Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
tace "Faruq yana gida? Hajiya Mariya ce ta turo
mu" (Mama) na fadada murmushi na nace "ohh okay. Yana nan. Bara a yi masa magana" sai na tashi
naje dakin sa na tashe shi "baki ne suka zo, ina jin yan uwan Mama ne" ya yamutsa fuska kamar mai
shirin yi min shagwaba. "Just attend to them please ni bacci nake yi" na ja kafarsa "wallahi ka tashi, ai
naje gurin nasu amma suka ce in kira ka" ya janye kafar sa sannan ya matsa inda hannuna ba zai kai ba
ya kuma dora pillow akan fuskarsa "tell them bana gida" na hawo kan gadon na haye samansa na dauke
pillow din tare da dukansa da pillown a both sides dinsa "na gaya musu kana nan ai, so kake in zama
makaryaciya? Ka tashi please kaga kar su ce anyi musu wulakanci" ya bude idon da yake cike da bacci
yana bubbuga kafa, da gaske shagwaba yake min "ni wallahi bacci nake ji, ki ce musu bana jin dadi ko
kice nayi disappearing" nayi dariya sannan nayi masa chakulkuli a sides dinsa "wallahi ba zan yi karya ba.
Ka tashi ko kuma in je in ce musu kace ba zaka zo ba"
Ya fara kokarin rike hannayena ni kuma na hana shi har sai da naga ya ware yanata kyalkyala dariya
sannan na rabu dashi tare da sauka daga kan gadon da sauri dan nasan in ya kama ni sai ya rama kuma
zamu bar baki suna jira. Nayi hanyar kofa da sauri na fita a lokacin da yake saukowa daga gadon, ina
komawa na wuce kitchen na kawo musu drinks da doughnuts din da nayi jiya da dare, sai kuma na dauko
fruits na yayyanka musu duk na hado muka kawo musu tare da Yasmin, na tarar yammatan sun dauki
Asad yana ta musu surutu da gwarancin sa su kuma suna dariya. Matar tayi min godiya sai na samu guri
na zauna.
Jimawa kadan Umar ya fito, ya saka kaya amma fuskarsa da alamar bacci a tare da ita, farko shima
kamar bai gane su ba sai kuma naga yayi murmushi. "Yaya Amina? Dama kin san hanyar gidan nan?" Tayi
dariya "Doctor Umar kenan, kai ma ai bana jin kasan hanyar gida na, rabon kada can tun kana zuwa
zance" suka yi dariya tare yace "bayan kin hana ni kanwar taki" tace "bayan ka ki auren kanwata dai"
suka kuma dariya sannan ya juyo yana kallona sannan yayi murmushi yace "baki san ta ba ko?" Na gyada
kaina yace "yayar Hafsat ce, can nake zuwa zance gidan ta shine take yi min gori" na gyada kaina cikin
gamsuwa, na tuno Hafsat yarinyar da Mama taso hada su da Umar, second cousins suke da Umar din, so
wannan matar ma second cousin dinsa ce kenan, su kuma yammatan maybe yayanta ne ko kuma suma
kannen hafsan ne.
Kamar mai amsa min tambayata sai naji yace "ba dai twins ne suka girma haka ba?" Suka kalli juna suka
yi murmushi, ya bude baki cikin mamaki "seriously, sanda nake zuwa gidan basu fi Yasmin ba" babbar
matar tayi dariya "a'a sun fi Yasmin mana, kai dai kawai ka manta. Gasu nan har sun shiga jami'a"
Ya gyara zama "wow. Lallai tsufa ya kama ni ban sani ba" ya juyo min fuskar sa "taya ni dubawa ko akwai
furfura" yammatan suka yi dariya.
Sai babbar matar tace "dama na kawo su makaranta ne, nan BUK suka samu, munje sunyi registration
shine mukayi waya da hajiyan ku tace ai gidan ka babu nisa sosai, ita tayi mana kwatance tace mu zo mu
huta"
Nace "gaskiya kun kyauta, ko babu komai ai anyi zumunci"
Sun dan jima a gidan, har na gama girki muka ci tare sannan suka yi min sallama tare da godiya Umar ya
mayar da su gida.
A week after that sai gashi ya dawo tare da yammatan a motarsa har da akwatinan kayan su, suka shigo
na bisu da kallo kawai sai yace su shigar da kayan su dakin yara sannan ya kama hannuna zuwa kitchen
"ina office Mama ta kira ni, ina zuwa gida sai tace ga Hassana da Usaina nan zasu dawo gidan nan da
zama wai gidan su yayi nisa sosai da school ba zasu iya zirga zirga ba. So zasu zauna anan for the mean
time, kafin a san me za'a yi akai"
Na fara girgiza kaina ina ja da baya, ya bini ya riko hannu na "Jidda please, Mama ce tace su zauna, we
can't say no to her kin sani, just for the mean time maybe for this semester kadai. Iyayen su ne suka
tambayi Mama ita kuma ta amsa musu ba zamu iya cewa a'a ba kin sani" na dafe kaina, I had no
problem with the girls and with zaman su tare da mu, zama su debe min kewa ne dan I did get lonely
sometimes musamman idan aiki ya chunkushe wa Umar, but still.........
Na dafe kaina da hannuna ina kokarin tunanin abinda ya kamata inyi, all I wanted to do was say no
amma kuma bani da kwarin guiwar fadin hakan a lokacin kuma bana jin no din nawa will mean anything
tunda na tabbatar ba zai ki bin maganar Mama ba akan tawa, I will just be putting him in a difficult
situation, na shafa fuskata ya sake matsowa "please just say yes, na san baki ji dadi ba ya kamata a gaya
miki tun kafin su zo amma ni ma ban san zasu zo din ba sai yanzu, ba zan iya ce mata no ba kin sani nima
kar ki ce min no dan Allah"
Na rufe ido na ina kokarin clearing kaina sannan na gyada kai "okay, su zauna din babu komai. It is okay"
Yayi ajjiyar zuciya sannan ya rungume ni "thank you Baby, I was so scared that you will say no" na danyi
dariya, trying to lighten up the situation sannan na ja kunnen sa "ban taba ganin namiji mai tsoro ba irin
ka" ya rike kunnen yana bata rai "ban taba ganin matar da take takurawa kunnen mijinta ba irin ki"
Lafiya lau muka zauna da twins din nan, sam basu da matsala kullum zasu shirya su tafi school basa
dawowa ma some times sai after six, da weekend kuma sai suje gida suyi weekend sai monday sai su
dawo. Matsala daya ita ce zuciyata ta kasa sakewa, musamman daga baya da suka tsiri bin Umar in zai
fita suce ya ajiye su a school, ko kuma ma in ba fita zaiyi ba in dai yana gida sai sun roke shi ya kai su,
wani lokacin kuma ina gida zan ga sun dawo tare sai yace kiran sa sukayi suka ce in zai shigo ya biya ya
dauko su. Gasu irin yan gayun nan be masu kyalliya, typical jambites.
A gidan ma kuma in dai zasu ganshi a zaune sai sun zo, auncle Umar this, auncle Umar that. Ban sani ba
ko kishi ne, saboda tabbas nasan ina kishin mijina, ko kuma I was being cautious, sai naji hankali na yaki
kwanciya da hakan, duk sanda suka tafi tare sai naji part of me ya tafi dasu, duk sanda suka dawo tare
musamman in tare da daya suka dawo babu dayar sai inji duk zargi ya shiga zuciyata. And one day na
tattaro courage dina nayi wa Umar maganar.
Da dare ne bayan na gama bashi kulawa ta ina kwance a kirjinsa shi kuma yana shafa bayana a hankali,
na jima ina ta tsara yadda zanyi masa maganar, sai da naga alamar bacci yake neman yi sannan nace
"Doctor" idonsa a rufe yace "uhmm?" Nace "ina son muyi magana"
Ya tsaya da shafa bayana da yake yi amma bai ce komai ba, nima kuma sai nayi shiru, sai ya bude idonsa
ya dago fuskata yana kallon cikin idona yace "fadi abinda yake ranki" na cire idona daga cikin nasa "akan
yaran nan ne, gaskiya ni bana son zamansu a gidan nan, kaga......" Yace " I thought mun gama magana da
ke, akwai wani problem ne da suke da shi?" Na girgiza kaina "basu da matsala ni ce mai matsalar, ka ga
dai yammata ne, kyawawa, kasan kuwa halin da muke ciki ni da kai a gidan nan, hankali na baya
kwanciya idan na ganka tare da su ko naga kun fita tare ko kun dawo tare"
Ya ture ni daga jikinsa sannan ya mike zaune "damn it Jidda. Kina nufin kina zargina da wadannan yan
mitsimitsin yaran?" Na tashi zaune nima, a raina ina jin haushin ture nin da yayi nace "ba zargin ka dasu
nake yi ba, ina tsoron kar in fara zargin naka dasu ne, maganin kar ayi hausawa sukace kar a fara, kai
kasan matsalar ka nima nasani, yaran nan are young, beautiful and tempting, kai nake jiye wa matsala
ba ni ba, kar azo nan gaba ana wallahi tallahi"
Ya zuciyo "wato duk abinda nake gaya miki kullum na cewa na daina, duk kokarin da nake yi dan ki
fahimci na daina din amma wannan abin ke har yanzu yana ranki ko? Duk kokarin da nake yi dan in samu
trust din ki amma kin rufe zuciyar ki kin goga min bakin fenti a ranki ba kya ta ba kallona da wani abu in
ba wancan ba, I don't believe this! Me kike so ne inyi wanda zai saka ki dawo kin yarda dani ne wai Jidda,
ki gaya min, me zanyi for you to trust me again"
Sai na debi kayana na saka, na juya masa bayana gyara kwanciya ta, "ni dai abinda yake raina na gaya
maka, kai kuma sai ka dauki matakin da kake ganin ya dace"
Ina jin sa shima ya kwanta, sannan yayi ta jera tsaki, ni dai har nayi bacci yana faman juyi. Da safe ya
tashi da fushi yana amsa magana ciki ciki, ni dai nayi masa duk abinda zanyi masa amma ban bashi
hakuri ba tunda ni a iyakacin sanina ban yi masa laifi ba, yana gama breakfast ya dauki Yasmin suka fita,
ina lura da twins suna ta sauri zasu bishi amma sai jin tashin motarsa suka yi, naga alamar sunji haushin
hakan sai na wayance da yi musu dariyar yau babansu ya manta da su
Ban kuma ganin ya fita da su ba kuma ban kuma ganin sun dawo tare ba, kwanaki kadan bayan nan
kuma sai gashi ya zo yana gaya musu wai ya sa an samar musu hostel a cikin makaranta "kun ga kun huta
da zirga zirga kullum, kuma zaku fi yin karatu a can" fuskokin su duk suka nuna rashin jin dadin haka,
daga alama sunfi son nan din amma sai ya tashi ya shiga ciki. Na bishi na tarar dashi yana shirin shiga
wanka na tsaya ina kallon sa sai yace "I hope you are happy now, you stubborn stubborn woman" ban ce
komai ba sai ya taho gaba na tare da saka hannu a baya na ya zuge min zip din riga "azo a taya ni wanka"
yace yana murmushi.
I felt guilty for what I did, duk da cewa 80% na zuciya ta yana gaya min cewa abinda nayi dai-dai ne,
kamar yadda nace, maganin kar ayi to kar a fara. Sai kuma nayi tunanin maybe dan na saka maganar
sosai a raina shi yasa na kasa cire zargi da damuwa daga raina. Watakila ma ya daina din, ni ce kawai na
kasa barin zuciyata ta yarda cewa ya daina din, cos wannan maganar kullum da ita nake wuni da ita nake
kwana no matter how much I try na kasa cire ta daga raina, in dai yayi late bai dawo ba sai nayi tunanin
me yatsayar da shi, in dai na kira shi bai dauka ba sai nayi tunanin me yasa bai dauka ba, in dai aka kira
shi a waya yaki dauka ko yayi rejecting sai nayi tunanin menene dalili? Waye yake kiransa?
And I thought rashin aikin yi yana daya daga cikin abinda yake saka ni nake over thinking, maybe if I am
to get busy, wasu abubuwan ma in yayi ba zan lura ba ballantana in damu, sai na fara tunanin ya kamata
in fara aiki, tunda dama sanda na gama makaranta cikin Asad ne ya saka ban nemi aikin ba yanzu kuwa
Asad ya bawa shekaru biyu baya, bayan haka ma kuma ina bukatar kudi nima ba wai dan Umar ya gaza yi
min wani abu ba sai dan nima ina da personal bukatu na kamar taimakawa mahaifiya ta da yan'uwa na,
kamar gudunmawar biki in ya tashi a dangi na ko nasa, ko yin kyauta haka ga wani a duk lokacin da nayi
niyya ba sai na tsaya ina tambayar Umar ba.
Sai na samu Umar nayi masa maganar, a raina ina doubting yadda zai karbi maganar tunda dai namiji ba
shi da tabbas, duk da shi ya tsaya min nayi karatun zai iya cewa ba zan yi aikin ba kuma. Amma sai naga
ya karbi maganar "babu komai insha Allah, in na fita zan fara following maganar in ji yadda za'a yi. It is
about time da ya kamata kema ki fara aiki, tun kafin wani babyn ya zo" ya karasa fada yana langwabe
kai, na san abinda yake nufi, kusan kullum sai yayi min nacin wai in cire masa bondage din dana saka
masa, wai ya gaji, so yake mu daina using condom, claiming cewa yana takura masa kuma Asad wai yana
bukatar kanne, ni kuma nayi kunnen uwar shegu da maganar ko yayi kamar ya manta sai na dauko na
saka masa da kaina, in kuwa ya bari ya kare bai siyo ba to ya tabbatar ba zai shiga daga ciki ba.
A lokacin ma ni ba std nafi tsoro ba, haihuwa nafi tsoro, cos the more yaya da muka haifa da Umar the
more bounded I will be to him, and the harder it will be for me to get away from him in case ya kara
maimaita halayyar sa.
Cikin abinda yake kasa da wata uku Umar ya samo min aiki a asibitin da yake aiki, babu bata lokaci kuma
na fara zuwa. Na fahimci dalilin da yasa ya dage sai in da yake zanyi aiki saboda tsananin kishin sa,
saboda yana so ya saka min ido kuma ya saka din, kullum sai yayi maganar baya so in ke kula wane ko
yayi ta tambaya ta yau waye da duty a ward din mu kuma me yace min nima mai nace masa, yayi ta
cancelling mutane daga list din wadanda yake so inke yiwa magana kamar yayi lokacin da nake karatu, ni
kuwa babu abinda ya dame ni tunda na tabbatar da cewa I have nothing to hide.
Babban kalubalen dana fuskanta da farko shine inda zan ke ajiye Asad, da farko munyi lissafin za'a saka
shi a daycare din makarantar su Yasmin sai kuma muka ga already shekarun sa sun kusa kaiwa ya shiga
pre nursery musamman tunda yana da baki, sannan kuma ga session din ya kusa karewa, so it will be a
waste of money mu saka shi yanzu gwara mu bari in za'a shiga sabon session sai a shiga da shi. Sai kawai
muka yanke cewa zan ke fita dashi ina ajiye shi a gidan mu gurin Umma in na dawo sai in dauko shi mu
taho, to wani lokacin kuma evening ne da ni sannan Yasmin ita ma ta dawo daga school amma kuma
zata je islamiyya, sai in rasa yadda zanyi, daga baya sai nake tafiya dasu duk su biyun in ina evening din
sai in ajiye su a gida baki daya, amma kuma hakan yana nufin Yasmin zata ke missing islamic school dinta
duk ranar da nake evening, sai Umar ya samo musu malamin islamiyya yake yi musu a gida da weekend,
but duk da haka bana jin dadin abin.
Sai dai kuma ina fara aikin naji ba zan iya hakura da shi ba gaskiya. Naji duk wasu problems dina in dai
har na fita daga gida kamar na bar su a gidan ne bani da wani tension in na zama busy sosai har
mantawa nake yi da cewa mijina yana da wani problem. Bani da wani lissafin inda yake ko abinda yake
yi. Farhan har cewa tayi nayi kiba wai, kuma na zama less moody, more focused.
Zuwa aikina bai hana min sauke duk wasu hakkokin Umar ba, musamman na shimfida, kula da gida ma
da girki da sauransu ina iyakacin kokari na duk da ba zan ce kamar kafin in fara aiki ba, amma
kasancewar bama zama sosai a gidan sai ya rage aikin gidan sosai.
Bayan wani lokaci ne Asad ya fara rashin lafiya, mura mai tsanani da zazzabi, kwanan mu biyu a asibiti
kafin ya samu sauki a sallamo shi ya dawo gida.
Bayan mun dawo gida ne Mama tazo gidan tare da wata yar budurwar yarinya. Umar yana nan, nima ina
nan, muka gaishe ta ta amsa mana ciki ciki sai tace yarinyar ta fita waje ta jirata sannan ta dauki Asad
tana yi masa sannu shi kuma ya langwabe mata yana ta mata complain din bashi da lafiya duk kuwa da
cewa ya warke.
Ta kama fada "ba dole kayi ciwo ba Asad tunda iyayenka basu dauki rayuwar ka da muhimmanci ba, ai
suna sane, sun sani sarai cewa ba lafiya ce ta ishe ka ba amma uwarka ta tsiri wani zuwa gurin aiki na
banza da wofi, dan tana ganin tafi karfin a hana ta abu in tayi niyyar yi, tun sanda tace zata fara aikin sai
da na kira ka ai nayi maka maganar bana son aikin nan da zata fara" ta fada tana addressing Umar,
"amma saboda kafi girmama maganar ta akan tawa sai ka saka kafa kayi ball da maganar tawa ka nuna ai
babu komai ai waye waye, ga shi nan zata yi maka asarar Da ai, duk da nasan ko mutuwa yayi ma ba dai
na zuwa aikin zata yi ba tunda ta riga ta saka kanta, bayan babu abinda aka rage ta da shi".
Umar yace "Mama please now, menene hadin aikin ta kuma da rashin lafiyar Asad, ba fa dashi take zuwa
office din ba ballantana ya dauki kwayoyin cuta a can ko wani abu" tace "rufe min baki, sallamamme, ko
yawon da take yi dashi kullum a mota ba zai saka masa ciwo ba? Ko gidan nasu da take kai shi kasan
abinda yake ci ko sha acan?" Umar ya dafe kansa "Mama" ta nuna shi "kar ka sake kiran sunana. Wallahi
a kirji na nake jinka Umar kar ka bari in amayoka, kai ba ka ganin laifin matarka kuma baka so wani ya
gane maka, ta shanye ka tas babu abinda yayi saura sai fanko. Bata so kowa ya rabe ka sai ita kadai, bata
son kowa ya more ka sai ita kadai. To wallahi baki isa ba" ta fada tana nuna ni "na gaya miki ranar nan
kuma zan sake gaya miki wannan yaron da kike gani wanda kika aura bayan ya riga ya zama mutum ba ki
san