Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
yake ciki shine cin jarabawarsa ba"
"A case dina kuma. Allah da kansa ya fada a cikin Alqur'ani A cikin suratun Nur, Aya na 3, Allah SWT yana
cewa:
َأ َأ
الَّز اِني اَل َينِكُح ِإاَّل َز اِنَيًة ْو ُمْش ِرَكًة َوالَّز اِنَيُة اَل َينِكُح َها ِإاَّل َز اٍن ْو ُمْش ِرٌك ۚ َوُح ِّر َم َٰذِلَك َعَلى اْلُمْؤِمِنيَن.
*Mazinaci ba ya aure face da mazinaciya ko mushirika, kuma mazinaciya babu mai aurenta face mazinaci
ko mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan muminai*
*An haramta wannan akan muminai* wannan ita ce ayar da malamai da alkalai da yawa suke amfani da
ita wajen raba aure idan daya daga cikin ma'auratan ka kasance mazinaci. Umar ubangiji da kansa yace
ya haramta min ni da nake ba mazinaciya ba zama da kai da kake mazinaci, umar gaya min wani abu da
yake sama da ayar ubangiji? Gaya min ta yadda in naki bin wannan ayar bayan na santa kuma bayan na
tabbatar kuma kai da kanka ka tabbatar min da halayyar ka ta yadda zan yi wa ubangiji bayanin a ranar
lahira, Gaya min idan rabuwa da kai ba shine cin jarabawa ta ba. Gaya min idan cigaba da zama da kai ba
son zuciyata ba ne ba"
Na fada ina kuka sosai. Sai ya dawo zuwa gabana ya tsaya, expression din fuskar sa unreadable, yace
"menene dalilin da yasa kika kira ni? Idan har kin yanke wannan shawarar menene dalilin da yasa kika
kira ni har kika bari na ganki na taba ki na kuma saka ran cewa zamu dai dai ta?"
Nayi shiru ina kallon sa cikin mamaki, yana nufin bai amince da ayar dana kawo masa ba ne ko kuwa
menene? Na share hawayena nace "I called you to say goodbye. Zan yi tafiya zuwa Ethiopia kuma
bansan sanda zan dawo ba. Abba yace zai baka lokaci ka rubuta takarda ka bashi, in kuma baka rubuta
ba zai......." "Zai kaini court" ya karasa "the same threat each and every day har na haddace. Now I have
a question for you. Kina tunanin you can just walk out of this marriage and live happily ever after?" Nace
"not happily ever after, dan mumuni baya rabuwa da jarabawa har sai an zare ransa daga jikin sa. But
yes, I can live happily, and you can too in dai ka..."
Ya tura ni baya da karfi har na fada kan kujera, yace "haka kika ce? Haka kike tunani? That you can live
happy without me? Kina ganin ni kamar ba zan iya rayuwa ba sai dake ko? Here is a news flash for you, I
will live happily without you too. Ba dai kina ganin zaki sake aure ba? To karkarin ta dai daya zaki aura ni
kuwa hudu zan aura kuma duk wadanda suka fiki komai wadanda kuma zasu zauna dani suyi hakuri dani
komai halina. Ko kina ganin idan kin rabu dani ne zan daina abinda nake yi? Ba dai takarda ba? Kar ki
damu zan aiko miki da ita kafin ma ki tafi din in yaso ki tafi da ita a matsayin guzuri"
Sannan without another look at me ya dauki key din motarsa da yake kan kujera ya juya zai bar falon, na
bishi da sauri na rike hannunsa a bakin kofa "Umar, kar ka fita like this, ka tsaya ka nutsu... " Sai ya zare
hannunsa daga cikin nawa ya juyo yana kallo na, yana yin idonsa yana tsorata ni sannan yace "goodbye
Hauwa'u".
Na daske a gurin har naji karar bude kofar motarsa da rufewa, sannan naji ya ja motar a guje, na daga
labule ina lekensa sai na ga ya hau titi da gudu ba tare da ko signal ya saka ba ballantana ya jira motocin
da suke wuce wa su gama wucewa.
Na lumshe idona na tare da ambatar innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Abinda na kira Umar dan shi ban
samu nayi achieving dinsa ba, I thought he will understand, yana da ilimi ba jahili bane ba, I thought inna
gaya masa ayar Allah zai fahimci hujja ta kuma zuciyar sa zata yi sanyi ya nutsu ya daina wannan
damuwar akan rabuwa dani yayi concentrating akan cin tasa jarabawar nima ya barni nayi concentrating
on mine. In da rabon zamu koma watarana idan ya gyara rayuwarsa, maybe, in haka Allah ya tsara, sai
mu koma din.
But definitely not now. Kuma ba nan kusa ba.
Na zauna bakin kujera tare da sauke ajjiyar zuciya, at least dai Abba bai kama mu ba.
Sai kuma nayi wani tunani cikin jin tsoro, tunda har Umar yaki tsayawa ya saurari maganar Allah, to me
zai saurara kuma?
*Umar*
Tukin motar kawai yake yi blindly. Ransa a matukar bace, shin wai me yarinyar nan ta dauki kanta ne da
har zata kira shi da mazinaci ita kuma mumina? Tana ganin she is too holy for him har tana cewa zama
da shi zai kaita ga halaka wato shine halakar ko? Bayan duk abinda yayi saboda ita? Bayan duk abinda
yake kan yi saboda ita? To hell with her then.
Zai tabbatar mata dacewa ita din ba kowa bace ba face just a passing episode in his life and he will do
just fine without her, watarana zata juyo ta kalle shi tayi nadamar abinda tayi masa.
Zuciyarsa ta gaya masa cewa But first dole yayi proving to himself cewa zai iya rayuwar ba tare da ita ba.
Kafin daga baya yayi proving to her.
Automatically hannun sa ya sauka akan wayar sa ya dauko ta yana neman wata number, number din
wata yarinya ce da aka hada su da ita gab da tafiyar Jidda kuma tun daga lokacin bai kuma bi ta kanta ba
sai yau.
Babu bata lokaci ta dauka "lallai yau wannan jumaar tawa ce, tunda har doctor Faruq ya tuna dani kuma
ya kira ni"
Ya danyi gyaran murya yace "ko kuma ni ince jumaar tawa ce tunda har kika dauki kira na"
Tayi dariya cikin jan hankali tace "da can ma da ka kira zan dauka, ba ka kira ba shi yasa ban dauka ba"
yace "to yanxu ai gani na kira ko? Kaina bisa wuyana ina kuma bada hakurin rashin kira" tace "to anyi
hakurin. No ai ba zan iya fushi da kai ba" yace "ko? Show me sai in tabbatar" ta sake dariya "Kana
tantama ne? Just tell me when and where ni kuma zan tabbatar maka" yace "now" tace "yanzu yanzu?
Da urgency haka?" Yace "sai kin zo ma sannan zaki san girman urgency din" cikin sigar hillata tace "how
big" yace "very, come and see"
Tace "can't wait. Kazo ka dauke ni in the next 30 minutes, I will get ready for the big urgency"
Ya juya motar da zuwa hanyar gidan su, few minutes ya kai shi unguwar ya samu inuwa yayi packing ya
gyara kujerar sa ya kishingida yana jiran ta gama shiryawa ta fito. Yasan shirin da take nufi ba zai wuce
shaye shayen magunguna irin nasu ba, to get herself in the mood, amma shi har yanzu baya jin sa in the
mood and that hurts him.
Ya dauko wayarsa ya shiga internet ya fara neman abinda zai saka shi in the mood din. Bai jima sosai ba
ta shigo tayi kwalliya sosai irin tasu ta matan bariki. Kamshin da take yi kawai da kuma kallon da take yi
masa ya saka yaji ya fara samun mood din da yake bukata, ya takarkare ya jefa mata his best smile tare
da cewa "you look good, really good" ta juya idonta tace "kai ma haka" sannan ta dora hannunta akan
cinyarsa can sama sama ta dan matsa da salo irin nata tace "shall we? Na matsu inga iyakacin
matsuwarka".
Bayan mintina kadan suka je gidan gonar su Dr Bashir. A lokacin masallatan juma'a suna kokarin fara
huduba. Yayi horn mai gadin ya leko cikin shirin tafiya masallaci sannan sai ya koma ya bude masa ya
shiga da motar ciki, gidan gonar katon gaske ne mai cike da dabbobi kala kala, daga side daya kuma na
gidan anyi gini wanda baban Dr Bashir yayi a matsayin gidan saukar bakin sa amma kuma sai dan nasa
shi da abokinsa suka mayar da gurin gidan saukar nasu bakin tun bayan auren Umar, da a gidan Umar
din suke aikata duk taasar su, bayan yayi aure kuma shine suka dawo nan saboda seclusion na gurin da
kuma kasancewar babu kowa a gurin sai mai gadi da masu kula da dabbobin wadanda ba ko da yaushe
ne ma suke zama ba. Gidan bakin dan karami ne, madaidaicin falo ne da kuma ɗakunan guda biyu masu
dauke da toilets a ciki.
Umar yana shiga sai ya zagaya da motar sa bayan building din yayi packing din ta a kasan wata bishiya, in
da kullum idan yazo dama anan yake packing saboda tsaro, baya son ya bar motarsa a inda tsautsayi zai
iya sakawa wani ya gani.
Ya fita da sauri ya zagaya gaban building din yana kwallawa mai gadi kira, mai gadin ya taho da sauri ya
miko masa key din dakunan dan yasan su yake tambaya, Umar ya karba ya juya ba tare da yace masa
komai ba ya bude kofar gidan ya shiga yarinyar ta sa ta bishi a baya cikin karairaya. Maigadin ya bisu da
kallo cikin takaici sannan ya girgiza kai tare da karanto addu'ar neman tsari daga shaidan a zuciyarsa.
Sai da suka shiga suka turo kofa sannan ya juya yana kallon gate din, Dr Bashir ya kira shi dazu ya ja masa
kunne akan kar ya sake ya tafi wani gurin dan zai zo anjima, kar yazo ya tarar baya nan, shi kuma gashi
yana son zuwa masallaci, yasan dai abinda zai kawo shi ba komai bane ba face irin abinda ya kawo
abokin sa, dan sun saba dama zuwa wani lokacin ma sukan zo tare, dan haka yasan abinda Bashir din zai
nema a gurinsa ba zai wuce bude gate ba da kuma mukullin dakunan aikata alfashar tasu, dan haka sai
ya dauki sallayar sa ya fita ya dan tura gate din kadan amma bai rufe ba yadda ko Bashir din yazo kafin ya
dawo daga masallaci zai iya budewa da kansa, cikin kuma dama abokinsa yana nan dan haka a bude
yake.
*Mama*
Tun ranar Alhamis da Farhan da Amira suka kai mata su Yasmin take jin babu dadi, tabbas taji dadin
ganin jikokin ta wadanda girman kai ya hana ta zuwa ta gansu tun da taji cewa sun dawo gida tare da
Jidda. Haushin Jidda take ji sosai a ranta tana ganin cewa kusan dukkan abinda yake faruwa da ɗan ta a
yanzu laifin Jidda ne, me yasa a matsayin ta na mace ba zata zauna ta rufe sirrin mijinta ba? Bayan laifin
ma Umar yayi rantsuwa cewa bai kai ga aikatawa ba amma zata tashi hankalin ta ta kwashi yaya ta shiga
duniya bayan akwai mazan da suke yin abinda ya ninka na Umar muni kuma matan su haka suke hakuri
da su suna zaman aure suna rufe sirrin su ko dan yayan da suke tsakanin su. Amma ita Jidda da yake
shafaffiya da mai ce ba za ta yi haka ba, ta gwammace ta yi ta yawo tana barbadawa duniya labarin
abinda Umar yayi da kuma ma wanda bai yi ba. Gashi yanzu a sanadiyyar hakan har ciwo ya kama Baban
sa yana kwance, ga wannan tsinannen auren da Baban yayi rantsuwa akan sai ya makala wa Umar, wai
Umar din ta ne za'a aurawa yar mai gadi? Wannan wacce irin masifa ce? Kuma ma ba wannan ba, abinda
yafi kona mata rai shine yadda alhajin ya dora kishiyar ya akan dukkan abinda ya shafi sabon auren da
yake neman yiwa Umar din, ta kuma tabbatar da cewa ya gaya mata duk abinda ya faru da kuma dalilin
yin auren dan ita ya saka ta kai yarinyar asibiti ma wai a duba ko an yi amfani da ita, amma kamar yadda
Umar din ya fada ai ba za'a gane waye yayi amfani da itan ba. Sai dai kuma babu hujjar da zata nuna
cewa ba Umar din bane ba. Bakin cikin ta shine yanzu ita auntyn zata yi ta yamididi da zancen a cikin
dangi da kuma cikin dukkan wadanda tasan sun san Umar kuma suna ganin mutuncin sa.
Sai dai in tasan wata ai bata san wata ba. Ita tasan ko da ace Umar yana aikata abinda Jidda take cewa
yana yi to kuwa tabbas a cikin biyu akwai daya, ko dai akai aljanun da suke saka shi yi ko kuma asiri akayi
masa, in kuwa asiri ne to tabbas auntyn ce tayi shi dan in banda ita bata ga wanda yake da motive na yi
wa Umar asiri ba bayan ita auntyn, ko dan daukakar da yake samu da kuma soyayyar mahaifin sa gare
shi.
Ana kawo mata yaran bayan ta rungume su cikin jin dadi sai ta saka aka mai musu kayansu dakin ta, ta
kuma kira Umar a waya ta sanar dashi lallai yazo ya saka a gyara musu tsohon dakin Muhsina kuma ya
siyo musu duk abubuwan bukata dan sun dawo kenan.
Aunty tana jinta tace "na dauka sun zo su gan mu ne kawai? Na dauka zasu koma gidan su idan Allah ya
taimaka an daidaita maman su ta dawo dakin ta?" Sai Maman tayi shiru bata ce komai ba, amma ita a
ranta in da son samu ne tafi son Umar ya cire Jidda a ransa dan ba matar zama bace ba tunda ita ba
matar rufin asiri bace ba, in komai ya lafa ita zata nema masa mace ta gari ya aura wadda zata kare masa
mutuncin sa da martabar sa a duk inda yake.
Amma kuma sai taji tausayin Umar din sanda ya shigo gidan ya rungume ƴaƴan na sa kamar zai mayar da
su cikin sa, suma suna ta murnar ganin sa Yasmin har da hawayenta sannan suka yi ta bashi labarin inda
suka je da abubuwan da suka faru. Kalma daya biyu zasu fadi mommy, idan mommy tazo, in muka dauko
mommy daga gidan Abba, shima kuma Umar din haka "me mommy tayi?" "Mai mommy tace?" Duk
shine hirar tasu. Tabbas in zasu cire ta daga ransu ma ba da sauki ba.
Daga nan ya dauki yaran suka fice, basu dawo gidan ba sai dare, da ta tuna masa maganar gyaran dakin
da zasu zauna sai yace "Mama su zauna a dakin ki mana for the time being, in Jidda ta dawo ai zasu
koma gida ne" bai jira abinda zata ce ba ya fice.
A ranar a dakin ta ta shirya su suka kwanta, addu'ar Yasmin ta bacci ita ce "Allah Allah Allah ka sa gobe
muje da Daddy mu dauko Mommy mu koma gida" sai ta shafa ta kwanta ta juya baya.
Asad kuma ya tashi zaune ya fara jera wa Mama tambayoyi
"Mama anan dakin zamu kwana?"
"Eh"
"A ina zamu kwanta? Akan dago ko a kan carpet?"
"Akan gado"
"Damu da wa zamu kwanta?"
"Da kai da Yasmin"
"Daddy kuma fa?"
"Ba'a nan zai kwanta ba"
"Mommy fa?"
"Itama ba anan zata kwana ba"
"To ke kuma fa? A ina zaki kwana?"
Ta nuna kan carpet
Ya zaro ido "a'a ki hawo kan gado ki kwanta kar dodo ya zuro hannunsa ta kasan gado ya kamaki. Amma
kuma in kika yi addu'a dodon ba zai zo ba, mommy tace idan mutum yayi addu'a dodo baya zuwa,
kullum sai sunyi mana addu'a ita da Daddy ni da Yasmin in zamu yi bacci, mu biyu muke kwana a dakin
mommy ita kuma mommy sai ta tafi dakin Daddy amma sai su bar kofa a bude saboda cikin dare in
munji tsoro sai mu falfala da gudu mu shiga dakin su mu buya"
Mama ta rufe baki tana dariya, "kai Asad ka fiya surutu ka kwanta kayi bacci" ya kwanta ya rufe idonsa
"mommy tana karanta mana story sannan tayi mana addu'a kullum kafin muyi bacci" ta zauna a kusa
dashi tana kallon sa, sosai yake tuna mata da yarintar Umar dinta, kamar su daya kuma surutun su daya.
Sai data samu yayi bacci sannan yi fita ta tafi dakin Mufida tana so ta tuna mata da zancen bikin yar
kawarta da akeyi gobe juma'a kuma tana so suje tare, dan mufidan ta tashi da wuri saboda in bata gaya
mata ba zata makarar dasu da wannan shegen baccin safen nata da sai azahar take tashi.
Dakin a bude yake, mufidan tana kwance a kan gado ruf da ciki da waya a kunnen ta ta juya bayan ta can
daya side din tana magana kasa kasa yadda ita kanta Maman da ta shigo dakin badan yadda gari yayi tsit
ba daba zata ji abinda take fada ba.
"Kayi hakuri, gobe insha Allah zan san dabarar da zanyi. Kasan dai halin da nake ciki a gidan nan"
"Eh tace gobe zan raka ta wani event na wani biki, zan ce mata cikina yana ciwo ba zan je ba in ta tafi sai
in fito"
"Okay in ta tafin zanyi maka waya kai ma ka fito. Around 12-1 zata fita"
Ta danyi dariya
"Babu wani wuni fa. Nasan na zata dade sosai ba Kasan saboda rashin lafiyar Baba lekawa kawai zata yi"
"So sharp sharp kawai please"
"Okay mu hadu a kofar gidan zoo"
"Can't wait to see you too"
Ta sake dariya.
Mama ta juya ta koma falo tana dafe bango tare da rike kirjinta. Menene wannan taji? Waye suke waya
da Mufida? Akan me suke magana? Mai zasu yi in sun hadu? Saurayinta ne? Me yasa ba zai zo gida ya
ganta ba har sai tayi karya ta saci jiki ta je sun hadu?
Taji kamar ta koma dakin ta chakumi mufidan tayi ta dukan ta har sai ta gaya mata gaskiya amma kuma
ta san cewa ba zata samu cikakkiyar gaskiyar daga haka ba, dan kusan shekara guda kenan Umar da
kansa yazo gida ya kwakwkwada wa mufidan mari ya cevya ganta tana shiga motar wani, sannan ya saka
mata takunkumin fita wanda ita Maman ta cigaba da ensuring, amma kuma har yanzu sun kasa gano kan
mufidan ta kasa tsayar da hankalin ta guri daya ta fitar da mijin aure ga kuma kumbiya kumbiyar da take
tayi wadda tafi kama da ta marasa gaskiya.
Sai maman ta ga kamar wannan chance ne nata na sanin gaskiyar halin da yar autar tata take ciki, na
sanin waye wanda suka yi waya yanzu kuma menene