Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
Sai muka tafi tare da Farhan da yayana Abbah.
A hanya ina ta addu'a da kuma fatan kar Allah ya hada ni da Umar a gidan kuma cikin ikon Allah bamu
same shi ba sai maigadi shi kadai a bakin gate, yana ganina ya taho da murnar sa "Hajiya! Sannu da
zuwa. Ina su uwar masu gida (Yasmin)" nayi murmushi kawai sai Farhan ce ta bashi amsa da cewa suna
gida. A rufe muka tarar da falon, da yake da akwai key jaka ta sai na bude mana, muna shiga sai ga mai
gadi da kayan sharar yana wai yazo zaiyi mana, gwoggo Habibah ce tace masa ai ba zama zamuyi ba kaya
muka zo diba, sai ga shi yana sharar kwalla.
Na jima a tsaye ina bin gidan da kallo, gidan dana yi tunanin nanne zan kare rayuwata tare da mijina da
yayana, gidan da nayi tunanin sai dai a fitar da gawata daga cikin sa yau gashi ni da kaina na zabi fita
daga ciki. Na bude corridor na shiga dakina, kayan Umar ne duk a barbaje a dakin, wannan yasa nayi
tunanin anan ya dawo da zama.
Farhan ta shigo muka sauke akwatinan saman wardrobe muka fara zuba kaya, ina yi ina tattare wa Umar
na sa, ignoring kamshin sa da yake jikin kayan. Sai da muka gama kwasa tsaf, na zagaya sauran dakunan
gidan ma na daukar mana abinda nake tunanin zamu bukata. Sauran kuma duk muka jirge su muka hade
su waje daya, kitchen ma duk muka zuba kayan a cikin kwalaye da buhunhuna. Furnitures ne nace da
gwoggo Habibah "shi ya siya wadannan, nawa sune yanzu a dakin Umma" ta daga kafada "sai menene
kuma? Ai tunda ya siya miki sun zama naki" yaya Kabiru yace "a'a kar a taba masa saboda gudun
wulakanci, duk abinda shi ya siya a bar masa kayansa idan ya bar mata ne to shi da kansa zai aiko da su
ko kuma yace azo a dauka"
Kusan wuni mukayi, sai yamma muka gama kuma har muka gama Umar bai zo gidan ba, muka hade duk
kayan da suke nawa a cikin bedroom dina muka rufe, sauran kuma muka bar komai a inda yake. Na
dauki suturar sa dana tarar a bedroom dina na kai masa nasa, sai na tsaya ina kallon dakin, zuciyata tana
bugawa da karfi my head blank, sai kuma na ajiye da sauri a bakin gado na kife frame din family picture
din mu na fito da sauri daga dakin.
A bakin gate gwoggo Habibah tace da mai gadi "idan mai gidan yazo ka gaya masa mun zo mun debi
kaya mun kuma hada sauran, za'a aiko da mota ta kwashe" yace "ai Hajiya tun jiya da safe da ya fita har
yanxu bai dawo ba, ina ta tunanin ma ko lafiya dan kwanakin nan kullum a gida yake kwana yake wuni
babu inda yake zuwa" gwoggo Habibah ta tabe baki "lafiya ce ai take yin shiru, in da wani abu ai dole
za'a sani. Allah ya kyauta" daga haka muka koma gida.
A ranar da daddare Hajiya ta shigo har daki tayi min jaje, tana ta sussunkuyar da kai, na amsa mata babu
yabo babu fallasa, sannan kuma yanuwana suma kusan kowa yayi min waya ya jajanta min wasu daga
ciki ma har gida suka zo, ban sani ba ko har zuciyar su suke alhinin abin ko kuma munafunci ne oho,
amma ni ban damu ba dan nasan bana nufin kowa da sharri a zahiri ko badini, kuma na yarda da cewa
duk mai nufi na da shi kansa zai koma kamar yanda wancan sharrin da suka kulla ya kwance a tsakiyar
kansu.
Babu bata lokaci shirin tafiyar mu ya kankama, dama rashin isassun kudin da zan tafi da yara ne ya saka
nake ta delaying abin amma yanzu tunda an dauki nauyin mu bani da stress, na sami Yaya Tahir da Abba
na roki ina son mu tafi da Amira dan itama ta ga yan uwa kuma naci sa'a Abba ya bari.
Kayan da na dauko wanda zamu tafi dasu kawai na diba sauran na jibge su a dakin Umma. Na san
maganar mutuwar aure na a yanzu ta gama zagaya yan'uwa da makota, na san da cewa masu zuwa
gidan da yawa suna kallo na da abin but I don't care, zasu yi magana na sani, zasu yi surutu na sani,
kamar kuma yadda na sani cewa abinda ya faru dani halal ne ba haram na aikata ba, na san kuma cewa
mutuwar aure ba'a kaina aka fara ba ba kuma a kaina za'a kare ba, kamar yadda babu wanda yasan
ranar mutuwar sa haka babu wanda yasan makomar auren sa.
Matsala ta farko da na fara fuskanta kuma dama ita ce matsalar da na saka ran zan fuskanta ita ce
matsalar yara na. Kullum zancen baban su, musamman da suka ga alamar munje gidansu mun debo
kaya. Kullum sai sun ce in kira musu shi a waya ni kuma sai in ki in kuma yi musu tsawa su rabu da ni.
Shima kuma bai ta taba kira ba.
Ranar nan sai ga Yasmin ta sako kaninta a gaba sun zo gurina. "Mommy tunda ke ba zaki kira Daddy ba
dan Allah in dauki aron wayarki in kira shi?" Na lura tsoron yadda ranar nan da ta kira shi na kusan
dukanta take yi. Na bude mata wayar na mika mata "kira shi" da sauri ta karbi wayar ta nemo number
dinsa ta kira ta saka a kunne, sai kuma ta bata rai tana kallona tace "wayar ta ki yi mommy, ko ta lalace?"
Na karba ina kallon sunansa "Umarul Faruq" sai na shiga edit na chanza sunan zuwa "daddyn Yasmin"
sannan na kira amma sai naji wayar a kashe. Na ajiye nace "wayar sa a kashe take Yasmin" sai suka bata
rai amma kuma suka hakura.
Sai dai ni a nawa bangaren ina jin babu dadi a raina. Duk da babu aure tsakani na da Umar amma shi din
wani bangare ne na rayuwata, kuma na tabbatar idan Umar zaiyi ignoring dina saboda dagewar da nayi
na rabuwa da shi ba zai ignoring yayansa ba, what if something bad has happened to him?
Na nemo wata tsohuwar number dinsa wadda yayi amfani da uta lokacin da yake pretending cewa ya
daina using layinsa, na kira amma shima not reachable, tunowa da nayi da lokacin da yayi using number
din da irin karerayin da ya ringa yi min ya sa nayi tsaki, in ma wani abun ya faru da shi ai yana da iyaye da
yanuwa da abokai, ko Bashir ya isa ya kula da shi.
Na tuna rantsuwar da ya dinga yi min cewa ya rabu da Bashir amma Farhan ta gaya min cewa tare da
Bashir din suka yi ta yawon nema na kuma babu wata alama ta rabuwa a tsakanin su.
Na jefar da wayar gefena ina jin haushin kaina na damuwa da nayi da sanin dalilin kashe wayar sa. He
doesn't deserve that from me does he?
Amma duk da haka ana ya gobe zamu tashi sai na shirya yara na hada su da Amira nace ta kai su gidan su
Umar suyi musu sallama. Bata jima ba sai gata ta dawo ita kadai wai Mama tace su zauna su wuni da
dare za'a dawo dasu. Kuma zasu je asibiti su duba baban su.
Na tsaya ina kallon ta. "Bashi da lafiya ne?" Ta daga kafada "haka dai naji tace, ni kuma ban tambaye ta
ba"
A ranar ne kuma da yamma nayi bakuwa. Surayya. Naji dadin zuwanta sosai na tare da da fara'a muka
shiga daki na gabatar mata da ruwa da lemo sannan muka gaisa. Tayi kyau sosai sosai, in ba saninta kayi
sosai ba ba zaka gane ta ba saboda yadda tayi fes da ita fatarta tayi kyau sosai. Ba zaka ce da ne take
gidan mai kudi ba yanzu kuma take gidan iyayenta masu rufin asiri.
Ta fara min mitar bani da zumunci na daga mata hannu "naji naji, na kuma karbi laifina hannu bibbiyu,
amma insha Allah gobe zan yi tafiya in na dawo zaki ganni har gida, nima zan samu ladan. Dama akwai
abinda yake rike zumuncin mu amma yanzu tunda ya kau zamuyi zumunci sosai" tace "ban gane ya kau
ba, me kike nufi"
Na yi shiru ina wasa da yatsuna sannan nace " baki ganni a gidan mu ba?" Ta gyada kai. "Naje can gidan
naki ai tun kwanaki mai gadin ku yace min bakya nan wai kina gida. To yan zu kuma nazo bayan layin ku
sai nace bara in shigo in gani ko kina nan"
Na danyi murmushi "mun rabu ai. Mun rabu da Umar" ta bude ido cikin mamaki sannan tayi salati. "Kun
rabu fa kika ce Jidda? Umar fa? Umar ne ya sake ki?" Na girgiza kai. "Ni na nemi Umar ya sake ni. He
didn't have an option, it was either ya sake ni daga ni sai shi sai waliyyan mu ko kuma in kai shi court ya
sake ni a gaban duniya. He chose the first option"
Ta rufe idonta ta bude "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Allahu ya sa hakan shi yafi muku alkhairi baki
daya" nace "ameen. Tare da ke"
Tayi dariya "ni kam alkhairi ne ma alhamdulillah. I have never been this happy. It was hard at first
musamman da yake ban samu support na iyayena ba but a hankali sai suka fara fahimtar it was for the
best, musamman da wasu daga cikin halayen Bashir suka fara fitowa yanzu a fili, duk da dai nasan ba
za'a taba fahimtar how deep yake a cikin harkar ba. Iyayensa ma basu yarda ba sunce sharri ne but ni na
san cewa sun sani ko ba su san komai ba sun san something kawai suna pretending cewa basu sani ba
dan gaskiyar sai ta fi musu da ci akan karyar"
Na gyada kai cikin fahimta. Sannan nace "ke kuma fa? Me kike ciki yanzu?" Tayi murmushi. "Na koma
school. Dama shi ya hana ni kuma I was naive na dauka it doesn't matter ko nayi karatu ko banyi ba
tunda ina ganin zai sauke nauyin sa. But now I am wiser" na gyada kai. Allah yasa haka shi yafi mana
alkhairi
Da dare su Yasmin suka dawo, tun kafin in tambaye su Asad ya fara bani labari "mommy munje gidan
Mama, nace mata ba zan zauna a gidan ta ba tunda tafiya take yi tana barin mu muyi kuka, kuma sai
muka je hospital muka ga Daddy bashi da lafiya ana yi masa allura"
Na juya ina kallon Yasmin nace "me yake damun daddyn naku?" Ta zauna tace "nima ban sani ba. Yana
kwance muka ganshi kuma baya magana" nayi shiru ban ce komai ba.
Jirgin mu da safe zai tashi dan haka da wuri muka fita. Muka je airport muka gama komai muka zauna
jiran lokacin tashin mu. But hankalina was somewhere else. I want to know yanayin jikin Umar da kuma
abinda yake damunsa, nayi tsaki ya kai cikin charbi. A karshe dai na dauko wayata na kira number dinsa
still switched off. Na sake wani tsakin na ajiye wayar. Mintuna kadan kuma sai na sake dauka na nemo
number din Mufida na kira. Remembering cewa tunda na bar gidan Umar bamu yi waya da ita ba.
Sai da kiran ya kusa katsewa sannan ta dauka. Muryarta sounds far away kamar wadda ta tashi daga
bacci ko kuma wadda take cikin damuwa. Na lumshe idona na bude. She was and still is a very good
friend of mine. Tun ranar da muka hadu Allah ya hada jinin mu but now? Now I don't even know
menene a tsakanin mu.
"Mufida?" "Na'am Jidda. Ya kike? Ina mamana da babana? (Yasmin da Asad) nace "lafiya lau suke. Ya
kike? Ya mai jiki?" Ta danyi shiru "da sauki" nace "uhmm. Me yake damunsa ne?" Tace "some kind of a
heart problem" na lumshe idona na bude "Allah ya bashi lafiya. Dama yau zamu tafi ne, muna airport
already. Shine yara suke so suyi sallama dashi and his phone is not going through. Ko zaki hada su suyi
magana if that is possible?"
Tace "bana gari ai. Ina Kaduna. Sai dai ki kira Mama ko Yaya Mubaraka. Na san daya tana tare da shi"
nace "ohh okay. Shikenan babu komai. Thanks. In kunyi waya kawai kya ce muna duba shi ni da yara"
Sai na katse wayar na rike ta a hannuna ina jujjuya ta. Ciwon zuciya? Umar? Nayi ajjiyar zuciya. Allah ya
bashi lafiya.
Mintuna basu fi biyu ba sai ga kiran Mama ya shigo wayata. Kamar ba zan dauka ba kuma sai na dauka
na gaishe ta. Ban tambayi mai jiki ba. Tace "Mufida ta kira yanzu tace in kira ki wai kin kira kina tambayar
jikin Umar ko? Jiki da sauki Jidda. Alhamdulillah jiya da dare ya farka. Yana ta neman ki da yara. Ban
dauka zaki kula shi ba shi yasa ban neme ki ba. Bara in bashi wayar ko a waya ne ku gaisa"
Na juya ido na. Did I say ina son magana da shi?
Some part of me wanted to cut the call but sai na kasa. And I heard muryar Mama "Umar Umar Umar.
Jidda ce a waya. Ta kira zata duba ka ne"
And I asked myself "ni na kira da ma?"
Sai kuma naji muryar sa. Can kasa "Jidda?"
Sai nayi magana cikin sauri
"Hello Umar ya jikin? Ashe baka da lafiya. Dama muna airport ne zamu tafi sai su Yasmin suke son yi
maka sallama. So, ba wai ni na kira ba. But ina maka fatan samun sauki"
Na dan jira kadan, kamar ba zaiyi magana ba sai kuma murya can kasa yace "ina zaku je?" Nace "baka
sani ba? Na dauka ka sani tunda su Baba sun sani. Zamu je Ethiopia ne. Muna airport ma already. Ga
yara zasu yi maka sallama. Allah ya baka lafiya" ban jira amsar sa ba na mikawa Asad da Yasmin da suka
saka ni a gaba suna jin abinda nake cewa. Nan da nan suka fara rige rigen yi masa magana yayin da ni
kuma na rufe idona ina jin tawa zuciyar tana yi min nauyi. Ban san ma sun gama ba sai gani nayi sun
miko min wayar. Na saka ta flight mode sannan na saka a jaka ta. Mintuna kadan aka kira jirgin mu.
*Wannan littafin na siyarwa ne bisa amana idan baki siya ba kar ki karanta idan kuma kin siya kar ki
sharing idan kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*
*The New Life*
**
Sai dana tabbatar Asad da Yasmin da kuma Amira sun zauna properly sannan nima na zauna na saka seat
belt na kwantar da kaina na rufe idona, all I can see a idona shine Umar a kwance a kan gadon asibiti
thinner than last ganin da nayi masa, na'urori a zagaye da shi. Sai da naji jirgin ya fara tashi sannan na
bude ido na ina kallon kasa har muka daga cikin sararin samaniya ina kallon garin kano, and I thought,
tabbas abinda na fada gaskiya ne, tabbas rabuwa da Umar itace jarabawa ta ba wai zama da shi ba.
Awa biyu ta kaimu garin addis ababa, Mun tarar da auncle Muhammad da matarsa sun zo airport daukar
mu daga nan muka tafi gidan sa inda acan Umma take a lokacin.
Murnar ganin Umma da yanuwana ya saka naji duk tunane tunanen da na kwashe entire journey din ina
yi sun dakata, na fara murmushi da dariya tare da karbar kulawa da soyayya daga yanuwana duk da dai
ban samu hakan daga gurin mahaifiya ta ba wadda tayi kicin kicin taki kula ni sai Amira taje yiwa magana
da kuma su Yasmin.
Na fahimci har yanzu ni mai laifi ce a gurin ta, na fahimci yaki na ba'a cire Umar completely daga zuciyata
kawai yake ba, yaki na ya hada da kokarin samun goyon bayan mahaifiya ta. Dan a matsayin ta na uwa ta
fushin ta a gare ni masifa ne.
Kwanan mu biyu da zuwa na fahimci target din ta, she was set on making my life miserable maybe a
ganin ta hakan ne zai saka in zabi komawa gidan Umar. Duk motsin da nayi sai ta gaya min magana. And
I realized ita a gurin ta kamar zinar da Umar yake yi ba wani babban laifi bane ba wanda ya chanchanci a
rabu da shi, a ganinta sauke hakkinsa da yake yi a gare ni ya shafe wannan zinar da yake yi. She kept
saying
"Mata nawa ne suke neman samun irin naki? Wata matar in dai zata samu miji kamar Umar to babu
ruwanta da bin kwakwkwafin sai ta san abinda yake aikatawa kuma ko ta sani ma ba zata daga hankalin
ta ba ballantana har ta nemi saki. Bana so inyi miki baki Jidda, amma ina jiye miki irin mijin da zaki aura
nan gaba sai kin yi kukan rashin Umar"
And I remembered some of the comments na mutane lokacin da na nemi shawara a social media, I
realized ba ita kadai ce take da irin wannan tunanin ba matan mu da yawa na hausawa suna da irin
wannan tunanin. Su a ganin su indai miji yana basu ci da sha da sutura shikenan ya gama musu komai,
wannan kuma shi yake kara bawa maza masu halin Umar license na cigaba da halin su, matan sun mance
cewa aure is beyond wadannan abubuwan, far beyond.
Dan ni dai a yanzu personally I rather marry wanda baya wadata ni da wadannan abubuwan amma zai
kiyaye mutuncin sa da nawa a zahiri da kuma badini than to marry mai irin halin Umar, in har rashin
wadata ne sai mu hadu mu rufa wa juna asiri, in kuma rowa ce sai in dauke kaina daga abinda kake dashi
in nemi na kaina.
Tunda naje ban ma saka layi a waya ta ba saboda ina bukatar quietness and peace, da wayar Umma
muke gaisawa da mutanen gida, but ban manta da rashin lafiyar Umar ba kuma ina yi masa addu'a
sometimes kuma ina saka yayansa suyi masa addu'a duk sanda suka yi sallah kamar yadda nima har yau
ban daina addu'ar zabin alkhairi a rayuwata ba da neman Allah ya sassauta min abinda nake ji a zuciyata
ya sanya min nutsuwa.
Satin mu daya a Addis Ababa muka tafi garin Nazret inda nan ne tushen su Umma daga tribe din Oromo
anan kusan dukkan yanuwansu suke auncle Muhammad ne kawai da few suke a Addis Ababa suna aikin
gwamnati. Sai da na bar inda Umma take sannan na samu nutsuwa na huta da maganganun da take gaya
min kullum, sai a lokacin hankali na ya kwanta na fuskanci halin iddar da nake ciki. Wannan yasa sanda
Amira zata dawo Addis Ababa sai na hado ta dasu Yasmin ni nayi zamana can gidan auntyn su Umma
wadda take a matsayin kamar kakarmu kenan a can. Daga gidan ta kuma sai gidan yarta Nuru wadda
take cousin din su Umma kenan kuma tana da yaya da yawa maza da mata ciki har da