Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
namiji kuma har sai ya balaga sai ya zabi inda yake so, sai kuma a yankewa mijin abinda
zai ke bata na ciyarwar ƴaƴan su dai dai da income dinsa"
"Wannan shine mostly abinda ake yi unless if ita uwar ceai problem kamar na rashin tarbiyya, yadda har
ake tsoron in aka bata yayan tarbiyyar su zata gurbata kuma bata da uwar da zata rike on her behalf to
sai a bawa uwar mijin su ta rike su"
"Dan haka mata suna da gata, gata mai yawa da addini yayi mana amma mu bamu sani ba, ko kuma mun
sani mun zubar da shi a kasa su kuma maza sun take ta kanshi sun wuce"
Na girgiza kaina "da yawan mata ba hakan bane kadai, da yawan mata tsoro ne, tsoron abinda zasu tarar
a gaba suke yi da kuma tsoron kallon da society zasu yi musu suke yi, tsoron kalmar bazawara suke yi,
tsoron responsibility din da zasu kai gida suke yi. Iyaye da yawa responsibility din ne suke gudu shi yasa
ba sa son yarinyar da suka aurar ta dawo gida da sunan zawarci"
Diyam tace "hakane, anan gabar ne kuma self dependency ya shigo ciki, ba wai ina nufin mace tayi
zaman kanta ko kuma ina nufin mace ta zama bata bukatar namiji ko iyaye ta a rayuwar ta ba, a'a i a
nufin mace ta kasance zata iya daukan nauyin kanta da ƴaƴanta, in terms of feeding da sauran daily
bukatu. Idan har ba zaki zama liability a gidan ku ba su kansu iyayen ba zasu ƙi ki dawo gidan ba, ina
nufin idan har marriage din ya kai breaking point. Idan kuma kin dawo din ba zaki zama liability ba,
kannenki ba zasu raina ki ba, yayanki ba zasu wulakanta ba, shima kansa mijin da kuka rabu ba zai ke
daga miki kai gurin kawo kudin feeding da yake kansa ba, sannan idan wani auren yazo miki wanda zai
aure kin ba zai ke feeling cewa taimaka miki zaiyi ya aure ki ba rather sai dai taimaka wa juna zakuyi ke
da shi."
"Ba wai ina nufin mace tayi kudi dole ba, ko kuma ina nufin in tanada sana'a ko aiki bata bukatar namiji
ba, a'a, amma in tana da abin hannunta ta wuce wulakancin a gurin maza da matan baki daya. Dogaro da
kai ba wai yana nufin lallai aikin gwamnati ba, ko kuma yana nufin lallai sai kina siyar da laces da
atampopi ko kina order din dogayen riguna daga Dubai ba, akwai wadda na sani ta fara sana'a da 1k, ta
siyo kayan hadin spices ta niƙa ta daddaura a leda take siyarwa naira 20 20, makota suka fara siya. Da
yake ta kyautata a cikin sana'ar ta, tayi hadi mai kyau nan da nan a hankali sai gashi fa tara daurin
hamsin hamsin tana kaiwa shagon unguwa ana siyar mata, daga nan sai zubawa a robobi, daga nan sai
gata har da yin sticker da sunan ta tana likawa a robar, daga nan sai ta fara yi da yawa tana kaiwa stores
ana siyarmata, sai tazo ta shigar da jan yaji da yajin daddawa, yajin tafarnuwa, yajin zogaye da sauransu.
Wanny sana'ar ita ce a yanzu take rike da ita.
"Nasan wata mata kuma da take yi kunun aya. Ta fara yi ne tana daurawa a leda a bawa almajiri ya
zagaya mata unguwa, a yanzu ta sanar min tana siyar da kunun aya a kullum musamman lokacin zafi na
more than 30k, tasha tasha kasuwa kasuwa ake kai mata, har yara ta dauka aiki suke taimaka mata, da
wannan kunun ayan da shi take rike kanta da yayanta"
"Misalai suna da yawa, na san ke ma kinsan wasu. Abin dai da nake nufi shine, if you can get aikin
gwamnati, it is good, idan kuma sana'a zaki yi that is even better, amma idan zaki iya hada aikin
gwamnati da kasuwanci that's even the best. As long as zaki tsare mutuncin ki zaki kiyaye dokokin
ubangiji shikenan. Mu tuna, ko da babu mutuwar aure akwai mutuwa, naturally maza suna riga mata
mutuwa, miji zai mutu ya bar ki da yaya, ya zakiyi kenan a lokacin?"
*Umar*
Tace "of course na fahimta. Kuma ina tunani ne da kwakwalwa ta sabanin da da nake tunani da zuciyata.
Tabbas na fahimci Abba zai raba ni da kai which is exactly why zan je gurinsa because that's what I want
with all my heart. Rabuwa da kai. Allah ya bawa Baba lafiya and I wish you best of luck a sabon auren ka.
Allah ya kawo kazantar daki"
Daga nan ta kife wayar. Amma shi yasan ko da bata ajiye wayar ba baya jin zai iya kara yi mata magana
ko da kalma daya ce. Maganganun ta sosai suka taba zuciyar shi fiye da yadda ita kanta da tayi su tayi
tunanin zasu taba shi. Ya saki kan wayar ba tare da ya mayar gurin ajiye ta ba sannan ya juya yana tafiya
duk kuwa da cewa baya ganin gabansa clear, yana jin mai gadin yana yi masa magana amma ya share shi
bai juya ba dan idan ya juya zai iya kikkifa masa mari duk da babu abinda yayi masa.
Wani irin haushin Jidda yake ji, wai me take tunani ne? Ya san tana fadar abinda ta fada ne kawai dan ta
bata masa rai amma yasan tana son sa, ya san kuma ba zata iya rayuwa babu shi ba kamar yadda shima
ba zai iya rayuwa babu ita ba. Kuma zamanta a gidan nan ne ya jawo hakan, they are brainwashing her,
suna gaggaya mata maganganu suna zuga ta suna nuna mata zata iya rabuwa da shi. Tabbas ko ba yau
ba sai ya dauki mata ki akan mai gidan nan da matarsa.
Sai da ya kai karshen layin a kafa sannan ya tuna cewa da mota yazo ashe, sannan ya juya ya koma kofar
gidan ya shiga motar, a ransa yana tunanin maybe maganar da mai gadin yake yi masa dazu kenan. Yana
cikin tafiya a hanya wayarsa tayi kara ya duba yaga waliyin Jidda ne ya sake kiransa, sai ya katse kiran ya
kuma kashe wayar ya saka a cikin aljihun mota. Su je su neme ta da kansu shi ba zai kai su ba. Sai kuma
ya tuna ta ce zata kunna wayar ta ta neme su da kanta.
Ya cigaba da driving, not knowing where to go or what to do.
*Farhan*
Tana kwance a dakin ta, yau duk bata jin dadi, duk abubuwa sun cushe mata a kanta ta rasa madafa.
Kuma ma yau zuciyarta duk babu dadi.
Wayarta tayi kara ta dauka ta ga sunan wannan saurayin da ya karbi number dinta a gidan su kawar
Jidda. Ta tabe baki, wannan shine kira da yayi mata na uku kenan tun sa da ya karbi number dinta. Kira
na farko kin dauka tayi, kira na biyu kuma ta dauka amma ta nuna masa bata gane waye shi ba duk da
cewa ta gane dan tayi saving number din tun sanda ya nemi tayi saving din.
Tayi kamar ba zata dauka ba, sunanan irinsu da yawa suna damunta kusan kullum, shamarin shaho masu
ado da walwali, masu daukan hankalin yammata da suke desperate for mijin aure a karshe kuma su jefa
su a ramin da ba zasu iya fitowa daga ciki ba.
Sai kuma ta dauka tare da sallama murya can ciki.
"Salamu alaikum"
"Ameen wa alaikumus salam gimbiya"
Ta juya idonta.
"Waye yake magana?" Yayi dan shiru ka dan, kamar ransa bai so abinda take masa ba yace "you still did
not save my number, did you?" Tace "ai ban gane waye ba ma ballantana inyi saving, waye?"
Yayi ajjiyar zuciya "okay. Mai nema ai ance baya zuciya ko? I called you yesterday and the day before
that, sunana Sadiq, na karbi number din ki ne a hannun ki sanda kuka je gidan mu neman address din
kawar ku Diyam. Kin gane ni yanzu? Though nayi wannan bayanin tun jiya"
Tace "ohhh okay. Nagane ka. Ya akayi?" Ya sake jin babu dadi, sannan yayi magana kamar mai hada
kalmomin, daga dukkan alama bai saba ba "ammm dama address din nan dai dana tambayeki jiya shine
dai zan sake tambaya yau. That's if it is okay with you. In kuma akwai damuwa just say so please so that
we won't waste each other's time"
Tace "damuwa kamar yaya?" Yace "damuwa kamar banyi miki ba, tunda kin ganni, ni kinyi min ne shi
yasa nake bibiyar ki, in banyi miki ba it is okay. Ko kuma maybe anyi miki miji a gida, ina ganin waɗannan
sune kadai dalilan da zasu saka ki hana ni address din ki at the moment"
Tace "ko kuma maybe ina gudun halin ku na maza ba?" Sai ya danyi dariya, relaxing a little. "Halin mu na
maza kuma? Me muka yi? Allah sarki mu maza bayin Allah" tace "yaudara ma na da dadin baki, yawancin
ku haka kuke" yace "nooo, kar ki bari wani mutum daya ko biyu su saka kiyi generalizing din mu. Kuma
idan har lissafi za'a yi na gaskiya mazan da ake yaudara sun fi matan da ake yaudara yawa"
Tace "sai dai in lissafin son zuciya za'a yi, dan ni I know a lot of matan da aka yaudara" yace "saboda ke
macece ba, ni kuma I know a lot of mazan da aka yaudara" tace "da zaka tsaya mu tantance zaka fahimci
ni ce da gaskiya" yace "da zaki bani address din da sai inzo mu tantance ido da ido" ta juya idonta "okay,
zan turo maka. But mind you you will have to see my father first".
Tana ambatar father din taji shi ya kwalla mata kira, tayi saurin katse wayar ba tare da yi masa sallama
ba sannan ta saka hijab din ta ta fita tsakar gida tana amsawa, daga sitting room ta jiyo muryar sa dan
haka tayi can din, tana shiga ta tarar dashi da babban amininsa ne a zaune, gabanta ya fadi, shikenan
cewa zasu yi sun fitar mata da miji tunda taki fitarwa. Ta durkusa ta gaishe su sannan ta rakube a gefe.
Abba yace "ya akayi kika san mijin Jidda ya san inda take?" Sai ta basu labarin kiran da yace Yasmin tayi
masa da kuma binciken da suka yi har suka samo address din Diyam. "Shi kadai yaje gidan ba tare da mu
ba, dan haka bamu tabbatar ya same ta acan din ba ko a'a" ta karasa labarin nata. Abba ya miko
hannunsa bani wayarki inga address din da aka turo.
Ta fara inda inda, tana tunawa da maganar da take karshen address din "ammmmmm dama...... Abba,
watooooo wayar......... Wayar tana daki bara in dauko" ta tashi da sauri ta fita suka bi ta da ido, da ta
dauko wayar mata jima tana juyata a hannunta tana tunanin abinyi, in dai tayi editing zasu gane tunda
zasu ga ba sending mata akayi ba kamar yadda ta fada, dan haka taje ta kai musu ta koma gefe tana sosa
kai, Abba ya karanta sannan ya dago yana kallon ta, ta sunkuyar da kai waiting for ruwan fada ya fara
zuba akanta amma sai taji yace "ki shirya ki je gidan, zaki iya ganewa?" Ta gyada kai, yace "ki je ki
tabbatar tana can sannan ki ce mata in ji ni nace indai nine ubanta ta zo ina nemanta" ta sake gyada kai
da sauri sai ya jefa mata wayarta tare da kudin mota.
*Jidda*
Cikin kankanin lokaci na gama hada mana kayan mu kaf, sannan na tafi gurin da yara suke wasa na zauna
tare da su ina kallon Subay'a tana koyawa Yasmin karatu ina ta mamakin yaran yanzu da irin abubuwan
da ake koya musu a school, wadansu abubuwan da suka sani a ni sai da na shiga secondary school na san
su.
Muna zaune Diyam tayi joining din mu itama tana correcting din su in sunyi mistake. A haka aka zo aka
sanar wai anyi bakuwa kuma tace ni take nema. Muka kalli juna ni da Diyam, abubuwa da yawa suna
zuwa min rai amma sai naji nafi zargin Mufida ce Umar ya turo. Sai na aika a tambayo wacece sai aka ce
Farhan. Haka kawai naji wani dadi a raina, duk da bansan abinda zai biyo bayan zuwan nata ba amma
tabbas nayi missing din ta da kuma dukkan sauran ya uwana.
Tunda nace ta shigo na mike tsaye ina kallon hanyar da zata shigo din, inajin excitement da faduwar
gaba a lokaci daya. Tana shigowa kuwa na tafi da gudu na rungume ta ina murna itama tana yi. Ta dago
kai tana kallo na "ke ya naga kamar har kin fara cikowa ne, me suke baki a gidan ne?" Nayi murmushi
"babu abinda suke bani sai kwanciyar hankali, bana fargabar me yake faruwa ko kuma menene zai faru,
na riga na gama yanke shawara na mika dukkan lamura na ga Allah kuma zan bi dukkan abinda yace"
tace "good for you. Mutumin ki yana can yana neman zaucewa" nayi murmushi kawai sannan na ja ta
muka zauna "bani labari, ya kowa da kowa? Ya Abba?" Ta tabe baki Tace "shi ya turo ni, yace ko dai ki
bini mu koma gida ko kuma ki sake wani uban" nayi murmushi "yana nan dai yadda yake kenan" tace "da
dan sauki kadan, kwana biyun nan kamar baya fada sosai. Ki je kawai kiyi facing dinsa in yaso in daka ki
zaiyi a turmi a tuka masa tuwo da garin ki sai yayi. Tunda dai you can't stay here forever ko?"
Sai dai kuma bai daka ni a turmin ba bayan Diyam ta kaimu gida da kanta a motar ta, asali ma bai ce min
komai ba sai key din dakin umma daya jefe ni dashi sannan yace "ki bude wayarki kuma ki kira uwarki,
tana can ta tashi hankalin ta tana neman ki".
A ranar da dare na kunna wayar ta wa na kuma kira auncle Muhammad wanda ya rufe ni da fada kamar
zai cinye ni danya, sannan daga karshe ya turo min number din da zan samu Umma. Ranar har kusan
tsakiyar dare muna waya da mutane, daga wannan sai wancan, na tambayi yaya Tahir dalilin da yasa bai
gayawa Umma da Abba ina turo masa message ba sai yace "yanzu ai gashi nan ta samu ta ga yauwanta"
na tambayeshi yaushe zasu dawo sai yace "ni dai zam dawo cikin satin nan, ita kuma sai ranar da Baba ya
turo mata kudin jirgi" ya karasa yana dariya, nayi murmushi kawai, wato yana sane so yake ya kai Umma
gurin yanuwanta kuma ya bar ta acan ta kara hutawa ta huce daga masifar Abba da ta Hajiya.
Washegari tunda assuba Umar yake kirana, wato ya gwada layin yaji yana shiga, ban kashe wayar ba
kuma ban yi blocking dinsa ba sai na bar wayar tana ta ringing amma sai na saka ta a silent dan kar karar
ta ta dami yara na da suke bacci abinsu. Sai da nayi baccina mai dadi na farka sannan na dauki wayar
naga 21 missed calls duk daga gurin sa. Sai kuma messages din da ko karanta su banyi ba na goge su dan
nasan magana daya ce a ciki, inyi hakuri ya daina halinsa, ba zai iya rayuwa babu ni ba and other stuffs.
Na dauka gari yana wayewa zan ganshi a gidan amma sai naga bai zo ba har yamma, sai na daure na
karanta some of his messages sai na fahimci Abba ne ba zai iya fuskanta ba shi yasa ya kasa zuwa gidan.
But he wants to see me and the kids.
A ranar ne na shiga har daki na gaishe da Hajiya, sai ta zauna a kusa dani fuskarta cike da damuwa.
"Sannu Jidda. Munji dadi da Allah ya dawo mana da ke gida lafiya. Allah ya daidaita ya raba mu da
mugun ji da mugun gani, rabuwa da miji irin Umar ai ba karamin mugun ji da mugun gani bane ba. Duk
da dai bansan abinda ya hada ku ba har kika yanke shawarar shiga duniya"
Na yi shiru ina lissafin ta inda zan fara mata sai nace "au baki san abinda ya faru ba Hajiya?" Ta gyara
zama "ban sani ba, Alhaji bai gaya min komai ba kinsan halinsa babu wanda yake jin cikinsa" nace
"gaskiya ya kamata ace kin sani a matsayin ki na babba a gida, to bara ni in gaya miki tunda shi bai gaya
miki ba duk da na riga na gaya masa, amma matsalar shine ban san ta inda zan fara baki labari ba, shin ta
abinda aka binne min a kofar falo zan fara ko kuma ta abinda ya faru sakamakon binne abin da akayi? Ko
kuma dai kawai in bar labarin har sai Mammy tazo sai ta baki shi kamar yadda ta bani har kuma nayi
recoding a waya ta. Ko da yake ai kin sani ma, duk da dai ba dukkan abinda ya faru kika sani ba, kin san
dai shukar da kuka yi amma baki san abinda kuka girbe ba"
Tamkar dutse haka ta koma a zaune. Sai ma mike da Asad a hannuna nace "Addu'a ita ce makami na a
lokacin kuma still har yanzun ita ce. Bani da hakkkin ku dan haka komai kuka yi kanku zai koma, Mammy
zata tabbatar miki da haka"
Daga haka na juya na fita, feeling so happy with myself.
A ranar Aunty Afia ta zo gidan tare da Aira da Amira, sai dai ranta a bace yake da ni kuma bayan tace su
Aira su bamu guri sai ta rufe ni da fada kamar yadda dama na riga na saka rai daga gareta.
"Jidda kin san mata nawa ne kuwa suke zaune da mazan da suka fi naki muni? Kuma suke hakuri basu
fita sun gudu ba? Shin hakuri dama ya taba karewa ne? Akwai wadanda mijin nasu yake da irin halin naki
kuma babu soyayya babu kulawa babu ci da sha da sutura, kuma suna zaune. Akwai mata da yawa a
yanxu da babu abinda ba zasu bayar ba dan su samu kansu a matsayin ki, me yasa ke ba zaki rike
matsayin naki ba? In kika rabu da shi yanxu wa zaki aura kenan? Ko zaki yi ta zama ne babu aure?"
Na sunkuyar da kaina ina jin ta amma ban bata amsa ba, dan bana jin zata fahimci amsar da zan bata.
Wadannan matan da take magana akansu daban suke nima kuma daban nake. Rayuwar su daban tawa
daban. Su sunga zasu iya ni kuma naga ba zan iya ba. Nayi iyakacin kokari na Allah ne shaida ta. Na
fahimci cigaba da zama da Umar zai kaini ga halaka kuma is a very high risk to my children shi yasa nayi
quiting.
Allah ya gani kuma ya sani. Kuma kullum shi nake roko ya zaba min mafi alkhairi kuma na ajiye a raina
duk abinda ya taho gare ni zan dauka da ikon Allah. Idan akwai sauran zama a tsakani na da Umar dole
zan koma masa, amma ko zan koma din