kwashe da dariya. Ni kuma naji babu dadi har cikin raina. Wato zama yake yi bakin layi with
hope cewa zan dauki wayarsa in fita gurinsa.



Sai nayi deciding cewa gobe juma'a zan ganshi, zan ganshi one last time kafin in bar kasar. Sai dai daga ni
har shi a lokacin bamu san abinda juma'ar zata zo mana dashi ba.



Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din



0779484494

Nafisa Tafida Usman

Access Bank



Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp

08067081020



Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020



Please banda kira, WhatsApp only




*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi
sharing, in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*
*Black Friday 1*




Ranar juma'a na tashi raina babu dadi, sai na saka hakan a matsayin rashin yayana a kusa dani dan na
jima ban kwana na tashi babu su ba. Bayan na gama adduoi na sai kuma na dauka waya ta na nemo
number din Umar na tura masa sako



"Ina son ganin anjima da karfe goma please, akwai maganar da nake so muyi"



Na tura masa. Mintuna kadan kira ya shigo waya ta daga gare shi. Na tsaya ina jujjuya wayar a hannuna
sannan na dauka na kai kunne na.



"Hello?"



Sai da ya danyi shiru sannan yace "Jidda" na amsa "na'am. Barka da assuba" yayi shiru bai amsa ba nace
"ya kwanan yara?" Sai yayi ajjiyar zuciya "dan yaran ki kika dauki kira na ko?" Na girgiza kai kamar yana
kallo na sannan nace "ba dan su bane ba. Ai nasan ba lallai ne suna tare da kai ba. Ina so ne muyi
magana in an jima" yace "a ina zamu hadu? Ki zo gidan ki zan je can nima" na sake girgiza kai na "ka zo
nan gidan" yace "Abba ba zai barni in shigo ba. Ki ce masa zaki je gidan Aunty Afia sai muyi waya in
dauke ki a hanya" na danyi guntun murmushi, Umar will never change, wato nima irin na yammatan
zaiyi min kenan.



Nace "Abba zai fita anjima, duk Friday yana zuwa wayon ziyarar yanuwa da abokai. Around 10 yake fita,
you come after 10. Akwai maganar da nake so muyi ne kuma bana so muyi a waya.

Zaka zo? Yace "okay zan zo. Amma please....." Nace "okay sai kazo" sannan na zare wayar daga kunnena
na kashe ta.



Bacci na koma na cigaba da yin abina tunda bani da wani nauyi, sai after nine na tashi na tarar Amira har
ta gama hada mana breakfast ta kuma gyara dakin Umma, ta tashi naci abinci na na shiga nayi wanka ina
shiryawa naji fitowar Abba, ya leko falon Umma yana magana ba tare da ya amsa mana gaisuwar da
muke mika masa ba "Tahir zai shigo an jima, sai kuyi maganar tafiyar ki da shi, shi yayi musu shirin tafiyar
sanda zasuyi da Aysha" nace "to Abba" sai ya fita yana cewa da Hajiya da take tsakar gida "yau ba zan
dawo da wuri ba, ina jin sao magrib, da akwai inda zamu je da Alhaji Aminu" yana fita na sauke ajjiyar
zuciya tare da bawa Amira umarnin ta gyara min sitting room.



Tana cikin gyaran wayata tayi kara, na daga naga sunan Umar sai na zauna ina embracing kaina, do I
have to really see him? Abinda zan gaya masan is it really worth risking Abba yazo ya tarar da mu tare?
But na riga na kira wo shi, wata zuciyar ta gaya min in kira shi ince na fasa fitowa amma dai sai na mike
bayan doguwar addu'a na saka hijab dina na fita.



Suna zaune a sitting room din shi da Amira, ban san maganar da suke yi ba. Sai na lissafa a raina idan
Abba ya shigo ya gansu a haka, shi da yace baya son Umar a kofar gidan sa saboda yana da yammata to
me zai faru idan ya ga Umar din a zaune tare da daya daga cikin yammatan nasa?



Abu na farko da na fara lura dashi a jikin Umar shine ramar da yayi, dan ma shi mutum ne mai fadin
kashi dan haka jikinsa bai nuna ramar sosai ba sai fuskarsa ce ta nuna, idonsa ne ya nuna, ban sani ba
kuma ko ramar ce ko kuma gashin daya tara a fuskar ne ya saka fuskar ta chanja idon ya fada ciki? Ya
mike tsaye yana kallona, and I realized tunda muka yi aure this is the longest da muka yi ba mu ga juna
ba. Amira ta mike ta dauki tsintsiyar da taje yin shara da ita sannan tayi mana sallama, babu wanda ya
amsa mata a tsakanin mu.



Sai da ta fita sannan ya taho da sauri zuwa inda nake da niyyar rungume ni, amma sai ya rike hannun
nawa ya juyasu bayana sannan ya jani zuwa kirjin ya rungume tare da sauke ajjiyar zuciya. Tsoro ya
kamani, idan Baba ko wani a brothers dina ya shigo na kade har ganye na, sai na tura shi baya cikin tsoro
nace "Umar menene haka kake yi wai? I didn't call you for hugs I called you for talks, idan kuma ka sake
kokarin runguma ta Allah zan shiga gida kuma ba zamuyi maganar ba" sai ya daga hannu sama,
"shikenan, no hugs, I get it" sannan na nuna masa kujera "ka zauna dan Allah. Magana zamuyi dan Allah"
amma still bai ji magiya ta ba sai ya rike hannuna sannan ya dora hannun nawa a fuskarsa tare da sauke
ajjiyar zuciya.



Sannan ya ja hannun nawa daga fuskar sa zuwa kirjin sa ya dora akan saitin zuciyarsa ya lumshe ido
sannan yace



"what have you done to us?"
Na karbe hannuna tare da goge shi a jikin rigata ina jin haushin maganar sa tare da nadamar kiransa ma
da nayi sannan nace



"still the same Umar dana sani. Blaming anyone but himself. Ni kake blaming kenan? I guess ni ce nake
bin maza ciki har Bashir abokin ka da ma'aruf din yaya Mubaraka nephew dinka, a karshe kuma naje
dakin mai gadi na danne shi sanda baka nan"



Yayi taku biyu baya sannan ya dafe kansa, "God of mercy. Jidda wai me kike so inyi ne? Me kike so in ce
miki ne? Have you being reading your messages ma kuwa? Sau nawa zan ce miki na daina ne wai, sau
nawa zan rantse miki ban taba yarinyar can ba? Do you have any idea what I have been through? What I
am going through right now? Kina tunanin after all that has happened zan sake wani abin kuma? Me
kike so inyi ne wai? In durkusa kasa in baki hakuri ince na daina?"



Sai kawai naji hawaye sun taru a idona, I thought abubuwan da suka faru din sun chanja shi amma ashe
dai shi din ne dai har yanzu.



Sai na ja jikina daga kusa dashi na zauna akan kujera sannan nace "abinda nake so Umar doesn't matter,
abinda nake so kayi doesn't matter, what matters is abinda Allah yake so kuma abinda Allah yake so kayi.
Wannan shine kuskuren ka wannan shine dalilin da yasa har yanzu ka kasa dainawa duk da cewa kana
kokarin ganin ka daina din. Saboda kana kokarin dainawa ne saboda ni, ba wai dan saboda Allah ba.
Kana kokarin ka farantamin ne ba wai dan ka farantawa Allah ba. A duk lokacin da mukayi rigima kana
yin nadama ka shiga damuwa, amma ba wai nadamar aikata sabo kake yi ba kana yin nadamar na kama
ka ka aikata sabo. Tabbas Umar kana yi min laifi, laifin cin amana, karya, yaudara, da kuma zubar min da
mutunci na da kake yi, amma babban wanda kake yi wa laifi shi ne Allah. Dokokin sa kake karyawa,
iyakokin sa kake ketare wa. Maganganun sa kake takewa. Shi yace kar a kusanci zina amma kai kuma
rungumar ta kake yi duk inda ka ganta"



Ya juyo da sauri zuwa gaba naya durkusa a kasa ya rike hannuna, nima sai na sauko daga kan kujerar
muka durkusa tare "Jidda. Ba haka bane ba. You know me. Na gaya miki it was an addition, jarabawa ta
ce, kuma yanzu na gama cin ta, na gama Jidda, me yasa ba zaki fahimta ba wai? Babu bawan da Allah
baya jarabtar sa komai karfin imaninsa ko rashin imanin sa, ni tawa haka ce, kuma ina fighting inga na ci
ta and we can do it together idan muna tare. In kika barni....."
Na dakatar da shi da cewa "na yarda jarabawa ce, na yarda ranar farko daka fara yi jarabawa ce, Allah ya
dandana maka zakin ta dan yaga yadda zaka yi da ita ya gani ko imaninka ya kai zaka iya over coming
abin ko kuma a'a, it was an exam and you failed woefully. And you continue to fail tunda har kake jingina
shiriyar ka da ni. Umar *only God can change you* ni ba zan iya chanja ka ba, zamana da kai ba zai
chanja kaba, rabuwa ta da kai ma ba zata chanja ka ba, kai ne zakayi deciding cewa zaka daina and set
your mind to it ka kalli gabas ka gaya wa Allah cewa ka tuba kuma kana so ka daina and mean it har cikin
zuciyarka dan zuciya ubangiji yake kalla ba wai furucin baki ba. If you do that then sauran kuma tsakanin
ka da shi ne, shi algafur ne kuma alrahim, idan kayu taubatun nasuha zai yafe maka kuma ya dora ka
akan tafarkin tsira. But without that, no matter how much you tell your self or me or Mama cewa ka
daina ba zaka sake ba you won't. Saboda ba daga zuciyarka kake fadar abin ba saboda a zuciyarka ka riga
ka saka cewa you are addicted to it, shedan yana cigaba da gaya maka you can't resist the urge,
zuciyarka tana gaya maka wannan ne na karshe daga wannan shikenan. And then it goes on kowanne
kana ganin cewa shine na ƙarshe amma wanne ne zai zama na karshen? A kowanne second ubangiji
yana iya daukan ranka shin ka taba tunanin abinda zaka tarar acan? Ba abu mai kyau bane ba Umar, ni
da kai mun sani. You are a good man I know, a good husband and a good father but you are not a good
muslim. Which is abinda ya kamata ya fara zuwa a farko kafin sauran characteristics su biyo baya. Ko
nayi maka maganar addini you will pretend to me cewa ka gyara bayan in reality ba ka gyara din ba,
bayan ni da kai munsan cewa ba ni zaka gyarawa ba kan ka zaga gyarawa saboda kabarin ka daban nawa
daban, littafin ka daban nawa badan. Ni yanzu nawa littafin nake kokarin gyarawa shi yasa na bar gidan
ka, saboda zama a gidan ka zai gurbata min dan abinda nake tanadar wa kaina saboda ranar gobe
kiyama"



Yace "duk naji kuma duk na yarda da dukkan maganganun da kika fada, kuma dan dai ba zaki yarda
bane ba amma ina tabbatar miki da cewa kusan duk abinda kika fada abinda nake kokarin yi kenan a
yanzu. Abinda kawai ban fahimta da maganar ki ba itace da kika ce wai cigaba da zama da ni zai bata
miki ibadun ki. How? Jidda shi auren nan fa gabaki dayan sa ibada ne, ibada nake yi ibada kike yi kema.
Me yasa ba zaki zo mu nemi aljannar mu tare ba?"



Nace "yes, aure ibada ne, shi yasa in akayi dai dai sai a samu lada in kuma akayi akasin haka sai a samu
alhaki. Ni turbar da na ke bi a zamana da kai ba ta samun lada bace ba ta samun alhaki ce Umar" yace
"ta yaya?" You have being nothing but good to me. In ma akwai wani abu da kika yi ni na yafe miki
Jidda, sai menene kuma? Shin ba kya ganin cewa kema taki jarabawar kenan? Kema aure na shine naki
jarabawar?" Ya sunkuyar da kaina ina wasa da yatsun hannuna nace "haka ne, tabbas auren ka shine
jarabawa ta Umar" sai ya saka hannunsa biyu ya rike fuskata "then come back to me. Ki dawo mu hadu
muci jarabawowin mu tare"



Sai na dora hannayena akan nasa da suke rike da fuska ta ina jin yadda yatsunsa suka sirance fiye da
yadda na san su. Idona cikin nasa, a hankali Nace
*"You don't get it, do you? Ba wai zama da kai shine cin jarabawa ta ba rabuwa da kai ne"*



Nan take yanayin fuskarsa ya chanja, kamar wanda aka kwadawa mari, na cigaba da cewa "Allah yasan
yadda nake son ka Umarul Faruq, shi yasa ya bani kai a matsayin miji kuma ya sa ka kasance da halin ka.
Dan ya gani ko zan bi hanyar dai dai in rabu da kai ko kuma zan bi son zuciyata in cigaba da zama da kai"



Sai ya karbe hannun sa daga cikin nawa sannan ya mike kamar wanda aka yi wa allura yace "nooo. You
are messing up the whole thing. In aka jarabci mutum hakuri yake yi akan jarabawar sa har a karshe ya
samu abinda yake bukata. Wannan shine cikakken imani"



Na mike tsayen nima sannan nace "ni a fahimta ta, ita jarabawa tana iya zuwarwa mutum ta kowacce
siga, zata iya zuwa a sigar abu mai kyau ko akasin haka. Misali. Za'a iya jarabtar mutum da kyau ko da
dukiya ko da mulki, ko da fame, ko da ilimi, ko da wata baiwa ta musamman dan aga ya zaiyi da ita. Ko
kuma a jarabce shi da muni, ko da talauci ko da kaskanci, ko da cuta, ko da wata musiba dan aga yadda
zaiyi shima. Yadda ake cin jarabawa kuma shine sai mutum yayi kokarin bin hanyar Allah da Manzonsa a
cikin jarabawarsa. Idan talauci ne sai mutum ya guji sata ko wani abu da zai kawo masa haram duk kuwa
da halin talaucin da yake ciki, idan arziki ne sai mutum ya fitar da zakka, yake sadaka yana taimakawa
addini da dukiyar, haka dai. Ba wai yayi hakuri da halin da

80 / 101
Connection failed: SQLSTATE[HY000] [2002] Operation not permitted