Chapter 67 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   67 / 101

198K to 201K   out of 300.2K words

kuma san me zanyi ba, amma ba zan koma gida ba har sai na tabbatar Abba yayi laushin da idan
na koma zai tsaya ya saurare ni sannan kuma ya tsaya min akan maganar kamar yadda ya kamata iyaye
suke tsayawa yayansu da suke cikin irin halin da nake ciki.



Gari yana fara wayewa Yasmin da Asad suka tashi, saboda sun riga su saba da tashi da sassafe saboda
makaranta. Sai a lokacin tunanin makarantar su yazo min? Ya zanyi da karatun su? Na girgiza kaina, dole
su hakura da karatu for now har sai al'amura sun warware mana, dan rashin karatun nasu a yanzu yafi
musu alkhairi akan cigaba da zama da babansu, dan tabbas suna tare da Umar watarana zai iya neman
mace a gabansu, ko kuma worst.



Nayi saurin kawar da maganar daga raina sannan na shigar dasu toilet nayi musu wanka na sa suka yi
alwala suka fito na mayar musu da kayan jikinsu tunda basu da wasu kayan sannan suka yi sallah.



"Mommy yau ba zamu je school ba?"



"Mommy daddy ne zai zo ya dauke mu daga nan gidan ya kaimu school ko?'



"Babu school, anyi hutu"



Na fada shortly
Asad ya fara tsalle yana murna, Yasmin kuma ta zauna kawai tana kallona ni kuma nayi kamar ban ganta
ba na cigaba da jan charbin hannuna ina yiwa Allah kirari tare da neman taimakon sa.



Bamu jimada tashi ba Diyam ta shigo, muka gaisa su Yasmin ma suka gaishe ta sai na tsokane ta "kika
tashi da sassafe kika taho nan kika bar mijinki ko?" Tayi murmushi "lah! Baya gari ai, yaje Maiduguri, da
yana nan ai da tun jiyan kun gaisa. Sai gobe nake saka ran dawowar sa"



Nace "Allah ya dawo dashi lafiya"



Sai ta kawo min kayan da nake tunanin nata ne ta ce in saka, "yara kuma na yi waya za'a kawo musu
kaya" nayi saurin cewa "da kin gaya min ai da sai in bayar da kudin" ta harare ni "yayan nawa in zan siya
musu kaya sai na karbi kudi a hannunki?" Nayi murmushi kawai tare da yi mata godiya amma bata amsa
ba.



Tare muka fita, ta kai yara falo ta kunna musu TV sannan muka shiga kitchen muka yi breakfast tare,
tana tabani labarin karatun da take yi a Oxford, "nan bada dadewa ba in sha Allah zan dawo Nigeria
gabakidaya a matsayin lauya mai kare hakkin mata, insha Allah wannan shine burina, in share hawayen
duk wata mace da take cikin halin kunci, in taimaka wa duk wata macen da namiji ko iyaye, ko al'umma
suka danne mata hakkin ta, in fadakar da mata su san menene hakkokin su su kuma san abinda ya
kamata suyi idan an danne musu hakkinsu, su san me ya kamata su dauka su san menene bai kamata su
dauka ba. Wannan shine mafarki na. Wannan shine burina"



Nayi shiru ina tunanin wannan dogon buri na Diyam, sai nace "Allah ya baki sa'a akan abinda kika saka a
gaba, amma babbar magana ce kika dauko Diyam, aikin ba karami bane ba bana jin zaki iya yi ke kadai
dole sai kin samu hadin kan su matan da kike so ki taimaka wa din, some will rather die a gidan miji akan
su bujirewa aure saboda sun riga sun saka akan su cewa sai a gidan miji zasu iya rayuwa, suna ganin sai
da namiji zasu iya rayuwa su ba zasu iya defending da kansu ba, wasu kuma sunyi believing kamar zama
a gidan mijin shi zai kai su aljanna, sun manta cewa ba wai yin auren ne yake kaiwa aljanna ba, a'a
abinda ake yi a cikin auren ne either ya kai mutum aljanna ko kuma ya dangana shi da wuta"



Ta gyada kai " shi yasa suke buƙatar enlightenment, a fadakar dasu tare da nuna musu abinda ya kamata
su dauka a addinance da constitutional rights, da kuma abubuwan da basu kamata su dauka ba dan zai
zama illa ga either physical ko mental health dinsu, ko kuma ya zamo illa ga tarbiyyar yayansu, ko kuma
ya zama illa ga addinin su dan wani auren zai kai mace wuta ne instead of aljanna"
Nayi shiru ina kallon ta amma ban ce komai ba sai ta cigaba "Duk auren da rashin zaman lafiyan cikin sa
ya kai matsayin da mace zata ke daga muryar ta sama data mijinta, wani lokacin har ta kai da duka ko
zagi ko cin mutuncin, ko ta ke gudun sa a gado, ko ta mayar da shi dashi da babu duk daya ne a gurinta,
to wannan auren a ganina matar da take cikinsa hanyar wuta ta kama bata aljanna ba"



Nayi shiru ina tuno marin da nayi wa nawa mijin jiya. Amma da nayi marin ma ba wai huce wa nayi ba.
Meaning akwai matan da in ransu ya baci irin haka suke abinda yafi mari, na tuno da matan da suke
kashe mazajen su har lahira.



Sai naji Diyam ta cigaba da cewa "kinga akwai wadda naji labari, wai mijinta neman mata yake yi tayi tayi
ya daina yaki dainawa sai kawai tace ita ta sallama shi ta bar wa duniya shi, yaje yayi ta neman matansa
amma ita ba zata kwanta dashi ba, za dai ta cigaba da zama dashi a matsayin matarsa saboda kar ta fita
al'umma su ce mata bazawara. Tun mijin yana binta yana nemanta har ya hakura shima ya barwa duniya
ita. To Yanzu menene amfanin wannan auren? Wacce aljanna mai wannan auren take tunanin tana
nema a cikin auren?"



Nace "most of mutanen yanzu ba dan neman aljanna suke yi komai ba, most of them dan duniya sune yi,
dan duniya ake zaman gidan auren dan duniya iyaye suke matsawa yayansu kar su fito daga gidan miji,
saboda kar duniya ta zage su, saboda kar su kunyata a idon makiyan su" na fada ina tuno da tawa uwar.



Sai Diyam tace "haka ne, wasu kuma ba dan haka ba. Wasu kuma dan rashin madafa ne. Mijin nan shine
yake yi musu komai maybe har iyayensu shine yake yi musu komai idan suka rabu dashi, bar ta gurin
zama, hatta abincin da zasu saka a bakin su gagararsu zai yi, sannan yayansu dole ko da ace sun san right
din su na cewa yaya su addini ya bawa rikon su ba miji ba, amma rashin inda zasu ajiye yayan da abinda
zasu ciyar da su dashi, da kuma tunanin zasu rasa wani mijin idan suka fito da yaya dan ba kowanne
namiji ne zai aure ki ya haɗa da yayanki ba, to wannan tunanin shine yake time su saisu zauna da sunan
zaman hakuri, amma in reality ba wai zaman hakurin suke yi ba fa, zaman babu yadda zasu yi suke yi"



Nayi shiru ina tunani, a raina ina lissafin to ko irin wannan zaman ne Aunty Afia tayi? Sai na tambaye ta
"to yanzu menene kike ganin mafita ga irin wadannan matan?"
Tace "mafita shine su nemi abinyi, ko aikin yi ko sana'a, na farko in suka samu abinyi ba zama su dora
ransu sosai akan mijin ba har wani abun nasa yadame su, damun da har zasu kai ga sainsa ko akai ga
daga murya ko zagin da har za'a samu alhaki. Na biyu su kansu mazan in kina da abin hannunki bakya
yawan ce masa bani bani to zaki ga bai fiya daga miki kai da fushi da sauran su ba, musamman ace kina
dan taimaka masa da wasu abubuwa na gida, kin san nauyin nan shine wani lokacin yake kufular da
maza su zo suna ta fadan babu gaira babu dalili, amma misali ace bai kawo cefane ba, ya dawo yana
tunanin zaki yi masa mitar cewa bai kawo cefane ba sai ya tarar har kin siyo kinyi girkin kin kawo masa
abincin, tabbas zaki ga yadda zai ji dadi, zaki ga yadda ko kinyi wani karamin laifi shima zaiyi overlooking,
dan haka samun abinyi ga mace yana kara zaman lafiya sosai a gidan aurenta. Kuma in the case if
extremist maza wadanda ba'a iya musu, da kuma masu manya manyan laifuka kamar zinace zinace da
shaye shaye, luwadi, da sauran manyan laifukan da ko a addini zama dasu bai halatta ba, idan mace tana
da abinyi rabuwar ma zata fi zuwa mata da sauki tunda tana da yadda zata kula da kanta da yayanta,
kuma su kansu iyayen, da yawa daga cikin su tsoron responsibility ne yake sakawa su bar yayansu suyi ta
shan wahala ba wai dan basa son su ba, amma in kina da shi zaki ga sai sun fi supporting dinki, kuma ko
wani auren ne yazo mijin ba zai wani damu da rikon yayanki ba tunda yasan kina da abin da zaki rike
kayan ki. Wannan duk ina magana ne akan idan ubansu bai sauke nauyin su ba, dan a shariance idan
aure ya mutu uwa za'a bawa rikon yaya, shi kuma uba za'a saka masa kudin da zai ke bata duk wata ko
duk sati na ciyarwa da sauran hidindimun yayan nasu, idan tana da ciki ko tana shayarwa har da nata
hidimar"



Nayi shiru ina kallon bango, ina jin idonta akaina tana kallona, sai na juyo ina kallon ta nace "akwai
matan kuma da baki fada ba, su kuma suna da yadda zasu rike kan nasu kuma sunada ilimi sun san rights
din su sai dai, sai dai halin mijinsu, halin da ya saka suke son rabuwa da shi, abu ne da ba zasu iya fada ba
dan zai zama bakin fenti bawai a kansa shi kadai ba har ma da kansu da kuma yayansu. Su kuma me zasu
yi kenan?"



Diyam tayi shiru tana kallona sai kuma ta kama hannuna tace "zo muje mu ci abinci, then you can tell me
all about it, and together, we can find a solution insha Allah"




Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din



0779484494

Nafisa Tafida Usman
Access Bank



Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp

08067081020



Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020



Please banda kira, WhatsApp only



*From the readers*



Assalamu alaikum.



Ina so in bawa masu karatu labari na tare da fatan wata zata dauki one or two lessons from it. Nayi
rayuwa a baya kusan irin ta Jidda. Allah ya jarabce ni da miji mai irin halin Umar. Sai dai kuma ni din na
kasance an extreme introvert. Bana iya magana, bana iya yin bayani, bana iya gayawa kowa abinda yake
zuciyata. I find it hard to express myself ko mai kusancin da muke da mutum. Shi yasa bayar da wannan
labarin yanzu yake min wahala. Ina kuma tunanin hakan ya samo asali ne tun daga kuruciyata da yanayin
yadda rayuwata ta kasance tun lokacin yayena, but that is a story for another day. Wannan yasa duk
tsahon shekarun nan da nayi da mijina a cikin wancan halin babu wanda ya sani, cikin yanuwana ko nasa
babu wanda yasan halin da muke ciki sai nayi ta boye bakin ciki a zuciyata.

Wannan ya jawo idan ya aikata abin da yake aikatawa kuma na kamashi nakan hada shi da wanda shi
kadai ya sani, na kan yi masa Allah ya isa. Daga baya bayan munyi shekaru a cikin wannan yanayin har
mun hayayyafa sai Allah ya dora masa lalura, paralysis, rabin jikinsa ya shanye, bayan paralysis din kuma
akwai sauran cututtuka da yake fama dasu, nima kuma haka.

To sai nake ganin kamar Allah ya isan da na ringa yi masa ce ta kama shi, tunda ya zalince ni kuma Allah
yana karbar addu'ar wanda duk aka zalinta.
Sai dai kuma......lalurar sa sai ta zamanto ni ta fi affecting akan kowa, tunda ni ce matarsa kuma uwar
yayansa dan haka yanzu ni nake zaune da shi nake jinyarsa for over 10+ years, nauyin sa da na yayan mu
da jikoki duk suna kaina yanzu, kuma nima ba lafiyar nake da ita sosai ba.



Wannan ita ce rayuwata a yanzu, ba kuma zan iya rabuwa da shi ba saboda yayan da suke tsakanin mu
ba zasu yarda in tafi in bar mahaifinsu a cikin halin da yake ciki ba, jama'a ma kuma zasu zage ni in na tafi
za'a ga kamar dan lalurar da yake ciki ne.

Amma duk wannan abin da ya faru, duk wannan halin da muke ciki, shekarun baya da ya dan samu sauki
sai dana gani a wayarsa wani abokin sa ya turo masa number din wata tsohuwar karuwar sa da muka sha
rigima da shi a kanta a baya.

Wani lokacin sai inyi wa kaina tambaya ko wannan ita ce rayuwa ta? Ko kuma akwai light at the end of
the darkness?



Allah ne masani.




*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi
sharing, idan kika yi kinci amana kuma ke da Allah*



*Be Safe*



Tare muka ci abinci da ita ya su Yasmin, though Yasmin kadan ta ci sai tace ta koshi, sai Diyam ta saka
aka tafi dasu dakin babbar yarta Subay'a tace su je suyi wasa a can. And then we sat down, ta bani
dukkanin hankalin ta tana jira in bata labarina but kamar kullum I became tongue tied, nayi ta juya
maganar a raina na rasa ta inda zan fara mata. Can I even trust her?



Bata yi rushing dina ba ta barni na gama lissafe lissafe na sannan na fadi kalmar da ba yau na saba
fadarta ba amma har yanzu tana da nauyi a harshe na kuma ta na da zafi a zuciyata. Nace "Diyam.
Mijina. Umar. Mazinaci ne"
Sai ta sunkuyar da idonta kasa tana kallon hannuna da ta rike a cikin nata, kamar ba zata yi magana ba,
amma fuskar ta ta nuna tsananin tashin hankalin da magana ta ta saka ta a ciki, sai kuma tayi gyaran
murya kadan sannan tace "kin tabbatar? Zina kike nufi ko kuma dai kwashe kwashen yammata irin na
mazan wannan zamanin?"



Na girgiza kaina "zina nake nufi Halima. Wallahi ni da ace Umar yammata ne yake yi kawai irin na
soyayya, ko kuma ma ace auri saki yake yi ko da kuwa nawa zai aura wallahi bana jin zan ji abinda nake ji
yanzu a zuciya ta. Ni da zaiyi aure da sai nafi kowa jin dadi, bana jin ko amaryar da zai aura zata kaini
murnar auren sa, amma yaki auren, but it doesn't matter anymore. Na gama auren sa ni kam yanzu, ko
yayi wani auren ko kuma ya je yake kwanciya da duk karuwan da suke Nigeria matsalar sa ce ba tawa
ba"



Na karasa ina tuno da yara na guda biyu da suke daki suke wasa, yaran da na haifa tare da shi, sai na ji
sabbin hawaye sun zubo min.



I can't even say that, can I?



Ta kama hannuna sosai ta rike tana kokarin hana kanta biye min muyi kuka tare "uhm uhm Jidda, kar ki
ce haka dan Allah. Kuskure ne babu wanda ya wuce yayi kuskure, kaddara ce babu wanda bata hawa
kansa, na tabbatar mistake ne yayi, ko kuma ma ke ce kika yi mistake din ba wai abinda kike tunani bane
ba, watakila ma rashin fahimta ce kuka samu. Insha Allah in yayi miki bayani zaki fahimci cewa ba abinda
kike tunani bane ba"



Sai na samu kaina da yin murmushin takaici "you sound so much like him da kika fadi wannan kalmar,
kullum abinda yake ce min kenan farko idan na kama shi da wannan laifin "Jidda ki saurare ni, I can
explain, ba abinda kike tunani bane ba. But har yau ge never really did explain. Har yau abinda nake
tunani din shine dai nake tabbatar wa. And yes, na tabbatar, ba sai daya ba ba sai biyu ba ba sau uku ba
ba sau hudu ba, wadannan kuma wadanda na sani kenan, and he is so good at covering up and at
pretending dan haka Allah ne kadai yasan yawan affairs din sa wadanda ban sani ba kuma maybe har
abada ba zan sani ba. Bana so ma in sani din. Dan na gama aurensa. Matsala ta daya shine yadda zan
rabu da shi a yanzu. Yadda zan samu ma iyayena su tsaya su saurare ni kuma su fahimce ni sannan su
goya min baya su karbo min takardar saki na daga hannunsa shine problem dina a yanzu Diyam, ba wai
yadda zan bullo masa ya daina zina ba dan na riga na rufe wannan page din and with him in it. Kuma son
samu na shine rabuwar tamu ta kasance ba tare da bayyanar wannan mummunar dabiar tasa ba, ba
waidan shi ba sai dan yayana da na haifa da shi. Diyam ya zanyi? Ki gaya min ya zanyi?"
Sai ta saki hannuna ta tashi. Ina ganin yadda idonta yayi ja amma bata ce min komai ba sai ta shiga wata
kofa. Ta dan jima a ciki sannan ta fito, daga yadda fatar idonta ta tashi na fahimci zuwa tayi tayi kuka a
bayan idona. Sai na fahimci cewa itama har yanzu tana da halin ta na saurin kuka kenan. Na tuna lokacin
da muke hada kai muyi ta kuka a jss1, ko da kuwa abinda akayi mana bai kai na kukan ba.



Sai ta zauna a kujerar kusa da ni sannan tace "kin tabbatar da abinda kike fada? I mean ba zargin sa kike
ba kin tabbatar?" Ban kalle ta ba nace "in by tabbatar wa kina nufin na taba kama shi turmi da tabarya to
amsa ta "no" ce, in kuma kina nufin na tabbatar a zuciya ta cewa yana yi to amsa ta "yes" ce. Bayan haka
kuma shi da bakin sa ya tabbatar min da cewa yana yi din, ya sha karbar laifin sa ba sau daya ba ba sai
biyu ba. Daga baya ma ya tabbatar min da cewa shi sex addict ne, sai kuma yayi min alkawarin cewa
yana iyakacin kokarin sa na ganin ya daina. But kusan shekari biyar kenan da yi min wannan alkawarin,
amma bai daina ba, saia kara gaba da yake yi"



A hankali naji ta ambaci "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Yanzu Jidda kina nufin shekara da shekaru kuna
cikin wannan halin amma ko iyayen ki basu sani ba? Jidda so kike hawan jini ya kama ki ki mutu yayanki
su zama marayu?"



Na dan yi murmushin ganin yadda hankalin ta ya tashi sannan nace "hawan jini na nawa kuma Diyam? Ai
na jima da hawan jini. Zuciyata ce kawai nake jira ta buga in mutu din, wannan kuma shine dalilin da
yasa nace na gama, saboda yayana. Dan kar nayi musu asarar kaina kuma dan kar nayi musu asarar
rayuwar su. Dan cigaba da zama da Umar tabbas tamkar na zuba rayuwar yayana a faifai nayi watsi da
ita ne. Diyam mai aikina ya nema. A cikin gidana. Gidan da yayana suke ciki"



Na karasa maganar ina rufe fuskata da hannaye na tare da rushewa da kuka, zafin abin yana dawo min
zuciyata sosai kamar yanzu ne Asabe take gaya min cewa ya neme ta.

67 / 101