Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
babban danta mai
suna Salem da kuma yarta mai suna Aida da take kusan sa'a ta kuma muka saba da ita, dan haka nafi jin
dadin zaman gidan ta
A haka time yayi ta tafiya har na kammala idda ta kuma a lokacin ne muka fara shirye shiryen dawowa
Nigeria musamman saboda sakon da aka aiko min dashi daga gurin aiki cewa ana bukatar ko dai in dawo
bakin aiki na ko kuma inyi resigning, wanda a gare ni is not an option a yanzu dan ina tsananin buƙatar
aikina. Wannan ya sa muka fara shirin dawowa gida.
Now; Tunda muka je na fahimci kudurin da Umma da yanuwanta suke shiryawa, suna so ne su hada aure
a tsakanin mu mu yan Nijeriya da kuma yanuwan mu da suke Ethiopia dan su karfafa zumuncin tsakanin
su.
"Idan ba'a samu auratayya ba duk ranar da mu iyayen muka mutu to yayan mu ba zasu yi zumunci ba"
Wannan burin nasu sun dora shine akan Amira, inda suka samo mata responsible samari har guda biyu,
daya cousin din su ne mai suna Djimon (pronounced as Jah-moh) sai kuma Salem dan Aunty Nuru. Daga
baya kuma sai wani family friend a Addis Ababa shima ya fara nemanta. Sai dai kuma inda aka samu
matsalar shine ita hankalinta yafi karkatuwa akan shi family friend din su kuma su Umma sunfi son dan
uwa dan dama saboda zumunci suke son hadin. Wannan yasa Amira a tsaka mai wuya, ni kuma na bata
shawarar neman zabin Allah duk da nima nafi son ta da Salem dan na yaba da tsarin sa da yanayin sa, kar
kuma ma ayi zancen kyau dan dama mutanen Ethiopia duk duniya ta shaida baiwar kyawun halitta da
suke da ita mazan su da matan su.
Sai bayan da na gama idda ne sannan maganar mutuwar aure na ta fara fita a cikin yan'uwa, da yake tun
zuwan mu kadan ne suka sani, sai nan da nan cousins din Umma suka fara mata suggesting "ga Jidda nan
itama? Ba sai a gwada duk biyun ba mu ga wadda Allah zai tabbatar mana?" Inji Aunty Nyala matar
auncle Muhammad da tazo ta tarar muna ta shirye-shiryen kayan mu.
Na rufe ido na ina ambaton Allah a raina da fatan kar idea din ta shiga kan Umma sai kuwa naji tace
"wacce Jidda? Rufa min asiri. Indai wannan yarinyar ce ba za'a gyara zumunci da ita ba sai dai a kara bata
shi, wanda ta aura ma tana son sa yana sonta ta matsa ya sake ta saboda kaddarar da Allah ya dora masa
ballantana wanda aka hada su? Ai ina jin in an hada da ita ko shiga yayi wadda bata yi mata ba cewa zata
yi sai ya sake ta"
Na ajiye kayan hannuna ina jin hawaye yana taruwa a gefen idona. Sai ta fara bawa Aunty Nyala labarin
irin soyayya da kuma kulawar da Umar yake yi min amma na guje shi, sai kuma ta rufe laifinsa ta kira
abinda yake yi da sunan kaddara. Aunty Hajar ta juyo kaina tayi ta yi min fada tana girmama laifina
musamman saboda su din mutane ne masu rikon aure sosai. Na yi shiru ina jinta hawaye yana zuba a ido
na. Ban san me yasa mutanen mu suke yiwa kaddara wata irin fahimta ba, ba komai ne mutum zai aikata
bisa son zuciyarsa sannan ya kira shi da kaddara ba.
Kamar yadda Diyam ta fada min ranar nan kuma na amince, idan har komai mutum yayi kaddarar sa ne
me yasa akayi wuta da aljanna? Idan har mutane zasu ke yin sata, kisan kai, rape, kuma suna jingina shi
da kaddara then me yasa muke da shari'ar da take yanke hukuncin ga mai laifi? Me yasa ba za'a barsu ba
kawai ace ai kaddarar su ce babu yadda zasu yi su kauce mata?
Idan har zinace zinacen da Umar yayi shekara da shekaru yana yi mai yasa a shariance za'a jefe shi da
ransa a musulunce?
Life is all about the choices we make. Shine ake kira da jarabawa. Allah zai jarabce ka da son abun wani
dan yaga zaka sata ko kuma zaka fi karfin zuciyarka. In case of Umar kuma jarabawar sa shine sha'awar
mata, dan Allah ya ga zai iya daurewa yaci jarabawar sa ko kuma zai bi bodily cravings dinsa ya fadi
jarabawar? And he chose to fail, his choice, babu ruwan Allah, babu ruwan shaidan, babu ruwan
kaddara.
Bayan ta tafi ne sai na sauko daga kan kujerar da nake zaune na durkusa a gaban Umma. Tayi kamar
bata ganni ba ta dauko wayarta ta kira Aunty Afia a Nigeria ta na bata labarin maganar Aunty Nyala da
kuma amsar da ita ta bata, suka cigaba da kushe maganar tare da kara girmama laifina. Ni kuma ina
durkushe ina fama da zafi a zuciyata.
Ba wai hadin da suke magana akai nake so ba har nake jin haushin kin amincewar su, a'a ni idan da sun
karbi hadin ma zanyi iyakacin kokari na gurin tsayar da maganar saboda babu aure a gabana a yanzu
haka, amma yadda har yanzu suka kasa fahimta ta shine yake damuna, shine kuma abinda nake so in
fahimtar da Umma.
Sai data gama wayar ta ajiye tare da jan tsaki tace "Allah ya kyauta". Na kira sunanta a hankali "Umma"
bata kalle ni ba tace "ina jin ki" nace "Umma kiyi hakuri akan abinda ya faru da ni, nasan ba haka kika so
ba, Allah ya huci zuciyarki".
Ta juyo tana harara ta "kina sane ai da cewa zaki bata min din ai amma kika yi abinda kika yi din" na
girgiza kaina nace "Umma na san ranki zai baci amma ina so ki san cewa nawa ran yafi naki baci akan
maganar, tawa zuciyar tafi taki shiga damuwa akan maganar....." Ta katse ni "karya kike yi Hauwa'u. Idan
ranki baya so me yasa kika yi. Mutumin nan babu abinda ya rage ki da shi. Mata nawa suke neman irin sa
sun rasa? Mata nawa ne suke zaune da wadanda suka fishi munin hali suna hakuri saboda sun san
bautar Allah suke yi? Sai ke yar gwal? Ke ce ba zaki iya ba?"
Na danyi shiru ina harhado maganar da zan gaya mata sannan nace "Umma aure ibada ne, hanya ce ta
samun aljanna kuma at the same time hanya ta samun wuta" ta kalle ni da sauri "wuta? Jidda auren ne
kike cewa hanyar shiga wuta? Anya kuwa kina da hankali?"
Na gyada kai na "Umma aure ibada ne, sunna ce mai karfi, amma kuma abinda za'a yi a cikin auren farilla
ne, in anyi dai dai a dace da aljanna in anyi ba dai dai ba kuma a samu zunubin da zai iya kai mutum ga
wuta. Umma na san kin sha jin labarai na matan da suka kashe mazajen su har lahira, shin wadannan
aure ba wuta ya kai su ba? Ko kuma matan da suke zama da mazajensu shekara da shekaru ba tare da
suna iya yi musu biyayya ba, ba tare da suna iya hada gado da su ba, shin wadannan aure ba wuta ya kai
su ba? Ko kuma matan da mazajensu suke halayya irin ta Umar sai suma suka dauki halayyar a matsayin
revenge suke yi dan su rama, shin wadannan suma aure ba wuta ya kai su ba? Umma ki zabar min, da in
zauna a gabanki a matsayin bazawara da kuma in fada cikin jerin wadancan matan da na lissafa wanne
ne dai dai?"
Na lumshe idona ina tuna marin da nayi wa Umar ranar da zan bar gidan sa da kuma yadda zuciyata tayi
ta gaya min in dauki wuka in je in caka masa, tabbas na kusa shiga sahun wadancan matan.
Na goge hawayen da ya fara zarya a kuncina nace "Umma ni ban san komai ba game da rayuwa, dan
ilimi na dan kadan nake da shi amma a cikin kadan din nan na san dai dai na san ba dai dai ba. Bani da
sani sosai akan rayuwa, amma nasan duk matan da suke zaune da mazaje irin Umar ko kuma wadanda
suka fi Umar munin hali to ba suna zaune ne da su saboda suna hakuri irin hakurin da Allah yace ayi ba,
da yawa daga cikin su suna zaune ne dan babu yadda zasu yi, wadansu daga cikin su dan suna tsoron in
sun rabu da su zasu rasa shinkafa da taliyar da zasu ci, idan kuwa har suna da sana'a ko aiki to dalilin
zamansu shine dan iyaye ba zasu karbe su ba in sun koma gida dan wasu iyayen da yarsu ta fito gwara ta
mutu dan bakin ciki, idan kuwa har iyayen zasu karbe su kuma still suke zaune to dan suna tsoron
zawarci ne suna tsoron loosing sunan su na matar aure da kuma tunanin mijin da zasu aura nan gaba
wanda ni a ganina ba dalili bane ba dan Allah ne mai zaben miji ba mutum ba, kamar yadda ya baka
wancan haka zai baka wani ko da kuwa shima mai irin waccan matsalar ne ko kuma wata daban sai ka
dauke shi shima a matsayin wata kaddarar ta daban. Idan kuwa har dukkan wadannan sharudan sun cika
kuma still suna gayawa kansu suna zaman hakuri ne to watakila suna yin irin hakurin da nayi shekara
shida ina yi ne, hakurin da babu lada a cikin sa "
"Umma mu'amala da fasiki haramun ne. Duk wanda kuwa ya san da haka amma yake cigaba da yi bisa
wani dalili nasa yake gayawa kansa cewa hakuri yake yi to tabbas bashi da ladan hakuri, dan bana jin
akwai lada a cikin aikin haram. Kuma ba dan Allah yake yi ba, kamar yadda na zauna da Umar dan ina
son shi na cigaba da gaya wa kaina cewa zaman hakuri nake yi"
"Umma ina ganin ubangiji ya haramta mu'amala da fasiki ne saboda hikimomi irin nasa, na farko kamar
yadda na fada ita halayya naso take yi, in kana abota ko auratayya ko ma wacce irin nau'in mu'amala ce
da akwai chance na cewa kaima zaka dauki fasikancin sa wata rana, ko ba zina ba ko da salon magana ne
in kana tare da mutum sai kaga ka koyi irin yanayin maganar sa ba tare da kai kanka kasan sanda ka fara
yi ba, hikima ta biyu a fahimta ta ita ce shi fasiki kullum yana tare ne da fushin ubangiji da kuma tsinuwar
malaiku, idan kuma ubangiji yayi niyyar saukar da fushin sa akan fasikin nan ba lallai ne masifar da zata
same shi ta same shi shi kadai ba, zata shafa ne har da wadanda suke tare da shi, duk wanda ya zauna
dasu har fushin ubangiji ya shafe shi shi ya jawo wa kansa tunda kiri kiri ubangiji ya haramta mu'amala
da su. Hikima ta uku a fahimta ta itace idan ana kyamar su ana kin muamala da su ana kuma kin basu
aure da kuma raba auratayya dasu hakan zai yi discouraging masu son joining dinsu, hakan zai saka
rayuwa tayi musu kunci watakila kuma sanadiyyar hakan su samu shiriya. Amma in ana cigaba da zama
da su ana cigaba da muamala da su ana nuna musu abinda suke yi ba komai bane ba kamar ana kara
musu karfin gwuiwar cigaba da abinda suke yi ne. May Allah forgive me if any of the things I said is
wrong but ni haka na fahimta"
"Umma ni ban san komai ba, amma na san banbancin halal da haram, na kuma san hukuncin kowanne
daga ciki. Na san cewa rabuwar aure halal ce....." Na fada ina bude mata hannu na na dama a gabanta,
"na san kuma auren fasiki haramun ne" na bude mata hannu na na hagu a gabanta sannan ina kallon ta
nace "umma a matsayin ki na mahaifiya ta wanne zaki zabamin tsakanin halal da haram? Wanne ne kike
ganin zai sa in dace a duniya da kuma a lahira?"
Ta jima tana kallona sai kuma ta dauke kai gefe tace "Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi" na sauke ajjiyar
zuciya nace "ameen Umma. Na gode" sai na mike zan shiga cikin daki.
Ta kira sunana "Jidda" na amsa tare da juyowa sai tace "Hajiya ta san maganar nan? Me tace akai?" Na
danyi murmushi nace "Hajiya ta sani Umma, bata ce komai ba kuma ba zata ce komai ba, ubangiji ya riga
yayi taking care of her for me"
Washegari muka bar kasar very relaxed and very satisfied. A jirgi na tuno da damuwar da na shiga ranar
da zamu taho saboda ina tunanin rashin lafiyar Umar sai na fahimci yanzu babu ko rabin damuwar a tare
da ni, na fahimci cewa Umar ya fara fita daga raina kamar yadda aurensa ya fice gabakidaya daga raina.
Muna zuwa muka tarar da yan taryar mu, Yaya Tahir da matarsa da babyn su, Abbah, da kuma Farhan. A
gida kuma muka tarar Abba har da sakawa a gyara wa Umma dakinta, mun lura har kwalliya yayi ya saka
kaya masu kyau, ni da Farhan muka yi ta gulmar sa muna cewa yayi wa amaryar sa kwalliya. Mun kuma
tarar neman auren Farhan ya kankama har an kawo kuɗi dan ma tace Abba ne yake ta delaying maganar
yace bai gama bincike ba, a raina nace "an sha Abba ya warke, ba zai kuma sake ba".
A sitting room na tarar da kayana, har furnitures din gabaki daya na bedroom dina dana falo dana dakin
yara, an cika su a sitting room din an daina amfani da shi, sai Abbah yake ce mana wai aiko dasu aka yi
daga gidan su Umar, ban ce komai ba na bar maganar.
Washegari na shirya yara suka da kayan su nace Amira ta kai su gidan kakannin su su kwana biyu tare da
su, bata jima ba sai gata ta dawo, a ranar da dare kuma sai Mama ta kira ni wai yara sun ce a kira ni su
gaishe ni, sai kace ba dazu muka rabu ba, bayan mun gaisa da su kuma sai ta karba tace min "su Yasmin
sunyi kyau kamar ba su ba, har fari naga sun kara yi" na danyi dariya nace "watakila weather din garin ce
ta karbe su" tace "haka ne. Allah ya sa zaku samu bikin Mufida. Tana ta nemanki a waya bata san yadda
zata same ki ba tace a social media ma kina offline" sai naji babu dadi wai za'a yi bikin Mufida ban sani
ba, nace zan kira ta a waya. Har munyi sallama kuma sai tace "gashi kuma su Yasmin basu samu babansu
ba, amma na kira shi a waya sun gaisa" sai naji babu dadi da ban tambayi jikinsa ba nace "ya jikin nasa,
ya samu sauki kenan tunda har yayi tafiya" tace "jikinsa da sauki. Amma yanzu ma yana asibiti a Dubai.
Muna dai saka ran za'a sallame shi kafin bikin Mufida" nace "ayya, Allah ya kara masa lafiya" sai tace
"zan turo miki number din da yake using a can sai ki kira shi ki duba shi, dan Allah" sai na kasa ce mata
a'a, nace to.
Muna ajiye wayar sai ga number ta turo min mai code din Dubai, nayi saving da sunan "Dubai" amma
ban kira ba kuma bani da niyya.
Washegari da safe na koma gurin aiki na, nayi cike ciken duk da ya kamata inyi sannan aka yi posting
dina paediatric ward aka saka ni a duty roster sai na dawo gida, ina zuwa na tarar da Abba a tsakar gida
na gaishe shi sai yayi min maganar kayana da aka zuba a sitting room, "ya zaki yi dasu? Dan babu dakin
da zasu shiga a gidan nan" na danyi tunani sai nace masa "siyarwa zanyi" ya gyada kai "hakan ma dai dai
ne, in an siyar din sai a ajiye kudin in Allah ya kawo wani auren kinga cikawa kawai za'a yi ayi wasu
kayan" nayi murmushi kawai, shi Abba har ya fara yi min lissafin wani auren.
Sai kuma yayi min maganar inda zamu zauna ni da yara. "Ga daki nan ciki daya inda yaruwarki take,
tunda ta kusa tashi ke sai ki zauna a ciki tare da yaran. Sai na samu kudi sai a danyi muku gyara a ciki a
shigar muku da bandakin tsakar gidan nan zuwa cikin dakin saboda sanyi"
Na danyi murmushi ina jin dadi nace "Abba akwai wasu kudade a hannuna sai ayi amfani da su gurin
gyaran" yace "ba wani gyara za'a yi da yawa ba ai, ɗan yadda zaku ji daɗin zama ne kafin Allah ya fito da
wani mijin" na sake murmushi. Abba will never change.
Da dare ina kwance ina kewar yayana sai ga kira ya shigo waya ta, na duba naga "Dubai" sai nayi tsaki na
ajiye wayar, I need to learn to say "no" and mean "no" bana son ayi ta kwan gaba kwan baya akan
magana ta da Umar, an riga anyi an gama sai dai kuma labari, labarin ma watarana ba za'a yi shi ba
Ganin wayar tana ta kara har Umma ta fara kallon ta sai na dauka na saka ta a silent sannan na kife ta
dan kar ta cigaba da haske. Sai da nayi bacci na farka sannan na duba wayar na ga 5 missed calls daga
Dubai, da kuma message guda daya "Jidda. Umarul Faruq ne" na ja tsaki, as if I don't know. Na san shi
din ne ai shi yasa naki dauka.
Washegari kafin in fita office na kira Abbah karami muka yi maganar gyaran dakin da Abba ya bani,
plaster kawai za'a gyara inda ya danyi cracks sannan ayi fenti, sai toilet da za'a yiwa gyare-gyare a shigar
da shi ciki, babu bata lokaci yayi min bill din komai na bashi aka fara aiki, cikin kankanin lokaci aka gama
gyaran dakin fes kamar na amarya.
Sai kuma muka koma maganar siyar da kayan dakina, dan sunyi wa dakin girma. Tunanin farko da yazo
kaina shine na wasu instagram accounts din da nake ganin suna siyar da second hand kayayyaki kuma na
fahimci suna ciniki sosai saboda yadda nake ganin responses na mutane. Sai nayi tunanin why not inyi
musu magana su zo su sayi nawa su siyar?
Sai kuma na sake wani tunanin, why not nima in bude irin wannan business din? Why not nima in siyar
da kayayyaki na da kaina through the same process da naga suna using sannan kuma in cigaba da siya
daga gurin mutane ina siyarwa?
I thought about it a lot and realized it wasn't such a bad idea, sai kuma nayi addu'a akan hakan na kuma
gayawa Umma nace itama ta gaya wa Abba in samu amincewar su and I set up my mind to it, sai fatan
Allah ya bani nasara.
Katifa kawai na dauka a cikin kayana na saka a sabon dakina na saka carpet a kasa tare da labulaye, sai
kuma na bayar aka yi min wardrobe madaidaiciya wadda zata shiga dakin kuma zata dauki kayan mu, na
zuba mana kayan sakawar mu ni da yarana, sannan a dakin ma na