Chapter 56 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   56 / 101

165K to 168K   out of 300.2K words

a
rufe" Mammy ta fara ja da baya na kalle ta nace "zan ci ubanki wallahi. Kin san dai abinda nace zanyi
miki ko?" Ta fara kuka "dan Allah Aunty Jidda kiyi hakuri, dan Allah" ban kula magiyar ta ba na saka tabi
sister Aisha ciki, jimawa kadan suka fito tare, Mammy tana ta kuka.
A'isha ta kalle ni fuskar ta cike da alhini, "kiyi hakuri sister. Yarinyar nan a bude take, kamar ma ba'a jima
da bude ta ba, the place is still healing" naji wani zafi beyond kwatance ya daki zuciyata, na dafe kirjina
na sunkuyar da kaina, hopping babban abokina wato kuka zai zo min amma bai zo ba sai Mammy ce take
ta kukan ta.



Sister Aisha ta dafa ni, "kiyi hakuri Hauwa'u. Yaran yanzu ne an haife su amma ba'a haifi halin su ba.
Kuma tarbiyya yanzu sai a hankali................"



Ta cigaba da magana amma ni ba jinta nake yi ba. Na gado kai at last na kalle ta sannan nace "babu
komai sister Aisha. Nagode sosai. Please let this be between you and me" ta gyada kai da sauri "insha
Allah".



Sai na mike nace da Mammy "mu je" sister A'isha tace "zaki ita tuki kuwa Hauwa'u? You don't seem so
well" na danyi mata murmushi nace "zan iya. Nagode."



Sai muka fito muka koma motar. A raina ina hoping zamuyi accident a hanya ko Mammy bata mutu ba ni
in mutu, maybe in na mutu zuciyata zata huta.



Na dauki hanyar gidan Umar a guje, ina fatan kafin inje gidan in tarar ya rubuta min takarda ta dan ko
bai rubuta ba yau a gidan mu zan kwana, ko kuma a gefen titi.



Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din



0779484494

Nafisa Tafida Usman

Access Bank



Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp

08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020



Please banda kira, WhatsApp only



Forgive the typos please.....,



*Wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar ki
sharing, in kika yi kinci amana kuma ke da Allah*



*Enchanted*



Gudu nake zubawa a motar kamar wadda zan tashi sama, ina kakkaucewa motoci da babura ne badan
bana so inyi accident ba sai dan bana so inyi accident intentionally dan in na mutu zai zamanto kamar na
kashe kaina kenan. Amma at the back of my mind da akwai wani voice da yake hoping muyi accident din
ko na samu in mutu in huta. Ba zan kwatanta yadda zuciyata take kuna ba kuma bana fatan ku fahimta
dan babu wadda zata fahimta sai wadda mijinta ya nemi yar yayarta, bana kuma fatan hakan ta kasance
ga duk wata yar uwata musulma ko da kuwa makiyiya ta ce.



Tun Mammy tana dauriya har ta tsorata sosai da uban gudun da nake zubawa, ta kankame jikinta ta cure
a guri daya tana kuka "dan Allah Aunty Jidda kar ki yar damu, wallahi bana so in mutu, in na mutu wuta
zan tafi wallahi" nayi kamar ban ji ta ba, na cigaba da abinda yake gabana ina godewa Allah da ban taho
da Asad ba yadda ko da munyi accident din babu shi. But ya rayuwar sa zata kasance idan babu ni a
duniya? Ya rayuwar su zata kasance shi da yaruwarsa? Na tabbatar uban su za'a barwa su a matsayinsa
na kammallen cikakken mutum. Ya tarbiyyar su zata kasance a hannun Faruq kuma a bayan ido na? Tun
da Faruq ya iya neman Mammy, bashi da shamaki akan wadda zai nema nan gaba, ko da kuwa Yasmin
ce.



Na sassauta gudun da nake yi ba fara controlling motar a hankali, now hoping not to die but inje gidan
Umar in karbi takarda ta da nake saka ran by now ya riga ya rubuta min sannan in debi yarana mu tafi
gida. Sai dai na kasa barin ƙwaƙwalwa ta tayi tunanin yadda zuwan namu gida zai kasance.....
Muna zuwa gida nayi packing, abinda na fara lura da shi shine rashin motar Umar a compound. Amma
ban karaya ba sai na bude kofa na fito sannan na zagayo na bude gaba na damki hannun Mammy da har
yanzu take rakube tana karkarwa na finciko ta daga cikin motar nayi cikin gidan da ita, not minding
kallon da maigadi ya bimu da shi.



Ina shiga falo na fara rafka masa kira "Umar Muhammad Gidado. Umar Faruq Gidado" da muryar da naji
ta kamar ba tawa ba. "Ka fito duk a inda kake ka bani takarda ta, ka fito ga ta na kawo maka ka bani
takarda ta in matsa in baku guri" sai dai babu shi babu alamun sa, daki daki nabi da Mammy a hannuna
har da su bude toilet amma ko inuwar sa ban gani ba.



Na jawo ta muka dawo falo, taa ta kokarin karbe hannunta daga cikin nawa tana cigaba da kukan ta "dan
Allah Aunty Jidda kiyi hakuri, dan Allah Aunty Jidda kiyi hakuri" .



Na saki hannun da sauri sannan na sauke shi a fuskar ta cikin karfin da ban san ina da shi ba, karfin marin
ya saka ta durkushe a kasa tare da rike kuncinta. Na nuna ta da yatsa "kar ki sake ambatar sunana
ballantana ki ambaci kalmar hakuri" naji a raina babu kalmar da na tsana irin ta hakuri. Na cigaba "tunda
babban munafikin baya nan zan fara settling ki ke karamar munafukar. Ki tashi mu koma gidan ku in je in
damka ki a hannun wannan mugun uban naki in kuma gaya masa duk abinda kika yi tare da nuna masa
shaida, in yaso ya saka gabanki gabas ya yanka ki, in uwarki tayi magana itama ya dora ta akan gawarki
ya yanka ta, all of you can go to hell for all I care".



Ta saki fuskar da sauri tana zare ido cikin tsoro "na shiga uku, Aunty Jidda ki rufa min asiri kiyi min rai
kamar yadda Allah yayi miki, wallahi da gaske nake kashe ni zaiyi in yaji maganar nan, wallahi in na mutu
Allah kona ni zaiyi. Kin ce in banyi abinda kika ce ba ne zaki gaya masa kuma nayi duk abinda kika ce"
nace "ai bance in kika yi ba zan nuna masa ba, ko na fada? Munafuka. Kina tsoron mutuwar kika aikata
abinda kika aikata? Ai ke ba yarinya bace ba da hankalin ki kina sane kin san abinda kike yi kuma kinsan
girman abinda kika yi"



Ta cigaba da kuka da sheshsheka "wallahi ba laifi na bane ba. Cewa yayi zai aure ni. Dan Allah Aunty
Jidda ki rufa min asiri. Wallahi na fasa auren sa ma ni. Zan gaya masa in ce ya rabu da ni babu ni babu
shi" na girgiza kaina "ko kadan bana so ki rabu dashi. So nake ki aure shi din dan the two of you deserve
each other. Ki tashi mu tafi gidan ku wallahi tun kafin inyi miki dukan da zaki kasa tashi" ta sake rike
kafata tana girgiza kai "dan Allah, dan Allah" na dauko wayata "okay tunda ba zaki je ba bara in kira uban
naki shi yazo nan gidan da kansa, maybe ma kafin nan surukin nasa ya dawo sai ya bashi sadaki kawai ya
daura muku aure a yau" ta mike da sauri tana rike hannuna da yake rike da wayar.



"Dan Allah ki rufa min asiri kamar yadda Allah ya rufa miki. Wallahi zan gaya miki komai in kinyi
alkawarin ba zaki gaya masa ba, dan Allah kar ki kira shi wallahi zan gaya miki duk abinda ya faru"



Na kwace hannu na daga nata "waye ya gaya miki ina so inji komai? Ku rike kazantar ku ke da shi, wanda
na sani ma da zan iya zuwa a goge min memory na da naje anyi min" na fada cikin zafin zuciya. Sai ta
girgiza kai tace "ba maganar shi zan gaya miki ba. Wata maganar ce. In dai ba zaki fadawa kowa abinda
ya faru ba"



Nace "oh ba maganar shi ba? Maganar ki kenan zaki yi min? Yadda kike kokarin maye gurbi na a cikin
rayuwata tun kafin in mutu? Maganar......." Tace "bani ba ce ba wallahi. Hajiya ce"



Na dakata da maganar da nake yi na juyo ina kallon ta "Hajiya? Ita ce ta saka ki cusa kanki a gurin mijina
kuma tace ki kwanta dashi?" Tace "ita ce ta bani magani tace in binne"



Na saki wayar hannu na ta fadi kasa ina jin numfashi na yana tsayawa a kirjina, sai ta zame ta durkusa a
kusa da kafafuwana tace "dan Allah, dan Allah, kar ki fada wa kowa wallahi tsoro nake ji. Zan fada miki
duk abinda ya faru kuma zan rabu da mijinki amma dan Allah kar ki gayawa kowa abinda kika sani
wallahi nayi nadama kuma danay na gaya masa ba zan kara zuwa gidan gonar nan ba" na runtse idona
na bude, har yanzu hawaye basu zo min ba, sannan nace "menene zaki gaya min?"



Tace "Hajiya ce wallahi, ta jima tana cewa in ringa yi masa kirki ina kiran sa a waya ina kuma zuwa gidan
ku, ita ce take matsawa wai in ringa zama a gidan nan ina yi masa magana to shine kuma sanda kuka
dawo daga Saudiya sai ta je gidan mu ta kirani ta bani wani abu tace za'a kawo ni gidan nan tace in binne
a kofar palon ku in da zai ke tsallaka wa kullum, ta kuma bani wani turare tace in ke shafawa kullum in
kuma tabbatar zai zo kusa dani yaji kamshin, kuma ta bani wani magani tace in saka masa a abinci amma
shi kadai, ta tabbatar min wai in nayi haka soyayyar da yake yi miki zata dawo ni yake yiwa ita, zai ji idan
bai aure ni ba kamar zai mutu ne, tace zai rabu dake kuma ni ya aure ni in zama ni ce matarsa ni zan
cigaba da zama a gidan nan ke kuma ki fita, ni za'a ke saiwa mota kuma ake kaini Makka"
"Bayan nazo shine ranar nan kuna bacci na binne abin da ta bani, kuma nake saka turaren data bani
kullum da dare lokacin da muke zama muyi kallo tare a falo, na abincin ne tunda tare kuke ci da kyar na
samu na zuba masa wataray da yaci abinci shi kadai. To shine sai yake turo min text yake ce min wai ina
da kyau, ko yace min yana son ganina, ko kuma ya kira ni a waya yace yana son jin muryata. Shine ke
kuma kika mayar da ni gida. Sai muka cigaba da magana a waya. Yace min yana sona sosai kuma yana
son ya aure ni. Ni kuma nace masa ya sake ki kamar yadda Hajiya tace in ke gaya masa, kullum sai yace
min to zaiyi amma yaki yi din, kullum yace zai zo gidan mu amma bai taba zuwa ba sai dai yace in turo
masa hotona ya ganni. Shine ranar nan ya fara yi min zancen abin nan, yace shi mutuwa zaiyi idan bai yi
ba, kuma yace ai aure na zaiyi in yayi din, yace in na yarda munyi zai sake ki ni kuma ya aure ni"



Ta rufe fuskarta tana kuka "na gaya masa dama ni tsoro nake ji, ina tsoron kar a kama mu. Nace masa ya
bari muyi auren amma yaki. Dan Allah Aunty Jidda kiyi hakuri. Dan Allah ki rufa min asiri"



Na mike tsaye ba tare da na kalli inda take ba na wuce kitchen na dauko the closest wuka da na gani, ina
fitowa falon sai ta mike da gudu ta shige dakin yara ta turo kofa. Na wuce kofar dakin da take na bude
kofar falon na tsaya ina kallon kasan kofar, inda kullum za'a tsallaka kafin a fita daga gidan kuma za'a
tsallaka idan za'a shigo.



Flowers ne a jere a gaban yar karamar varandar da kofar falon take ciki, a cikin ramin flowers din aka yi
matakala biyu da zaka taka ka hau varandar, hakan ya saka kasan stairs din ya zama kasa ce, amma
mostly tsallakewa akeyi dan space din ma kafa ba zata iya shiga ba.



Na durkusa a gaban gurin na fara tone kasan gurin da wukar hannu na a rikice, ban jima ina hakar ba na
ga abinda nake nema.



Wani abu ne mai suffar kwai, amma yafi kwai girma sai dai jikinsa kamar shell din kwai. Na dauka a
hannuna ina kalla, jikina gabakidaya yana karkarwa, rubutu ne a jiki kacakaca da larabci wani kan wani
wani kan wani, a ciki na tsinci sunayen Umar, da nawa dana Mammy.



Na mike tsaye da abin a hannuna, jiki na yana karkarwa kamar ana kadani, karkarwar da nake yi ce ta
saka abin ya zame daga hannuna ya fadi a edge din barandar sannan ya tarwatse a cikin flowers, wasu
layu suka bayyana, yan kanana kanana har babu kyan gani wadanda aka dinka su wata a jikin wata wata
a jikin wata.
Naji wani amai ya taso min, na koma cikin gidan da sauri sannan na shige dakina na shiga toilet nayi amai
kamar zan fitar da yayan hanjina. Na dawo daki na zauna a gaban gado na dafe kaina ina mayar da
numfashi, sai a lokacin kukan da nake nema yazo min, na hada kai da guiwa kuwa nayi shi kamar raina
zai fita.



Farko kaina ya kulle ban ma san tunanin menene zanyi ba, tunanin mijina ya kwanta da yar yayata ko
kuma tunanin matar babana da kuma yan uwana da muke uba daya, duk da ban tabbatar da hadin bakin
su ko kuma hadin Hajiya ne ita kadai ba, sun shirya rabani da mijina da yayana da gidana sannan su saka
yar yayata a madadi na.



Wannan wanne irin tashin hankali ne?



Wannan wacce irin rayuwa ce.....



Na sani cewa tun ina karama ta Hajiya da yayanta basa sona, with exception of Farhan, na kuma sani
cewa tun sanda Umar ya fara neman aure na basa son auren na mu either, na kuma sani dan ina gani a
idon su cewaa suna hassadar irin rayuwar da suke tunanin ina yi a gidan mijina amma ban taba tunanin
har abin ya kai wannan matsayin ba. Ban taba tunanin they can stoop this low ba.



Sai da nayi kuka na na koshi sannan ƙwaƙwalwa ta ta fara aiki. Na fahimci motive dinsu shine su cirewa
Umar so na su saka masa son Mammy, su saka ya sake ni sannan ya aure ta. In koma gida ita kuma ta
shiga rayuwar da suke tunanin ina yi.



Sai dai abin nasu sai yazo musu ba yadda suka shirya ba, sai Umar din yaki sakina da wuri kamar yadda
suka saka rai, sannan kuma asirin nasu ya tarar da halinsa wannan ya hadu har ya kai shi ga neman
Mammy. Yes, sunyi masa asiri amma halin sa ne ya kai shi ga neman Mammy. Abinda suka kawata masa
suka ce zaiji idan baiyi ba kamar zai mutu, sun dauka zai aure ta ne kafin yayi, shi kuma yayi ba tare da ya
aure ta din ba.



Maybe da sun san ainahin halin Umar, da ba zasu kawata masa Mammy har haka ba. Tabbas sun haka
min ramin mugunta ne amma sai ya rufta da su tunda Allah ya ga zuciyata ya kuma san bana nufin kowa
da sharri, ko kuma in ce ya rufta da Mammy tunda stain din yanzu a jikinta yake, and will forever be on
her.



Tunowa da nayi da Mammy ya saka na mike na wanke fuskata a toilet na fita, sai dai babu ita babu
alamun ta a cikin gidan, ta gudu, na fita bakin kofa, layun da suka zubo daga cikin kwan suma basa gurin,
ko tantama kuma bana yi cewa ita ce ta dauka ta tafi dasu. Na juya na koma falo, sai na kalli agogo nayi
realising lokacin dauko Yasmin daga makaranta yayi har ma ya wuce, na koma na shiga mota naje na
dauko ta na dawo. Muna shigowa na hada mata cornflakes na kunna mata tv sannan na wuce dakina na
fara gada kayana a jikin yar karamar jaka.



Tabbas duk abinda Umar yayi yayi ne under the influence of asiri amma kuma that did not change the
fact that yayi din, he slept with my niece, and that is something I will neither forget nor forgive. Dole my
step four will happen. Dole zan je gida kuma zan gaya wa iyayena halin da aurena yake ciki ya rage nasu
su fahimta kuma su dau makaki ko kuma su ki fahimta kuma suki daukan mataki ni kuma in shiga step
five dina.



Na dan debi kaya na kadan, na wuce dakin yara na debar musu suma wadanda zasu dan kwana biyu a
raina ina lissafin kafin a aiko a kwashe min kayana daga gidan Umar. Amma kuma a son samu na nafi son
in tafi da takarda ta a hannuna yadda Abba will have no choice then to listen to me, sai dai kuma Umar
din babu shi babu alamun yana da niyyar zuwa gida yanzu, ni kuma ba zan iya cigaba da zama har in jira
shi yazo ba dan iskar gidan kanta ji nake yi tana min yaji yaji kamar zata yi suffocating dina.



Sai da na gama diban iyakacin wadanda zan diba sannan na juyo zan fito daga dakin, sai wani siririn voice
a cikin kaina ya tambaye ni "idan kin je gidan me zaki ce ya faru?" Na dakata da tafiyar tawa ina lissafa
tambayar, sai na bada amsa "zan bada labarin duk abinda ya faru ga duk wanda zai saurara" "zaki ce
Umar mijinki uban yayanki ya kwanta da yar yayarki? and then what?" Na kuma tambayar kai na..



Sai na zame kasa na zauna na dora kaina akan jakar da na hada mana kaya. Tabbas Hajiya tayi wa Umar
asiri kuma sanadiyyar hakan hadi da halinsa, ya saka ya kwanta da Mammy. Amma babu wanda ya san
hakan sai su da suka yi asirin sai kuma ni da Mammy ta gaya wa, and I realized a yanzu bani da shaida ta
cewa asiri suka yi masa, ina dai da shaidar yiyuwar kwanciyar sa da ita, but in na nuna wannan laifin
toward wa zai yi pointing? Toward Umar, dan a hirar tasu shi yake ta hillatarta har tana nuna masa tana
tsoro shi kuma yana kara insisting, har da cewa zaiyi protecting dinta with his life.
A yanzu na san maybe labari ya iske Hajiya na cewa na tone na kuma fada asirin su, meaning asirin ya
karye kenan, meaning babu zancen soyayya tsakanin Umar da Mammy, kuma na tabbatar the Umar I
know ba zai auri Mammy ba ko da kuwa ya sake ni din kamar yadda nake fata, dan haka burin su bai cika
ba kenan, and their next target will be to destroy me, Umar da duk wani abin da ya shafe mu, including
yayan mu.



Da zarar wannan maganar ta shiga kunnen su, they will turn it around, knowing the Hajiya I know zata
ma

56 / 101