Chapter 58 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   58 / 101

171K to 174K   out of 300.2K words

kona masa gida sai yaji haushi ya sake ni, wata kuma zuciyar ta ce in jira shi
ya dawo in ambato sunan Baba da Mama, da duk wanda nasan yana holding dear to his heart in zaga, in
yaji haushi ya sake ni.



Babu abinda ban lissafa ba, wasu abubuwan ma ba zan iya fadar su ba saboda munin su, duk a matsayin
hanyar da zan raba kaina da auren Umar.



Ina nan kwance har ya na jiyo shigowar su shi da Yasmin, sai bayan sun shigo sannan na fahimci har da
Asad. Yaran suka taho gurina da gudu suka fada jikina kowa yana kokarin bani labarin abubuwan da suka
faru a yan awannin da bama tare, sai kuma suka fara fada a tsakanin su akan wanda zan fara saurara a
tsakanin su, na kirkiri murmushi nayi musu sannan na sa suka yi taking turn one by one kowa ya bani
labarin da yake so a bani, na kuma basu amsar da zan iya basu sannan muka fito na fara nema musu
abinda zan basu su ci.



Suna cikin ci ya shigo, daga alama daga masallaci yake sai ya zauna yana kallona, na juyo nima ina kallon
sa nace "ka rubuta?" Yayi sauri ya kalli yara sannan ya juyo yana kallona, na sake cewa "in ka rubuta ka
bani in kuma baka rubuta ba inje in dauko maka takarda da biro yanzu ka rubuta min"



Ya girgiza kai yana kallon yaran da suka juyo suna kallon mu yace "Jidda please not now" nace "saboda
me not now? Saboda kar yara suji? Matsalar ka kenan kar yaranka su ji? Kar su fahimci cewa they are
living in a broken home? Ni kuma dan su nakeso in karasa tarwatsa perfectly painted home din naka dan
shine mafi alkhairi a gare su akan su tashi tare da uba irin ka. Gwara su san halin da suke ciki tun yanzu
yadda duk ranar da suka bude daki suka ganka akan mace zuciyar su ba zata buga ba tunda sun san halin
ka already. Sun san....."



Ya mike da sauri sannan ya kama hannuna ya fara jana ciki, na fara tirjewa ina dukan hannun nasa "ka
cika ninka barni in gaya musu, ka barni in gaya musu cew kayi lalata da cousin din su"



Muna shiga corridor ya tura kofa "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Jidda menene ya same ki ne?" Nace
"menene ya same ni? Menene ya same ni fa kace? Hauka nake yi, ciwon hauka ne ya same ni dan Allah
ka sake ni tunda ba zaka iya zama da mahaukaciya ba. Kuma yaran ka sai na gaya musu, sai na gaya
musu dan su fara takatsantsan da kai kar wata rana mu wayi gari ka danne Yasmin....."
Ya toshe bakina da hannunsa tare da daka min tsawa "Jidda!" Na bude ido tare da ture hannun nasa
"what? Kana tunanin zanyi mamaki ne in na ganka akan Yasmin? Ko kadan ba zanyi mamaki ba saboda
nasan ka wuce haka, zaka iya aikata abinda yafi haka, tunda har ka iya hawa kan Mammy, yarinyar da
take a matsayin ƴa a gare ni dan haka a matsayin ƴa a gare ka, kuma ka iya yin sanadiyyar lalacewar
Ummi, yarinyar da take a matsayin kanwa a gare ka, bana jin kuma duk wata mace da take da rami a
tsakanin kafafuwanta is safe around you, dan haka gwara in dauke ya ta tun kafin ka lalata ta itama"



Fuskarsa tayi jajawur, I was sure babu abinda yake so a lokacin irin ya dake ni amma sai ya sake ni ya
shige dakin sa, na bishi a baya da sauri na shiga tun kafin ya rufe kofa. "What? Ba zaka yi magana ba, ba
zaka dake ni ba? So nake ka dake ni dan Allah, so nake ka bani hujjar da zanyi amfani da ita gurin rabuwa
da kai, dan bani da wani sauran dalilin cigaba da zama da kai, babu abinda nake so irin rabuwa da
kai......"



Ya juyo da sauri sai kuma na fara ja da baya har na hadu da bango sai ya tsaya a kusa dani. "In zaki rabu
dani, ba yanzu ne lokacin da ya kamata ki dage sai kin rabu dani ba, ba akan wannan case din ya kamata
ki rabu dani ba. In zaki rabu dani, kamata yayi ki rabu dani akan laifin da na san na aikata, akan laifin da
nayi intentionally ba wanda ni kaina mai laifin van tabbatar da cewa nayi ba, dan ban san sanda nayi ba,
ba kuma zan iya tuna lokacin da nayi ba, just a bunch of messages ba zasu tabbatar min da cewa nayi
ba....."



Nace "nina tabbatar. Na kai yarinyar asibiti an duba min ita kuma an tabbatar min an shige ta" naga
yanayin sa ya chanja completely dan calmness din da yake keeping ya tarwatse da karfi yace "kuma sai
aka tabbatar miki da cewa ni ne?" Nace "sai na tambayi yarinyar ita kuma ta tabbatar min da cewa
kaine" ya fara ja da baya, sannan ya dora hannunsa daya aka ya juya ya kifa fuskarsa a jikin bangon
dakin, na matsa kusa da shi a hankali nace "ka bani takarda ta kawai shine solution, ni ba zan iya cigaba
da zama da kai ba Allah ma ya gani. Ma sauwake min sai ka auri wata, ko Mammy din ce ko Maryam ko
kuma yaya Jamila tunda tana nan har yau dattin abinda kuka yi yana bin ta ta kasa samun miji, ka sake ni
ka samu dai dai da kai nima in je in samu dai dai dani"



Ya juyo yana kallona da idanuwan sa da suka kada suka yi jawur yace "I can't, and I will never" sai kuma
ya kama hannu na yace "ba zan iya sakin matata da nake so ba bayan baya yi min komai ba, bazan iya
sakin ki ba akan laifin da bansan ma sanda na aikata shi ba" ya saki hannun ya rike fuskata, idonsa taf da
hawaye "Jidda ina son ki, fiye da yadda nake son kaina. Wallahi ba zan taba iya hurting dinki intentionally
ba, ke ma kanki kinsan ba zan iya ba, wannan kadai ya kamata ya tabbatar miki da cewa ba'a cikin
hayyacina na aikata abin nan ba, in ma na aikata kenan. Dan Allah Jidda kiyi hakuri, in kika ce zaki barni
rayuwata zata karasa tarwatse wa, ki taimaka min ki kara min wata damar albarkacin dan guntun so na
da yake zuciyarki a yanzu. Albarkacin yayan da Allah ya bayar a tsakanin mu. Albarkacin matsananciyar
soyayyar da nake miki"



Ban san kuka nake yi ba sai da naga hawayena suna zuba a hannunsa, sai ya saka fuskar sa a wuyana
sannan ya zagaye ni da hannayensa. Na fara kokawar kwacewa amma yaki cika ni har sai da karfi na ya
kare na hakura, sai da shima da kansa ya gaji ya hakura sannan ya sake ni ya koma ya zauna a bakin gado
tare da dafe kansa da hannunsa, na karasa gaban sa na tsaya, har lokacin kukan nake sannan nace
"soyayya, in dai irin wadda kake yi min ne Allah ya tsine mata albarka"



Sai kuma na juya na fita na shiga dakina na rufe kofa. Naji bana son ganin kowa bana son jin maganar
kowa, na kwanta kawai na lulluba da bargo duk da cewa ba sanyi nake ji ba amma naji bargon zai
ƙaramin security ne kawai. Har dare ina haka, sallah kawai na tashi nayi na koma na kwanta, Umar yayi
ta shigowa dakin, ina jin sa har gadon ya hau ya taba jikina sannan ya fita, daga baya yara suka shigo sai
ya dawo yazo ya janye su yace kar su dame ni, daga baya naji sun fita a mota sai kuma suka dawo. Sai
gashi ya kawo min abinci wai in tashi in ci, sai dana yi threatening dinsa nace in bai fita ya bani guri ba
zan juye masa abincin a jiki sannan ya fita.



A lokacin kawai shawara nake nema. So nake in samu wanda zai ce min ga abinda ya kamata kiyi,
someone da zai dora ni akan hanyar da zata bulle. And I decided to do something that I shouldn't have
done, something that thought me a great lesson in life kuma nake fatan yan bayana ma zasu dauki
darasi daga gare ni.



I went to one of the famous blogs a social media, inda naga mutane masu problems suna zuwa su fada a
sirrance ba tare da ansan su waye ba sai kuma a basu shawarar yadda zasu warware matsalolin su, I
thought nima bara in gwada ko Allah zai sa in samu wadda ta taba shiga irin matsala ta kuma ta samu
hanyar warwarewa nima ta gaya min yadda zanyi.



Na shiga inbox din admin din na rubuta mata labari na in brief, matsalar Umar, yadda yanayin iyaye na
suke da kuma yadda muka yi da nasa iyayen, Sai kuma na basu labarin abubuwan da suka yi ta faruwa
tun auren mu har zuwa case din Mammy na yanzu. Ma tura tare da rokon tayi hiding sunana kamar
yadda naga anayi.



Sai da safe bayan na sallami Yasmin sannan na koma daki na na dauki waya ta ina dubawa hoping ko
anyi posting sakona, and I saw it posted, da kuma tarin comments under it. Na shiga na karanta
comments din duk da suna da dumbin yawa amma sai da na karanta su tun daga farko har karshe. And
about 80% na comments din zagi ne da cin mutumci gare ni da iyayena, da Umar da iyayensa. Wata ma
direct ta kira ni da "jaka" wata tace min kwakwalwar kifi ce dani, wadansu sunce kwadayin kudin Umar
ne ya saka nake zaune dashi saboda gidan mu babu ac, wadansu kuma suka yi min fatan ganin ranar da
Umar zai haike wa Yasmin wai a ranar ne zan san abinda zanyi tunda yanzu nace ba sani ba. Wadansu
kuma suka kare dukkan tsinuwar su akan Umar



Few ne suka yi min magana mai dadi, da yawa daga cikin su suka bani hakuri suka ce inyi ta addu'a
komai zai zo karshe.



Abinda naje nema a gurin mutane a lokacin shine shawara, shawarar yadda zanyi solving problem din
zamana da Umar ba tare da na bata sunansa ko nawa ko na yayana ba. Tabbas nasan Umar yana da laifi,
kuma nasam iyayensa suma da laifi, na kuma san nawa iyayen suna da laifi dan dalilin yanayin sune ma
ya saka har naje social media neman shawara ban je gurin su ba su da ya kamata ace sune na farko da
zan fara fadawa matsala ta, kuma nasan nima ina da laifi dan Dan Adam tara yake bai cika goma ba ko
waye shi kuwa. Dan haka ba laifuffukan mu naje media dan a gaya min ba, na riga na sani, ba kuma zuwa
nayi dan a tsine wa mijina kuma uban yayana ba, sannan ba zuwa nayi dan a zage ni ayi making dina feel
like dukkan abinda yake faruwa laifi na bane ba. Shawara naje nema daga gurin yanuwana mata
wadanda kullum suke cewa ai ciwon ya mace na ya mace ne, but I saw and felt different.



Ranar cin mutuncin da na gani a social media ban taba ganin irinsa ba a dukkan rayuwata. I felt bad, very
bad har sai da naji na tsani kaina. I felt tun daga auren Umar har zuwa yanzu duk abinda suka faru laifina
ne, naji na tsani kaina, na tsani Umar, na tsani kowa na tsani komai, naji na tsani rayuwata. And I
stopped crying and spent the entire day a cikin daki in bed. I became depressed.



Abinda na fara yi daga farko shine na daina kuka, na daina fita daga daki na daina shara da gyaran gida
na waina wanka. Farko Umar ya fara kyaleni, in ya shigo yayi ta yi min magana na rabu da shi sai ya
kyaleni ya fita kuma ya fitar da yara, daga baya sai ya fara damuwa, sai yazi ya takuwa min yayi ta
nemana da fada ma dan muyi amma ko kallon shi ba zanyi ba. Sai ya debo yayan mu ya kawo min suyi ta
hawa jikina suna min hira amma suma ko kula su ba zanyi ba, daga baya sai in rufe kofata ma in kuma
rufe taga in saki labule kuma in kashe fitila in kwanta in lulluba, amma da zaka bude rufar zaka ganni a
kwance ne idona a bude ba wai bacci nake yi ba.



Sai Umar ya dauke key din kofar, ya lalata lock din yadda dole bana iya rufe kofar. A cikin wannan lokacin
bana jin Umar yana zuwa aiki, he took over taking care of the house and the kids and me, shi zai shirya
Yasmin ya kaita school a lokacin da nake kwance, yayi wa Asad wanka ya shirya shi yayi breakfast ya
kuma zo ya matsa min lallai sai naci. Da rana zai fita ya siyo abinci sannan ya dauko Yasmin yazo yayi
mata homework.



Gaba ki daya suka tattaro suka dawo dakina, anan suke wuni suna wasa su ci abinci suyi kallo duk anan
amma ko kallo basu ishe ni ba ballantana in shiga cikin maganar su. Umar har hausa novels da yaga ina
karantawa yake samowa yazo ya zauna da daddare in yara sunyi bacci yayi ta karanta min yana dariya
shi kadai in anyi abin dariya. Da assuba kuma zai dauko Alqur'ani guda biyu ya bani daya ya rike daya
yace wai inyi masa dori, farko shima share shi nake yi, sai yake rabuwa da ni yayi karatun sa shi kadai,
daga baya sai na fara bin sa muna yi tare.



A hankali kuma sai nazo na dawo ina magana, zanyi magana da yara shima in yayi min magana zan amsa
amma babu alamar walwala a tare dani. And it went on for weeks.



A haka har akayi wa yara hutu, wata rana ina kwance a daki kamar yadda na saba sai gashi ya shigo tare
da yara gabaki daya suka hawo gadon suna ta murna, ya kama ni ya tashe ni zaune daga kwancen da
nake yace "look, i have some news that will cheer you up" na bishi da kallo kawai ban ce komai ba sai
Asad da Yasmin suka miko min wani dan abu mai kama da littafi da yake hannayensu, na karba ina
dubawa, a raina ina hoping takardar saki na ce ya saka a cikin abin, sai naga passport ne da sunayen su a
jiki, na juya ina kallon sa sai yayi murmushi, "we are going to pay a visit to auncle Muhammad. We are
going to Ethiopia"



Na sunkuyar da kaina ina kallon passports din hannuna, ya matso tare da rike hannuna a cikin nasa
"common Jidda at least smile mana, ni da yara duk muna ta murna at least kema ki danyi murna mana,
you were so happy lokacin da suka zo I thought ganin su yanzu will make you happy. Ina son ne in samu
amincewar ki sai inje inyi mana visa gabakidaya, zan kai ku can sai in dawo, kuyi holidays acan ku huta ku
ji dadi"



Nayi shiru ina kallon sa ina jujjuya takardun a hannu na, ya shafa gefen fuskata "please smile and say
yes" sai kuma ya juya yana kallon Yasmin "Yasmin ki roki mommy ta ce yes sai muje mu shiga jirgi"
Yasmin ta hau jikina "mommy say yes please" Asad ya taho ya rike hannuna shima da maganar sa da
bata gama nuna ba yace "ce yech" na danyi murmushi, the first in weeks, sannan na shafa kan yara na
na kalli Umar nace "okay, yes zamu je".
Wannan ma is another thing na Umar da ba zan manta da shi ba, shi yayi uniting dina da lost family na,
shi ya kaini dangin Umma har gidan auncle Muhammad muka je sannan ya juyo ya bar mu a can. A
lokacin ina ta tunanin ina ma ya samu kudin daya shirya mana tafiyar nan sai daga baya na fahimci
motarsa da yake hawa ya siyar yake using tawa.



Ba karamin murna yan uwana suka yi ba da suka ganni, ba kuma karamin murna Umma tayi ba da taji
labarin tafiyar mu har sai da tayi hawayen dadi "in Allah ya rage ka ta wani bangaren sai kuma ya faranta
maka ta wani, tunda ni Allah ya hadani da mijin da ya raba ni da dangina ke kuma sai Allah ya hada ki da
wanda zai sada ki da su. Allah ya saka masa da alkhairi".



A can ma haka suka yi ta cewa, tunda babana ya hana babata zuwa ni gashi nan mijina dan albarka ya
kawo ni da kansa. Suna ta yaba masa shi kuma yana ta yi musu ladabi da biyayya. A kwana biyun da yayi
kafin ya juyo ya siye zuciyarsu gabakidaya.



Satin mu hudu acan, a cikin sati hudun nan kullum babu fashi sai Umar ya turo min da sakon ban hakuri
ta WhatsApp safe da dare babu fashi, kuma kullum sai ya kira wayar Layla yace ta bani amma sai in ki
karba in bawa yayansa suyi ta hirar su, har Maman su Layla ta lura ta saka ni gaba da nasiha wai in nayi
wasa wasu matan zasu zo su kwace min miji, ta saka ni a gaba tana koya min wai tips din mallakar miji
babu boka babu malam, ni kuma na zauna ina sauraron ta ba tare dana fahimci komai ba dan last abu da
nake son yi a lokacin shine mallakar Umar.



Naji dadin tafiyar mu sosai kuma na fahimci dalilin da yasa Umar ya shirya mana ita, zuciyata ta rissina,
har sai gani ina hira sosai ima dariya a cikin yan'uwa na, wani lokacin ma in ba message dinsa ne ya shigo
ba sai in ma manta dashi da problems dinsa.

Sai da lokacin dawowa yayi Umar ya aiko wa da auncle Muhammad return tickets din mu sannan
hankalina ya tashi, ba wai Nigeria din ce bana son komawa ba gidan Umar ne bana son komawa.



Amma haka suka tattaro mu, tare da goma ta arziki suka sako mu a jirgi muka dawo. Umar ne yaje dauko
mu a airport, dashi da yaya Tahir da Amira. Har da sabon dinki naga yayi da sabuwar hula. Su Yasmin
suka tafi gurinsa da gudu suna murna, ya rungume su daya bayan daya briefly sannan ya wuce su ya taho
inda nake tahowa ya karbe jakar hannuna ya ajiye a gefe sannan ya rungume ni, without minding su
Yaya Tahir da kuma tarin mutanen da suke gurin. Ya sauke ajjiyar zuciya "God! I missed you" ban ce
komai ba har ya sake ni sai na wuce shi na tafi gurin su Amira ina murnar ganin su.
Gidan mu muka tafi, Umma tana can tayi shirin taryar mu bakinta har kunne, ranar wuni mukayi ina ta
bata labarurrukan garin su da bata taba zuwa ba ina kuma nuna mata hotunan dana dauka tare da
cousins dinta da yayansu, most of which bata sani bama. Naje na gaishe da Abba

58 / 101