Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
ce, free woman mai cikakken yanci ba baiwa ba, Allah ya baki daraja mai yawa
kuma ya baki zabi a duk al'amuran rayuwar ki. A cikin zabin nan har na zama da mijinki ko akasin haka.
Allah ya bayar da saki a hannun maza, amma saboda adalci irin nasa sai ya bawa mata suma nasu damar,
ba wai damar ki ce ki saki mijinki ba a'a, sai dai zaki iya zuwa Shari'a court gaban alkali ki ce kina so a
raba auren ki da mijin ki ba kya son cigaba da zama da shi. Wannan dama ce da addinin ki ya baki. Kuma
alkali zai saurare ki tunda ya san damar ki ce. Zaki iya fadar kowanne dalili a matsayin dalilin da yasa kike
son rabuwa da shi. Zaki iya cewa ma ba kya son sa ne yanzu ba kya son cigaba da muamalar aure da shi,
shima wannan dalili ne da addini ya yarda a duba. Tabbas addini dan sulhu ne, musamman tunda ana
maganar aure za'a yi kokarin yi muku sulhu, za'a kira shi da shi da waliyansa da naki sai ace ku je kuyi
sulhu. Zaki iya amfani da wannan damar a gaban iyayensa da iyayenki da wakilin alkali wanda za'a hada
ku da shi ki fadi duk labarin da kika fada min yanzu. There is a very high chance na cewa Umar zai rikice
yayi admitting a gaban su sannan yayi kokarin rokon su su baki hakuri. Daga yayi admitting magana ta
kare, alkali zai raba auren ku dan addini bai amince da aure tsakanin mumina da kuma fasiki ba. Alkalai
da yawa suna raba aure in an tabbatar cewa miji ko mata fasiki ne".
"Idan kuma a zaki iya fadar wannan maganar a gaban waliyyanku ba saboda tayi miki nauyi ko saboda
kina son kiyi preserving mutuncin sa da naki da na yayanku to kina da second option, zaki iya dagewa
lallai ke ba kya son sulhu ke rabuwa kike so. To anan alkali zai nemi ki dawo wa da Umar sadakin da ya
bayar lokacin da zai aure ki. Wadansu alkalan suna neman a dawo da har saura kudaden da aka kashe na
al'ada musamman idan ba'a jima da yin auren ba, in an jima ma yawanci sadaki kadai ake karba tunda
shine farilla sauran duk al'ada ce. But ya danganta da alkalin. But either way zaki bawa Umar wani abu
alkali zai baki takardar da take nuna cewa ya raba auren ku. Shikenan."
Na yi shiru ina tunani, ta bani zabi har biyu, hanyoyi har biyu da zasu bullo da ni zuwa freedom from
Umar, but kowacce akwai kalubale a cikin ta. Hanya ta farko zata wanke ni amma zata yi leading to
abinda bana so, tonuwar asirin Umar ga jama'a tunda ba iyayen mu ne waliyyan mu ba, ni abokin Abba
ne shi kuma kanin Baba, wadanda bani da tabbas din zasu boye maganar.
Option na biyu kuma ni zan fada a ciki, everyone will blame me for breaking my marriage for no reason,
amma na shirya karbar blame din indai har ba za'a shafawa yayana fentin babansu ba. Sai dai kuma
iyayena, Umma da Abba su nake so su fahimce ni kuma su goya min baya. If I can get them to do that
then I will go for the second option.
Nace "matsala ta shine iyayena. Banaso in yi komai ba tare da amincewar su ba. Bana so suyi fushi da ni"
tace "tabbas. Nima ba zanso kiyi komai ba tare da yardar su ba, dole sai mun nemo yadda zamu bi su
fahimce ki tukunna" na fara jujjuya hannuna "ba wai fahimtar ba Diyam, yadda Abba zai tsaya ya saurare
ni ma nake nema ni yanzu. Ita kuma Umma ba zata taba yarda cewa rabuwa da Umar a yanzu shine dai
dai ba. Yajin da nayi ma already babban laifi ne a gurin Abba ballantana kuma guduwar da nayi. Ni tsoro
nake ji ma kar ya tsine min akan wannan guduwar"
Ta rike hannuna "no ba zai yi haka ba Jidda, he is your father kuma yana son ki sosai in his own way.
Wannan way din muke so mu samu muyi using mu jawo hankalin sa. Ban san how ba but nasan rashin
sanin inda kike a yanzu will help him alot in realising how much he loves you. In kin yarda ki cigaba da
zama anan gidan har zuwa lokacin da zamu ga is the right time da zaki koma gida, lokacin da muka ga in
kika koma zai zauna ya saurare ki"
Na ce "ba zaki gane ba, baki san halin Abba ba. Shi fa Abba tun da nake da shi babu wanda na taba jin
yace masa a'a, komai yace eh ake ce masa. Sai ni da ya cewa in koma gidan Umar naki kuma na gudu na
bar gidan, in Abba ya kama ni kashe ni ne kawai ba zaiyi ba wallahi" tace "kiyi hakuri. Ki daina fadar haka.
Insha Allah in muka hada kai dani da ke zamu samo zaren yadda zamu warware matsalar. In Sadauki ya
dawo gobe zan yi masa bayanin ki da duk problem din ki. Insha Allah zai shiga cikin maganar kuma zai yi
using that smart brain of his ya samo mana yadda zamuyi mu shawo kan Abba. Kuma zan nemi
amincewar sa akan ki cigaba da zama anan kafin mu shawo kan matsalar. Zaki zauna ai ko".
Nayi shiru ina tunani. Tabbas gidan Diyam is perfect hideout for me and my kids. Umar bai santa ba, I
might have mentioned her name to him once or twice a matsayin kawata dana rabu da ita tun a junior
school amma bana jin ma zai tuno sunan ballantana wani abu da ya shafe ta. Mufida bata san ta ba dan
sai bayan Diyam ta bar school din sannan Mufida ta shigo. Yan gidan mu basu santa ba, maybe tun sanda
muna tare da ita zasu san sunanta amma tunda aka cire ta daga school akayi mata aure na daina
maganar ta a gida suma kuma haka. Friends dina kuma da suka santa sun san bama tare shekara da
shekaru, bana jin akwai wanda zai kawo ta ransa in ana nemana.
But amma babu takura? Inje gidan kawa in zauna har da yara?
Nace "bana so in takura muku Diyam, gidan ki daga ke sai mijinki da yaran ku kuma kawai sai inzo in
zauna muku? Babu dangin iya babu na baba?" Sai ta mike "in kin yarda zaki zauna shine kadai abinda
nake bukatar ji. Ni na riga nayi alkawarin I will help you get through this, in ba kya son gidan nan zan iya
kama miki haya ki zauna for the mean time, amma ni nafi son ki zauna anan din saboda security"
Sai na mike nima ina rike hannayena a cikin juna "zan zauna din to, Nagode sosai Diyam. Allah yasa
wannan taimakon da zaki yi min ya kasan ce sanadiyyar da ubangiji zaiyi farin ciki da ke" tayi murmushi
tare da cewa "ameen. Nima Nagode da wannan addu'ar".
A ranar da yamma ta fita da kanta tayo mana siyayyar kayan sawa set biyar biyar ni da yara, da undies da
sauran kayan bukata, da nayi mata maganar kudi sai tayi fushi, ni kuma ji nake kamar na dora mata
nauyi da yawa ya kamata ace ta barni da siya mana kaya da kudina tunda akwai kudi a tare da ni sai dai
haka na hakura dan nasan bazata karba ba.
Washegari, lokacin kwana na biyu a gidan, kwana na biyu rabona da gida, da yamma mijinta ya dawo
kamar yadda ta fada kuma yadda naga tana ta shirin taryar sa tun safe, sai na tuno da zuwan Umar Zaria
sanda nayi ta shirin dawowar sa da kuma tsarabar da ya dawo min da ita. Sai na samu kaina da yi mata
addu'ar Allah ya kare mata mijinta ya raba ta da mugun ji da mugun gani irin wadanda nayi ta haduwa
da su.
Muna tare da ita a falon ta ya dawo, ya mike da sauri ta tafi taryar da yayin da ni kuma naji ni odd a
gurin, banso ya shigo ya same ni ba. Na dauke ido na daga kansu a lokacin da ta dane jikinsa shi kuma ya
daga ta suna dariya. Sai naji sun tuno min da wani abu, naji zuciyata ta motsa da memories masu cike da
zaki da kuma daci.
Ina jin tana masa Magana kasa kasa, ban san abinda take cewa ba amma na fahimci kokarin sanar da shi
wanzuwa ta a gurin take yi dan kar ayi abin kunya. Sai ya ajiye ta sannan suka karaso but still yana
makale da ita duk da dan kokarin ture shin da take yi cikin dabara.
"Bakuwa muka yi?" ya fada da rich husky voice din sa. Na daga kai na kalleshi. He is dark skinned, giant,
and very handsome. Tun daga jikin sa, shigarsa, yanayin sa, da confidence din da yake fitowa daga jikin
sa zaka fahimci kalmar rich may just be his surname.
Na gaishe shi "ina wuni? Ya hanya?" Yayi murmushi yana kara jan matarsa zuwa jikinsa "lafiya lau. Ya
gida?" Sai kuma ya rada mata wani abu a kunne. Na sunkuyar da kaina yayin da Diyam ta janye daga
gare shi tana dariyar abinda ya gaya mata duk da ban san menene ba sai kuma tace "Jidda ce fa? Ka tuna
Jidda kawata ta taura science?" Ya dan yi shiru yana tunani sannan yace "wadda kuke kuka tare?" Duk
muka yi dariya tace "yeah. Ita fa. After shekara da shekaru Allah ya sake hada mu" ya gyada kai, "yayi
kyau. Yayi kyau sosai"
Sai nace "uhmmm lokacin sallah yayi. Bara in je daki inyi sallah" duk suka amsa sannan na fita da sauri na
rufe musu kofa tare da sauke ajjiyar zuciya. Ina ma ina ma? Ina ma Umar is not who he is? We could
have be just like Diyam da Sadauki.
Ban sake ganin ta ba sai dare, tazo ta tabbatar bama bukatar komai ni da yara, ta danyi wasa da Yasmin
da ta wuni tana kunci, sannan ta fita.
Na kwanta rigingine ina kallon ceiling, ina jin abinda ya motsa dazu a zuciya ta yana kokarin hana ni
tunani straight, nasan dama it is there, bakin ciki ne kawai ya danne shi and I intend to cigaba da danne
shi har ya tafi gabaki daya.
And I heard my foolish heart asking me "ko me Umar yake yi yanzu?" Nayi tsaki tare da juyi ina kallon
yaran mu da suke bacci a gefe na "Yana can yana ta hauka, that's for sure" Na amsa wa kaina.
A wannan daren ma haka na kasa bacci, na ringa yi ina mafarkan Umar yana ta haukan, da kuma
mafarkan Abba yana kumfar bakin in ya kamani sai na lahira ya fini jin dadi. A haka har agogo ya kai kan
karfe ukun dare. Na jawo handbag dina na dauko wayata da kwananta biyu a kashe na kunna ta,
messeges suka yi ta shigo wa kamar an bude famfo, sai da ta gama settling sannan na shiga messeges
din na ga kusan duk daga Umar ne, har ba zan iya irga adadin su ba. Na kashe kawai na karanta.
"I know I have been a very bad husband. Na san nayi miki abinda zuciya ma ba zata iya dauka ba. And I
deserve ko ma menene daga gare ki. But please, just talk to me. Reply me ko da da alphabet daya ne. Ko
da da kalma marar ma'ana ne. So that in san cewa you are okay. Please Jidda."
Na fita daga kan sunan sa ina fatan a cikin messages din akwai wanda zan iya using a matsayin shaida
akan sa.
Na ga kuma na yaya Tahir "call me"
Na fita and I resist the urge to open my WhatsApp, amma sai na bude instagram, hoping to find pictures
and videos da zasu debe min kewa har bacci ya dauke ni. But the first post a saw was from Umar, yayi
posting around 12 na daren ranar.
Hoton hannunsa ne with my band on it, ya juyo dai dai gurin rubutun "beauty queen". I noticed yadda
strings din duk suka tsufa wadansu ma dun tsinke. Yayi captioning picture din
"Be Safe. Please"
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi
sharing in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*
*The Phone Call*
Na kife screen din wayar tare da jan karamin tsaki, sai kuma na juya baya na tare da jan abin rufa na rufe
har fuskata, mintuna kadan sai na bude idon sannan na juyo na kuma daukan wayar na sake duba post
din nasa.
"Be safe. Please"
Na runtse idona ina jin hawaye suna zubowa daga idona suna bin gefen fuskata zuwa cikin kunnena. Na
kuma bude idon tare da sake kallon hoton, sai na shiga cikin comments naga yan uwan mu da abokan
arziki suna ta yi masa jaje, from their comments na fahimci an dauka bata muka yi ko sace mu akayi,
wadansu ma suna tunanin kidnapping din mu akayi, cikin masu yin jajen har da Bashir. But nasan shi
Umar din ya san ba sace mu akayi ba, Umma da Abba ma sun sani. Sai na samu kaina da tambayar kaina
ko me suke ciki? Ko wadanne matakai suka dauka na ganin sun gano in da muke? Ko kuma sunyi fushi
sunce sun bar wa duniya mu?
Na fita daga instagram din sannan na kashe wayar na mayar da ita cikin jaka na ajiye, amma bacci ya
gagari idona and my stupid heart want to know halin da Umar yake ciki. It belongs to him dama na sani,
it always does, but a hankali it will learn to live without him. Sai na hakura da baccin na tashi nayi alwala
nayi sallah ina rokon Allah ya bani juriya da karfin zuciyar fuskantar battles din da suke gaba na, the
battle with iyayena, with yayana, with the society and with my heart.
Washegari Diyam ta same ni da maganar cewa tayi wa mijinta magana ta kuma ya amince da in zauna a
tare da su zuwa muga yadda Allah zaiyi da ni, ya kuma ce in bashi address din gidan mu da kuma na
Umar dan ya saka a ke bincika min halin da suke ciki kuma muke sanin duk moves din su dan musan
move din da zamu yi mu kuma.
Sannan kuma yace in zauna in bari su nemo ni da kansu, in their struggle to find me zasu fahimci how
much they love me, sai dai kuma in lokaci ya ja da yawa ba tare da sun samo ni din ba sai ni in neme su
saboda auren da yake kaina. Ya kuma yi min alkawarin tsaya min da duk karfin sa na jiki da na aljihu,
yana kuma yi min fatan alkhairi.
Naji dadin haka sosai, naji dadin kulawar su da shawarwarin su da maganganu masu dadi dana samu
daga gare su, sai naji ina fatan ina ma dai al'umma zasu yi koyi dasu? Ina ma dai sauran mata zasu zama
kamar Diyam suke taimakawa tare da tsayawa yan uwansu mata a duk sanda suke buƙatar hakan?
Amma mata da yawa su suke haka rami su binne yaruwarsu mace dan kawai suyi replacing position din
ta in a society. Sun manta karma, what ever you do will be done to you.
Time started moving, slowly at first sai kuma ya fara gudu, days turned in to weeks and week turned to
month
Har na yi wata daya a gidan Diyam. At first rayuwar da wahala, na kasa adapting haka yara na ma
musamman Yasmin har sai da tayi ciwo farkon zuwan mu kuma har yau bata warware ba. She kept to
her self and cry for her Daddy some times, other times kuma ta kan saka ni a gaba da tambayoyin
yaushe zamu koma gidan mu? Me muke yi anan? Ina daddyn su yaushe zai zo ya dauke mu?
Asad kuma ya saki jikinsa daga farko, musamman da babbar yar Diyam Subay'a tazo gidan take kuma
daukan sa suyi wasa har ta koya masa swimming a pool din gidan, amma daga baya shima sai ya fara
gajiya ya fara damuna da tambayoyi, daga karshe ma sai ya tsiri yin kuka kusan kullum da daddare yace
shi gurin Daddy zai tafi ya kwana a can.
I kept telling myself cewa zasu saba, nima zan saba, but in reality kullum in suna kukan nima rufe kaina
nake yi a toilet inyi abina in wanke fuskata in fito cos I was also battling with my own heart amma na riga
na yanke hukunci kuma I don't think zan chanja magana, na gama auren Umar.
Diyam har been so supportive, ta taimaka min sosai da kalamai da shawarwari sannan tana iyakacin
kokarin ta gurin debe min kewa a hanyar ja na a jiki da involving dina a dukkan household activities
dinta, but bana shiga musamman in nasan mijinta yana nan, in yana gida kullum ina daki duk da nasan
gidan ba lallai ne ma in na fito mu hadu ba but bana son in zama na takura musu in any way.
In sunyi baki ma bana fitowa, wannan kuma shawara ce muka yi da ita dan bamu san irin bakin da zata yi
ba maybe wadanda suka san ni ne ko kuma suka ga cigiya ta wadda a yanzu babu inda cigiya ta bata kai
ba. Kuma duk mutane sun tafi akan cewa sace mu akayi ni da yara saboda son da Umar yake yi mana.
Mijin Diyam ya taimaka min yayi amfani da connections dinsa gurin karbar min leave daga gurin aiki,
wannan shine kadai sakon da na tabbatar Umar ya samu daga gare ni. And a ranar da daddare bayan na
kunna wayata kamar yadda na mayar aladata sai naga sakon sa.
"Thank you. Thank you for letting me know you are safe"
Nayi tsaki ina jin haushin yadda ya dauka saboda shi nayi haka. Wata zuciyar ta bani shawarar inyi masa
reply ince ba dan shi bane ba wata kuma ta ce in rabu da shi, kulawa ma ai yabawa ce.
Na kan turawa yaya Tahir sako duk sanda na bude wayata, telling him am okay, ina kuma rokonsa da ya
gaya wa Umma cewa lafiya ta kalau, he kept insisting in kira shi amma naki, ya fara tambayata inda nake
shima ban bashi amsa ba. Kamar yadda ban taba bawa Umar amsar sakonnin sa da yake turowa
endlessly duk rana duk dare ba, most of which bana ma karantawa, da yawa dana karanta kuma rantse
rantse ne akan cewa karya Asabe take yi masa, sai kuma alkawarirrikan cewa ya tuba ya daina halayyar
sa, da