Chapter 24 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   24 / 101

69K to 72K   out of 300.2K words

hannun sa yana nuna min "wannan agwalumar
sai da na zagaye Kano kaf kafin in samo miki ita, shi yasa ban dawo da wuri ba"



Sai a lokacin na tuna da cewa na bashi sakon agwaluma. Nayi kokarin hadiye wannan dogon abu sannan
nace "sannu da zuwa dear" sai ya bude min hannayensa. Come and give me a hug now, don't just stand
there like a statue"



Na yi kokarin takawa amma sai na kasa, sai ya ajiye ledar shi ya taho ya saka ni a kirjinsa ya rungume tare
da kissing saman kaina. "Kinyi kyau sosai Baby" ya sunkuyo yayi kissing ciki na. "Hey there little Jidda.
Kina ta jiran Daddy ko?" sai kuma ya dago fuskata "what's wrong. Yana ganki wani iri ne" sai ya saka
hannunsa a wuyana yana testing temperature dina. "jikin ki yayi zafi, are you sick?"



Yadda ya nuna concern dinsa sai naji ya taba zuciyata. Karyar banza ma suke yi wadancan mutanen a
kansa, har zasu saka inyi tunanin daga wani guri yake ba daga inda yace min ba, daga wani mummunan
guri. Na girgiza masa kai "no am fine. Kawai dai mood dina ne bana jin dadinsa" ya sake ni "ahh. The
mood swings. Me zanyi ne in cheering dinki, ga agwaluma nan dai na siyo miki, in still baki ji dadi ba in
nayi wanka sai in fita dake yawo. Ko muje gidan Aunty Afia ko gidan yaya Mubaraka duk wanda kika
zaba"



Na je na dauki ledar daya ajiye ina jin kamar babu abinda na tsana irin agwaluma. Na ajiye nace "na
gode. Ga abinci nan a dining zaka ci ko a nan" na nuna jikinsa "bara in yi wanka first. Ko zaki zo ki taya
ni?" Ya fada yana kashe min ido. Na sunkuyar da kaina bance komai ba. Yace "not in the mood right?"
Sai yayi ajjiyar zuciya "yaya dan Adam zaiyi da ransa tunda yayi wa matarsa ciki dole ya dauki hakurin
duk abinda zai biyo baya"
Ya wuce ni ya shiga corridor.



Na zauna akan kujera ina rungume ledar agwalumar daya siyo min a kirjina. Ina sake tambayar kaina
suwaye bakin da nayi dazu? Su waye su da har zasu zo su saka min shakku akan mijina? Har suna dariyar
cewa nace yana office, har suna making jokes with it, making me think yana wani gurin da bai dace ba
ashe shi ni ya tafi nemo wa abinda nace masa ina so. Sai naji banji dadin yadda nayi masa ba.



"Karyar banza" na fada a fili, sai maganar tawa ta tuno min dawani memory na last time da na fadi
wadannan kalmomi. Lokacin da Jamila ta same ni a daki ranar kunshin biki na, naji kunnuwa na suna
dawo min da kalamanta dana tura su na boye a deepest part of my mind.



"Karyar banza" na sake maimaita wa ina kokarin hada memory din maganganun ta dana wadannan
matan in tura su zuwa inda na fito da natan yanzu. Amma sai suka ki tafiya, suka tsaya suna zagaye a
kwakwalwa ta.



Na ajiye ledar nabi bayansa na tarar har ya shiga wankan sai na bishi toilet din na tsaya a bakin kofa ina
kallon sa yana cire kaya. Ya langwabe kai "please ki zo ki taya ni mana. I will cheer you up i promise you.
Duk wannan mood din zan chanja shi" naje na karasa balle masa buttons din rigarsa sai ya fara kokawar
cire min tawa.



Na rike rigar "ni fa nayi wanka na wallahi" yace "wanka ai baya yawa, sake wa zaki yi" na fara mita "kai
wallahi sai ka saka mutum mura kayi ta saka mutum wanka kamar wani kwado" ya karasa cire rigar
sannan ya jani cikin shower ya hadani da jikinsa da hannu daya daya hannun kuma ya kunna shower
dashi, ya sunkuyo dai dai fuskata yace "I will warm you up" sannan ya hade bakin mu......



Sai daya tabbatar ya karbi dukkan abinda yake so ya karba sannan muka fito daga toilet din, ina ta mitar
ya sakani na jika gashina bayan da kyar na samu nayi drying dinsa dazu. Shi kuma as usual yana ta lallaba
ni. A karshe ma sai ya dauko hand dryer dina yace zai yimin drying gashin.



Na zauna a gaban madubi yana min drying gashin ni kuma ina shafa mai, sai nayi masa maganar baƙin
sa.
"Dazu kayi baƙi dear" yana cigaba da abinda yake yi yace "nayi baƙi ko munyi baƙi? Su waye?" Nace
"oho. Nima abinda nake so ka gaya min kenan" ya dakata da abinda yake yi muna kallon juna ta
madubin, his face looked tensed.



Nace "daya daga cikin su tace min sunan ta Zuwaira. Tace in na gaya maka haka zaka gane kuma zaka
gaya min wacece ita"



Ya ajiye dryer din yayi two steps back. In ka kalli fuskarsa zaka dauka fatalwa ya gani. "What?" Ya
tambaya his voice deep. Na mike tsaye sannan na juyo muna kallon juna. Na gyara bath robe din jikina
ina kara studying dinsa, zuciyata tana so tayi placing reaction dinsa.



"Su waye?" Na tambaya. Ina kallon shi ya hadiye wani abu a makogwaronsa sannan yace "how can I
know. Ni da ban gansu ba, you tell me su waye ke da kika gansu" naji mamakin maganar sa.



"Ban gane ba. But you sounded and acted as if ka san su, as if kayi mamakin da nace maka sun zo" ya
tako ya dawo gaba na yana kallon fuskata. "Ni ban san wata mai irin wannan sunan ba, ni ko a family da
friends dina da kuma abokan aiki na ban san mai irin wannan sunan ba. Yes I was surprised saboda kin ce
sun ce zan fada miki ko su waye su so I automatically know sunzo su tayar min da fitina ne"



Nace "but yanayin yadda suka yi magana ya nuna sun sanka Umar. Har magana fa naji sunyi akan wai an
chanja tsarin gidan da ba haka yake ba......."



Ya dafe goshinsa, looking frustrated. "They can be anybody Jidda. Zasu iya zama yan leken asiri ko
wadansu masu mugun nufin ko kuma su zama one of those girls dana fada miki might be crushing on
me, yanzu sunji nayi aure shine zasu zo su gaya miki maganar banza. And you are sounding as if kin
yarda dasu haba Jidda. Wacce yarinya ce kuma zata zo tace tasan gidan nan gidan da in ba sisters dina
ba bana jin akwai wanda ya taba zuwan sa kafin muyi aure, nima kaina ban taba kwana a gidan ba sai da
kika shigo shi"



Na dauke kaina gefe ina lissafa maganganun sa. They sounded real. Zata iya yiwuwa da gaske a cikin
masu son nasa ne shine zasu zo da wannan maganar to hurt me.
Ganin maganar ta shige ni sai ya kamo kafaduna. "Did they hurt you?" Na girgiza kaina "not physically"
ya hade rai "me da me suka ce?" Nace "just some stuffs about you. Wai ba daga office kake ba. Wai kana
can kana jiran ta. And they said something about cikina"



Ya bude ido ya dora hannu akan cikin kamar mai protecting dinsa "me suka ce akan cikin?" Sai yanzu naji
dacin maganganun su yana kara kona zuciya ta "na dora nawa hannun akan nasa a saman cikin, hawaye
ya silalo daga idona nace "wai kafi gwanancewa ta wannan bangaren, wai za'a iya baka numbar yabo a
wajen"



Ya saki kafada ta ya saka hannunshi a cikin gashinsa looking very angry, "damn it" sai naji banji dadin
yadda na bata masa rai ba. Dana sani ma da ban gaya masa ba na bar maganar a raina kawai ni kadai tun
da dai karya suke yi.



Ya juya ya daki kofa da hannunsa sai kuma ya rike hannun alamar yaji zafi sannan ya bude kofar ya fita.
Nayi sauri na nemi kaya na saka a jikina nabi bayan sa. Baya falo, na dawo na duba dakina can ma baya
nan har na fara tunanin ko fita yayi sai kuma na leka naga motarsa tana nan.



Ina kokarin tashi inje inyi sallar da naji ana yi a masallaci sai gashi ya sake shigowa daga waje, ransa a
tsananin bace kamar ma yafi sanda ya fita bacin rai. Bai ce min komai ba ya wuce ni ya shiga dakin sa ya
rufe kofa. Na tashi na bishi sai naji yayi locking kofar dan haka na wuce nawa dakin nayi alwala na tayar
da sallah.



Na jima akan sallayar bayan na idar ina ta saka wa da warwarewa. Ina ta so in dai daita tunani na ya tafi
a direction daya amma na kasa. Shin menene gaskiyar maganar? Da gaske bai san su ba? Da gaske sunzo
ne dan su hada mu? Ko kuma dai akwai abinda yake boye min kamar yadda na gani a fuskar sa a first
moment dana kira sunan Zuwaira. Who is she?"



Ban san amsar ba, amma kuma na saka a raina cewa tabbas sai na binciko ta na kuma warware kullin
data daura min a zuciya ta.



Anan na zauna har aka kira sallar isha nayi sannan na sake fita inga ko ya fito, banji motsinsa ba na dawo
na kwanta a falo ina chatting da friends dina, trying to take my mind off duk abinda ya faru, daga baya
kuma na mike na hada tea na sha sannan na tafi dakina na fara shirin kwanciya.
Sai da na gama komai na kashe fitila na kwanta sannay kuma na fara jin haushin Umar, me yasa zaiyi
fushi da ni kuma? Me nayi masa? No da akayi wa laifi ba ni ya kamata a lallaba ba kuma sai ayi fushi dani
a rufe min kofa? Nayi tsaki ya kai cikin charbi, in naji haushin sa sai kuma inji haushin kaina da nake jin
haushin sa.



Zuwa can bacci ya fara dauka na sai naji motsin an bude kofa an shigo dakin. Ya kunna fitila sannan ya
kashe na hawo gadon ya shigo cikin rufar da nake ciki sannan ya saka hannu ya jawo ni ta baya ya hada
ni da kirjinsa, nayi kamar banji shi ba sai ya fara min magana



"Am sorry Baby, na rufe dakina ko? Raina ne a bace bana son zama inda kike kar in miki tsawa ko in gaya
miki wata magana marar dadi, shi yasa na rufe kaina sai da na huce tukunna. Kiyi hakuri kinji?" Yayi
kissing bayan kunne na.



Nayi shiru nayi kamar banji shi ba. Amma kuma a zuciya ta sai naji na daina jin haushin rufe kofar da
yayi. Ya cigaba da cewa. "Dama na taba gaya miki tun kafin bikin mu cewa zamu iya samun matsala irin
wannan a gidan nan. Akwai yammatan da ni ban ma sam dasu ba da suke kallon kansu a matsayin
yammata nane, while ni kuma ba haka bane ba a wajena, kuma nasan wadansun su dole zasu iya yin
kokarin yin wani abu dan su shiga tsakanin mu, bazan iya hanasu ba Jidda tunda bansan plans din su ba
amma ke zan iya warning dinki dan ki san da su kuma ki toshe kunnuwan ki da kuma zuciyarki daga
dukkan abinda zasu zo su gaya miki"



"Nasan akwai wadanda zasu iya zuwa su yi kokarin hada mu, yes, amma bansan har zasu kai ga fadar
maganar da zata saka miki zargi na a zuciyarki ba Jidda. Wannan shine abinda ya bata min rai sosai.
Kuma the fact that na gani a idonki cewa kin yarda da abinda suka ce shi yafi komai daga min hankali.
How can you believe such a lie?"



Ya fada kamar zai yi kuka. Na juyo ina kallon sa, sai kuma na gyara kwanciya ta na juyi sosai muna facing
din juna, na saka hannu ina wasa da sajensa sannan nace "ba wai na yarda da maganar su bane ba akan
ka. Ba wai na yarda da maganganun banzan da suka fada bane ba. But I believe somehow akwai sanayya
a tsakanin ku. Sun sanka tabbas, kuma sanda na ambaci sunan yarinyar nan sai naga kamar kai ma ka
gane ta. I just want the truth shikenan"
Sai ya cire hannu na daga fuskar sa ya fara kokarin mikewa. "Na gaya miki ban san ta ba, ban san taba.
Me yasa kuma zaki cigaba da tambayata? Ni da ace nasan su waye da yanzu suna hannun police dan ba
zan kyale su ba wallahi" na mike zaune nima nace "well, I can describe them, and their car. Har number
din motar na rike" ya juyo da sauri yana kallona duk da cikin duhu ne. Na daga masa kafada "maybe in
na bada description din su police zasu iya nemo su"



Sai ya mike bai ce komai ba ya fita daga dakin, har na dauka wani fushin ya kuma yi sai gashi ya dawo da
jotter a hannun sa da biro, ya kunna fitila sannan ya zauna a bakin gado.



"Oya fada min duk abinda zaki iya tunawa in rubuta, gobe sai in biya ta police station in shigar da
complain, cos zasu iya sama masu yiwa robbers leken asiri. Na kuma gaya wa mai gadi daga yau kar ya
sake barin kowa ya shigo sai yazo ya gaya miki waye kuma kin yarda tukunna"



Na gyada kai sannan na fara zayyana masa tiryan tiryan duk abinda zan iya tunawa na daga kamannin su
da kuma motar da suka zo da ita da kuma maganar da suka yi. A karshe nace "kamar daya daga cikin su
tana yin gyaran jiki na mata. Dan naji tayi magana mai kama da haka. Kuma kamar shago ne da ita da
take yin aikinta a ciki" sai na ga ya dan ajje biron ya dan dage goshinsa kadan sai kuma ya sake dauka ya
rubuta abinda na fada.



Sai da ya gama ya ajiye takardar, ni kuma na dauka na tabbatar ya rubuta duk abinda na fada sannan
nace masa "baka ci abinci ba, kar ka kwanta da yunwa bara in kawo maka nan kaci" ya girgiza kai "no,
kiyi kwanciyar ki kawai, zanje in ci" ya sauka daga kan gadon kamar zai fita sai kuma ya juyo yana min
murmushi "but don't sleep fa. Ki jira ni inyi miki tatsuniya" na gyara kwanciya ta "tatsuniya bayan wacce
kayi min dazu? Nagode Allah ya saka da alkhairi" ya marairaice "mutum dai zaiyi bacci ai zai so a lallaba
shi ko?" Na girgiza kaina. "Ni zan iya lallaba kaina"



Washegari da zai fita ni da kaina na dauko takardar na saka masa a hannun sa "kar ka manta" ya saka a
aljihunsa "ina sane ai. I will never forget"



Sannan ya sunkuya gaban cikina "bye bye little Jidda" na juya ido na "ko kuma little Umar ba" ya daga
yana dariya "kar kiyi wa kanki wannan fatan. I wasn't that cute sanda ina yaro dan lukuti ne da dan
mitsitsin hanci da baki, duk kumatu ya cika fuskar" nayi dariya "zan so in ga pictures din ka" ya zaro ido
"ko da wasa ba zanso ki gansu ba, salon ki ce kin fasa. Ai da na girma a haka ko da na tabbatar baki ce
min yes ba" na girgiza kai na. "Sanda na fara sonka ban ma kalli fuskarka ba. Bana jin kuma ko wanne
kama zan ganka da ita a lokacin zata chanja abinda naji a zuciyata a game da kai. Besides, lukutayen
mutane are cute"



Ya bata rai "kar kisa in fara hada kiba dan kike ce min cute fa" sai muka yi dariya tare. Forgetting about
all the tensions na jiya.



Sai dai ban manta ba, yana dawowa ya cire kayansa na duba aljihun hoping inga babu takardar but it was
there, exactly yadda na ninke ta daga alama ma ko bude ta ba'ayi ba. Na tsaya da ita a hannu na zuciyata
tanayi min zafi, me hakan yake nufi? Dama bashi da niyyar reporting din kawai ya shirya min karya ne?
Dama kamar yadda nayi tsammani already ya santa, bashi da niyyar bincikar ko wacece ita" na ajiye rigar
da sauri na tafi zanje falo gurinsa amma sai zuciyata ta tunamin wani abu. In naje ma zai iya ce min
mantawa yayi, ko kuma ya sake shirya min wasu kalaman. Ni kuma yanzu so nake in tabbatar idan har da
gaske ya sanya din.



Na mayar da takardar inda na ganta sannan na ajiye kayan kamar yadda ya ajiye su na fita, na tarar dashi
a falo suna wata da Mama, suka gama ya bani nima muka gaisa tana tambayata saukin jiki. "Akwai wasu
magungunan gargajiya na yarabawa, in zan dawo zan taho miki dashi suna taimaka wa mata sosai
musamman in ciki yayi nauyi da kuma lokacin haihuwa" nayi murmushi kawai ina jin dadin yadda take
damuwa da ni da cikina.



Bayan na ajiye wayar ne nace masa "ya zancen zuwa gurin police din kuwa? Kaje ?" Bai kalle ni ba yace
"naje, can na fara zuwa kafin ma in karasa asibiti, sun karbi takardar kuma sun tabbatar zasu binciko min
su, sunce babu matsala musamman tunda akwai plate number din mota ba zasu yi wahalar samu ba"



Na dauke kaina gefe ina jin tamkar garwashin wuta ya dauka da hannun sa ya saka min a zuciyata. Wasu
hawaye masu zafi suka taho min nayi sauri na hadiye su amma sai naji tamkar sun kara min zafin da yake
kirjina. Wato wasa kawai yake min da hankali tun jiya. Tun jiya ko kuma tun kafin muyi aure?



Tabbas ya san su, ya san wacece wannan Zuwaira din, shin amma abinda ta nuna min akwai a tsakanin
su menene gaskiyar wannan maganar? Sai naji ba zan iya zama a gurin ba dan sosai nake so inyi kuka. Na
tashi na shiga kitchen na turo kofa sannan nayi kuka na silently, still maganar Yaya Jamila tana sake
tugging zuciya ta. "I gave him myself" na girgiza kaina da sauri. "No, please God no"
Na jima a kitchen din sannan naji motsinsa ya taho, na dauko albasa na fara yankawa duk da babu
amfanin da zanyi da ita, ya turo kofar yana kallona "Baby zan dan fita amma bazan jima ba zan dawo,
zamu hadu da Bashir ne" ya danyi dariya "kinsan mutumin yana ta kokarin ya shiga daga ciki fa, to gidaje
zan taya shi dubawa" ban kalle shi ba kuma banyi dariya ko murnar cewa Bashir zaiyi aure ba dan sam
hankali na baya gurin maganar sa, I was in no mood for that.



"A dawo lafiya" na fada shortly, hoping zai fita ya barni da hawayena, amma sai naga ya karasa shigowa
"are you okay?" Ya fada cikin concern. Naji kamar in kikkifawa kyakykyawar fuskar sa mari amma sai na
dauke kaina na cigaba da yankan albasa ta. "Lfy ta kalau fa. Kaje kawai a dawo lafiya" sai ya ja kujera ya
zauna. "In ba kya so in fita na fasa, zan kira shi ince ya sake booking dina next time. Yanzu Baby bata so"



Na juyo ina kallon sa, sai kuma ya mike ta karbe chopping board din da yake hannuna ya ajiye a gefe "ji
albasar nan yadda tasa idon ki yayi ja? Me zaki yi da ita wai?

24 / 101