Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
rike
hannunsa. Ya juyo yana kallona yace "in an zo duba ta ki ce su sake duba ciwon na, naji kamar yayi tauri
kuma gurin yayi duhu, ina tsoran kar ya zama infected" na gyada kai kawai. Sai shima ya sunkuyar da
kansa sannan yace "kin duba ta? Ko su suka duba ta? Me suka yi mata a gurin mai suka ce?"
Nace "me zasu yi mata banda suyi mata dinki su bata magani?" Ya rintse idonsa tare da dafe kansa yace
"innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Wanne wacce irin masifa ce ta saukar mana Jidda? Yarinyar nan is just a
baby, how can they?"
Na dauke kaina gefe nace "exactly ta yadda ake yi ta haka akayi, ko in bude maka ka gani?" Ya girgiza
kansa sannan ya dafe kan da hannu biyu yace "I can't, I can't" ya juyo yana kallona yace "did you?" Na
gyada kaina a hankali bance komai ba, yace "how bad is it?" Na sake yin shiru ban ce komai ba sai ya
mike tsaye tare da kwantar da ita a hankali, Ina lura da yadda yake lallabata, sai ya jawo drawer din
magunguna ya dauko allurar pain relief din da suka sako mata a ciki, probably saboda ciwon goshinta,
yazo ya bude cannula din hannuta yayi mata sannan ya juyo yana tambaya ta in akwai abinda muke so.
Shiru na sake yi masa sai kuma yafita, yana fita na bi bayansa na rufe kofar sannan na dawo naci gaba da
lallaba Yasmin.
Ranar da wuri Amira tazo tare Asad da Abba, Abba ya duba jikin Yasmin ya tambayi ko muna da abinda
muke nema nace masa babu komai sai ya tafi ya bar Amira da Asad a gurina, Asad yana ta murna tare da
kuma complain din duk mun tafi mun bar shi shi kadai yana ta kuka yana neman mu, na lallabashi tare
da bashi fruits a cikin ledar da saurayin Farhan ya kawo mana, sai kuma na tashi Yasmin na bata abincin
da Amira ta kawo mana kuma na samu taci sosai ta sha ruwa har suna ta hirarsu da Asad.
Sai kuma ga mufida ta shigo tare da aunty suma sun kawo mana abinci, aunty tana ta murnar ganin jikin
Yasmin yayi kyau har tana tsokanar ta, Mufida kuma na lura da yadda tayi wani irin chanjawa kamar ba
ita ba ta zama kamar mutum mutumi, na tambaye su jikin Mama suka ce da sauki, na san ya kamata inje
in duba ta amma ban je ba har suka gama zamansu a nan suka tafi.
Basu jima da fita ba Diyam ta zo itama tare da Subay'a, itama ta ji dadin ganin Yasmin tana magana har
da dariya duk da dai tana complain kanta yana mata ciwo. Wannan yasa muka saka Amira ta dauki yara
suka fita dan kar su dame ta, basu jima da fitar ba kuwa sai tayi bacci.
Bayan tayi baccin ne muka samu muka yi magana sosai na vata labarin abinda ya faru da kuma hukuncin
da na yanke na boyewa Umar gaskiyar abinda ya faru dan ina so ya cigaba da dauka cewa anyi din dan
ya kara samun regret, duk da nasan nan gaba zai iya sanin gaskiyar magana amma Ina fatan kafin ya sani
din yayi nisa a cikin nadamar sa. Sai kuma na gaya mata fear dina na cewa wannan attack din on Yasmin
kamar somin ta bi ne, bisa la'akari da irin tarin laifuffan babanta a wannan bangaren.
Sai ta yaba wa idea ta ta boye wa Umar gaskiya amma kuma sai ta kwantar min da hankali ta hanyar
bani misalai da yawa akan mutanen da suke lalatattu sannan kuma sai Allah ya fitar da shiryayyu daga
gare su, kamar yadda yakan iya fitar da Yaya masu munin hali daga jikin iyaye tsarkaka. Ta kuma sake
encouraging dina akan dagewa da addua akan kaina da kuma yayana, amma kuma sai tace "amma kuma
ba kya ganin kamar babanta wannan karon da gaske ya gyaru?" Na tabe baki nace "ban sani ba, Umar is
very unpredictable, a duk sanda na kama shi da laifi yana irin haka ai, jiya da dare har da su tashi yayi
sallar dare, amma ya kan yi hakan dama a lokuta da dama kuma daga baya ya cigaba da halayyar sa, dan
haka a yanzu ma bani da tabbas and I am not going to take chances gaskiya, dan naga kamar kina son
kiyi min magana ne akan komawa gidan sa" tayi dariya "Ni va haka nace ba, mayar da wukar, kawai dai ji
nayi na fara jin tausayin sa musamman da kika ce min ya fadi. Yana son yarsa sosai kuma for him to think
anyi raping his five years old daughter gaskiya dole a tausaya masa" na bata rai "kafin zancen Yasmin ma
something has happened, something related to him da kuma Mufida duk da bansan ko menene ba
amma nasan yana da dangantaka da dalilin da yasa maman su take asibiti a yanzu. Kuma ya gaya min
wai ya hadu da wata masifa bayan ya bar gidan mu jiya ".
Na rike "na shiga uku ni Halima, kar dai garin dauke dauken sa aka dauko masa kanwarsa. Kin san kin
gaya min dama itama kamar ta fara daukan hanyarsa?" Na daga kafada "I don't know, and to be frank
with you I don't want to know gaskiya. Ni yanzu bani da interest akan duk wani abu da ya shafesu
interest dina kawai akan yayana ne. Da kuma fatan zai bani takarda ta ba tare da an kai ruwa rana ba.
Fatana kawai in samu in tsayar da hankali na guri daya in bawa yayana tarbiyya"
Ta yi shiru tana kallona sannan tace "you are innocent Jidda, you don't deserve all this mess" nayi
murmushi tare da girgiza kaina "no am not. Akwai laifuffa na a cikin abubuwan da suka faru. I was
warned akan Umar tun farkon fari amma soyayyar sa ta rufe min ido na kasa ganin gabana, ko bayan
auren mu ma I should have acted faster than I did, amma na cigaba da zama da kuma cigaba da bashi
uzuri da kuma cigaba da bashi chances ina gaya wa kaina cewa hakan da nake you shine dai dai bayan in
reality still soyayyar sa ce take sawa har nake bashi wadancan madammakin. Dan haka I deserve all what
has and is still coming my way"
Sai tayi kokarin lightening mood din ta hanyar tambayata game da auren da Umar yace za'a daura masa
da Asabe "an daura din kuwa?" Na yi dariya "ni ban sani ba fa, bai sake yi min maganar ba kuma babu
wanda yayi min maganar a yanuwansa. Ban sami ba ko an daura din" tayi dariya "kuma haka ake kishiyar
babu kayan fadar kishiya balle a gaiyace mu mune dannar kirji?"
Nima nayi dariya "sai dai a gayyace ku diban kaya ba wai dannar kirji ba" tace "ke kuwa ki bar mata
kayan ki mana, a matsayin ki na uwar dakinta ai dama ke ya kamata kiyi mata kayan daki" nace "kinga
kuwa dama kayan sun dace da ita, sai ku rakani in debo mana kawai sauran kayan sawar mu da sauran
kayan amfani, sai ta samu ma ta tare sosai tunda bedroom dina shi yafi dacewa da ita a matsayin ta na
matar gida, kinga wannan kawar tata shikenan buri ya cika sai take zuwa gidan a matsayin gidan
kawarta"
Sai kuma Diyam din ta koma serious tace "ni fa wasa nake yi, amma har a raina bana son auren nan, ke
kuma sai nake ganin kamar babu abinda ya dame ki" na daga kafada "kamar kin sani kuwa, babu abinda
ya dame ni, in fact na ma ji dadi da za'a yi auren dan ya zama darasi ga Umar"
Da zata tafi ne tayi min sallama akan cewa zasu tafi Canada gurin surikan ta tare da maigidan ta da
Subay'a da twins, na rakata har bakin mota suka tafi tare da alkawarin zamuyi waya
Kwanan mu uku a asibitin aka sallame mu, a cikin kwana ukun nan kullum Umar a gurin mu yake kwana
amma da rana bana ganinsa kuma ban taba neman sa ba. Kwanan mu biyu a asibitin naje na duba Mama
sai dai na lura da yadda take ta kokarin kin hada ido da ni, ban san dalili ba kuma ban tambaya ba tunda
na gaishe ta tayi shiru nima nayi muka jima a haka sai na tashi na tasa Asad a gaba muka tafi.
A ranar da aka sallame mu ne bayan naje gida Abba ya kira ni yake gaya min cewa ya kira waliyin Umar
yayi masa maganar takarda ta "ina ta daga musu kafa ne saboda ina ganin mutuncin iyayen sa kuma
gashi uban babu lafiya" na dago kai nace "har maman ma tana asibiti" yayi shiru "amma bana son zaman
ki da aure a kanki, kuma vana
So nake da zan samu in karbi takardar sai ki tafi gurin ummanki kiyi idda a can"
Nayi shiru bance komai ba ina jin kalmar idda tayi min nauyi a zuciyata. Sai yace in tashi in tafi. Na dauka
zaiyi min magana akan zancen da na gaya masa akan Hajiya amma sai naji bai ce komai ba.
A ranar da dare Umar ya kira ni, ina ganin kiransa na fahimci cewa yaje dakin da muka zauna kamar
yadda ya saba zuwa da daddare ya tarar bama nan. Sai na amsa kiran amma sai na sakawa Yasmin wayar
a kunnenta ina kallon yadda murmushin ta ya fadada tace "Daddy mun dawo gidan Abba, yaushe zaka
zo ka dauke mu mu koma gidan mu?" Sai kuma naga ta bata rai ta miko min wayar. Na karba wata
zuciyar tana ce min in katse kiran in ajiye wayar amma dai sai na saka a kunne na nace "hello?" Yace
"yanzu saboda Allah ace an sallame ku amma ba zaki gaya min ba? Ko message ai ya kamata ace kin tura
min in ba zaki iya kirana ba" nace "ban dauka kana bukatar sani ba" yace "ina bukatar sani? Yasmin ce fa
babu lafiya, ƴata ce fa a asibitin" da sauri nace "yanzu ai ka san an sallame ta ko? Sai me kake bukata
kuma? Akwai wani abu ne da kake so?"
Sai ya danyi shiru, daga alama ya rasa abinda zai ce ne, Umar of all people ya rasa abinda zai ce? Sai
kuma yace "kiyi hakuri in tambayar da nayi laifi ce. Allah ya huci ziciyarki" na juya idona ina mamakin
yadda zai making maganar to sound as if I am the bad guy. Nace "ameen tunda haka ka dauka amma ni
ina da more important things to do than jin haushinka, na kuma fadawa yanuwanka da suke asibitin dan
haka na dauka zaka ji a gurin su. In yarka kake son gani you are always welcome ka zo ka aiko a kira
maka ita ka ganta, in kuma muryar su kake son ji I suggest ka siya musu karamar waya ka basu yadda
zaka ke kiran su duk sanda kake so"
Sai na katse kiran tare da yin tsaki, wai shi ya dauka dan zaman da mukayi a asibiti hakan yana nufin mun
shirya kenan?
Bai daddara ba da sassafe sai gashi ya sake kira, lokacin Yasmin ma bata tashi daga bacci ba sai na dauki
kiran na mikawa Asad wayar, ai kuwa ya kama zance kamar an bude pampo sai da yayi iyakacin yin sa
sannan ya miko min wayar wai Daddy yace ya bani. Na karba sai na kashe na ajiye. Jimawa kadan sai ga
sako ya shigo daga gare shi.
"I lost everything Jidda. My job, my dignity, my parents and my daughter's dignity. Ke kadai kika yi min
saura. Please kar ki bari in rasa ki kema"
Na karanta na ajiye wayar ina jin zafi a raina, sai kuma na dauka na aika masa da reply
"You lost me tun kafin ka rasa wadancan. It is over. Get over it"
Na aika masa sai kuma na zauna ina tunanin abinda yake nufi da cewa ya rasa iyayensa dan ni nasan har
jiya suna nan da ransu duk su biyun sai dai in yanzu da safe suka wuce. But ai dai ba zai kira ni har suyi
hira da Asad ba idan har iyayen sa sun mutu da safen nan.
Sai ya turo min da wani sakon
"Bani da lafiya Jidda"
Nayi masa reply
"Allah ya baka lafiya yasa kaffara ce"
"Bana jin zan tashi Jidda. Nafi tunanin mutuwa zanyi"
"Allah yaji kanka ya yafe kurakuran ka"
Sai kawai na kashe wayar dan nasan ba rabuwa zai yi dani ba.
Da yamma yayan Hajiya suka zo gidan gabakidayan su, ina ganin su babu wanda yace min wani abu
bayan gaisuwa nima babu wanda na cewa komai, daga baya kuma sai na ga sun hau saman Abba
gabakidayan su, tun daga inda nake ina jiwo fadan Abba muryar sa har dashewa tayi akan fada amma
bana gane me yake cewa sosai, sai daga baya sai gasu sun sauko. Amira ta leka ta tsakanin labule tana
tsegumi sai tace min Mama Sa'a suna ta kuka ita da Hajiya, sai nace ta duba min ko anzo da Mammy, ta
duba tace bata ganta ba.
Sai dare duk suka watse, a lokacin ne Farhan ta shigo inda muke ta saka ni a gaba da tambaya wai tana
son jin gaskiyar abinda ya hada ni da su Hajiya, wai Abba yace sune silar da na baro gidan mijina nake
zaune a gida, wai Abba yace asiri suka yi suna son Umar ya sake ni ya auri Mammy, wai kuma tana son ta
ji gaskiyar me ye tsakanin Umar da Mammy.
Na girgiza kaina "Farhan Hajiya mahaifiyar ki ce, ko me tayi marar kyau ba zaki so ki ji shi ba, da ma dai
ace abin bai riga ya faru ba shine zan iya gaya miki ko zaki iya preventing amma ya riga ya faru daga ni
har ke babu abinda zamu iya yi akai sai dai mu dauki darasi daga abinda ya faru dan gudun faruwar sa a
gaba. shima Abba na gaya masa ne ba dan ya dauki mataki ba sai dan yasan gaskiyar abinda ya faru.
Sunyi min ba dai dai ba tabbas, amma Allah ya riga ya saka min tun kafin ma insan sunyi din. Dan haka ni
babu wani abu a tsakani na da su sai fatan alkhairi"
Ta yi shiru duk zuciyarta babu dadi, sai tace " yanzu me kike ciki? Zaki koma gidan Umar ne?" Sai na
girgiza kai da sauri. "Ban san me Allah ya rubuta min ba, amma ni in a zabi nane zance na gama auren
Umar Farhan, auren Umar ya fitar min daga raina gabaki daya. Sai dai ko da mun rabun ina so ki san
cewa ba saboda Hajiya ko Mammy ko wani ne daban ba ne, zan rabu da shi ne saboda shi, saboda na gaji
da halin sa" ta dafa ni "amma fa ni ina ganin kamar ya bari da gaske, naga yayi laushi da yawa Allah
kuwa, kin san dai am not a fan of Umar tun kuna dating ballantana kuma da nasan halin sa amma still ina
jin tausayin sa kwanan nan duk sanda na ganshi ballantana ma a asibitin nan" tayi murmushi ta kara da
cewa "duk da dai ance "kowa ya tuba dan wuya ba lada" nayi murmushi nima nace "fadin hausawa ne
kawai. Tuba duk tuba ne idan dai har mutum ya tuba ne daga zuciyarsa kuma tsakanin sa da Allah. Kuma
ni a iyakacin sanina ma da wahala ki ga mutumin da yayi nisa a aikata sabo kawai ya tuba yana cikin jin
dadin aikata sabon, da yawa sai wani abu ya faru mai taba zuciyarsu sannan imani yake dawo musu,
kuma in sun tuba in dai har taubatun nasuha ne ana saka ran Allah zai karba insha Allah, tsakanin su ne
da shi. In dai har taubatun nasuha Umar yayi ina masa fatan alkhairi, komawa gidansa ne dai kuma ba
zanyi ba"
Haka kwanaki suka ja. Kullum Umar sai ya kira ni ni kuma in bawa yaransa suyi magana. Sai ya cigaba da
yi min messages ta text message da kuma through WhatsApp amma sai na daina kula shi, sometimes ma
bana karantawa sai in goge dan bana son ya fadi abinda zai dame ni. He kept saying bashi da kowa sai ni,
kuma bashi da lafiya and other stuffs, and I ignored him.
Ranar nan he texted me cewa wai Baffa Halilu ya kira shi yace wai yana umartar sa da ya rubuta takarda
ya bani.
"Jidda I don't know what to do. Baba yaki saurara ta. And I can't even talk to Mama. Ban san ma wa
zanyi wa magana ba dan bani da kowa sai Allah sai ke"
And I replied
"If you trust Him then He will guide you"
Daga nan ya dauke min wuta, ya daina text din, sai dai ya kan kira in hada shi da yayansa suyi magana
shikenan.
Sai kuma ranar nan ina kwance ina baccin rana kamar yadda na saba sai naji muryar Abba yana kira na.
Na tashi da sauri na amsa sai ya leko palon Umma yace in shirya in je sitting room munyi baki. Na koma
toilet na wanke fuskata sannan na saka hijab na gaya wa Amira ta kula da yara zanje in dawo sannan na
fita.
A sitting room din na samu bakin, Abba da Baba da Baffa halilu da Mama, sai kuma Umar a can bakin
kofar shigowa a zaune. Na durkusa daga bakin kofar da na shigo na gaishe su suka amsa min, Baba har
da tambayata yara, sai na zauna ina lissafa yatsun hannuna ina lura da yadda Umar ko dago kai bai yi ya
kalle ni ba.
Baffa Halilu ne ya fara magana "to kusan dai nasan kowa ya san maganar da ta kawo mu nan, amma ba
wai zuwa mukayi dan muyi ta mayar da magana ba, zuwa muka yi dan mu tura abinda ya faru ya wuce
mu kuma fuskanci abinda yake gaban mu"
"Ni dai nine waliyin Umar, ni nazo na nema masa aure kuma ni na riko sadakin sa na bayar na karbar
masa aure, amma kuma ban san duk matsalar da ake ciki ba sai yanzu. Sai yanzu da mahaifin yarinyar
nan yayi min magana yace wai yana bukatar a bashi takardar ƴar sa shi baya so ta cigaba da zama da
aure a kanta, sai a lokacin ya ke gaya min duk abubuwan da suka faru wadanda ni ban sani ba saboda
bana gari. Bayan ya gaya min ne kuma na samu mahaifin Umar shima ya gaya min nasa bangaren naji.
Bana bukatar jin magana daga bakin ki ke Jidda ko kuma daga gurinka kai Umar dan ina ganin kusan duk
abinda zaku fada din an riga an fada. Kuma dukkan bangarori biyun sun yadda akan magana daya ba wai
an samu rashin fahimta bane ba. Wannan ya sa naxe zan zaunar daku a tare gabakidaya ni kuma in fadi
tawa fahimtar watakila ko za'a samu maslaha"
"Tabbas abinda ya faru dukkan