Chapter 14 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   14 / 101

39K to 42K   out of 300.2K words

ma haka zanyi in gama.



Ta dawo inda nake kwance da sauri ta kama ni ta mikar da ni zaune sosai tana kokarin kirkirar murmushi
"babu komai Jidda, ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru misunderstanding kawai aka samu am
sure misunderstanding ne. Just breath please" na rufe ido na ina gaya wa kaina cewa misunderstanding
ne, maybe ba Umar dina bane ba, maybe mai kama da shine, ai akwai masu kama iri daya a duniya
right? Musamman tunda ba ido da ido suka ganshi ba a video ne.



Ina jinta ta saka hannu cikin rigar bacci na tana balle min bra dan ta kara taimaka min wajen numfashi,
na jingina kaina a kafadarta ina jin numfashin yana fara shiga hunhu na.



A lokacin ne Umma ta shigo dakin da sauri hannunta rike da blue inhaler ta, ta dago kai na tare da saka
min ita a baki sannan ta matsa sau biyu. Na mayar da ido na na rufe ina jin sanyinta a makogwarona
zuwa kirjina kuma ina jin airways dina suna clearing numfashi na yana kuma daidaita.



*Saurayin Jamila ne, shine wanda zata aura* na tuna da maganar gwoggo Habibah.



Na dago kai ina kallon Umma, hawaye yana bin idona nace "Umma wai da gaske ne? Da gaske Umar ne
saurayin yaya Jamila?" Ta zauna a kusa dani tare da kara mika min inhaler ta, na dauke kai gefe ina so inji
ta gaya min cewa ba haka maganar take ba ji ne banyi dai dai ba. "Ki nutsu ki mayar da hankalin ki guri
daya, ki kwantar da hankalin ki ki dawo da lafiyar ki jikinki kafin kiyi kokarin neman sanin wani abu da ba
zai amfane ki da komai ba" na mayar da kaina kafadar Farhan, bansan me Umma take nufi da maganar
da ba zata amfane ni da komai ba a yayin da ake magana akan mijin da zan aura, wanda nake da niyyar
spending the rest of my life with, wanda nake saka ran zai zama uban yaya na. Shin bani da right din
sanin komai a kansa?



Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din



0779484494
Nafisa Tafida Usman

Access Bank



Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp

08067081020



Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020



Please banda kira, WhatsApp only




*Episode Eleven: The Denial*




Wahalar da nasha a attack din dana samu yayi exhausting dukkan karfi na, hakan yasa duk da halin da
zuciyata take ciki sai da bacci mai nauyi ya dauke ni a jikin Farhan.



Sanda na tashi ni kadai na ganni a dakin, daga alama rana ta fito sosai



Na mike zaune nayi salati tare da dafe goshina, ko kadan ban manta abinda ya faru ba duk da cewa ganin
shi nake yi kamar a mafarki, ina tunawa da yadda Abba yayi biris da maganar yayi kamar ba wani abin da
za'a yi doguwar magana bane ba a kansa, na kuma tuna da hukuncin da ya yanke a karshe, wai Umar zai
iya auren mu mu biyu ni da yaya Jamila in dai yana son haka shi bashi da problem. Na mike tsaye da
sauri dan tabbas ni ina da problem da haka.
A palon Umma na same ta a zaune da kayan abinci a gabanta, daga dukkan alama bata dade da gama
breakfast ba, babu kowa a tare da ita dan nasan Amira tana school. Na zauna a gefenta cikin
matsanancin sanyin jiki, ta bini da kallo har na zauna sannan tace "ya jikin?"



Na gyada kai kawai ina jin babu isasshen yawu a bakina balle in amsa mata, ta dauko flask din gabanta ta
zuba min kunu sannan ta miko min "ungo ki sha" na karba na ajiye a gabana ina zagaya dan yatsa na a
rim din kofin sai ta fara magana



"Nasan kinji maganar da gwoggon ku tazo da ita, farko ni ma kamar yadda hankalin ki ya tashi haka nawa
hankalin ya tashi akan maganar amma kuma da baban ku ya sauko ya yi magana sai naji hankali na ya
kwanta" na dago kai da sauri ina kallon ta sai tace "ba wai na yarda da maganar sa bane ba ko ina goyon
bayan abinda yace ba a'a ina nufin na fahimci abinda ya faru.



"Jidda ke yarinya ce amma duk da haka nasan zaki fahimci cewa namiji ba mijin mace daya bane ba, da
wahala ki ga saurayin da yake da budurwa daya, bance ba'a samu ba amma da wahala, haka zalika shima
mai auren da wahala ki ga wanda bashi da wata budurwar kuma, haka Allah ya halicce su shi yasa ya
basu damar auren mata har hudu in dai zasu iya"



"ba abin mamaki bane dan Umar yana soyayya da ke kuma da Jamila a tare, watakila nufin sa ya aure ta
bayan ya aure ki, kuma ba zamu ce yana da laifi ba akan hakan tunda addini ya bashi dama, amma
abinda nafi tunani nima kamar babanki shine bai san dangantakar da take tsakanin ku ba, bai ma san
kunsan juna ba. Sai dai abinda ban yarda dashi ba a maganar babanku ita ce na cewa zai iya hada ku,
kamar yadda Habibah tace ba zata bar hakan ta faru ba ni ma ba zan bar hakan ta faru ba dan tabbas zai
iya raba zumunci a tsakanin ku"



"Dan haka yanzu tunda Allah yasa lokaci bai kure ba sai mu dauki mataki, ki dauki waya ki kira shi kice
kina son ganinsa, in yazo ki tambayeshi game da Jamila ki kuma fada masa dangantakar da take tsakanin
ku sannan ki tabbatar masa da cewa ba zaku zauna kishi ba, ki bashi dama ya zaba ko ita ko ke. Idan ke
ya zaba to ki tabbatar masa cewa iyayen Jamila ba zasu bashi ita ba indai ya aure ki, tsakanin sa da ita sai
dai mutunci a matsayin ta na yaruwarki. Idan kuma ita ya zaba to ya janye maganar aurenki ya kuma
aiko a karbar masa kudinsa da sauran kayansa, ke kuma Allah ya baki wanda ya fishi alkhairi".



Na gyada kai na da sauri ina yadda da hukuncin ta, amma kuma wani bangare na zuciyata yana cike da
tsoro "what if ya zabe ta? Zan iya rayuwa babu shi anya kuwa?"
Na mike da wayata a hannu, sai Umma ta dakatar dani tare da nuna min kunun data zuba min, na zauna
na shanye ina bata fuska kamar mai shan magani, ina gamawa na dauki waya ta na koma dakin mu.
Missed calls din Umar na gani har guda biyar a dai dai time din daya saba kira na kullum dan yaji yadda
na kwana.



Nayi dialing number din sannan na saka a kunne na. Seconds biyu ya dauka



"Hey Baby"



Na lumshe ido na na bude ina jin muryar sa tana taba zuciyata. "Hi" na fada da muryar da naji kamar ba
tawa ba.



"What's up Baby. Naji muryar ki wani iri ko yanzu kika tashi daga bacci?" Na girgiza kaina kamar yana
kallo na ina jin hawaye yana kawowa ido na, nayi kokarin boye emotions dina nace "lafiya lau. Kana
ina?" Yace "ina office, nayi ta kira dazu ai kina ta bacci ko? Are you sure you are okay?" Nace "ina so ne
in ganka yanzu, if you are free, akwai maganar da nake so muyi" ya danyi shiru sannan yace



"Baby, is everything okay?"



Sanyin da yayi min maganar da shi ne ya saka hawayen da nake rikewa suka zubo, can he really do it?
Yana dating dina yana dating wata kuma daban? Ko da bai san yaruwata bace ba amma still.......



"Lafiya lau. Kazo kawai zamuyi maganar in kazo" "are you crying?" Ya tambaya, sai naji hawayen ya
sake ballewa "oh my God, gani nan zuwa yanzu. I am about to go into surgery but zan ajiye yanzu in
taho...." Na katse shi "no.. lafiyar patients dinka tafi duk wata maganar da zamuyi, ka gama kawai sai
kazo" yace "wa? Ba dai ni Umar din ba, Jidda tana kuka kuma zan iya surgery? Ai tabbas zanyi barna ne a
ciki. Ba emergency bane ba scheduled cs ne, zata iya jira inzo in ganki in dawo ko kuma wani doctor din
yayi taking over amma ni ba zan iya ba Baby, not when you are crying"
Sai ya kashe wayar, na dora ta akan kirjina ina jin bugun zuciya ta yana vibrating a jikin wayar "can he
really do it?" "Will he chose me?" Na tuna Yaya Jamila, zuciya ta tana lissafo min yawan abubuwan da ta
fini, kusan ta fini komai da wayayyen hadadden namiji kamar Umar zai so a gurin matarsa.



Na tuna da wayar da take raba dare tana yi sanda muka je gidan su, da wa take waya? Umar?



Ina nan a zaune Farhan ta shigo dakin, ta zauna tana ta yi min labarin abokin mijin yaya Hudallah da take
kokarin hada su "kinga katon cikin sa kuwa?" Ta fada tana dariya, daga dukkan alamu so take ta saka ni
dariya amma ganin bani da niyyar yi sai ta fita ta bani guri.



Bata jima da fita ba ya kirani "ina waje" ban amsa ba na kashe wayar sannan na tashi na wanke fuskata a
tsakar gida sannan naje dakin Umma na saka kwalli, bana so yasan how much nayi kuka a kansa. Amma
gyaran fuskata bai yi komai ba wajen gyara zuciyata, dan a tsorace take sosai, ko wannan ne zai zamo
gani na karshe da zanyi masa? Menene makoma ta idan na rasa Faruq? Har na fito daga dakin kuma sai
na koma na dauko wayar Umma na fito da ita a hannu na.



Yana mota bai fito ba, har na fito daga cikin gidan bai fito ba nasan kuma hakan yana da alaka da saurin
da yake yi dan lokuta da dama in yana sauri yakan zauna ne a mota.



Na zagaya na bude kusa da shi na zauna. Yana sanye da kayansu na doctors, wannan ita ce ranar dana
fara ganinsa da kayan kuma sai naga kamar sunfi yi masa kyau akan kowane kaya, sai naga kamar yafi yi
min kyau akan kullum.



But he looked worried.



"My God! Da gaske kuka kike yi Jidda" na girgiza kaina, trying so hard not to continue crying. Sai na
dauko wayar Umma na bude sannan na nemo hoton Yaya Jamila na nuna masa direct nace



"ka san wannan?"
Na lura da yadda yanayin sa ya chanja a lokaci daya, sai kuma naga ya dawo dai dai sannan ya karbi
wayar daga hannuna yana kara kallon ta kamar mai tunani sai yace "Jamila ko? Jamila something......na
manta second name dinta" sai ya miko min wayar "a ina kika santa?" Na karba still ina kallon yadda yaki
hada ido dani yana kallon waje, duk damuwa da seriousness din fuskarsa sun tafi, he looked
uninterested"



"menene a tsakanin ka da ita?" Na sake tambayarsa. Ya juyo yana kallo na kamar mai mamakin
tambayar sannan yace "wai wannan yarinyar? Ni kuwa menene hadi na da ita? Wani abun aka gaya
miki? Is that the reason da kike kuka?" Nace "I will be the one asking the questions, and you will be the
one answering" sai ya sara min kamar yadda ake yi wa masu khaki yace "yes ma" na lura gabakidaya ya
mayar d maganar wasa.



Nace "menene tsakanin ka da ita?" Yace "nothing really, na santa a buk tun kafin in fita India, she is a
friend of girlfriend din Bashir ta lokacin, so in na raka shi gurinta muna haduwa kuma most of the times
in zai fita da ita suna tare kuma nima ina tare da shi. So bayan sun rabu ma muna dan gaisawa haka in
mun hadu, shikenan...... please ki gaya min mai ya faru?"



Na ajiye wayar a tsakanin mu ina kallon gaba na, trying to think using my head but my heart is already
jumping with joy cewa ba wai yana son Jamila bane ba, it was a misunderstanding.....



"Yayata ce" na fada "yar gwoggo Habibah ce...ita ce autarta" ya kalle ni "really? What a small world.
Amma menene ya saka ki kuka a cikin maganar? Oh sorry ma, ashe fa kece mai yin tambaya ni mai
amsawa" yayi dariya, shi bashi da wani problem.



"Dazu gwoggo Habibah tazo gidan mu da sassafe........." Sai na bashi labarin abinda ta fada na daga
dangantakar da tace akwai a tsakanin sa da Jamila. Amma ban fada masa abinda Abba yace akan
maganar ba.



Anan ne naga hankalin sa ya tashi "ya salam...... wannan yarinyar sharrin da zata yi min kenan? Yaushe
ne muka yi haka da ita..." Na bishi da kallo kawai "ta cuce ni amma wallahi shikenan ta bata min suna a
gidan ku" sai yayi kamar zai riko fuska ta sai kuma ya dauke hannun sa yana yarfarwa a gefe "na shiga
uku. Wallahi Jidda karya take yi min babu wani abu mai shigen kama da wannan a tsakani na da yarinyar
nan, ni ban taba cewa ina sonta ba ballantana har in yi mata alkawarin aure. My God!" Ya fada yana
shafa gashin kansa
"Look Jidda, Wallahi karya take min. Look, ban damu da wasu su yarda ko kar su yarda da abinda nake
cewa ba, but Please ki gaya min cewa ke baki yarda ba. You think zan yi miki haka? Bayan na same ki
kuma Jidda mai zanyi da wata mace kuma?"



Na dauke kaina gefe a kokari nana kara jan zaren aji na, "tace jiya ma kuna tare" ya danyi frowning
fuskarsa sannan yace "jiya? Jiya naje dinner ne ta bikin wani friend dinmu" sai kuma yace "ohh I
remember seeing her there, sunje a matsayin kawayen amarya mun gaisa haka briefly but it doesn't
mean muna tare as in kamar naje 'zance' gurinta" yadda ya fadi zancen kamar wani abun kyama.



Nayi shiru ina assessing maganar sa, ido na akan band dina da yake hannunsa. Ya sake cewa "idan baki
yarda ba bara in kira Bashir, zai fada miki komai....." Na girgiza kaina "no need" ya dauko wayarsa tare da
cewa "I insist. Bana son ko trace na wani abu mai kama da wannan ya shiga tsakanin mu" yayi dialing
number sannan ta saka a handsfree tare da dora ta akan dashboard.



Ina jin Bashir ya dauka "hey namiji" yace "hey Bash. You are on speaker. Ina tare da baby na ne kuma ina
bukatar taimakon ka. Please help me clear something out. Ka tuna yarinyar nan Jamila kawar Nafisa ta
ka?" Yace "yeah. Na tuna Jamila, me ya faru" sai ya fada masa abinda na gaya masa a game da Jamila



Bashi yace "look Jidda,ba tun yau ba na gaya miki cewa guy din nan ya sace zuciyar yammata da yawa,
amma tasa zuciyar ke kadai kike da mallakin ta, and it happens that Jamila is just one of those girls. Guy
ka manta na taba gaya maka yarinyar nan kamar she is into you kace min ba haka bane ba?" Umar yace
"yeah, anyi haka, da nasan zata bata ran baby na dana tare ta a hanya na kora mata jawabi tun a
lokacin"



Bashir ya cigaba "to kinji, babu wani abu mai kama da wannan a tsakanin su. Ke kadai ke da zuciyar
Umar. My guess is tana sonsa sai kuma ta ganshi a matsayin wanda zaki aura and she wants to break you
guys up dan ta gwada tata sa'ar. Wannan shine gaskiya"



Ya dauki wayar ya saka a kunnen sa "thank you bro, I really appreciate this" sai kuma ya kashe ya mayar
da ita aljihunsa ya juyo yana kallo na "I really hope kin yarda da magana ta yanzu, I also really really hope
zaki yi dropping maganar nan and we will never discuss it again. Jamila ba budurwa ta bace ba, I don't
and I will not love her talk less of marry her. Ni saurayin mace daya ne, kuma mijin mace daya, sunanta
Hauwa'u Maijidda" ya karasa yana murmushi, nima na sunkuyar da kai na kasa ina taya shi murmushin a
raina ina jin dadin yadda maganar ta warware ba tare da tayi affecting tsakani na da shi ba.



Tabbas biri yayi kama da mutum, yadda Jamila take da rashin kamun kai zata iya shirya sharri dan ta
samu wanda take so, kuma na san gwoggo Habibah bata san fuskar samarin Jamila ba ballantana ta gane
ko akwai Umar di na a ciki ko babu.



"Jidda" ya ambaci sunana, na dago ina kallon sa amma ban amsa ba sai yace "wannan ne
misunderstanding da muka samu na farko, kuma am sure ba zai zama na karshe ba tunda aure zamuyi
kuma shi aure akwai challenges da yawa irin wadannan a cikin sa. Sai dai abinda nake so dake shine ki
saka a ranki Umar naki ne ke kadai, duk wata wadda zata yi kokarin saka doubt a zuciyarki ki karyata ta,
dan ni bayan wadannan relationships din guda biyu da na fada miki ban taba zuwa wajen wata da niyyar
ina sonta ba ballantana har ta kaimu ga maganar aure"



"Sai dai wadansu mata suna misunderstanding maza iri na. Ni ina da faran faran da mutane, in naga lady
ina treating dinta as a gentleman should, misali sakin fuska gurin amsa gaisuwa, getting a seat for her, ko
offering a helping hand when needed, su kuma wasu matan sai su dauka wannan soyayya ce, sai su fara
tagging kansu as 'budurwa ta' when ni kuma babu wannan maganar a raina"



"Sai magana ta tashi kuma nace ba haka bane ba sai a fara fadar maganganu. I have been tagged as
'mayaudari' several times. Wannan shine dalilin da yasa Mama tayi kokarin hada ni da cousin din nan
tawa da nayi miki bayani kwanan baya. Ladies need to understand that if a guy loves you he will say it
out. Mu ba mata bane da zamuyi ta boye boye waiting for the other one to say it first. A guy smiling at
you doesn't mean a guy is in love with you"



"Dan haka please, ko nan gaba ko bayan bikin mu in wata ta gaya miki magana irin wannan please kar ki
tayar min da hankalin ki har kiyi min asarar hawayenki a banza, ki dauka kawai direct cewa karya take yi.
Ni Umar mijin JIDDA ne ita kadai babu kari"



Nayi murmushi ina jin dadin maganar sa amma sai na girgiza kaina nace "dadin baki ko? Zaka yi min
dadin baki ko? Umma ta gaya min ai ku maza are polygamist in nature, dan haka Umar is free yayi
adding second, third and fourth wife after Jidda duk da dai hakan ba zai yiwa Jidda dadi ba amma zata yi
accepting"
Yace "wai kina nufin Umma tayi comment akan maganar nan?" Nace "eh mana, ita ce ma ai ta saka na
kira ka, tace in gaya maka ka zaba tun yanzu ko ni ko Yaya Jamila dan ba zanyi kishi da yaruwa ta ba" ya
dan daki stirring "damn it, wannan yarinyar ta cuce ni ta bata min suna a gurin su Umma" nace "kar ka
damu, zata fahimta

14 / 101