Chapter 49 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   49 / 101

144K to 147K   out of 300.2K words

kina cikin damuwa ki gaya min menene yake damunki?
Wani abu ne ya faru ko yake faruwa?"



Tun kafin in amsa mata sai naji hawaye ya fara taho min, it felt so good a tambaye ka abinda yake
damun ka ba wai a kawai a kalleka ayi assuming you are okay ba. Ta bude ido "innalillahi, Jidda kuka kike
yi ai, abin har yayi girma haka? Dan Allah ki gaya min menene ya faru? Faruq ne yayi miki wani abu?" Na
dago kai ina kallon ta, ina jin nauyin abinda zan gaya mata, sai kuma na tuna tsakanin su da Umar tabbas
ba zata tona asirin sa ba.



"Yaya... Faruq....... Umar neman mata yake yi"



Na saki hannu na sannan ta rufe bakinta tana matsawa daga kusa dani "innalillahi wa inna ilaihir rajiun.
Jidda? Kin tabbatar? Ya akayi kika sani? Wani ne ya gaya miki? Kama shi kika yi?"
Ta jero min tambayoyin. Farko sai na rikice na rasa amsar da zan bata. Sai kuma na tattaro nutsuwa ta na
fara bata labari "tun farkon auren mu na sani. Tun da cikin Yasmin"



Sai na bata labarin zuwan Zuwaira gidan da duk abinda ya wakana har zuwa munanan hotunan su da
zuwairan ta turo min waɗanda har yau basu bar cikin kai na ba. Sai kuma na cigaba da bayani "tun a
lokacin ya yarda, har ma ya tabbatar min da cewa sun dade tare, har ma a gidan nan ya taba ajiye ta na
tsahon lokaci sanda yana karatu a buk, amma kuma sai yayi min alkawarin ya daina tunda ya aure ni ya
daina wannan karon ma tsautsayi ne da sharrin shaidan"



Sai na cigaba da bata labarin abubuwan da suka cigaba da faruwa, bayan nan, yadda ya ringa yi min
karya, yadda ya dinga yi min alkawarin ya daina kuma yazo ya karya da kansa, irin munanan hirarrakin su
shida Bashir dana ringa gani har zuwa case din Maryam.



"Shi yasa na yanke shawarar in gaya miki ke kuma ki gaya wa su Mama dan su san halin da yake ciki suyi
masa fada da nasiha sannan kuma suke saka shi a cikin adduoin su dan na fahimci ni kadai ba zan iya ba,
ina bukatar taimako, ina bukatar taimakon ku Yaya Mubaraka tun kafin ya zama too late. Lamarin Umar
gaba yake yi yaya Mubaraka tunda har zai iya neman kawata nan gaba ban san wadda zai sake nema ba
kuma. Na gaji, zuciyata ta gaji, ki taimaka min dan Allah..........."



Kuka nake yi sosai, itama kukan take yi......"har akayi har abin nan yayi nisa bamu sani ba? Ni dai ban
taba sani ba Jidda ban taba ko tunanin jingina wannan mummunar halayyar akan Umar ba" na share
hawaye na "ya dade fa sosai, ya gaya min tun yana Lagos, tun yana secondary school"



Ta dafe kai "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Jidda shi ya gaya miki hakan da bakinsa? Da kansa ya amince
da laifukan sa kuma har ya iya furta miki da bakin sa?"



Na gyada kai "shi ya gaya min. Yace he is addicted to it. Amma sai yace yana iyakacin kokarin sa wajen
ganin ya daina, abinda yasa kullum nake ta lallashin zuciyata nake kuma gaya wa kaina cewa zai daina
din tun da yana iyakacin kokarin sa, kinga na hana shi social media kuma ya daina, na ce ya rabu da
Bashir kuma ya rabu dashi, then I have no reason to think cewa bashi da niyyar dainawar, amma sai ya
saka min da neman kawata. Bayan kuma ta tona musu asiri a giri na shine ya kala mata sharrin sata ya
saka aka kamata, duk da laifinta ne amma hakan ai ba dai dai bane ba kuma yana da alhakin ta"
Yaya Mubaraka ta gyada kai "tabbas naji maganar a gida, mamanta ta je gurin Mama jiya ni kuma na
shiga gidan sai naji suna zancen da Mufida bayan uwar yarinyar ta fita cewa kawarku ce taje office dinsa
tayi masa sata, har muke zancen abin kunya ki je office din mijin kawarki kiyi sata"



Na girgiza kaina nace "ba sata tayi masa ba" na sake yi mata bayanin abinda ya faru.



Yadda nayi tunanin hankalin yaya Mubaraka zai tashi sai naga yafi ma hakan tashi, tayi ta rantse min
akan cewa basu sani ba.



"Mu dai munsan shi da wayan yammata, tun farkon shigarsa jami'a yake da yammata wasun su har gida
suke zuwa nemansa, dan tun ina gida nasan akwai wasu da Mama ta taba zagewa tas da ta gansu sunzo
gurinsa amma bamu taba tunanin abinda yake tsakanin su kenan ba. Gidan nan kuwa tunda aka siye shi
Baba yace ba zai zauna a ciki ba sai yayi aure,dan na tuna lokacin har sai da yayi ta nacin a barshi ya
dawo nan tunda yafi kusa da school amma Baba ya hana yace a gida zai cigaba da zama sai yayi aure
tukunna. Ashe shi akwai abinda yake yi a gidan"



"Abinda kawai zan iya ce miki na sani shine case din Ummi"



Na bude ido "Ummi. Me ya faru da Ummi kuma? Wani abu ya faru tsakanin Umar da Ummi? Na shiga
uku ni Hauwa'u"



Sai naga hankalin ta ya kara tashi "baki sani ba? Bai gaya miki ba? Ni na dauka kin sani da ba zanyi
mentioning ba"



Na sake rikicewa, kar dai Umar har lalacewar sa ta kai ya nemi Ummi, Ummin da yace min is like a sister
to him, in har ya nemi Ummi to tabbas babu wadda ba zai iya nema ba kenan "dan Allah ki gaya min
Yaya, tunda kin riga kinyi mentioning hankali na ba zai jwnta ba sai naji gaskiyar magana in ba haka ba
zanyi ta sake sake ne a raina"
Ta fara kokarin kwantar min da hankali "kinga, ba wani abu bane ba, ba abinda muke magana akan shi
bane ba. Amma kinsan Ummi bata gida yanzu ko? Kinsan ta koma gidan su ko?" Na gyada kai "sanda
mukaje Lagos Aunty tace mana ta mayar da ita gida"



"Ba Aunty ce ta mayar da ita ba, guduwa tayi da kanta" Na bude ido "me yasa ta gudu?"



Tace "tun farkon zuwan Ummi gidan mu suka saba da Umar yana kulata sosai kamar yadda yake kula su
Mufida, sai ta mayar dashi kamar abokin shawarar ta dan komai na Ummi in kana son ji to a gurin Umar
zaka ji shi. To wai ashe ta dade tana gaya masa zancen wai tana so ta shiga Hausa film, kuma wai tana ta
yi masa zancen wai Aunty tana takura mata tana cin zalin ta, ita ashe so ma tayi sanda kuka yi aure ya
mayar da ita gidan sa shi kuma wai sai yaga bakya so shine yaki yarda. To wai yanzu bayan ta gama
makaranta shine suka shirya zai saka ta a film din, wai akwai wani abokin sa daya san wani producer,
shine suka shirya plan ta ringa daukar kayanta a hankali tana bashi yana boye mata har ta gama diban
waɗanda zasu ishe ta kawai rana daya yazo gidan tace wai zata je gidan su friend dinta ashe zuwa tayi ta
shiga motarsa da yayi packing acan gefe, shima ya gama abinda yake yi ya bi bayan ta suka tafi"



"Shiru shiru Aunty taga bata dawo ba, har dare, sai ta kira maman yarinyar da tace zata je gidan su sai
aka ce ai bata je ba. In gaya miki tashin hankali, akayi ta kiran number din yarinyar nan wallahi taki dauka
daga baya ma sai ta kashe wayar. Nema nema nema, kwana da kwanaki babu Ummi babu labarin ta.
Baba yana Lagos lokacin dole ya biyo jirgi ya taho aka zo akayi ta nema. Kuma abin haushin har da Umar
a neman ta kusan shine ma kan gaba a neman ta ashe yasan inda take"



Nace "amma Yaya, duk wannan abin ace bani da labari?"



Tace "to ai duk mun dauka kin sani, tunda mijinki ne yake ta kokarin nema dan haka ya za'a yi muyi
tunanin bai gaya miki ba? Sai da aka kusan kwana goma sai kawai ga kira daga gidan su Aunty wai ga
Ummi can taje gida ita da wani film producer wai yazo neman iznin iyayen ta zai saka ta a film, dama wai
suna da ka'ida duk mace sai da saka hannun iyayenta"



"Suka sallami masu film din suka ce a'a su ba zasu saka yar su a film ba, sannan suka lakada mata shegen
duka, sai da taji kamar zasu kashe ta sannan ta fadi gaskiyar cewa da saka hannun Umar, shi ya hada ta
ma da yan film din a bisa alkawarin ba zata fadi shine ba"
"Haka baban Aunty yazo yayi wa Aunty tas, yace sakacin ta ne, amma da yake masu kawaici ne ko kallon
Umar ba suyi ba. Ita kuma Aunty tayi masa Allah ya isa tace babu ita babu shi kuma ba zata taba yafe
masa ba. Yarinyar nan Allah kadai yasan abinda ya faru da ita a cikin kwanakin da bata gida, sun ce ma
aure zasuyi mata"



Nayi shiru ina tunani, ina tunanin wanne irin cin amana ne wannan? Wanne irin mutum ne Umar?
Wanne irin mutum na aura? How Aunty must have felt!



Sai naji kuma ina jin tsoron Allah ya isan ta kar ta dawo ta shafe mu ni da yayana.



Yaya Mubaraka ta yi ta bani hakuri "tabbas nasan kinyi hakuri sosai da sosai Jidda, amma dole zan kara
baki wani hakurin, Allah ya kara miki hakuri shi kuma Allah ya shirya mana shi. Kuma gobe insha Allah
zan je gida in samu Mama, zan gaya mata komai kuma insha Allahu zata dauki mataki mai kyau, nima
kuma zan neme shi muyi magana. Sai ran sa ya baci wallahi. Stufid boy kawai"



Naji dadin yadda yaya Mubaraka ta karbi maganar, sai dai kuma maganar da muka yi da ita sai ta tayar
min da damuwa ta na wuni cikin kunci da bacin rai. Ga maganar Ummi da ta zo min a matsayin sabuwa
sai abin ya hadu ya saka min rashin lafiya, ciwon kai, daga baya kuma sai zazzabi mai zafi ya rufe ni.



Ina nan kwance a daki da yara suna ta hawa kaina suna wasan su sai gashi nan ya shigo. Ya tsaya yana
kallona "are you sick?" Ya fada muryar sa da damuwa, na gyada kai kawai, sai ya hawo gadon ya bude
bargon dana rufa da shi yana taba wuyana "subhanallah. Jiddah me yake yi miki ciwo?" "Kaina ne yake
ciwo, sai kuma zazzabi"



Ya sauka daga kan gadon yana cewa "kuma shine kika kwanta? Ba zaki kira ni ki gaya min ba? Da kuma
ban dawo da wuri ba fa?" Ya fita sai gashi da robar ruwa da magani, ya kamani ya tasar dani zaune
sannan ya bani magani "oya sha magani, in bai sauka ba kuma sai inyi miki allura" na karba nasha sannan
na koma na kwanta ya gyara min rufa ta sannan ya dauki Asad ya ja hannun Yasmin "ku taho mu bar
mommy ta huta"



Bayan sun fita bacci ya dauke ni, sanda na tashi sai na ganshi shi kadai a zaune a gaban gadon da wayata
a hannun sa yana daddanna wa, yana jin motsin na juyo yana kallona, fuskar sa da damuwa
"Sannu Baby, bara in samo miki wani abin ki ci" nace "ina su Yasmin?" Yace "nayi musu wanka na
kwantar da su a dakina dan kar su dame ki" na rufe ido na, anya kuwa akwai miji a wannan zamanin mai
kula da matarsa kamar yadda Umar yake kula dani? Anya kuwa akwai miji mai wulakanta matarsa kamar
yadda Umar yake wulakanta ni?



I find it hard to place him, a wanne matsayi yake? Miji na gari ko mugun miji?



Ya mike zai fita sai na rike hannunsa, ya juyo yana kallona sai nace "ka saka an saki Maryam?" Ya juyo
yana kallona "kin damu da ita?" Nace "na damu da kai" sai ya hawo kan gadon ya dora kansa akan
pillown da nake, fuskarsa kusa da tawa yace "me yasa zaki damu da kamatan da akayi?" Nace "saboda
bana so ka dauki alhakin ta, saboda kai mijina ne, duk hanyar da zaka bi zan so ace kyakykyawa ce, in
kuma kabi hanya marar kyau zan yi iyakacin kokari na in dawo da kai kan hanya mai kyau, duk abinda
nayi ko zanyi dan kai ne, dan nutsuwar ka ita ce tawa ni da yayan mu wadanda muke da su da wadanda
zamu haifa nan gaba"



Ya shafa fuskata yana murmushi "Nagode. Kuma an bada bail din ta tun jiya. Ina son kuma ki sani cewa
you are the best thing that happened to my life, and I love you too" na rufe idona ina jinjina kalmar love,
anya kuwa da akwai sauran ta a cikin zuciyata akan Umar, in ma da akwai bana jin ya kai 30% din yadda
yake da, sai dai kyautatawar sa, kulawar sa da nuna damuwar sa akaina su suke rike da wannan sauran
30 din.



Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din



0779484494

Nafisa Tafida Usman

Access Bank



Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp

08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020



Please banda kira, WhatsApp only




*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana ne idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi
sharing, idan kika yi kinci amana kuma ke da Allah*



*A lesson for all*



Kwana na biyu ina kwance ba lafiya, a karshe Umar bayan yayi min allurai sai ya tafi dani asibiti ya yi min
tests, har da cewa "Allah ya sa ciki ne" na kalle shi kawai ban ce komai ba sai yace "kar kiyi mamakin in
muka ga shine, kin san condom is not 100% reliable" a hankali nace "I am glad you know that" ya kalle ni
kawai sai yayi shiru.



A asibiti pregnancy test din da yayi min turned out negative, babu abinda ya gani sai high bp, tun daga
asibitin yake kumbura. "Ni ban san matsalar ki ba Jidda, gabakidaya kin chanja kullum cikin tunanin gashi
nan kina neman kiyi wa kanki illa, ni nafi so in kina da problem kiyi min magana, in nayi miki wani abu
kiyi min magana mu zauna mu tattauna, bana son wannan bacin ran da kike sakawa kanki akan abinda ni
bansan menene shi ba. Yanzu dole in dora ki akan magani"



Nayi shiru kawai ina jin sa, a raina nace pretender, ya kware gurin pretending everything is okay bayan ni
da shi munsan it is not. Bansan me ya shiga kansa ba sa da ya nemi Maryam, bansan wacce zuciyar ce ta
gaya masa cewa we will continue being okay bayan ya kwanta da kawata, ban san ta yaya yake tunanin
zan iya cigaba da enjoying kwanciya da shi ba. Ban san ta yaya yake tunanin zan cire memory din daga
zuciyata ba.



Ko da yake shi a ganinsa na yarda da maganar sa cewa Maryam office din sa ta shiga tayi masa
sata.............
Sai dai wannan ba shine abinda ya fi daga min hankali a yanzu ba, abinda yafi tashin hankali na shine
jiran tsammanin sakamakon aiken da nayi gurin Mama da Baba.



Kamar amsar magana ta naji ya dauki wayarsa "Hello Mama. Bama gida ma yanzu, na kai Jidda asibiti
muna hanyar komawa gida. Okay zamu shigo"



Naji zuciyata ta buga da karfi "na juya ina kallon sa naga shima ni yake kallo yace "Mama ce wai take
neman mu yanzu, she sounded upset, Allah yasa ba laifi muka yi ba" sai na juya ina kallon side dina,
nasan kiran na menene amma ban dauka zata kira mu ne tare ba, na dauka zata kira shine ta bincike shi
ko ta saka a bincike shi ko ta gaya wa baba shi ya bincike su tabbatar da gaskiyar ko rashin gaskiyar
maganata sannan sai su kira shi suji side dinsa su kuma yi masa fada tunda ni na riga na fadi nawa side
din.



Daga nan bamu je gida ba gidan su muka tafi, kowa cikin mu yayi shiru sai Yasmin da take ta surutun ta
mostly ita kadai.



Har muka je gidan yayi packing ya zagayo ya bude min ya kuma kama hannuna na fito ina dafe kaina da
yake yi min kamar zai tsage "sannu" yace "sannan yayi "da na sani ma gida na kaiki tunda dai na riga na
gaya mata ba kya jin dadi" na girgiza kaina "no, muje kawai tunda mun riga mun zo" ya dauko Asad ni
kuma na kama hannun Yasmin muka shiga.



Babu kowa a babban palon gidan, na samu guri na zauna shi kuma yashiga dakin Mama. Shiru shiru bai
fito ba, a lokacin da za'a sake auna bp na da nasan kadan ya rage ya kai ga ƙwaƙwalwa ta ta buga
gabakidaya. Ga dai TV nan a gaba na amma babu abinda nake fahimta a cikin abinda suke yi. Ina ta
kallon dakin Mufida wai ko zata fito maybe in tayi min magana zan dan dauke hankali na daga maganar
da Umar suke yi da Maman sa a cikin daki.



Kamar daga sama ya bude kofa ya fito, sai ya tsaya yana kallo na da handle din kofar a hannun sa, mun
jima muna kallon kallo sannan na sunkuyar da kaina kasa ina ambata "innalillahi wa inna ilaihir rajiun"



Maganar Mama naji tace "sannu Jidda" yadda ta fadi sannun da gatse ya saka nayi saurin dago kaina ina
kallon ta, ta wuce Umar tazo ta zauna akan kujera tana kallona da wani irin expression a fuskarta dana
kasa fassara wa. Na gaishe ta "barka da fitowa Mama"
Bata amsa ba tace "daga farko dai ina son inji bayan Mubaraka wa kika gaya wa maganar nan" na dago
kai na kalle ta na kuma sunkuyar da kaina, automatically hawaye yana tahowa ido na, "ban gaya wa
kowa ba Mama, dama so nayi ta gaya muku tukunna....." Ta katse ni "to alhamdulillah. Tambaya ta biyu
da zanyi miki ita ce, menene Umar ya rage ki dashi? Menene kike so wanda bai yi miki ba?" Na sake dago
kai tare da kokarin bude baki zanyi magana amma voice din sai yaki fitowa, ta daga murya "ki fada min
mana ina jin ki? Meye bai yi miki ba da zaki bishi da wannan sharrin?"



Na fara kuka sosai, Umar ya karaso da sauri ya durkusa a gaban Mama "Mama dan Allah ki bar maganar
nan, na gaya miki sabani ne muka samu kuma zamu daidaita, bata da lafiya kinga dan Allah kar kiyi mata
fada"



Ta kai hannu kamar zata doke shi, "matsa daga kusa dani tun kafin in targada ka, yanzu lalacewar taka
Umar har ta kai haka? Har ta kai yarinyar da ta dubi idona ta kala maka wannan sharrin ita kuma zaka zo
kana karewa a gaba na? Anya kuwa Umar ba sai na hada ka da addu'a ba? Anya kuwa wannan soyayyar
ta Allah da Annabi ce"



Ta juyo kaina ta nuna ni da dan yatsa "wallahi Jidda kiji tsoron Allah. Yaron nan babu

49 / 101
Connection failed: SQLSTATE[HY000] [2002] Operation not permitted