Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
a ajjiye"
Raina ya karasa baci nace "to sai menene? Ina ruwanki? Mijina ne menene dan ya kula da ni ya lallabani
ina ruwan ki menene na zuwa kima gaya wa mutane, in na hau motarsa ina ruwanki dashi da motarsa
dukkan su mallakata ne menene naki a ciki?"
Ta juya kai gefe "Allah ya baki hakuri naga kin dau zafi, matar gold mai mijin diamond" nace "diamond
kadai? Ai ni a gurina mijina yafi daimond daraja da daukaka da kima wallahi dan diamond kowa zai iya
saka kudi ya siya mijina kuwa kyauta ce daga Allah ya bani shi ta yadda kudi ba zasu iya siya min
soyayyarsa ba"
Ta juyo tana harara ta "ban da dai kuri da cika baki, ni baki san duk mace mai yabon mijinta a gaban
mutane haushi take bani ba?" Nace "yabo ai ke kika fara, ke kika zauna a gabana kina yabon mijina shi
yasa ni kuma nake taya ki, kuma hausawa sunce yabon gwani ya zama dole shi din kuma gwani na ne
dan haka dole in yaba masa"
Maryam tace "ban da dai cika baki gwara kiyi yabon saffa saffa dan wani gwanin in aka tono kazantar da
yake aikatawa kuda ma ba zai bi ba"
Sai a lokacin Mufida da take ta faman daddanna wayar ta ta dago sannan ta mike tsaye "ke dalla can da
dakata haka nan, kar ki ce zaki yiwa mutane maganar banza anan ina ruwanki wai da mijinta ne?
Munafuka kullum kina hanyar gidan ta kullum kina bibiyarta kina kalle mata miji kuma ki zo ki ce zaki fadi
maganar banza dan yace baya son ki? Ji nake nan kika same ni da magiya wai in hada ki dashi naki yarda,
kika je kina ta binsa yana wulakanta ki ya kuma gaya miki baya son ki amma shine har yanzu ba zaki fita
daga harkar shi ba, ba ranar nan na gaya miki kar in kara ganin kin je gidan su ba? Amma baki ji ba ko?
To yau zan kunce miki zani a kasuwa munafuka"
Abinka da mata, nan da nan sai aka zagaye mu ana tambayar abinda ya jawo hayaniya, Mufida ta fara yi
musu bayani wai ashe tun zuwan da Umar yayi makarantar, tun ranar da muka hadu dashi itama
Maryam ta ganshi kuma tun a lokacin ta gaya wa Mufida cewa tana sonsa ita kuma Mufida tace babu
ruwanta, bayan munyi graduation ma wai haka ta ringa zuwa har gidan su Mufida tana neman sa, har
office take binsa sai daya gaya wa Mufida yace tayi mata warning ta fita harkar sa, tunda lokacin muna
dating, ashe duk zuwan da take yi gidan mu dan ta ganshi ne ba dan ni ba.
Dama ni nayi tunanin biri yayi kama da mutum dan in dai muka hadu bata da magana sai tasa, ta ringa
hirarsa kenan ta na min tambaya a kansa tun ina biye mata har abin ya fara isa ta har ta kai ga yau munyi
sa'insa.
Ai kuwa nan aka yi caaa akan Maryam aka yi ta caccakar ta har da masu kiranta da mugayen suna ye,
"ina ruwan ki da mijinta? In ma kina son sa a da tunda ya auri kawarki kuma ya gaya miki baya son ki ai
kamata yayi ki rabu da shi. Wannan ai cin amana ne" har da masu bani shawara "duk sanda ta sake zuwa
gidan ki tayi miki hirar mijinki ki gurje bakin shegiya a kasa"
A na cikin hayaniyar ashe Maryam ta sulale ta bar wajen, sai daga baya wata tace ta ganta a bakin gate
ta hau babur ta tafi tasha. Sai naji a raina banji dadin rigimar da akayi ba, Mufida kuma tace "Umma ta
gaida Aysha, dama ni ba'a son raina muka taho da ita ba"
Bayan mun gama mun taho a hanya ne Mufida take gaya min Baba yace ta fitar da miji a hada aurenta
dana Muhsina. "Wai wani nan ma aure za'a yi min, chafdi, ai kuwa zasu san wadda zasuyi wa aure ba ni
ba. Kowa sai da aka barta ta gama karatunta tayi service ta huta sannan akayi mata aure amma ni ace
wai na karasa karatun a dakina? Saboda me? Saboda ni ba'a so na ko me?"
Nayi dariya "yar lelen Mama waye zai ce baya son ki? Gata ne fa za'a yi miki, ke auren fa da dadi" sai
nafara yi mata hirar aure da irin albarka da take ciki da dadin damace take ji musamman inta dace da
miji na gari, ita dai kawai ji na take yi tace "kyayi kya gama ma, ni ba yanzu zanyi aure ba" nace "sai
yaushe to?" Tace "sai nagama zaba na gama tantancewa da gama screening sosai tukunna. Ai dai ba
zasu yi min auren dole ba dai ko? Ni kuma ba zan fitar da mijin ba".
Duk a yadda nayi da Mufida ta gane cewa babu harm in aure yanzu amma bata gane ba.....
Sati daya cif bayan taron mu. Muna kwance da dare a dakin Umar bayan mun kwantar da yara a dakina.
Ina kwance a jikinsa ina bashi labarin wani Hausa Novel dana karanta wai shi Maimoon, shi kuma yana
game a wayata daga alama ma ba sauraron labarin da nake bashi yake yi ba amma ni ban daina ba
saboda son da nake wa littafin.
Muna cikin haka aka kira wayata, ya nuna min screen din naga number ce babu suna sai nayi cutting "da
daren nan ba za'a bar mace ta kwanta a jikin mijinta taji dadi ba sai a dame ta da waya?" Yayi dariya "a
bar mace dau ta damu mijinta da labarin da ba gane wa yake yi ba" nayi juyi akansa "kai, labarin soyayya
ne fa, ka tsaya kaji Allah da dadi" yace "ni ba zanji labarin soyayyar wasu ba sai dai ki zo muyi tamu
soyayyar" ya fada yana ajiye wayar a daidai lokacin da aka sake kira, na dauka na ga waccan number din
ce dai, yace "ji dauka, maybe it is important, in kinji ba important bace ba sai ki katse"
Sai na tashi zaune sannan na dauka
"Assalamu alaikum"
Sai naji muryar Maryam tace "golden wife matar diamond husband, na ajiye miki sako amma har yanzu
banga alamar kin gani ba shi yasa na kira in gaya miki inda yake dan in saukaka miki nema. Ki duba bayan
motar diamond husband dinki akwai sako na ajiye miki, idan kuma baki yarda da cewa abinda zaki gani
nasa bane ba zaki iya kaiwa kowanne asibiti a gwada miki dan a tabbatar miki. By the way, I think it is so
romantic the way ge carries a band mai sunan ki a jiki kullum a hannunsa, nasan hakan yana miki dadi
sosai shi yasa na cire na saka masa nawa dan nima in gani inji dadi. Like I said, not all that glitters are
gold"
Sai ta katse wayar. Na dago kaina ina kallon sa sai naga shima ni yake kallo, sai ya bude ido "what? Waye
a wayar? Me akace?" Ban ce komai ba sai na kama hannunsa da sauri ina dubawa, zuciyata tana bugawa
da karfi amma tun kafin in kai hannuna kan band din na fahimci ba nawa bane ba, wannan yafi nawa
sabuntaka dan nawa duk color din sun goge saboda har wanka Umar yake yi da shi a jikinsa, na juyo
gurin sunan da sauri "Mery G" na ga an rubuta.
Tabbas nata ne dan na tuna sanda aka bamu tana da mita cewa ita ba wannan sunan tace a saka mata
ba. Ya kalla shima da sauri sai naga ya zaro ido "what? Menene wannan din?"
Bance masa komai ba sai na sauka daga kan gadon na fita da sauri na bude kofar falo, ina fita daga gidan
naji ya biyo baya na "Jidda" ban amsa ba na bude kofar baya na motarsa, zuciya ta tana bugawa da sauri
a raina ina cewa "God please no, don't let it be"
Da farko banga komai ba, sai dana shiga ciki sannan na ga alamun kaya a kasan kujera, na zaro su sannan
na fito daga motar a lokacin da ya karaso inda nake, na daga su ina kalla, pant ne da bra. Ya fara girgiza
kai "Jidda listen, dazu Yaya Mubaraka ta karbi aron motata, maybe kayan ƴaƴan ta ne" na jefa masa su
"yaya Mubaraka bata da yayan da suke saka brazier, kuma na tabbatar itaba zata cire nata ta bar maka
su a mota ba"
Kayan suka daki jikinsa suka zube a kasa, sai na lura wani abu ya fado daga cikin su, na sunkuya na dauka
ina kallon abin a cikin hasken security light din gidan.
A used condom.
Shine abinda Maryam tace min idan ban yarda nasa bane ba inje a gwada min.
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din
08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*wannan littafin na siyarwa ne a bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta idan kuma kin siya kar ki yi
sharing, in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*
*The Trash*
Ya fara girgiza kansa yana ja da baya "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Jidda menene wannan a hannun
ki? Jiddah wa ya saka min wannan a mota ta? Waye ya kira ki a waya?" Ban ba shi amsa ba sai na jefar da
abin hannuna, sannan ba tare da cewa komai ba na juya nayi hanyar cikin gida.
Tafiya kawai nake yi ba wai dan ina ganin gabana ba sai dan na riga na saba da duk wani inch na gidan,
har na wuce falo na shiga corridor sannan na shiga dakina, ban tsaya ba na zarce toilet na dauro alwala
dama banyi sallar isha ba dan haka na fito na shimfida sallaya, ina saka hijab ya shigo dakin da waya ta a
hannun sa
"Jidda kiyi min magana, waye ya kira ki a waya? Me aka ce miki kuma? Jidda kayan nan wallahi bansan
yadda akayi suka shiga mota ta ba"
Na saka hijab dina na hau sallaya na tayar da sallah, shi kuma ya zauna a bakin gado da waya ta a
hannun sa yana ta dannawa yana saka wa a kunne daga dukkan alama number din da Maryan ta kira ni
da ita yake kira.
A sujjada ta ta karshe kamar yadda na saba kai wa Allah kuka na kullum a kowace sallah sai yanzu ma
nayi kokarin yin hakan, amma sai naji na kasa jero kalaman da zanyi addu'ar dasu, sai kawai naji kuka ya
zo min nan na fara yi da sheshshekar da ta saka gabakidaya jikina yake karkarwa, kadan ya rage jikina
baiyi giving up na fadi ba amma ban daina kuka a gaban wanda nasan shine kadai zai share min
hawayena ba, wanda ko ban ambata komai ba yasan komai kuma shi zaiyi min maganin komai.
Sai da naji numfashi yana neman gagara ta sannan na dago na kammala sallah ta nayi sallama. Sai na
ganshi ya sauko daga kan gadon ya na durkushe a gaban gadon a kusa da sallaya ta, idonsa yayi jawur
tamkar in aka watsa turaren wuta a ciki kamshi zai tashi.
Na dauke kaina daga kansa sannan na fara gabatar da adduoin rufe sallah kamar yadda nake yi kullum.
Bai yi magana ba har na gama na mike da niyyar nade sallayar sannan in bar masa dakin tun kafin kallon
fuskar sa ya saka zuciyata ta buga in mutu. Sai dai ina mikewa wani irin jiri ya debe ni, nayi sauri na dafe
kaina da hannu daya dayan kuma na dafe bango dashi ina ambatar sunan Allah.
Na jima a haka kafin kaina yayi clearing jirin kuma ya rangwanta min, sai dana dawo hayyacina na lura a
jikin Umar nake, ya zagayo hannunsa daya ta saman cikina ya rike ni tsam a jikinsa dayan kuma ya dora
akan hannuna dana dafe kaina da shi. Shima yana maimaita abinda nake fada. "Innalillahi wa inna ilaihir
rajiun"
Na juya da sauri na tura shi baya da dan karfin da nake dashi. Kasancewar turewar da nayi masa tazo
masa a bazata sai ya tafi da baya kamar zai fadi amma sai ya dafe jikin gado ya tsaya yana kallo na fuskar
sa cike da tashin hankali.
"Jidda" ya kira sunana.
Na nuna shi "dan Allah, dan girman Allah Umar kar ka sake ambatar sunana bana son ji, dan Allah da
girman Allah ka fita daga dakin nan bana son ganin ka, dan Allah dan girman Allah kar ka jawa yayana
asara kayi musu sanadiyyar da zasu tashi marayu, na tabbatar in ina cigaba da ganin ka kuma ina cigaba
da jin muryar ka to gobe za'a saka ni a kabari na, na tabbatar kafin gangar jikina ta fara decomposing kai
already ka saka wata akan gadon ka, su kuwa sai dai su kasance yayan riko a gurin matar da zaka aura ko
kuma a gurin wadda zata rike su a cikin dangi. Please ba dan ni ba, dan su, kuma dan Allah ka fita ka bani
guri"
Ya rufe bakin da ya saka yana kallona sannan yayi kokarin clearing muryar sa yace "ba zan iya ba, ba zan
iya fita in baki guri ba a wannan halin da kike ciki, you are sick Jidda, kin san kina da hawan jini ko? Ya
zaki yi kiyi shiru kuma ba zaki yi min bayanin abinda ya faru ba ballantana in amsa laifina ko in karyata
abinda banyi ba in kwantar miki da hankali? Please kiyi min magana Jidda, please kiyi min bayani dan
barin magana a cikin ki ita ce zata cutar dake ba wai ganina ko jin muryata ba" .
Na sake sunkuya wa na dauki sallayar da na yar ban sani ba na fara ninke ta sai dana gama sannan na
lura a baibai na ninke sai na warware na sake ninkewa sannan na ajiye, na cire hijab din jiki na na fara
ninke shi shima amma sai ya zame ya fadi kasa, sai a lokacin na lura ashe karkarwa hannuna yake yi, na
sunkuya zan dauka sai ya riga ni sunkuyawa ya riga ni dauka sannan ya ajiye shi a gefen gado, na wuce
shi na sake daukan hijab din na cigaba da kokarin ninkewa ina jin yadda kaina yake wani irin sarawa
sakamakon rike tunani na da nayi a guri daya not letting myself think, dan a tunani na in na bar kaina
nayi tunanin mijina kwance da kawata to tabbas zan zama gawa.
Yakama hannuna ya karbe hijab din ya sake jefar dashi yace "don't do this please Jidda kar kiyi haka, kiyi
fada kiyi kuka and hit me if you want, but ki fada min waye ya kira ki a waya, ki fada min waye ya saka
min kayan can a mota, ki fada min waye ya chanja min wannan band din" ya karasa yana ciro abin daga
hannunsa sannan yayi jifa dashi, fuskar sa tana nuna bacin rai, tsananin bacin rai.
Nace "waye ko wace? Kuma dan me zan zauna ina yi maka bayanin abinda na tabbatar ka fini sanin
amsoshin, dan me zan bata raina da lokaci na da kuma yawun baki na a gurin yin maganar da ba zata
amfane ni da komai ba sai karin takaici da bakin ciki, dan me zan baka damar yi min bayanin da already
na riga na san amsar shi"
Sai ya sunkuya ya dauki band din da ya yar ya juya shi yana karanta sunan "Mery G" ya karanta a fili,
"wacece wannan?" Ya fada yana nuna min abin "how in God's heaven did she changed my band" na
daga kafada "ta yaya zanyi in san lokacin da ta saka maka, was I there?"
"Mery G" ya maimaita, "wannan abin na kawayen ku ne yan makarantar ku, kawar ki ce kenan, yar
secondary school din ku" ya fada yana kallona kamar mai jiran in bashi amsa, sai kuma ya saki abin ya
dafe kai, fuskar sa tayi jawur kamar yadda idonsa yayi
"wallahi sai na ci uban yarinyar nan, wallahi sai tasan ni tayi wa wannan sharrin"
Ya juyo yana kallo na "Jidda wallahi abin nan da kika gani a mota ba nawa bane ba" na wuce shi na zauna
akan gado, yadda ya dauki zafi yana kara min takaici.
"Zan iya yarda cewa ba naka bane ba, zan kuma iya yarda cewa baka san yadda akayi kayan suka shiga
motar ka ba, zata iya yiyuwa makirci ne ta shirya take so tayi maka sharri bla bla bla, amma ta yaya ta
kama hannunka har ta chanja maka band din da ya kama hannunka ma ba rawa yake yi ba ba tare da ka
sani ba? Can you explain that? Shin asiri tayi maka ko rufa ido tayi mana gabakidaya ko kuma tayi
drugging dinka ne har ta chanja baka sani ba?"
Ya daga kafada "I don't know, maybe asirin ne ni ban sani ba, kuma it is very possible dan akwai mata,
yammata da suke asiri dan su samu abinda suke so, kuma wannan bushashshiyar karmasashshiyar,
kodaddiyar, jemammiyar, mokadaddiyar yarinyar babu abinda ba zata iya ba dan ta samu abinda take
so"
Na gyara wa yayana kwanciyar su nima na kwanta ina jin ciwon kaina yana ƙaruwa nace "eh zata iya
komai na sani, zata iya seducing dinka ma na sani, but the fact that you fall for it knowing well cewa
kawata ce shine abinda yake cin zuciyata a yanzu. It is one thing ace ka nemi mace, some faceless
nameless prostitute wadda ban sani ba kuma babu wata alaka a tsakani na da ita but it is totally a
different issue ace ka nemi friend dina, a very close friend of mine for that matter" na fada ina jin wani
irin ciwo mai zafi wanda tun dazu nake rikewa bana so in jishi, naji yana sukar zuciya ta.
Tabbas Maryam ta ci amana ta, amma Umar tasa cin amanar tafi girma a gare ni dan shine nafi kusanci
da shi akan Maryam.
Tabbas ban yi zeroing mind dina ba akan cewa Umar kwata kwata ya daina halinsa, amma na saka ran
cewa abin yayi sauki, kuma ban taba tsammanin cewa karuwa abin nasa yayi ba, karuwar da har zata kai
shi ya kwanta da friend dina, ya kwanta da Maryam.
Na juya baya na dan bana so in cigaba da kuka a gabansa, bana so ma in cigaba da maganar dashi dan
bana jin akwai abinda zai gaya min wanda zai saka in yarda da cewa bai nemi Maryam ba.
Ina jin sa ya dan zauna a bayana kadan, sai kuma ya mike yace "ban taba tunanin cewa gap din da muka
samu a tsakanin mu har ya kai girman da wasu zasu shiga ciki ba. Yarinyar nan ta jima tana bina, idan
baki yarda ba ki tambayi Mufida dan na sha gaya mata tayi mata warning ta daina bina in ba haka ba zan
gaya miki, ban taba gaya miki