Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
ya zauna "a'a bata dauka ba, amma
wancan karon da muka samu matsala can taje gurinsa kuma yace in wani abu ya kuma faruwa ta gaya
masa zai dauki mataki" Abba ya mike, ransa a bace "shi Tahir din? Dama shi yake daure mata gindi
kenan, zai zo ya gaya min ni na haife ta ko shi ya haifar min ita?" Umar ya dafe kansa yana jin haushin
kansa, wani lokacin ma dai surutu bashi da dadi.
Abba ya shiga gida yana bambamin fada "Aisha! Kina ina! Ki kira Tahir ki ce masa ya dauko yarinya ta ya
dawo min da ita yanzu yanzun nan" Umma ta fito daga daki hannunta rike da wayarta, fuskar ta rubuce
da tashin hankali "Tahir? Bata gidan sa, na kira shi a waya ai. Sai dai ko in ta akan hanya. Na kira Afia ma
bata can. Sai dai mu jira anjina muji inda zata bulla. Ai ba zata wuce wadannan guraren ba"
Ya juya ya koma gurin Umar yana cigaba da fada. "Duk inda taje ma zata dawo ne, za kuma ta same ni ne
tunda ni zata mayar mutumin banza. A baro gidan mijinta kuma in umarce ta ta koma amma ta nuna
min ban isa ba, sannan ta kama hanya ta fita kuma in kira ta taki dauka"
Fada yake yi har bakinsa yana kumfa, yana yi Hajiya tana bashi hakuri "kar kaje wani ciwo ya same ka
Alhaji, ba ita kadai ce yar ka ba, in ka mutu ita bata da matsala ma tunda iya yar gatan miji ce"
Umar dai yana zaune yana cigaba da kiran wayar Jidda, daga baya ya koma tura mata messages.
"Jidda please don't do this"
"In kin fi son zama anan ni zanyi wa Abba magana ya barki ki zauna anan din"
Ya cigaba da kira amma bata da niyyar dauka. Ya sake tura mata sako
"Just pick up the damn phone"
Amma bata dauka ba.
Time ya cigaba da tafiya. Duk inda zata je ya kamata ace yanzu yaje, amma kuma babu wanda ya kira
yace gata nan taje gidan sa. Daga nan suka fara kiraye kirayen yan'uwa ana tambaya ko ta je, duk siblings
dinta an kira su bata je ba, aka koma kiran cousins suma babu wani bayani. Farhan kuma ta yi ta kiran
friends din su sji kuma Umar ya na kiran nasa dangin amma da yake mai yawo ne baya nuna Jidda yake
nema sai dai kawai ya kira a gaisa, knowing in tana can za'a ce masa gata tazo, duk da dai bayan gidan
yaya Mubaraka baya jin akwai gidan wanda zata je a cikin yan uwan sa. Amma babu amo babu labari.
A haka har dare yayi sosai. Lokacin Tahir yazo gidan ai kuwa Abba ya huce haushin sa akansa yayi masa
tas yace shi yake ziga Jidda taki zaman aure, daga baya ma yace sai ya fito masa da yarsa, hakan ta sa
dole Tahir din ya bar gidan ba tare da ya shirya ba ya fara yawon neman Jidda a duk gidan da yasan suna
da alaka kuma zata iya zuwa. Sai dai duk inda yaje babu Jidda babu dalilin ta.
Dole ya hakura ya koma gidan sa, yana zama ya sake kiran number dinta still bata dauka ba sai ya tura
mata message
"Jidda Call me"
Bayan wani lokaci reply ya shigo masa "I am safe. Ka gaya wa Umma".
Umar bai bar gidan Abba ba sai da Abban da kansa yace masa ya tafi gida ya huta sai da safe tukunna sai
su ga abinda zasu yi, in police za'a shigar cikin maganar to, dan shi Abba ya fara tunanin ko sace su akayi
tunda kusan duk wanda suka san ta sani sun kira amma basu samu ba.
Umar ya shiga motar sa ya fara driving da hannu daya daya hannun kuma ya dafe kansa da shi. Bai ma
san tunanin da yake yi ba amma shi dai yana da tabbacin babu wanda ya sace Jidda da yayansa, guduwa
tayi, saboda shi kadai yasan irin girman laifin da yayi mata kuma shi kadai yasan irin bacin ran da ya gani
a tare da ita dan baya jin ko sanda suka yi case din Mammy ranta ya baci irin haka. Guduwa tayi ya sani,
so take ta hukunta shi kuma yasan yayi deserving duk hukuncin da zata yi masa koma fiye da haka. Sai
dai abinda bata sani ba shine abinda take tunanin ya faru is not entirely true, amma baya jin ko yayi
mata bayani zata fahimta tunda shi din tsohon mai laifi ne a gurin ta.
Gidan su ya nufa, dan baya jin zai iya zuwa gidansa a yau not without her and their kids. Amma sai dai
me?
Yayi horn mai gadi ya bude masa, sai da suka hada ido sannan ya tuna da wata halitta wai ita Asabe, yayi
sauri ya dauke idonsa daga cikin na maigadin yana tambayar kansa ko ina yarinyar ta tafi, ko dame dame
ta je ta fada? Ko wanne sharrin kuma ta sake yi masa?
Sai dai jin maigadin bai yi masa maganar ta ba yasa ya amsa gaisuwar sa sama sama sannan ya shiga
cikin gida.
Mufida kadai ya tarar a falo kwance akan kujera da waya a hannunta tana yi, sai dai tana ganinsa ta yi
saurin katse wayar tare da tura ta bayan ta, idan ba rudewar da yake ciki bace tayi deceiving dinsa zai iya
cewa har tsorata tayi.
"Yaya Doctor sannu da zuwa" ta fada tana kallon agogo. Bai amsa mata ba yace "ina Mama? Shiga ki kira
ta" sai ya zauna akan kujera tare da dafe kansa da hannu biyu da yake jin yana sara masa kamar zai bar
jikinsa. Me Jidda take tunani ne wai? Dan me yasa zata gudu bayan aurensa kaddarar ta ne kamar yadda
shima halinsa yake kaddarar sa?
Hannun mutum yaji a kafadar sa, yayi saurin dago kai yaga Mama da Mufida a tsaye a gaban sa, shi bai
ma san sanda suka shigo ba. Mama tana yi masa magana amma sai yaji baya jin ta sosai, nesa nesa yake
jin muryar ta amma daga dukkan alamu tambayar sa take yi me yake damunsa.
"Mama Jidda ta tafi, ta dauki Yasmin da Asad ta tafi bansan inda ta tafi ba"
Ta zauna kusa dashi itama nata hankalin ya fara tashi "ban gane ba. Ta tafi kamar yaya? Fada kuka yi?
Bata gidan su?"
Sai kawai ya mayar da idonsa ya rufe sannan ya jingina kansa da jikin kafadar ta yayi shiru, tana jin yadda
jikinsa yake hucin zafi, tace da Mufida ta bata aron wayarta da take hannun ta amma maimakon ta bata
sai ta wuce daki ta dauko mata tata ta miko mata, Umma ta kira, ita kuma Mufida ta kira number din
Jidda sai ta jita a kashe, tace "wayar bata shiga ai" a hankali yace "ta kashe ai, da wayar tana shiga
amma yanzu ta kashe ta"
Mama ta fara fada "kuma dan kunyi fada sai ta debi yara ta tafi? Tayi ta tafiya mana ai ba ita kadai ce
mace a duniya ba amma ta dawo maka da yayanka tunda dai ba dasu aka auro ta ba. Ni ban taba ganin
irin wannan rayuwa ba. Ni ban taba ganin mata irin taka ba, mace babu abinda aka rage ta dashi amma
ba zata bar mijinta ya huta ba? Jarabar yau da ban ta gobe daban? Ita bata yi kiba ba bata bar ka kayi
kiba ba gashi nan duk kayi duhu ka lalace"
Sai kuma ta dora hannunta a goshinsa tana jin hankalin ta yana kara tashi "innalillahi wa inna ilaihir
rajiun. So take ta kashe min kai, abinda take so kenan ka mutu kabar mata duniyar"
Ya zame daga jikinta ya kwanta akan kujerar yayinda ita kuma ta kira Umma suka fara mayar da abinda
ya faru
Jin bata yi masa zancen Asabe ba ya tabbatar masa da cewa yarinyar ba nan gidan ta taho ba.
Bayan Mama ta gama wayar sai ta saka Mufida ta kira Doctor Bashir tace yazo ya duba Umar bashi da
lafiya sannan ita kuma ta kira Baba tana gaya masa abinda yake faruwa. Bata ma tuna da wata Asabe ba
ballantana ta nemi inda take tunda matar gidan bata nan.
Umar bai taba ganin tashin hankali irin na ranar ba kamar yadda bai taba ganin dogo kuma bakin dare
irin wannan ba, shi gani ma yayi kamar batteries din jikin duk agogunan gidan duk sun mutu dan gani
yayi kamar daren a tsaye yake shak baya tafiya. Kamar yadda bai yi bacci ba haka bai bar mama da
Mufida sunyi bacci ba, a daren bayan Bashir yazo ya duba shi sai ya saka Mufida ta rubuta masa list na
dukkan kawayen Jidda da ta sani da kuma addreses din su, haka ta zauna ta rubuta masa list, gari yana
wayewa ya saka ta fara bin su daya bayan daya tana kira tana tambayar su ko sun ga ko kuma sunyi
waya da Jidda, sannan ta roke su da in sun ganta ko sun ji labarin wanda ya ganta su kira ta.
Wadanda kuma bata samu a waya ba sai Umar ya kira Bashir yazo suka fita tare har da Mufida suna bin
su zuwa gidajen su. Daya bayan daya. Amma babu wadda take da labarin Jidda. Basu dawo gida ba sai
dare, kowa ya kalli Umar a cikin kwana daya da wuni dayan nan sai ya tausaya masa, gabakidaya ya fita
daga hayyacin sa in kana masa magana ma ba ganewa yake yi ba. Dole doctor Bashir ya dawo dashi gida
yace ya kwanta amma Umar yaki yarda sai da ya ce masa "in ba ka kwanta nayi maka allura kayi bacci
ba, zaka fadi ka mutu, ko sun dawo you won't be there to see them" wannan ya saka shi yadda akayi
masa allurar, Bashir ya rufe shi a tsohon dakinsa dake gidan su tare da cewa
"Allah na gode maka da baka dora min wannan cutar ba wai ita soyayya"
Bashir da Mufida ne suka karasa zagayen sauran kawayen sannan suka dawo gida. A ranar Baba ya shigo
Kano shima cikin tashin hankali da alhinin faruwar wannan abu, ya kuma zarce gidan su Jidda gurin Abba
suka yi maganar sosai, sai dai daga shi har Abban basu san takamaiman abinda ya hada Jidda da Umar
har yayi tsamari haka ba, a lokacin ne kuma Baba ya nuna wa Abba rashin dacewar kin sauraron korafin
ta da tazo gida "da ka tsaya ka saurare ta da bamu kai ga wannan matsayin ba, yanzu rashin sanin halin
da suke ciki shine babban tashin hankalin, ga rayuwa yadda ta zama duniya ta cika da marasa imani.
Allah dai ya jishe mu alkhairi kawai"
Sai Abba yaji wani abu ya tsaya masa a rai, tabbas da ya tsaya ya saurare ta da ba'a kai ga hakan ba.
Yanzu in wani mummunan abin ya same ta ko ya sami yayan da ta tafi dasu fa? Anya kuwa ba za'a raba
alhakin har da shi ba a matsayin sa na ubanta. To wai ma menene ya hada ta da mijinta da ta gwammace
ta gudu ta shiga duniya akan ta koma gidansa?
Tambayar da Baba yayi wa Umar kenan yana komawa gida. "Me ya hada ku da har tayi yaji ta tafi gida?"
Ya shafa kansa, ya shirya wa wannan tambayar tunda yasan dole za'a yi masa ita, in ma kuma ba'a yi
masa ita ba Asabe zata bayyana da nata part of the story din, gwara yayi sauri ya shigar da nasa kafin
nata.
Yace "nima Baba takamaimai bansan abinda ya faru ba tunda taki tsayawa tayi min bayani, kawai ta
tambaye ni ne wai menene hadi na da wannan yarinyar da Mama ta kai gidan. Na gaya mata babu komai
sai ta ki yarda ta kama kuka ta hada kaya ta tafi gida"
Mama tayi saurin cewa "kaji ko? Na gaya maka matsalar yarinyar nan shegen kishi ne da ita, bata son
kowa ya rabe shi idan ba ita ba, dan na kai musu yar aiki wato shine take son ta tsiri maganar da zata
saka a dauke yarinyar daga gidan. To Allah ya dawo da ita lafiya daga duk inda taje ma, aure zaka yi, in
yaso ta hadiyi zuciya ta mutu dan bakin ciki"
Baba ya girgiza kai "uhm uhm Faruq, in babu rami me ya kawo zancen rami? Kai menene hadin ka da
yarinyar" Umar ya girgiza kai kamar zai yi kuka "Baba wallahi babu komai. Yar maigadin gidan nan ce fa.
Baba kaga yarinyar kuwa? Ita Jiddan ai ta san ko magana bana yiwa yarinyar ban san me tace mata ba,
ban san kuma me yasa ta yarda da abinda tace mata din ba".
Sai a lokacin aka tuna da Asabe, Umar yace shi bai san inda tayi ba shi bai ma lura da ko ta fita daga
gidan ko a'a ba, aka tambayi iyayenta suma bata je musu ba.
Washegari kuma Umar ya nemi sister Aisha, kawar Jidda da suka yi nursing school tare ya nemi data
bincika masa kawayen su na nan bangaren ko akwai wanda yaji labarin Jidda. Ranar ita ma kamar wadda
ta gabace ta, wuni suka yi suna yawo shi da Bashir, gida gida, loko loko duk inda suka san Jidda ta sani,
ciki harda abokan aikin ta, duk wanda suka je kuma sai su nemi ya gaya musu wani ko wata da suka san
Jidda tana mu'amala da shi.
Dogon list suka ji suna cancelling duk wanda suka gama dashi sai kuma su kara da wani sunan. Ranar ma
da kyar Bashir ya dawo da Umar gida dan yaga alamar zai ce su fara bi gida gida ne, shi kuwa dama
already Umar din ya fara bashi haushi, shi bai ga abin tayar da hankali ba, ai tana da hankali kuma ta san
me take yi, in ta gaji da gudun ai zata dawo ne dan kanta tunda dai ba zata cigaba da rayuwa da aure a
kanta ba.
But ko da Umar ya kwanta babu bacci a idonsa, sanda baccin ya sace shi kuwa munanan mafarkai yayi
tayi da Jidda da yaran su a wani hali marar kyau, dole ya hakura da baccin ya tashi, zai iya bayar da ransa
a lokacin in dai zai san halin da suke ciki, in dai zai san suna raye kuma suna cikin koshin lafiya.
Ya dauko wayarsa yayi ta rubutu yana aikawa number dinta, hoping ko zata kunna wayarta ta karanta ta
bashi amsa ko da da alphabet daya ne, ko da da kalma daya marar ma'ana ne, burinsa kawai shine yasan
cewa suna lafiya lau. A lokacin ya dauki hoton band din ta da yake hannunsa yayi posting a instagram
"Be safe. Please"
Ya rubuta, hoping ko zata gani ta tausaya masa ta yi replying messages dinsa. Shi ko da wannan kwana
biyun ta barshi tabbas ya wahala, tabbas yaji jiki, amma abinda bai sani ba a lokacin shine wannan
kwana biyun wasa farin girki ne.
Haka sati na daya yazo ya wuce, a cikin satin sai da Umar ya dangana da gadon asibiti, duk kuwa wanda
ya san Umar inya ganshi sai ya tausaya masa, tabbas babu tashin hankalin da ya wuce ace iyalinka sun
bata ba'a san inda suke ba.
Sai dai a karshen satin ne aka kira shi aka sanar da shi cewa an aiko daga sama an karbar bata leave a
gurin aiki. Sakon ya kwantar masa da hankali ya fahimci cewa tana lafiya, sai dai kuma ya kara tayar
masa da hankalin neman ta. Amma duk yadda yayi kokarin sanin wanda ya aiko aka karbar mata din abin
ya gagara, tun daga lokacin ya kullaci one particular person da yaki bashi information din, yana ganin bai
kyauta masa ba musamman tunda yasan matarsa ce, kuma ya san nemanta yake yi, amma still yaki gaya
masa yace shima nasa aikin is on the line in ya fada.
Tun daga nan sai ya fara zurfafa binciken sa zuwa sama, ya fahimci duk hannun wanda take to yana da
say a gwamnati ko kuma yana da kudi, bai kuma san wani wanda Jidda ya sani mai irin wannan matsayin
ba, wannan ya sa kishi ya turnike shi babu abinda baya aiyanawa, maybe ma a hanya suka hadu kawai ya
ga kyakykyawar mace tana bukatar taimako shine ya dauke ta ya kaita gidan sa. Wannan tunanin kadai
ya kusa saka Umar ya hadiyi zuciya ya zama gawa.
Sai damuwar sa ta tashi daga kan ko suna lafiya ya koma kan abin abinda Jidda take yi a inda take.
Time went by. Har akayi wata daya da tafiyar su. A lokacin ne yaji Baba yana zancen suna shiryawa da
Abba zasu tura Umma da Tahir zuws Ethiopia neman Jidda a can, duk da dai anyi waya da su kuma sunce
bata je ba amma hankalin su bai kwanta ba gwara aje a gani.
Sai dai shi Umar bai damu da maganar ba dan jikin sa baya bashi ta bar kasar, yafi tunanin tana kasar
nan kuma tana hannun wani babban mutum, and that's making him as frustrated as frustration goes.
Kawai kuma sai ga query daga office, wai baya zuwa aiki, shi yanzu ba aiki ne a gabansa ba dan har
mantawa yake yi cewa yana da aiki. Amma abinda yafi kona masa rai shine the query was signed by the
same person daya hana shi information akan inda Jidda take.
Sai kawai ya dauki mota yaje asibitin ya je har office din mutumin yayi masa kwararen naushin da suka
fitar masa da jini sannan ya shiga motarsa ya dawo gida. Washegari suka aiko masa da takardar kora
daga aiki.
And washegarin ne kuma da daddare yana kwance a dakin da ya mayar nasa a cikin gidan su kira ya
shigo wayarsa.
Ya mike zaune a tsorace yana mayar da numfashi saboda jin kidan da yayi, kidan da ya saka mata ne. Ya
dauki wayar da sauri yana kallon screen din "Baby Dove" yaga sunan ta rangadadau a jiki. Cikin
karkarwar hannu yayi sliding ya dauka tare da saka wa a kunnen sa, bracing himself for anything, maybe
ma ransom za'a nema or worst.
Amma sai yaji muryar diyarsa, hasken idaniyar sa "Daddy?"
Ya mike tsaye kamar wanda akayi wa allura
"Yasmin! Baby girl is this really you? Oh my God!"
"Daddy ka zo ka dauke ni, ni gurinka nake son tahowa bana son gidan nan" ta fada kamar zata yi kuka.
Yaji kamar zuciyar sa zata fito, kalmomin sun makale ma sun ki fitowa
"A ina kuke? A ina kuke Yasmin ki gaya min yanzu zan zo in taho da ku, are you okay? Ina Asad? Lfy lau
kuke?"
Tace "lafiya lau muke Daddy, amma ni da Asad muna kuka kullum, mommy ma tana kuka a toilet, kuma
tace ba zamu dawo ba. Shine yanzu ta fita gurin kawarta na dauko wayarta a jaka na kirawo ka kazo ka
tafi da mu"
Ya lumshe idonsa ya bude, baya jin akwai wani abu da za'a gaya masa a rayuwa da ya kai wannan dadi,
na farko they are okay, na biyu mentioning