Chapter 89 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   89 / 101

264K to 267K   out of 300.2K words

waccan ranar yau bata yi masa
murmushi ba. And he knew it was over.



Sama sama yaji Mama tana magana, kamar rokon Jidda take yi ta janye decision dinta. But she said



"Na yafe masa Mama, na yafe miki kema. Amma auren sa na gama"



Ya dauke idonsa daga kanta ya sauke shi zuwa hannunsa yana kallon band din ta dake hannunsa,
remembering the time she gave him a cikin falon nan. Yaji Baffa Halilu yayi masa magana. Sai ya samu
kansa da cewa.



"Babu komai Baffa. Allah yasa hakan shi yafi mana alkhairi. Na gode da kulawa"
Sai ya mike kamar wanda ake jansa ya fita zuwa motarsa ya bude aljihun motar ya dauko wata jotter
wadda itace da kanta ta ajiye ta a gurin. Ya dauko biro ya dora akai. Ya rufe idonsa tare da sauke ajjiyar
zuciya ya dube sannan yayi rubutu a ciki ya ninke da sauri ya fita daga motar ya koma inda suke ya shiga
ya durkusa gabanta yana kokarin hada ido da ita one last time amma taki yarda.



Sai ya kamo hannunta ya saka mata takardar tare da fadar wani abu da bai ma san me yace ba, yaji
itama ta fadi wani abu da bai fahimta ba, abinda ya fahimta kawai shine ta karbi takardar, meaning ya
tabbata kenan, sannan kuma ta tsinka band din hannunsa.



How cruel!



Ya mike ba tare da ya kalli kowa a gurin ba ya fita ya shiga motarsa ya kunna ya bar unguwar.



Ya jima yana driving da hannu daya dayan hannun dafe da kurjinsa saitin zuciyarsa da take kuka, kuka
mai tsanani. Shi yasan bashi da lafiya, ya kuma san cewa ciwon nasa karuwa yake yi kullum amma baya
komai gurin neman magani kuma bashi da niyyar, gaya wa kansa yake yi cews ciwo ma wani bangare ne
na kankarar zunubi, maybe ciwon nasa ya zame masa wani sabulu da zai rage masa dattin jikin ruhinsa.



Sai da yayi nisa sosai sannan yayi packing saboda yadda yake jin ba zai iya cigaba da tukin ba. Ya dafe
kirjinsa da hannayensa duk biyun yana numfashi sama sama ga gumi duk ya lullube masa jiki, ya kwashe
mintuna da yawa a haka sannan numfashin sa ya fara daidaita. Sai kuma ya dauko wayarsa ya nemo
number din ta "Baby Dove"



Ya tura mata message.



"I did what you want. Ba wai dan ni ina so ba sai dan na fahimci abinda kike son proving, cewa zaki iya
rabuwa da ni. Ina so ki san cewa na fahimta, kowa ma ya fahimta. Then what's next?"




*Jidda*
Na ga ya mime da sauri sannan ba tare da ya ce wa kowa komai ba ya fita daga falon sannan muka ji
tashin motar sa a waje. Ina kallon Mama ta mike kamar zata bishi sai Baba yayi mata magana ta dawo ta
zauna.



Baffa Halilu ne ya fara magana yace min "bani takardar in gani" na mika masa ita kamar yadda Umar ya
miko min. Sai ya karanta a fili.



"Assalamu alaikum wa rahmatullah. Ni Umar Faruq Muhammad Gidado na yanke igiyar aure na da
Hauwa'u Mahmud guda daya. Tare da fatan hakan ya zama alkhairi a gare mu baki daya"



Ya ninke takardar ya mika wa Abba, shi kuma ya karba yayi ta juya ta a hannun sa. Baba yayi ajjiyar
zuciya "Allah ya sa haka shi yafi alkhairi"



Baffa Halilu yace "insha Allahu ba karshen maganar nan kenan ba. Insha Allahu zamu dawo mu sake
zama a gurin nan da murmushi a fuskokin mu" Baba yace "ameen"



Mun jima haka a zaune babu wanda ya sake iya magana a gurin sai ajjiyar zuciya da ake saukewa, sannan
Baba yace "in babu damuwa Alhaji ina son yara su zauna a gurinta for the mean time, kar abin yayi musu
yawa. Ni ina ji a jikina nan bada dadewa ba zamu sake dawowa"



Abba ya girgiza kai. "Bana jin hakan mai yiyuwa ce. Kayi hakuri Alhaji. Ana so muyi ta jainja da kai akan
maganar nan dan Allah. Ita yanzu na riga na gama duk shirye shirye ina do ta tafi kasar mahaifiyarta tayi
idda a can saboda bana son surutun mutane akan maganar nan, ni in son samu ne ma zan so yanzu a
dauko muku yaran tare da kayan su ku tafi dasu kawai"



Baffa yace "haba Alhaji. Kar muyi haka mana. Ai addini ma ita ya bawa rikon yayan ta in ma aure ne
zatayi nan gaba kuma ba zata tafi da yayan ba sai mahaifiyarta ta rike su, haka addini ya tsara ba wai mu
muka tsara ba, saboda ubangiji ya san muhimmancin uwa ga yayanta. Dan Allah ka bar mata yaranta"
Abba yace "to tafiyar kuma fa? Yanzu mahaifiyar tata bata nan waye zai rike mata su in ta tafi?" Baba
yace "sai su tafi tare. Mu zamu dauki nauyin tafiyar ta su insha Allah. Su zauna tare da ita kar abin yayi
musu yawa"



Abba ya juyo yana kallona ina tattare strings din da suke kan cinyata yace "tashi kije ciki" na mike nayi
musu sallama murya ta ciki ciki na shiga cikin gidan sai dai ban shiga dakin Umma ba inda na bar yara
suna kallo sai na shiga dakin Farhan wadda bata gidan a lokacin, na zauna akan katifar ta ina kallon
strings din da suka hannuna.



Na yi bitar takardar Umar a kaina.



"Ni Umar Faruq Muhammad Gidado na yanke igiyar aure na da Hauwa'u Mahmud guda daya....."



Na saki igiyoyin hannuna suka zube a kasa.



Guda daya yace, ni kuwa guda nawa na tsinka? Na fara irga strings din kamar tababbiya, in na kirga sai in
bata a lissafin sai in sake irgawa.



Ina yi ina tuno tarin alkawarirrikan sa gare ni.



"My heart and my body belong to only you"



"I will never do it again"



Na tuno Bashir



"Dama nasan ba ka wuce tayi ai shi yasa nayi masa"
"She was your favorite pet"



Ma tuno Maryam



"Na ajiye miki sako a cikin motarsa, idan kuma baki yarda nasa bane ba ki kai asibiti ayi miki DNA test"



Na tuno Mammy



"Cewa yayi zai aure ni"



And Asabe



"Wallahi mommy sau daya ne"



Na runtse idona ina jin hawaye suna falla gudu a kan kunchina. Ban san jimawar da nayi a haka ba sai jin
maganar Yasmin nayi a kusa dani



"Mommy are you crying again? Na dauka kin daina kuka yanzu"



Na dago kai ina kallon ta sannan na share hawaye na da bayan hannu na. Nayi kokarin yin magana. "Ba
kuka nake ba" sai ta miko min waya ta "anyi miki message. Daddy ne. Mommy ki karanta mana. Cewa
yayi zai zo mu tafi gida?"



Naji wani irin takaici ya kama ni. Message kuma? Mai zai ce min? Na dauka it is finally over na yar da
kwallon mangwaro na huta da kuda.



Na karba na bude na karanta
"I did what you want. Ba wai dan ni ina so ba sai dan na fahimci abinda kike son proving, cewa zaki iya
rabuwa da ni. Ina so ki san cewa na fahimta, kowa ma ya fahimta. Then what's next?"



Naja tsaki ina jin zuciyata tana min zafi. Gwara ma in gaggauta barin kasar nan dan a kowanne lokaci zai
iya cewa ya mayar da ni tunda minutes kadai bayan saki ya fara min bita da kulli.



Har na ajiye wayar sai kuma na dauka na yi masa reply



"Ba wai ina so inyi proving zan iya rabuwa da kai bane ba. Ina so inyi proving zan iya rayuwa babu kai.
And that's what I will do"



Na tura masa tare da jan dogon tsaki.



Yasmin ta bini da kallo.



"Mommy komawar zamuyi gida?"



Na kalle ta ina jin kamar in sharara wa kyakykyawar fuskar ta mari, sai kuma nayi murmushi nace "guess
what? Tafiya zamuyi. Jirgin sama zamu shiga muje garin su Muƙaffa" (dan auncle Muhammad)



Ta bude ido cikin murna sai kuma ta fita a guje. Nabi bayanta da kallo sannan na dawo da kallo na kan
wayata.



Now I have opened a new chapteri n my life. Page of zawarci. Page din da mata da yawa suke sacrificing
rayuwarsu saboda tsoron budewa. Ko menene a ciki? Allahu a'alam. Amma abinda na sani shine zanyi
iyakacin kokari na na ganin cewa na karance shi daki daki kuma na bi shi cikin nutsuwa har Allah yayi min
jagora in samu kyakkyawan rabo, ko a duniya ko kuma a lahira.
*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta idan kuma kin siya kar ki
sharing in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*



*The Divorcee*




Na koma da baya na kwanta akan katifar tare da runtse idona, trying so hard inga cewa ban cigaba da
kukan da nake yi ba amma ni kaina na san ba zan iya hana kaina ba, sai dai har cikin zuciya ta ban
tantance kukan da nake yi ba, na murna ne? Dan for the past few weeks babu abinda nake so irin
rabuwa da Umar, ko kuma na bakin ciki ne dan for the last seven years Umar has been a greatest part of
my life. Shi ya saka ni a school da kudinsa da karfinsa da jajircewar sa har na samu aikin da a yanzu shine
zai rike ni a zaman zawarcina, ya soni iyakacin so, soyayyar da mata da yawa suke kwadayin samun irin
ta a gurin mazajen su, but then ya ci mutuncina iyakacin cin mutunci, yayi min abinda ya sakani tunanin
anya kuwa soyayyar gaskiya ce yake nuna min ko kuma ta fatar baki ce? The betrayal, the emotional
blackmail, the lies. Some of the things I went through a hannun Umar in na tuna har mamakin yadda
nayi surviving dinsu nake yi. Babu wanda zai gane sai wanda ya samu kansa a matsayi na. I mean it is one
thing for mutumin da baya nuna maka yana son ka yayi betraying dinka and it is totally a different thing
ace mijin da yake nuna duniya kamar babu mace kamar ka ya kuma kwanta da friend dinka, da niece din
ka ya kuma kwanta da yar aikin ka a cikin gidan ka.



Tabbas babu wanda zai gane halin da zuciyata take ciki a lokacin sai wanda ya shiga matsayin, bana
kuma yiwa kowacce mace fatan shiga wannan matsayin.



Ina cikin tsiyayar da hawayena a cikin pillow naji muryar Abba yana kiran sunana, na mike zaune ina jan
hanci sannan nayi kokarin amsawa da dasashshiyar murya ta, "kina ina ne wai? Ko ta zama kurma ne?"
Na ja dankwali na na goge hawayena sannan na mike ina kara daga murya ta gurin amsawa, kafin in fita
daga dakin sai gashi ya shigo, ya tsaya a bakin kofa yana kallona, da alama ya lura da chanjawar idona. Ya
dan dauke kansa kadan yana kallon gefe ni kuma na durkusa a gabansa ina kara jan hanci a kokari na na
ganin na rike sauran kukan da yake kokarin sake balle wa. Yace "kiyi hakuri, kiyi addu'a. Sannan kuma ki
shirya gobe kuje da gwoggon ki Habibah ki debo muku sauran kayan sawarku ke da yara da kuma
abubuwan amfani. Sai kuma ki karasa muku shiri ke da yara tare zaku tafi Ethiopia, kakannin su sunce
zasu biya musu kudin jirgi".
Na gyada kai da sauri. Har ya juya ya fita kuma sai ya dawo yana nuna ni da yatsa yace "saura kuma ki
kwanta kiyi ta koke koke kamar Aysha ta mutu, in yaso hawan jinin da ya riga ya saka miki ya tashi ki
mutu shikenan bashi da asara".



Ya fita yana maganganu kasa kasa. Na mike na koma na zauna a bakin katifa ina cigaba da gitsitstsira
strings din dana tsinka a hannun Umar. Sai naji ina mamakin Abba a raina, ban taba tsammanin samun
goyon bayansa akan maganar nan ba, I thought ba Mammy ba ko Amira Umar ya nema Abba zai ce ne in
koma in cigaba da hakuri ina biyayyar aure. Sai na fahimci abinda Diyam ta gaya min ranar nan cewa
Abba yana sona, kuma duk tsaurin sa a tunaninsa yana yi ne for our own good bai san yadda rayuwa ta
koma ba, ya dauka mazan yanzu irin na da ne, ko a mafarki bai taba tsammanin Umar zai iya yin abinda
yayi ba.




Ina nan zaune aka kira sallar azahar na tashi na koma falon Umma na tarar daga Asad har Yasmin sunyi
bacci, sai na tsaya ina kallon su ina lissafin yadda rayuwar su zata kasance, abinda na tabbatar shine their
life will never be the same amma gwara hakan sau dubu akan yadda rayuwar tasu zata kasance idan da
ace na zabi na cigaba da zama da babansu. Mai zai faru ranar da suka kama babansu in the act a cikin
gidan su? Ko kuma su kawo kawarsu gidan ya nema dan tabbas zai iya, ko kuma Yasmin ta zama
budurwa shaidan din da yake kwadaita masa sauran mata ya kwadaita masa ita. Dan tabbas idan zina ta
ci zuciyar mutum har muharramansa yake sha'awa.



Na girgiza kaina da sauri ina kara tabbatar wa kaina dacewar decision dina. Nayi alwala nayi sallah na
gode wa Allah akan niimomin da yayi min sannan na nemi alkhairi a cikin wannan sabon babin na
rayuwa da na bude.



Ban jima da idarwa ba Farhan ta shigo dakin, fuskarta fal da murmushi, daga gani bakin ta a cike yake da
labari. Ta zauna akan kujera tana kallona nima ita nake kallo sai tayi dariya tana girgiza kai. Na gara
zamana ina kallon ta nace "bani in sha" ta sake murmushi. Sai kuma ta tabe baki trying to hide her
excitement tace "wai wannan din nan ne, yace wai in na amince yana son ya fito maganar aure" na dan
bata fuska "wanene wannan din nan?" Ta juya ido "Sadiq yake ko wa? Wannan dai dan uwan kawar nan
ta ki" na dan yi murmushin da bai kai ciki ba duk da ina matukar yi mata murnar samun miji kamar
wannan amma kuma zuciyata tana cikin zullumin nima tawa rayuwar nace "munafuka, har da wani nuna
kamar baki wani damu da shi ba ko? Har da wani pretending baki san sunan sa ba ko?"
Tayi dariya tana juya ido tace "dallacan, irin jan ajin nan ne fa nake yi" na taya ta dariyar, duk da dai tawa
ta yake ce nace "to ai bani zaki ja wa ajin ba shi zaki jawa" ta zauna sosai. "Amma gaya min gaskiya, yayi
miki?" Na dauke kaina daga kan ta ina kallon sallayar da nake kai na tuna da sanda nayi mata
makamanciyar wannan tambayar akan Umar, sai nace "it doesn't matter idan yayi min ko bai yi min ba,
what matters is idan yayi miki tunda ke zaki aure shi bani ba. Mu namu shine muyi muku addu'a, Abba
kuma nasa shine ya bincika halayyar sa da nagartarsa. Idan ma nace baiyi min ba bana jin hakan zai
hanaki auren sa kamar yadda nima sanda kika ce min Umar bai yi miki ba ban fasa aurensa ba".



Ta sauko daga kan kujerar ta zauna a kusa dani tana girgiza kai tace "noooo. Indai kika ce min baiyi miki
ba zan tambaye ki dalili, idan kika gaya min dalilin kuma naji nai karfi ne tabbas zan rabu da shi, I waited
for years kafin in same shi and I can wait for more years har in samu wani. It is not as if ina yi masa irin
mugun son nan" na gyada kai na cikin fahimta. That was what I lacked a lokacin soyayyar mu da Umar,
nayi masa mugun so, forgetting fadin Manzon Allah kan cewa kar mu zurfafa soyayya kuma kar mu
zurfafa kiyayya.



Na dan dafa ta "wasa nake yi miki ke. Personally yayi min. Ban ga wata makusa ba a tare da shi a zahiran
ce. Ina ganin ki fada masa ya fito din. Allah yasa albarka a ciki"



Sai ta zagaye ni da hannayenta cikin murna tace "ameen summa ameen sister. Nagode. You are the best
sister in the whole world" nayi dariyar yadda tayi maganar dramatically sannan ta tashi da sauri zata fita
sai na kira sunan ta. "Farhan" ta juyo tana kallona sai na ga ta yar da jakar hannunta ta tana kallona.
"Lafiya?" Na sunkuyar da kai na ina jin mugayen hawayen nan suna kokarin dawowa nace "dazu Umar
yazo, tare da iyayensa. Ya rubuta min takarda. Saki daya. Mun rabu da Umar Farhan"



Ta zauna dabas a gaba na. Na danyi murmushi tare da saka gefen hijab dina na goge hawayen daya taru
a idona nace "babu komai. Haka rayuwa take. A ranar da ake haifar wani a ranar wani yake mutuwa. A
ranar da wani yake warkewa daga ciwo a ranar wani yake kwanciya. A ranar da wani auren yake mutuwa
a ranar ake dasa foundation din wani. Fatana shine Allah yasa hakan ya kasance alkhairi a gare mu baki
daya".



A ranar da dare na kira Umma na gaya mata abinda ya faru. Na kuma kira Aunty Afia itama. Sai dai
dukkan su baji dadin yadda suka karbi maganar ba dan har yanzu suna nan kan bakansu na cewa dadai
na xauna na cigaba da hakuri da zai fi.
Maganganun damuka yi da su ya saka naji duk zuciyata tai babu dadi, nafara questioning decision dina.
Ina bukatar someone to assure me cewa akan dai dai nake. Sai na kira Diyam da number din ta ta canada
data kira ni da ita ranar nan.



Sai bayan da kiran ya shiga sannan na fara adduar Allah yasa time din is convenient tunda ban san time
difference din dayake tsakanin mu ba.



Luckily sai gata ta dauka. Muka gaisa. And I told her abinda ya faru. Kamar yadda nasaka rai sai ta
kwantar min da hankali ta kuma jajanta min tare da fatan alkhairi. Na kuma gaya mata fear dina na
tsoron rayuwar da take gabana, rayuwar zawarci. Sai ta kwantar min da hankali da cewa babu komai.



"In dai kin saka Allah a gabanki to kin wuce fargaba. Kin samu support din Abba, a hankali kuma sai kiyi
kokarin fahimtar da Umma itama. Kuma ke kinji dadin ki ma kin yi karatun ki kina aikin ki kina samun
albashin ki ba zaki tagayyara ba, babu wanda zaki dorawa responsibility sai dai maki rage musu nasu
responsibilities din, dama shine amfanin aikin ko sana'ar. A shawarce kuma yanzu ko kin gama idda ki
ajiye batun aure a gefe in dai ba karfin sha'awa ne dake ba kina gudun fadawa halaka, ki bari kiyi healing
sosai ki nutsu kuma kiyi addu'a sosai kar kiyi rushing sai kiga Allah yayi miki jagora ya baki wanda ma baki
taba tsammani ba. People will talk, no matter what you do, just let them talk, zasu yi su gama ne dan
kansu. In da kin tsare mutumcin ki shikenan. Shi Allahn dakike yi da shi yana ji kuma yana gani".



Washegari kamar yadda Abba ya fada sai ga gwoggo Habibah tazo a motar babban danta yaya Kabiru.
Na samu na bar su Asad a tare da Amira saboda bana son zuwa gidan su dasu dan kar su zama
emotional, musamman idan suka hadu da Umar a gidan.

89 / 101