Chapter 7 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   7 / 101

18K to 21K   out of 300.2K words

ba zai iya tafiya
can da ita ba, ga kuma tafiye tafiyen da yake yi zuwa kasashen duniya duk ba zai iya yi da matar sa ba kin
gane? Shine kawai naji ina yi miki sha'awar aurensa wallahi, na san yana ganin ki zai amince dan dama
irin ku yake nema, kar ki wani damu da babba ne dan sai yafi ma saurayin kula da ke da tarairayar
ki........."



Ta cigaba da maganganun ta amma ni hankali na ya tafi wani gurin daban, ina duba rayuwar yayye na
mata ne, irin jouney din da suka samu kansu a ciki sai na fara wondering what my own jouney will be,
wanne kalubale ne ni kuma zan fuskanta a nawa gidan auren?



Mun zagaya suma mazan kamar yadda muka zagaya matan, sai dai ni duk banji wani dadin ziyarar sosai
ba dan ban saba da matan su ba sai dai gidan yaya Mukhtar wanda bai jima da aure ba, amaryar sa
Aunty Halima tana da kirki sosai kuma munyi dace halin mu na karatun hausa novels yazo daya, muka yi
ta hirar littattafai da kuma marubuta wadanda muka sani, sai dai kuma yanzu ita ta daina karanta
published novels ta dawo karanta online ones, ni kuma tunda ba waya ce dani ba ban ma san ana rubutu
online din ba.
"Kuma Aunty Halima suma kamar bugaggu ne?" Tace "sosai ma, akwai online writers da suka iya labari
sosai wadanda in kika fara karanta books din su ba zaki daina ba ko da kuwa sun mayar da su na
siyarwa" na bata fuska nace "na siyarwa kuma Aunty Halima? Ta yaya za'a siyar da littafi online?" Ta fara
yi min bayanin WhatsApp groups da Okada books da Wattpad amma ni tunda duk ba sanin su nayi ba
ban wani gane sosai ba. Nace "kuma nawa kuke siya?" Tace "wani 300 wani kuma 200, most dai haka
kudin yake" Farhan tace "amma yayi tsada, ji nake bugaggen ma haka ake siyar dashi, wannan kuma na
waya in wayar ta bata fa shikenan ka rasa shi" Aunty Halima tace "bai yi tsada ba, ni yayi arha ma a
ganina sosai saboda yawanci littafi daya suke yi babu zancen part one two three kamar yadda bigaggun
littattafai suke, wasu ma har part four zaki ga, kuma ki sayi kowanne dari uku, kusan dubu daya da wani
abun kenan a labari daya. Sannan kuma maganar bata ni ina siya nake kai shi e-mail dina in ajiye a can,
yadda ko waya nawa na chanja yana nan a ajjiye babu inda za shi"



Na fahimci wannan bayanin duk da dai ban gane zancen e-mail din ba. Sai dai kawai nace "duk ranar da
nayi waya zan zo ki koya min duk wadannan abubuwan sannan ki tura min duk books din inyi ta
karantawa" tace "Allah ya kaimu kanwata" muna cikin hirar yaya Mukhtar ya shigo, sai take yi masa
korafin ya kamata a ce an siya mana waya "yanxu ace yammata babu waya? Ta yaya zasu yi samari?" Ya
bude baki "waya? Rufa min asiri, ai wadannan yammatan haka zaki gansu kuma haka zaki kyale su, duk
wanda ya sake ya siya musu waya to rigima shi da Abba har koton koli" muka yi dariya baki daya, sai ya
zauna a tare damu muka cigaba da hirar Abba da irin dokokin sa.



Daga nan munje gidan gwoggo Habiba, dukkan ƴaƴan ta sun yi aure kuma suna kula da ita sosai dan
kusan babu abinda ta nema ta rasa, daga ita a gidan sai mijinta da yar autarta, Jamila.



Jamila kyakykyawar budurwa ce yar gayu mai ji da yammatanci, a lokacin tana shekarar ta ta karshe a
jami'ar Bayero, tunda muka je gidan muke ta kallon ta cike da sha'awa ni da Farhan, komai na yaya
Jamila burge mu yake yi, yadda take kwalliya da dressing, yadda take magana ana yi ana jefa turanci a
ciki da tafiya kamar ana tausayin kasa, a ranmu sai muke ji ina ma dai mune muka samu wayewa irin
tata. Sai dai kuma a cikin kwana biyun da mukayi a gidan su muka lura da irin tsananin soyayyar da yake
tsakanin yaya Jamila da wayarta. Ko da yaushe tana hannunta tana daddanna wa tana murmushi, ko ita
da waye oho. Cikin dare kuwa har mu farka fitsari tana cike da waya a kunne tana hira kasa kasa yadda
mu da muke daki daya gado daya bama fahimtar abinda take cewa. Bamu tashi tabbatar da zargin mu a
kanta ba sai da muka ga ta chanchada kwalliya ta gayawa gwoggo cewa zasu fita unguwa da wani friend
dinta, irin yadda tayi maganar kamar mai sanarwa ba wai neman izni ba sannan ta fice ba tare da ta jira
amsa ba, har sai da muka yi bacci sannan ta dawo ta kwanta tare da cigaba da magana a cikin wayarta
tana dariya kasa kasa. "Yes, I really enjoyed myself" ta fada a hankali. Sai muka kalli juna ni da Farhan
sannan muka gyada wa juna kai alamar duk irin tunani daya muke yi. Sai na kwanta ina tunani a raina
"shin irin wannan wayewar da irin wannan rayuwar Abba yake gudar mana shi yasa yake takura mu? In
haka ne shima yana da tasa gaskiyar kenan.
Gidan Aunty Afia (Mami) shine gida na karshe da muka je. Tun a hanya nake ta zumudin ganinta, ina
balain son ta har cikin raina ita da yayanta, Aira da Aarif. Aira kusan sa'a ta ce, Aarif kuma da kadan ya
girmi Amira. Ni a idona gani nake kamar Mami da yaran ta sunfi kowa kyau a duniya amma sai inji
mutane suna cewa wai kamar mu daya da Aira wai kamar an tsaga kara ni kuma dariya nake yi in aka
fadi haka.



Tun daga gate mai gadi ya karbi kayan mu yana mana sannu da zuwa, ya sanni kuma yasan dangantaka
ta da gidan. Mijin Aunty mai kudi ne, gidan su kato mai cike da duk abinda suke bukata. Muna shiga na
tafi da gudu jikinta na rungume ta ina jin hawaye yana taruwa a idona, ta rungume ni ta na shafa bayana
tana dariya, sai kuma ta dago fuskata tana kalla tace "sai yau babanki ya ga damar barin ki ki zo ki ganni
ko? Kema so yake ya mayar dake kamar Ayesha ko? So yake ki zama daddawar cikin daki ko? To Allah ya
fishi" nayi dariya ina goge hawaye na, "kai Aunty Abba ne fa" tace "Abban ki ne ai ba nawa ba. Tun da ya
raba yaruwata da kowa nata sai shi kadai ai nima ba zan raga masa ko inji nauyin sa ba. Wannan ne yasa
baya son kuke zuwa gurina" na yi kokarin kawar da maganar ta hanyar fara neman yanuwana. "Aira!
Arif!" Tayi dariya suna islamiyya, zasu dawo ai su same ku" sai a lokacin Farhan ta samu ta gaishe ta, ta
amsa mata babu yabo babu fallasa sannan ta kira masu aiki ta bada umarnin suyi entertaining din mu.
Muna cin abinci su Aira suka dawo nan take muka cika gidan da hayaniya da murnar ganin juna.



Kwana dayan da mukayi a gidan sai naji kamar second daya ne, nan da nan wai har dare yayi kuma har
gari ya waye. Duk da cewa ba wani baccin kirki mukayi ba dan kusan raba dare mukayi da Aunty tana
bani labarin yanuwanmu da yadda take so watarana Abba ya bar mu muje mu gansu. "insecurity ne yake
damun babanku, shi kansa yasan Aysha ba sa'ar auren sa bace ba amma ta dage lallai sai shi, to tsoro
yake yi kuma kar takoma cikin dangin tata guje shi, kuma kuma yana tsoron kar kuje can idon ku ya bude
ku fi karfinsa, wannan shine matsalar sa. Amma kinga yanzu in kika yi aure ai kin tashi daga ikonsa kin
koma ikon mijinki kuma zaki ke zumunci damu yadda kike so insha Allah. Wai in tambaye ki mana, akwai
wani ne yanzu da yake zuwa gurinki?"



Nayi shiru ina tunani, Musa dai bana son sa kuma bana jin ya kamata in gayawa Aunty labarin sa, Umar
kuma ban ma san menene matsaya a tsakanin mu ba. Na girgiza kai "babu kowa Aunty" ta gyada kai "to
Allah ya kawo nagari. Ni in a so nane ma nafi son kiyi aure a dangin mu dan mu karfafa zumuncin mu,
amma babu wanda yasan ki a can ballantana ya ce yana son ki"



A ranar da muka dawo gida, bayan mun gama murna da gaishe gaishe sai na ja Amira gefe "ke! Sanda ba
ma nan babu wanda yazo nemana?" Tace "a cikin gida ko a waje?" na sosa kai "a ko'ina ma" tayi dariya
"wai Musa? Zuwansa biyu fa, ana biyun Umma tace inje in gaya masa ranar da zaku dawo dan kar yayi ta
zarya" naji raina ya fara baci duk da babu abinda Musa yayi na bacin rai.



"Bayan shi babu wanda ya zo?" Ta girgiza kanta. "Babu kuma wanda ya kira Umma yana nemana?" Ta
kuma girgiza kai "ni dai bansan kowa ba, sai dai in Umma zaki tambaya ko an kira sanda bana nan" nayi
saurin cewa "a'a, shikenan" sai kuma na wayance dan bana son tayi ta yi min tambayoyi "kinsan number
dinta na bawa kawayena a makaranta, to ina tunanin ko wasu daga ciki sun kira ta ne."



Amma duk da wannan interview din da nayi wa Amira ban hakura ba sai da nayi ta duba call history din
Umma wai ko ya kira bata dauka ba kuma bata bi ba, sai dai babu wadansu missed calls daga unknown
number, kuma babu daga number din Mufida. Na ajiye wayar tare da yin ajjiyar zuciya. "Ya fasa" na fada
wa kai na, "dama karya yake yi" na maimaita. Sai dai kuma zuciya ta taki amincewa da wannan
musamman idan na tuna da abinda na gani a idonsa, it looked so real.



Da dare ina tsakar gida Umma ta kira ni ta gaya min cewa Mufida ta kira ni yanzu, da sauri na karbi
wayar "Allah sarki Mufida, bara in kira ta mu gaisa" sai dai a wani bangare na raina ina fatan ba Mufidan
bace ba. Ina kira kuwa ta dauka, muka yi ta hira tana bani labarin hutun da suke yi a Lagos gabakidayan
su, amma ko a cikin magana bata ambaci ko da sunan yaya Doctor ba nima kuma ban tambayeta ba.



Sai dai washegari da yamma ina wanke wanke sai ga dan aike. "Wai ana sallama da Jidda" naji raina ya
baci, naki bashi amsa ma saboda takaici sai da Umma ta leko tace "kaje kace tana zuwa" ta kalle ni "baki
ji ana magana bane ba? Yaron nan zuwansa biyu ba kya nan kuma ni nace masa ya dawo yau kafin nan
kin dawo" na mike bance komai ba na wanke hannu na ina lissafin abinda zanyi masa idan na fita. Hade
rai zanyi yayi hirar sa shi kadai, haka zan ke masa a haka har ya hakura ya rabu dani.



Na wanke hannuna da fuskata sannan naje daki na dauko hijab dina na fito, Umma ta bini da kallo
sannan tace "ki koma ki shafa mai a kafarki duk tayi jirwaye, sannan kuma ki saka powder a fuskar ki da
dan man lebe" na juya still ba tare da na ce komai ba na koma nayi abinda tace ba dan raina yaso ba, na
tsaya ina kallon fuska ta a madubi ina hango kamar da ake cewa muna yi da Layla. Nayi ta gwada
fuskokin bacin rai iri iri ina lura da yadda suke chanja min kamanni, so nake in samu wadda zata saka inyi
muni dan in naje inyi masa yaga muni na yace ya fasa.



Ina tsaye naji kiran Umma, na fita da sauri ina lura da kallon da take min tana noticing ko nayi abinda
tace, ina shiga sitting room na goge lipstick din dana shafa har da tabbatar wa cewa ya bata gefen baki
na dan inyi muni. Na dan gyara sitting room din na kunna fitila da fanka sannan na bude kofar waje na
fita da niyyar kiran Musa.



Sai dai me?.....



Na gane motar sa kamar yadda na gane tsayuwar sa, ya juya bayan sa yana daddanna wayar sa. Gaba na
ya fadi "Umar" zuciya ta ta kira sunansa. Kamar tashi zuciyar taji kiran da tawa tayi masa sai ya juyo da
sauri ya saka idonsa a cikin nawa. For a brief second babu wanda yayi magana a cikin mu, but I can feel
my heart talking to his sai-dai bana jin amsar da tashin take bayarwa. "You!" Na fada a hankali. "You are
here" ya juyo sosai tare da saka wayar hannun sa a aljihunsa ba tare da ya dauke idonsa daga cikin nawa
ba. Sannan ya rungume hannunsa a kirjinsa yana sakar min lallausan murmushin sa. "Ni din nan da kike
gani, murucin kan dutse ne ni ban fito ba sai dana shirya" na dan bata rai cikin rashin fahimtar maganar
sa. "Muruci kuma? Wanne irin shiri? Ban gane ba?" Ya taho zuwa gabana ya tsaya, towering over me
yadda sai da na daga kaina sannan na ke kallon fuskar sa, fuskar da bana so in daina kalla kamar yadda
shima yake rarraba idanuwan sa akan tawa fuskar kamar mai son haddace suffar duk abinda yake cikin
ta.



Nayi saurin sunkuyar da kaina dan tunawa da nayi da abinda nayi a fuskar tawa, na wayance da yin tari
sannan na rufe bakina da gefen hijab dina ina kokarin goge lipstick din da nayi messing a gurin.



Nayi taku biyu baya tare da nuna masa kofar sitting room din. "Bismillah" nace "sannu da zuwa" na sake
fada tare da yin gaba da sauri. Zuciya ta tana tsalle a kirjina.



A tsakiyar falon na tsaya har ya shigo na dan nuna masa kujera a farkon falon sannan na zauna a kujerar
karshe "ina wuni" na gaishe shi kaina a kasa, bai amsa ba yace "ya ilahi yarinyar nan kin wahalar da ni.
Kinsan kuwa ta yadda nayi nazo gidan nan?" Nace "driving kayi daga gadon kaya zuwa gandu. Babu nisa
ai sosai" ya bude baki "wato kin san ma gidan mu kenan. Ya ilahi! Duk wannan wahalar da nasha ashe ke
kinsan gidan mu? Yarinyar can karya take yi min kenan" nayi shiru ina lissafi, ni ban fahimci abinda yake
so yace ba, nace "wacce wahala kake magana akai?" Ya gyara zama yace "kin san kuwa ta yadda akayi na
samu address dinki? Wai ku dama mata haka kuke friendship dinku? Ace babbar kawar ki bata da
number din ki kuma bata san gidan ku ba?" Nayi shiru ina accessing maganar, ya cigaba "ashe wai
Mufida bata da contact dinki, idan da ace nasan hakan da bazan taba barinki ki fita daga mota ta a ranar
nan ba, a cikin kwanakin nan sau uku ina komawa taura makarantar ku wai ko zasu gaya min address
dinki amma suka ki gaya min, har bribe na bawa principal dinku ta karbe kuma taki gaya min, sai
shekaran jiya suka bani address din wani tsohon malamin ku Malam Abdulrashid, to jiya naje wajensa
shima ya gama jirgani ya kuma gama yi min dogayen tambayoyinsu irin na tsofaffin malamai sannan ya
bani address din"



Tun da ya fara maganar nake murmushi, ina jin dadin yadda yayi going through wannan dan ya zo gurina
sannan kuma ina kara tabbatar wa kaina cewa zargin da Mufida take yi masa ba gaskiya bane ba. Ya lura
da murmushin fuskata yace "dariya ma kike yi min ko?" Na girgiza kaina da sauri ina kara fadada
murmushi na. Yace "babu komai. Ko yanzu na fanshe duk wahalar da nasha, wannan murmushin kadai
ya biya ni duk abinda nayi har da kari. And I can do it all over again for it, for the smile"



Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din



0779484494

Nafisa Tafida Usman

Access Bank



Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp

08067081020



Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020



Please banda kira, WhatsApp only




*Episode Six : The Sweetest Thing*



Na dan boye fuskata kadan a jikin kujera, yayi murmushi mai sauti sannan ya taso ya kuma dawowa
kujerar kusa da tawa yace "amma gayamin, dan Allah wai Mufida bata san gidan nan ba? Kuma wai da
gaske bata da number din da za'a same ki? Ni fa jikina yana bani wasa tayi min da hankali. Tana sane ta
wahalar dani a banza"



Na dan juyo ina kallon sa ina tunanin ta yadda zan kare kawata. Wata idea ta zo min sai na sunkuyar da
kaina nace "jiya ma munyi waya da ita. Suna can Lagos ko?" ya hada yatsunsa suka yi kara yace "I knew
it. Yarinyar can ta shiga uku a hannu na, sai na yayyanka naman ta na cinye duk sanda na kama ta. Nace
"kawar tawa? Besides, shi abu mai daraja ai dama sai an sha wahala ake samun sa ko? Duk abinda aka
samu cikin sauki to anfi saurin wulakanta shi"



Ya rufe fuskarsa da hannu daya yana dariya a cikin kirjinsa sannan ya bude idonsa yana kallo na, ni kuma
na rufe tawa fuskar sai yace "na gane, sai yanzu na gane komai. Issoryt. Wato kun hada kai ne dan ku ja
min aji ko? Duk abinda nake ciki ashe kina sane ko? I like it, ina fatan dai naci test din?" Nace "ai ba test
bane ba, screening ne dan muga how far you can go. Kayi passing first phase saura phase na biyu"



Na mike tsaye, shima ya mike da sauri "dan Allah, kar kice gida zaki koma. Ki barni na cigaba da ganin ki"
nace "ganin kama da nayi yanzu a matsayin mai laifi nake. Ba'a gani na sai an samu izni daga Abba na. Ka
neme shi, ka ganshi, kayi masa bayanin dalilin da yasa kake son ganin yarsa sannan in ya amince maka
sai ka dawo' na juya zan shiga gida naji ya kira sunana "Jidda" na tsaya amma ban juyo ba, naji ya tako
xuwa bayana ta tsaya sannan yace "zan je inga Abban mu, sannan zanyi iyakacin kokari na dan in samu
karbuwa a gurinsa sannan zan dawo in sake ganin murmushin ki da license dina a hannu na"



Sai da na kai bakin kofa sannan na juyo, muka hada ido yayi min murmushi na mayar masa sannan na
shige cikin gida.



Daren ranar is one of my happiest. Dan har sai da Farhan ta gaji da jin hirar Umar ta rufe kunnuwan ta da
pillow. Duk da haka kuma ban fasa bata labarin sa ba har sai dana tabbatar tayi bacci sannan na kwanta
nima na rufe ido na, fuskarsa ta bayyana gare ni, nayi murmushi, tabbas nasan yau dole ne ma ya shigo
cikin mafarki na.



Two days after that, da yamma muna tsakar gida muna cin abinci tare da Farhan da Amira sai Hajiya ta
leko daga barandar Abba ta kira ni, na amsa tace in zo inji Abba. Gaba na ya fadi na

7 / 101