Chapter 85 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   85 / 101

252K to 255K   out of 300.2K words

girman maganar a bakina ba, na bashi
labarin case din Mammy ban boye masa komai ba har abinda Mammy ta fada min na maganar asiri da
kuma abinda na tone da hannu na da kuma shi abinda Faruq ya gaya min na cewa bai san duk abinda ya
faru a tsakanin su ba. Na kara da cewa



"Wannan shine daya daga cikin dalilin da yasa na cigaba da zama da Umar bayan abinda ya faru, na farko
saboda na tabbatar asiri Hajiya tayi masa dan ta raba ni da shi ta saka jikarta dan tana ganin kamar cikin
jin dadi nake, na biyu kuma saboda bana son maganar ta fita, dan in maganar nan ta fita to zata ruguza
dan kwanciyar hankalin da yake tsakanin mu da yanuwanmu, kuma bani da shaidar da zan nuna cewa
asiri aka yi masa dan haka na tabbatar Hajiya zata tabbatar tayi amfani da maganar wajan bata sunana
da sunan yayana har zuwa girman su. Sannan kuma bayan faruwar hakan Umar ya shiga tashin hankali
da kuma nuna min kamar yayi nadamar gaskiya, sai na dauka rabon shiriyar sane ya saka abin ya faru, sai
na kuma bashi dama tare da fatan cewa zai zama na karshe duk kuwa da cewa zama da shi bayan sanin
abinda ya shiga tsakaninsu da Mammy ba karamin tashin hankali bane ba a gare ni. But I did it"



Sai kuma na bashi labarin Asabe, tun zuwanta gidan mu da kuma abinda naji daga bakinta da kuma
abinda naji daga bakin shi Umar din.



Yayi shiru idonsa a kasa yana kallon kafafuwan sa, sai kuma yace "na jima ina tunanin cewa mata
karamar kwakwalwa ce dasu basu da zurfin tunani, na jima ina ganin mata a matsayin masu raguwar
zuciya, saurin gazawa da kuma korafi, wannan shine ya sa ka nake kin saurarar yayana mata akan duk
wani korafi da zasu zo min dashi daga gidajen mazajen su, gani nake in na biye musu ba zasu yi zaman
aure ba, zasuyi ta kashe auren su ne akan abubuwa marasa ma'ana ballantana tushe, na dauka hakan da
nake yi ina basu kariya ne daga rudin zamani, a yau a fahimci cewa abinda na ke tunani ba haka bane ba,
a yau na tabbatar mata ba kananan kwakwalwa ne dasu ba dan Jidda zurfin tunanin da kika yi ba
kowanne namiji ne ma zaiyi irinsa ba, hakurin da kika yi da kawar da kai ba kowa ne zai iya irinsa ba.
Allah yayi miki albarka. Allah ya shiga lamarin ki ya zaba miki mafi alkhairi a rayuwar ki"



Nace "ameen" sai ya mike yace zai koma gida ya turo min Farhan da Amira su taya ni harkar asibiti, ni
kuma sai na lissafa masa abubuwan da nake bukata waɗanda zasu taho min da su.



Bayan ya tafi sai na zauna na fara tunanin Abba da iyaye ire-iren sa, they thought they are doing what is
best for us, kuma tsoronsu ne ya saka bama iya sakin jiki mu gaya musu magana dan muna ganin ko
munyi ba zasu saurare mu ba, but if we find a way to tell them zasu fahimta, kuma insha Allah a karshe
za'a samu fahimtar juna dan suna son mu kamar yadda kowane iyaye suke son yayansu, kawai dai basu
iya nuna soyayyar bane ba kamar iyayen zamani.



Bai jima da fita ba Umar ya dawo, daga alama daga masallaci yake, ya dawo gaban Yasmin ya tsaya yana
kallon ta ya sunkuya yayi kissing goshinta sai kuma ya dauki takardun bills din da na ajiye a gefe ya juya
zai fita, har ya kai bakin kofa kuma sai ya dawo ya bude jaka ta ya dauki ATM card dina ya sake fita.



Na bishi da kallo ina lura da yadda yake tafiya kamar zai fadi. Sai kuma na tashi na shiga toilet nayi alwala
na fito nima nayi sallah. Ina idarwa su Farhan suka shigo tare da wani da ban gane ba, har da kayan
dubiyar sa a leda ya kawo wa Yasmin sannan yayi min ya mai jiki ya tafi, bayan ya tafi ne Farhan ta gaya
min wai sunan sa Sadiq, suka duba Yasmin tare da jajanta abinda ya faru da kuma godiya ga Allah da
abin ya tsaya a haka, muna tare kira ya shigo wayata daga Aunty, na dauka ta tambayeni asibitin da
muke na gaya mata tace gasu nan zuwa ita da Baba, nayi mamaki saboda nasan shima Baban ba lafiya ce
da shi ba.



Kafin su zo ne Umar ya dawo daga siyan magani, yana tafiya yana dafe bango kana ganin sa kasan ba
lafiya ce dashi ba sai na tashi na karbi ledar hannunsa na fara yi masa fadan cewa shima fa bashi da
lafiya har da shi aka bawa gado, kafin in karasa fada na ya fado jikina, saura kadan mu zube a kasa gabaki
daya sai na rike shi da kyar na karasa da shi gadon da aka kwantar dashi, na kuma tura Amira ta kira
ma'aikatan asibitin.



Ina kwantar da shi ya rike hannuna ya dora shi akan kirjinsa, ina jin yadda jikin sa yayi zafi sosai kamar
ana gasa nama. Yana magana a hankali amma ban ma ji mai yake cewa ba kuma bani da niyyar sake
tambayarsa dan ban damu da inji din ba, sai da nurse ya shigo sannan na zare hannuna daga cikin nasa
na kuma gaya wa nurse din cewa in ba allura yayi wa Umar ba to ba zai kwanta ba, kuma zai iya faduwa
in yana yawo.



Bai jima da yin bacci ba Baba suka shigo tare da Aunty, na tausaya halin da naga Baba a ciki, na durkusa
har kasa na gaishe shi ya amsa tare da tambaya ta abinda ya faru ni kuma na bashi labarin kiran da
police suka yi min da kuma abinda suka ce min, Aunty sai ta fara kuka "mun shiga uku mun lalace.
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ta fada tana dafe kan Yasmin da ta dan bude ido kadan tana kallon su.
Baba ya ja kujera ya zauna yana ambaton hasbiyallahu wa nieemal wakeel. Sai duk suka yi tagumi suka yi
shiru suna tunani, jimawa can Aunty tace "har yanzu kuma su Mama babu wanda yake daukan waya, ko
kunyi waya da Mufida?" Na girgiza mata kai kawai. Baba ya juya yana kallon Umar yace "shi kuma
wancan fa? Me ya same shi shi kuma?" Nace "faduwa yayi ana gaya masa maganar, shine suka bashi
gado ya dan huta" ya gyada kai yace "shi namiji shine da faduwa ke mace ke ce a tsaye? You really are a
very strong woman Jidda, da wasu matan ne da yanzu sun cika asibitin nan da koke koke da fadar
maganganu marasa dadi, amma ke ga ki nan a tsaye akan yar ki har da sokon babanta da ya kasa daukan
kaddara"



Nayi murmushi ina jin dadin yabon da yayi min, amma kuwa anya ni din strong woman ce? Ni da ko
mutum na gani yana kuka sai na taya shi ko da kuwa bansan dalilin kukan nasa ba, ko dai wannan ma is
another kind of strength?



Muna cikin jajanta maganar sai wayar Aunty tayi kara, a lokacin already ana kiraye kirayen sallar ishai, ta
kalli wayar tace "alhamdulillah, ga Mubaraka nan tana kira na maybe sunyi waya da Mama" duk muka yi
shiru muna sauraron ta ta daga wayar "Mubaraka" sai kuma ta bude ido tare da saka salati "asibiti
kuma? Mun shiga uku" "to gamu nan zuwa, yanzu kuwa".



Ta dago kai tana kallon Baba, yace "what now?" Ta hadiye yawu tace "Mama ce, wai ashe ta fadi ne a
gidan bikin da suka je da Mufida, ashe wai tun dazu suna asibiti da ita, sai yanzu mufidan ta kira
Mubaraka ta gaya mata, yanzu mubarakan taje gurin su shine ta kira ni".



Nan take wani tashin hankalin ya karu akan wanda already ake ciki, a karshe sai Baba yace da Aunty taje
ta nema wa Yasmin da Umar transfer zuwa asibitin da Mama take, sai mu tafi can kawai gabaki daya
tunda yana ganin can din ma zasu fi samun kulawa tunda private hospital ne. Babu jimawa aka gama
komai aka yi releasing din mu muka tafi a ambulance din asibitin, su kuma su Baba suka biyo bayan mu a
mota. Muna zuwa aka sake duba Yasmin aka sake tabbatar mana da cewa ba'a taba ta ba, suka kuma
bamu dakin da da zamu kwana saboda suna so suyi monitoring dinta sosai saboda buguwar da tayi a
kanta dan su tabbatar babu wani internal injury. Ni dai daga nan ban san ya suka kare da Umar ba, ban
kuma bi ta kan Mama ba na tafi na cigaba da kula da ƴata, su Farhan ma suka yi min sallama suka tafi da
driver din su Baba zasu biya gidan su dauki Asad sannan su tafi dashi gida sai da safe zasu dawo.



Sai da na nutsu sannan nayi waya da Umma na gaya mata abinda ya faru, na tabbatar mata babu abinda
ya samu Yasmin sannan bayan munyi sallama sai na kira Diyam itama na gaya mata, hankalin ta ya tashi
sosai tayi min jaje sannan tayi min alkawarin zata shigo da safe ta ga jikin Yasmin. Daga nan sai na tashi
nayi sallah nayi godiya ga Allah tare da adduoin neman cigaba da kariya daga dukkan masifu. Har zan
kwanta sai na gwada number din Mufida dan inji jikin Mama tunda ance tare suka zo asibitin, sai dai
wayar tata bata shiga ba, sai na kira Aunty ita kuma tace min jikin da sauki duk da dai har lokacin basu
san abinda yake damunta ba, likitoci dai suna tunanin firgita tayi amma basu san abinda ya firgita ta ba.



Kafin in kwanta na samu Yasmin ta tashi na dan bata juice da biscuit a cikin kayan da saurayin Farhan ya
kawo mata, ta dan ci kadan sai ta koma ta kwanta amma sai ta kasa baccin tace sai dai in taho kan gadon
mu kwanta tare, dole na katse duk abinda nake yi na kashe fitila ba hau gadon muka kwanta tare ta
kankame ni ta cusa kanta a kirjina tana ta sauke ajjiyar zuciya cikin tsoro. A haka bacci ya dauke mu.



Sanda na farka dare yayi sosai, ina kokarin mikewa naga Umar akan sallayar da nayi sallah akanta, nayi
mamakin yadda akayi ya shigo ama sai na tuna banyi locking kofar ba, sai dai na koma na kwanta. Next
farkawa da nayi sai na ganshi a zaune a gaban gadon da muke kai hannayensa rike dana Yasmin, duk da
duhun dakin sai da na fahimci yadda idanuwansa suka kumbura kuma suka yi ja. Na jima ina kallon sa ba
tare da ya lura ina kallon sa ba, sai kuma na juya na cigaba da bacci na.



*Baba*



Tunda yaji zancen Mama tana asibiti hankalin sa ya tashi, babu abinda yake sai innalillahi wa inna ilaihir
rajiun a haka har suka zo asibitin da take din. Sai da ya yi komai ya kammala da jikarsa da dansa ya
tabbatar ya hada su da doctors din da zasu gansu sannan ya nemi Mubaraka a waya ita kuma ta kai shi
dakin da Mama take. Mufida tana kofar dakin da Mama take ciki ta hada kai da guiwa, sai yaga ta juye
masa gabakidaya ta zama kamar ba mufidan da ya sani ba, duk ta firgice ta rikice.



Ta gaishe shi, yayi mata fadan dalilin da yasa bata daga wayarta ba duk kiran da akeyi mata kuma bata
fada cewa Mama ba ta da lafiya ba tun azahar sai dare. Sai tayi masa karya da cewa ta bar jakankunan su
ne a mota kuma wayoyin suna ciki kuma ba zata iya fita ta dauki ba tunda babu kowa a gurin Maman.
Daga yadda take maganar ya san karya take yi amma bai musa mata ba sai ya shiga ciki.



Kamar yadda Mufida ta chanja haka ya ga Mama ta chanja masa, yaga kamar tayi wani tsufa tayi kamar
wadda ta shekara babu lafiya duk kuwa da cewa idonta a rufe yake. Ya tambayi Mubaraka abinda
Doctors suka ce sai ta maimaita masa abinda ta fadi a waya "sunce kamar ta tsorata ne kawai, amma
lafiyar ta kalau, sai jininta da suka ce ya hau itama. Kuma tunda nazo take ta fitgita tana kiran Umar wani
lokacin kuma ta kira Mufida, in ta farka kuma sai ta kama kuka. Dazu data farka kuma kai take nema tace
in kira ka"
Baba ya zauna a gaban gadon yana kallon fuskar ta tare da ambatar sunan ta "Maryam. Maryam gani
nazo. Menene ya faru?"



Ta dan bude idonta a tsorace ta kalle shi sannan ta kalli dakin "ina Umar? Ina Mufida?" Baba ya kalli
bayasa shima a dai dai lokacin da Mufida ta juya da sauri ta fita daga dakin, ya dawo da kallon sa kan
Mama yace "ba sa nan. A kira wo miki su?" Sai ta mayar da idonta ta rufe tare da girgiza kai sai kuma tayi
wa yaya Mubaraka magana "jeki waje ki bamu guri", sai bayan da ta fita sannan ta dawo da hankalin ta
kan Baba da ya riga ya gama rudewa tace "magana nake so muyi, ina so in nuna maka irin tarin nadamar
da take tare da ni akan kuskuren da nayi a tarbiyyar yayanmu, wanda kuskuren nawa shi ya jawo
tarbiyyar su ta gurbata, gurbata kuma mafi muni" ta fada hawaye yana zuba a idonta.



Sai ya rike hannunta yace "uhm uhm, ba laifin ki bane ba. Ni nafi kallon abin a matsayin laifina. Da ace na
zauna tare da yayana na taya ku tarbiyyar su na taya ku saka ido a kansu da Umar bai zama abinda ya
zama yanzu ba. Ana gaya min kin fadi a gidan biki dama maganar dana kawo a raina kenan, na san wani
abu ne da ya danganci halayyar Umar kika ji ko kika gani. Ki gaya min Hajiya Maryam, mai kika ji? Mai
kika gani?"



Ta rufe idonta tana kokarin cire munanan hotunan yayanta daga zuciyarta tace "abinda na gani ina fatan
kar Allah ya nuna maka shi. Abinda na gani ina fatan babu wata uwa da zata kuma ganin irinsa a duniya,
ko da kuwa uwa ce irina mai take laifin yayanta saboda son zuciyata" Baba yace "inna lillahi wa inna
ilaihir rajiun. Maryam ki gaya min abinda kika gani" tace "har abada bakina ba zai furta abinda na gani
ba, zan tafi da shine zuwa kabari na. Kafin mutuwa ta kuma Zan dauki abinda na gani a matsayin darasi,
babban darasi a gare ni da zai saka in gyara halaye na, in sauka daga kan hanyar da nake kai ta son kai da
son zuciya in koma kan hanyar gaskiya ko Allah zai dube ni ya taya ni gyaran yayana"



Baba yace "ƴaƴan ki? Ko dai dan ki kike so ki ce?" Ta girgiza kai. "Yayan mu Alhaji Muhammad. Yayan
mu. Zina tayi naso a cikin zuriar mu. Dole sai mun tashi tsaye dan ganin mun dakile ta in ba haka ba zata
mamaye mu gabaki daya ba tare da mun sani ba"



Ya saki hannunta ya dafe nasa kan yana jujjuya shi kawai cikin tashin hankali. Ta sake kamo hannunsa
tace "ni yanzu alfarma nake nema a gurin ka. Dan Allah. Ina so ka samo wani babban mutum mai
mutuncin wanda ka san yana ganin darajar mu kuma zai rike mana amanar mu, ina so ka daura wa
Mufida aure a cikin satin nan"
Ya bude idonsa yana kallon ta tashin hankalin sa yana karuwa yace "Mufida? Hajiya mai kika gani?
Mufida kika gani da Umar?" Ta girgiza kanta "Mufida na gani da Umar, amma ba irin ganin da kake nufi
ba. Ni dai dan Allah kayi min wannan alfarmar, ka samu tsayayyen namiji wanda ba zata gagare shi ba.
Ka daura mata aure a cikin satin nan".



Ya sunkuyar da kansa kasa, baya bukatar ta gaya masa cewa abinda ta gani yana da dangantaka da cewa
Mufida ita ma ta bi layin Umar.




Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din



0779484494

Nafisa Tafida Usman

Access Bank



Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp

08067081020



Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020



Please banda kira, WhatsApp only



*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi
sharing, idan kika yi kinci amana kuma ke da Allah*
*The Letter*



Da asuba da na farka Umar baya dakin, sai na tashi nayi alwala nayi sallah, ina cikin adduoi na ya sake
shigowa, nayi shiru ina jin haushin dalilin da yasa zai ke shigo mana daki bayan nasan shima an bashi na
sa.



Ya sake komawa kan kujerar da nake tunanin akai ya kwana, ya zauna tare da kife fuskar sa a kusa da ta
Yasmin, sai na gyara zamana akan sallayar na cigaba da azkar dina sai kuma naji muryar Yasmin tana
magana cikin tsoro "mommy! Mommy" na mike da sauri na tafi gurinta a lokacin da shima Umar yake
mikewa daga zaunen da yake yana rike ta. "Mamana! Mamana! Daddy is here. I am here"



Ta zagaye hannunta a wuyansa tana jera ajjiyar zuciya, na karasa kusa da su ina shafa bayanta ina tofa
mata duk adduoin da suka zo bakina. Sai kuma ta dago kai tana kallona sannan ta saka kuka "mommy! Ni
ba zan koma gidan Mama ba tunda tafiya tayi ta bar mu kuma Asad yake ta kuka wai zai taho gurinki,
shine na ce ya zauna inje in kira daddy ya kai mu gurin ki, shine kuma ban ga daddyn ba shine na fita
waje ina neman sa, shine wani yace inzo ya kaini gurinsa, kuma bai Kai ni ba sai ya kaini want guri kamar
gidan dodo, Ni kuma nayi kuka nace ya kaini gurinsa daddy na, shine ya ke dukana wai in daina kuka,
kuma... kuma...kuma shine ya daure min hannuna, shine nake kuka ina kiranki kizo ki hana shi duka na,
kuma baki zo ba, kuma daddy ma bai zo ba....kuma ni ban san me nayi masa ba, daddy me nayi masa?"



Ta fada tana kallon Umar, ya saka hannu ya goge mata hawayen fuskarta yace "Babu abinda kika yi masa
daughter, shi din azzalumi ne kuma sai Allah ya saka miki kinji?" Ta gyada kai tana kallona kamar mai
jiran taji abinda ni ma zance sai na shafa kanta nace "ba zai kuma kama ki ba kinji, Allah ba zai bar shi ko
wani azzalumin ya kuma kama ki ba kinji? Zamu ke yin azkar kullum da safe da kuma da yamma, Allah ba
zai bar wani ko wata halitta ta mutum ko aljan ya kuma taba ki da niyyar zalunci ba kinji?"



Ta sake gyada kai tana sauke ajiyar zuciya, har yanzu fuskarta cike take da tsoro. Ina lura da Umar yana
ta kokarin ganin bai bari ta ga hawayen sa ba, ya taba ciwon goshinta ta danyi wincing tare da

85 / 101