Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
sannan na sunkuyo muna kallon juna nace "Allah ya
kiyaye hanya" ya dan bata fuska "amsa ta fa? In zo gobe in karba?"
Na girgiza kai "ba gobe ba, nan da sati biyu ko wata biyu, ko kuma shekara biyu, depending on the mood
din da zan samu kaina a ciki" ya lumshe ido ya bude yace "then I will make sure nayi keeping dinki as
happy as possible har sai na samu amsata, daga nan kuma insha Allah I will keep you happy for the rest
of our lives".
Na matsa baya sannan na rufe masa kofa, wannan ya hana min ganinsa saboda tinted glass din motar,
amma shi nasan yana kallona sai na juya na fara normal catwalking dina feeling his eyes on me, fuskata
dauke da madaukakin murmushi, zuciya ta tana screaming with excitement ta yadda har bana ganin
gaba na sosai, da ace ni kadai ce a wajen , da ace baya kallo na da tabbas na yi tsallen dadi.
Ban ankara ba sai ji nayi munyi karo da mutum,nayi saurin dawo da hankali na jiki na ina kokarin bada
hakuri sai naga Mufida ce ashe, ta bini da kallo, fuskarta dauke da wani yanayi mai wahalar fassara.
Wanda yasa naji murmushin fuskata yana raguwa nace "Mufida.......ammm kije ku tafi.....sai na taho"
tace "he is handsome right? Kuma ya iya kalamai ko?" Na kalle ta sharply, ina tunanin inda zanyi placing
maganar ta, nace "Mufida? Menene wai? Menene problem dinki? Bakya......" Ta dakatar dani ta hanyar
daga min hannu, ba dan na san Mufida kuma daga labaran da take bamu na gidan su nasan cewa Doctor
yayanta bane uwa daya uba daya da zan iya yanke hukuncin cewa kishi take yi dani.
Maganar da tayi ce ta goge wancan zargin amma kuma ta dasa min wani sabon yanayi na daban "Yaya
Umar yaya na ne, uwa daya uba daya muke ni da shi, yana daga cikin mutanen da nake so sosai a duniya.
Ke kuma kawata ce da nake so a cikin kawaye, ban san menene a tsakanin ku ba amma koma menene,
no matter how it ended, bana son in rasa ki a matsayin kawa. Yaya Umar yayi relationships da yawa,
kuma he has left a trail of broken hearts, I don't want yours to add to that. I don't want you to get your
heart broken" sai ta kama fuskata a hannunta ta riƙe a hankali tace "I trust you will do the right thing"
sannan ta sake ni da sauri ta tafi inda yake jiranta.
Ban juya ba har naji ya tayar da motar sannan naji sun zo sun wuce, nabi motar da kallo har suka je gate
aka bude musu suka fita,a lokacin ne kuma motar Abba ta shigo daukana, amma sai naji duk murnar
graduation din da kuma murnar maganar Doctor tana fita daga jikina kamar yadda motar da yake ciki ta
fita daga makarantar. Wani bacin rai da wasi wasi yana replacing dinsu. Na rufe ido na tare da jingina
bayana da jikin bishiyar da take gurin a hankali nace "Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun".
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*💔 Jidda 💔*
*By*
*Maman Maama*
*Episode Three: Pilot*
Free Episode
Tun da muka fito daga makarantar, na juya ina kallon gate din amma sai naji bana jin wani excitement
kamar yadda nayi tunanin zan ji. Na yi ajjiyar zuciya tare da mayar da kaina na kwantar a jikin tagar mota
tare da lumshe idona.
"Bana son in rasa ki a matsayin kawa"
"He has left a trail of broken hearts"
"You will do what is right"
Wadannan maganganun su suke ta yi min yawo a kaina. Muryar yaya Tahir naji "ban taba ganin wadda
bata murna da zuwa gidan su ranar candy ba sai ke. Unbelievable. Wai kuka kike yi?"
Na dago kai ina kallon sa, sannan na kalli yaya Muslim da yake driving, na dan goge idona ina kallon
hawayen da ban ma san sanda suka fito ba nace "ina murna mana yayana, ina murna sosai da sosai,
kawai dai ina jin babu dadi ne zan rabu da kawaye na dana saba dasu shekara da shekaru, wadansu fa
shekarar mu shida tare kaga kuwa ai sabon mai yawa ne"
Yaya Muslim yace "to ba kina da numbers din su ba? Ai zaku ke waya ko? Kuma kina zaki sake wasu
kawayen da har zasu mantar dake wadannan. Ni yanzu few abokai na na secondary school ne yake da
contact dasu, duk kowa ya kama gabansa" sai suka cigaba da hirar abokai a tsakanin su, tunda kusan duk
abokan su daya, ni kuma na koma na kwanta na rufe ido na ina ganin fuskarsa "smile please" na danyi
murmushi sai kuma na bata rai, shin da gaske abinda Mufida ta fada min akan yayanta haka ne ko sharri
take yi masa? Amma kuma akan wanne dalili zata yi masa sharri? In kuma gaskiya ne mai yasa ta gaya
min? Kamata yayi ace ai ta kare image dinsa a matsayin sa na yayanta dan na tabbatar cewa tafi sonsa a
kaina.
Amma dai whatever the case warning ne tayi min, ya kamata kuma inyi wani abu a kai, Amma me zanyi?
Tace ba ta so yayi breaking heart dina, abinda ya kamata nayi shine in nisanta kaina dashi dan kar in fada
cikin soyayyar sa but Oops! am already in. Sai dai zan iya fita tun kafin in nutse har kai, tun kafin inyi
drowning. Menene abinyi?
Zan bawa Farhan labarin sa, nasan kuma in muka hada kai ni da ita zamu samu mafita..........amma me
yasa in na hango rabuwa dashi a matsayin mafita sai inji zuciyata tana min zafi? In kuma na hango cigaba
da alaka dashi a matsayin mafita sai inji murmushi yazo kan fuskata?
******************************************
Sunana Jidda. Sunan Mahaifina Alhaji Habib Mahmud wanda yake haifaffen cikin garin kano ta bangaren
uwa da uba gabaki daya, malamin makaranta ne wanda a halin yanzu yake da matsayin principal a daya
daga cikin manyan makarantun secondary school na jeka ka dawo na maza dake garin kano. Alhaji Habib
yana da rufin asirinsa dai dai gwargwado dan gidan mu bamu taba rasa ci ko sha ko kuma wasu basic
needs na rayuwar duniya ba, duk wadansu bukatun mu Abban mu ya dauke mana su dai dai gwargwado.
Ba zamu kira kanmu direct da masu kudi ba, kamar yadda ba zamu amsa sunan talakawa ba. Mata biyu
Alhaji Habib yake dasu, Hajiya Maryam ita ce uwargidan sa wadda muke kira da Hajiya, sai kuma Hajiya
Ayesha wadda muke kira da Umma, ita ce kuma mahaifiya ta. Mu goma sha biyu Abba ya haifa, takwas
daga ciki yayan Hajiya ne wadanda suka hada da Sa'adatu (Mama Sa'a), Hadiza (Mama Hadiza), Yaya
Shamsu, Yaya Aminu, Yaya Hudallah, Yaya Mukhtar, Yaya Muslim da kuma Aysha (Farhan) wadda take
takwarar Umma kuma autar Hajiya.
A dakin Umma kuma mu huɗu ne, Yaya Tahir ne babba, sai Mahmud (Abbah) sannan ni Hauwa'u (Jidda)
sannan autar mu Maya (Amira) wadda take autar gidan gabaki daya.
Mahaifiya ta Ayesha, yar asalin kasar Ethiopia ce, duk da cewa bata taba taka kafarta zuwa kasar ba har
yanzu. Mahaifinta, Amadi, ya baro kasar su ne ya taho neman kudi har ya sauka a Nigeria kuma ya kafa
kasuwancin sa anan Kano, Allah yayi anan abincinsa yake, saboda son ya koma gida ya saka iyayensa a
lokacin suka nema masa auren kakata Maya, takwarar Amira, dan suna tunanin idan suka yi masa aure
zai koma gida, sai dai ya koma din amma ana daura masa auren sai ya dauko matar tasa ya taho da ita
Nigeria itama, suka ci gaba da zamansu anan a dole yan uwa suka hakura ya zamanto tsakanin su da juna
sai dai ziyara da kuma ta hanyar waya.
Yaya uku Allah ya basu, Umma ta ce babba, sai Aunty Afia, sannan Uncle Salim, shikenan. Umma ta da
yanuwanta babu wani yare ko kabilar da suka sani sai Hausawa tunda a cikin su suka taso, yaren ma
sunfi iya hausa akan nasu yaren, kamanni ne kawai suke tona asirin cewa ba hausawa bane ba, bayan
haka babu wanda zai iya ware su dan har birth certificate dinsu na Nigeria ne. Sai dai kamar yadda muka
samu labari cewa ba'a jima da haihuwa ta ba sai Allah yayi wa kakata rasuwa anan kano, a lokacin ne
babansu ya nemi ya tafi dasu gabakidaya can garin su dan dangi su gansu kuma suyi musu gaisuwa
amma sai Abba ya hana Umma zuwa saboda tana jego na kuma lokacin, wannan abu ne da Umma har
yau bata manta ba saboda a can ne bayan sunje Allah yayiwa babanta rasuwa shima. Wannan yasa
Aunty Afia ce kadai ta dawo Nigeria dan Uncle Salim shima zamansa yayi a can cikin yan'uwa. A inda
yanzu har yayi aure, sai dai lokaci zuwa lokaci ya kan kawo wa su Umma ziyara kuma aunty Afia tana dan
zuwa babu laifi amma Umma har yau bata je ba, ita tayi fushi ta daina tambaya shi kuma Abba bai ma
san fushi tayi ba ya dauka hakura tayi.
Umma na da yan gidan su mutane ne masu rikon addini sosai, sannan suna da dauke kai da hakuri da
juriya da tawakkali duk da dai zama da Hajiya ya chanja Umma sosai, kamar yadda muke ji wani lokacin
Abba yana fada "ba haka halin ki yake ba, ni bansan ki da rigima ba, ni hakuri na san ki dashi" amma yau
da gobe bata bar komai ba. Tabbas duk hakurin ka indai kana zaune da mutum mai irin halin Hajiya to
dole sai ka tanka mata.
Hajiya mace ce mai tsananin fada, mai tsananin kishi, fadanta kuma bai tsallake kan yayanta ba dan
suma ba kyale su take yi ba idan suka yi mata abinda bata so. Bata son Umma ko kadan, ko zaman hour
daya idan kayi da ita zaka fahimci bata son Umma, in kuwa kana son kaga bacin ranta to ka fadi wani
alkhairi a game da Umma ko kuma abinda ya shafe ta.
Wannan rashin jituwa ya wuce daga tsakanin su ya tarar har kan mu mu yayan su. Manyan yayan Hajiya
duk sunyi aure tun muna kanana. Ni da nake yar Umma ta uku nice sa'ar autar Hajiya (Farhan), wannan
banbancin shekarun ne ya kara saka distance a tsakanin mu da rashin shakuwa tunda bamu taso tare ba
musamman Mama Sa'a, Mama Hadiza, yaya shamsu da yaya Aminu, duk bamu wani saba dasu sosai ba
dan ko mun hadu tsakanin mu ba ya wuce few words, words din ma kuma most of the times marasa
dadi. "Barbarar yanyawa" shine sunan da Hajiya take kiran mu dashi ita da manyan yayanta.
Abba mutum ne mai rikakken ra'ayi, babu wanda yake saka shi kuma babu wanda yake hana shi, hakan
kuma ya samo nasaba ne da cewa bashi da mahaifa a raye sai kannen mahaifan sa wadanda kuma
yawanci a gurinsa suke samun kwandala dan haka babu wanda yake iya ce masa "a'a". In yayi magana
abinda kawai yake bukatar yaji shine "to" baya son jayayya ballantana shawara. Baya kuma shawara da
kowa idan zaiyi abinsa sai dai kawai ki ga yayi, wani lokacin ma sai yayi sannan zaku sani daga baya.
Baya wasa ko kadan. Ba wai yana takura mana bane ba ko kuma baya son mu a'a ba ya nuna mana
soyayyar sa ne, typical uban bahaushe, zai providing dukkan basic needs din mu sannan zai tsaya a
dukkan al'amuran mu amma babu emotions a ciki.
Sannan kuma yana da wani ra'ayi wanda da ban fahimce shi ba sai da na kara girma sannan na fahimta,
sai kuma na lura ba shi kadai bane ba yawanci mazan hausawa suna da wannan ra'ayin, suna kallon
mata a matsayin masu karamar kwakwalwa kuma weak ba zasu iya yin tunanin komai ba, ba zasu iya
bayar da shawarar komai ba, ba kuma zasu iya tsayawa kansu ba ballantana su tsayawa wanin su sai dai
su a tsaya musu.
Wannan dalilin ne ya saka baya barin ƴaƴan sa mata suyi dogon karatu kafin yayi musu aure dan yana
ganin za'a iya yi musu wayo a yaudare su a lalata su, ko kuma su fitsare su daina jin magana su daina bin
umarnin sa suyi tunanin dai dai suke da maza suma.
Sai dai deep inside him yana son suyi karatun su mori ilimin su, wannan ya saka duk wanda zai aura wa
yarsa yana yin yarjejeniya da su cewa zasu barsu suyi karatu bayan aure, har alkawari yake yi cewa shi
zai dauki nauyin kudin karatun burinsa dai kawai a bari din, amma cikin ikon Allah kaf surukan nasa babu
wanda ya cika masa wannan burin, daga an shiga sai ciki, sai reno sai wani cikin, sai kuma ace an tara
yaya karatu ba zai yiwu ba. Aunty Hudallah ce kawai tayi diploma a Legal, shikenan kuma bata kara
komai ba.
Abba yakan yi mita akan haka wasu lokutan, amma bai taba samun surukan nasa yayi musu mitar ko
kuma ya tilasta musu suyi abinda yake so ba, saboda ya riga ya saka a ransa cewa duk wanda ya auri
yarsa kuma ya rike ta bai sako masa ita ba to ba karamin rufa masa asiri yayi ba.
"Dakin miji shine babban rufin asirin mace. Duk abinda kuke so na daga kudi ko wani abu ku zo ku same
ni in dai ina da shi zanyi muku, amma duk wata matsala data shafi mazajen ku ku barta a cikin ku, bana
son ji, ko iyayen ku mata kar ku gaya wa sirrin auren ku. Ku je ku sasanta a tsakanin ku ba tare da kowa
yaji ba, wannan shine halin mace ta gari".
Wannan ita ce nasihar da mukan ji yana yiwa yayyen mu mata idan sunzo gaishe shi. Wani lokacin idan
yana cikin fada yakan ce
"Duk wadda taki bin mijinta a cikin ku babu ni babu ita. Duk wadda ta yi yaji wai dan tana ganin mijinta
yayi mata wani abu na rashin kyautawa to ta tafi gidan wani ba gida na ba. Duk wadda ta kashe aurenta
to ta nemi wani uban bani ba. Duk wadda ta jawo min magana ta zubar min da mutunci Allah ya isa
tsakani na da ita"
Wannan maganar, hatta mu da bamu yi aure ba a lokacin, mun rike ta tamkar karatu a kan mu....
Har yanzu ina iya tuno yarintar mu da irin cin zalina da yaya Muslim ya ringa yi har sai da ya kasance ko
tsakar gida bana iya fitowa dan inya kama gashina ya murde sai nayi kamar zanyi fitsari a wando, sai da
yaya Tahir ya ritsa shi yayi masa duka sannan na samu sa'ida amma duk da haka in dai baya kusa in ya
ganni sai ya dake ni, daga nan kuma sai rigima ta balle tsakanin Umma da Hajiya.
In short, abinda nake so in nuna muku shine gidan mu babu zaman lafiya, babu soyayya a tsakanin mu
da yanuwan mu, akwai yan ubanci sosai a tsakanin mu da yan uwan mu.
But there is one exception.......
Ni da Farhan tamkar tagwaye ne, babu yadda iyayen mu mata basuyi ba dan su raba tsakanin mu tun
muna kanana amma basu samu nasara ba, Farhan ce babbar kawata, ita ce kuma babbar aminiya ta tun
kafin in san menene kalmar aminiya, na dai san duk sanda muka hadu sai ma bata labarin duk abinda ya
faru a lokacin da bama tare ita ma kuma sai ta bani. Kasancewar kwana bakwai ne kawai tsakani na da
ita ya saka ajin mu daya aboko da islamiyya, wannan yasa dole iyayen mu mata suka barmu muke tafiya
tare, in mun dawo gida ma tare muke karatu, ina kaunar Farhan sosai dan har cikin zuciyata bana jin
suna da banbanci ita da Amira.
Bayan kammala primary school din mu ne sai Farhan taci jarabawar da muka rubuta ta day science ta
kano, ni kuma na fadi, lamarin da har yau Umma ta kan alakanta shi da kasancewar kanin Hajiya a cikin
masu ruwa da tsaki a gurin marking jarabawar "ita ta saka aka kayar dake, babu wata faduwa da kika yi,
bata so ki je ne" wannan rikicin ya saka Abba ya yi ta cuku cuku har ya samo min admission a GSSS
Taura, ta hanyar principal din makarantar wadda suke da dangantaka a matsayin su na masu aiki iri
daya.
Makarantar daga senior ta fara,amma sai akayi sa'a a shekarar suka dauki jenior section da niyyar zasu
raine su, naci sa'a na fada cikin wannan tsarin. Abba ya so ta bashi space din mutum biyu sai ya hada ni
ni da Farhan amma bai samu ba, dole ya hakura aka kaini ni kadai aka bar Farhan a Day Science.
Zan iya tunawa da ranar da aka kaini ina ta kukan rabuwa da gida da kuma rabuwa da Farhan sai aka
kawo wata itama daga Kano itama tana kuka, aka hada mu seat daya malamar da take ajin tace mun
zama kawaye tunda muna kuka. Sai kuwa gashi kawancen namu ya dore, kusan halayyar mu daya da ita
da kankantar jiki, da yanayin mu. Sunan ta Halima Usmam Kollere, bafulatana ce, nima kuma da yake
mutane da yawa basa gane kabila ta sai ake min kallon fulani dan haka kawancen mu ya dace sosai.
Babban abinda nafi tunowa a tare da Halima shine yayanta kuma saurayinta Sadauki. I doubt in ta ma
san soyayya a lokacin, dan ni dai ban sani ba, abinda kawai na sani shine duk sanda kuka zauna sai ta
baku labarin Sadauki, kalma biyu uku in tayi to ta hudun sunan Sadauki ce. Babu wanda ya san Halima ba
tare da yasan sadaukin ta ba. I can remember in yazo mata visiting har satar jiki muke yi muje muyi ta
leken su muna dariya.
Sai dai.......muna gama jss munyi hutu mun dawo Halima bata dawo ba, muka yi ta cigiyar ta sai wani
malami da yake abokin baban ta ya gaya mana babanta ya rasu sannan kuma anyi mata aure, wannan
labarin ya girgiza mu sosai, mun kuma yi takaicin rabuwa da ita da kuma alhinin mutuwar mahaifin ta,
sai kuma muka yi mata murnar auren saurayin ta da take mutuwar so. Sadauki.......
Bayan munyi hutu har gidan su naje, saboda na taba karbar address dinta sanda muna tare, amma sai na
tarar da gidan a rufe, na tambaya a makota aka gaya min mai gidan ya rasu su kuma sun tashi daga
gidan. Wannan shine rabuwata da *Diyam*
Bayan mun rabu da Halima, bayan mun shiga ss1 ne aka kawo Mufida, ita tayi replacing Halima a gurina.
Zainab Muhammad Gidado ƴa ce a gurin attajiri Alhaji Muhammad Gidado Fata, mutumin daya shahara
ya kuma yi suna akan sana'ar sa ta siyan fata, sarrafa ta tare da fitar da ita zuwa kasashen waje da siyar
da ita a can. Sana'ar sa ta karbe shi kuma yayi arziki da