Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
kira, WhatsApp only
*Wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar ki
sharing, in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*
*Mammy*
Na koma na zauna a kusa da ita sannan na dago kanta ina share mata hawayen ta. "Kiyi hakuri Aira. Kiyi
hakuri ki daina kuka dan Allah" tace "ni yanzu yaya zanyi? Yanzu Jidda ashe wai Daddy na ne yake da
wannan mummunar dabi'ar?" Na girgiza mata kai "kar ki ce haka Aira, Daddy ne fa, maybe ma ba abinda
kike tunani bane a tsakanin su da wannan matar maybe abokiyar aikinsa ce ko something like that" ta
girgiza kai da sauri, "baki gansu bane ba Jidda, baki ga matar nan ba kina ganin ta zaki san ko ita wacece
daga yanayin shigarta, kina ganin yadda suke yi zaki fahimci abinda yake tsakanin su" sai ta sake wani
sabon kukan. "wai babana. Jidda babana ne. Mutumin da duk mazan duniya babu wanda ya kai shi kima
da mutunci a idona, mutumin da har addu'a nake Allah ya bani miji kamarsa saboda yadda yake kula da
mu da mahaifiyar mu amma ashe da akwai abinda yake aikatawa a boye bamu sani ba. Shin anya ma
kuwa akwai wadda tafi kowa rashin dacen uba a duniya iri na?" Na rufe mata baki da sauri "menene
haka kike cewa Aira?" Sai naji hawaye ya taho idona, na rasa dalilin da yasa nake kwatanta Aira da
Yasmin. Will Yasmin one day find out about her Daddy ita ma? Will she say tafi kowa rashin dacen uba
itama? Will she ask me me yasa na zaba mata shi a matsayin uba? Wacce amsa zan bata then?
Ta sake tambaya ta. "Jidda me zanyi? Ta ina zan bullowa wannan lamarin? Yanzu dole sai na rabu da
musaddiq dan ba zan iya nuna masa tsohon da ya gani tare da karuwa a supermarket kuma yayi wa
dariya ya kira shi da gara in gaya masa cewa shine babana mahaifina da kullum nake nuna ina takama da
shi ina takama da kasancewar sa mahaifina ba. Ya zanyi Jidda?"
Na sunkuyar da kaina ina tunani, sai kuma na dago ina kallon ta nace "nima bansan abinda zaki yi ba
Aira. Bansan ta yadda za'a warware wannan lamarin ba. Amma ina ganin shi wanda ya kulla komai shine
ya kamata ya san yadda zaiyi ya warware komai" Tace "ban gane ba" nace "Daddy. Shi zaki kaiwa
pictures din nan ki luma gaya masa abinda ya faru. Ki kuma nuna masa yadda kike ji a zuciyar ki a game
da shi. Tsuntsun da ya ja ruwa hausawa suka ce shi ruwa kan doka. In kin gayawa Aunty kin nuna mata
pictures zata tashi hankalin ta taji kunya bayan ba ita ta aikata abin kunya ba, zata shiga damuwa da
kunci bayan ba ita ce mai laifi ba. Za ta fara neman maganin matsalar da ba tata bace ba. Problem dinsa
ne dan haka let him face it by himself. Kar ki matsawa Aunty tayi miki bayani akan laifin da ita ba ita tayi
ba, rather ki matsa masa shi da yayi laifin shi yayi miki bayani kuma yasan solution din dazai samar miki a
matsalar da shine ya saka ki a ciki"
Ta yi shiru tana kallona, daga alama maganganu na sun shige ta sai kuma ta dauki wayar ta da sauri ta
mike. "Nagode Jidda, zanje in same shi kuma sai yayi min bayanin dalilin da yasa ya zabi ya kunyata mu
mu ƴaƴan sa a idon duniya, sai ya gaya min dalilin da yasa zai zama sanadiyyar da dole zan hakura da
auren Musaddiq"
Tayi hanyar waje da sauri ranta a tsananin bace, na sauke ajjiyar zuciya tare da goge hawayen fuskata a
raina nace "good. Yau zaiyi facing abinda maybe bai taba tsammani ba. Maybe kunyar wannan abin ya
zama sanadiyyar shiryuwar sa".
Ranar duk zuciyata babu dadi, har Umar yazo na gama sallamar sa na kuma gama da yara kawai sai na
tafi daki na bar su tare a palo, a haka har suka yi bacci sannan ya shigo yace inje in kwantar dasu shi
kuma ya shiga wanka. Ina kwantar dasu a dakina na dawo na kwanta a dakinsa na juya bayana na rufe
ido na, a raina ina lissafin rayuwar da Aunty Afia tayi a baya da kuma irin alkawarirrikan da na tabbatar
daddyn Aira yayi mata na cewa ya daina, maybe tun bata yarda ya daina din ba har tazo ta yarda kuma
ta cigaba da yarda har yau. I can't even imagine how broken she will be in wannan labarin ya same ta. I
can't imagine how broken I will be idan ni ce a matsayin ta.
Har dare ranar bana cikin walwala, har Umar ya dawo na sallame shi na kuma gama da yara suma sai na
tafi daki nayi kwanciya ta na barsu a falo, sai da suka yi bacci sannan Umar ya zo ya ce inje in kwantar
dasu, na kwantar dasu a dakina nayi musu addu'a sannan na dawo dakin Umar na tarar yana wanka sai
na kwanta na juya bayana na rufe idona, hoping in ya fito zaiyi kwanciyar sa dan ni kam bana cikin mood
kuma bana jin duk dadin bakinsa akwai abinda zai yi ya sakani in the mood.
Ina kwance ya fito, naji ya watsamin ruwan gashin kansa a fuskata. Na bude ido ina kallon sa yace "nasan
dama ba bacci kike yi ba. A penny for your thoughts?" Na danyi murmushi kawai na mayar da ido na na
rufe. Naji ya hawo kan gadon na sake bude ido na ganshi kwance ruf da ciki yayi tagumi da hannu daya
ya zuba min ido. Na lura ko ruwan jikinsa bai goge ba nace "hey, zaka jika min gado da ruwa fa?" Yace
"me yake damunki?" Na dan bata rai, there is no way da zan bashi labarin cewa tsohuwar karuwar sa
yanzu ta koma karuwar mijin kanwar mamana. Nace "babu komai fa na gaya maka" ya kwaikwayi
muryata "babu komai fa na gaya maka. Tun ina falo nasan in na tambayeki cewa zakiyi babu komai
bayan ni nasan akwai komai. But ko ba zaki gaya min gabakidaya ba ki gaya min in yana da dangantaka
da zuwan matar Bashir gidan nan"
Na yi shiru ina kallon sa sannan nace "akwai wani abu ne da zai saka ni damuwa idan Surayya ta zo gidan
nan?" Ya daga hannu "nooo. Kawai dai bana jin dadin yadda kike yi ne tun ranar da ta zo din, shi yasa
nake so in confirming babu abinda tace miki. Ni yaushe rabona ma da in ganta, ko mijinta?"
Na dauke kai amma bance komai ba. Sai ya kara matsowa ya dora kansa akan kirjina yace "you know, I
was thinking. Kudin da nace miki na samu last month, shine nake tunanin yi mana gyaran gidan nan da
shi. What do you think?" na bude idona, tun last year Baba ya matsa masa ya zuba kudi a cikin business
din sa da yake yi na fata, yace masa aiki kadai ba zai rike shi ba sai ya hada da business. Shine last month
aka turo masa wasu kudi a matsayin ribar daya samu na shekara daya.
Nace "gyaran gida kuma? Haka ake business din dama? Daga samun riba sai a kashe?" Yayi dariya "to
dan me ake business din dama? Ba dan a samu riba a kashe ba?" Na ja kunnen sa "nooo, in aka samu
riba sai a kara karfin jari, har sai jari yayi karfi sosai sannan ake fara kashewa" ya tashi zaune tare da
jawo ni zaune nima "I just want to do something to make you happy, you don't seem happy" na shafa
fuskar sa "ba sai ka kashe min kudi zan zama happy ba, kuma gidan nan babu abinda ya same shi"
Yace "yes, babu abinda ya same shi amma chanji yana da dadi, ko ya akayi gyaran zaki ji dadi am sure"
nace "wai wanne irin gyara za'a yi ne ma?" Ya gyara zama. "Kawai tagogi da kofofi za'a chanja a mayar
da su na zamani, sai ayi penti, sai kuma a chanja furnitures da curtains da carpets, if kudin zasu isa sai a
chanja TV set suma"
Na girgiza kai "uhm uhm, ni furnitures dina babu abinda sukayi" yayi dariya "furnitures din ki ko
furnitures din mu? They are mine as much as they are yours tunda sanda kina gida ai ba'a yi miki ba sai
da aka aura miki ni sannan aka yi mana" nace "whatever. Amma dai babu abinda sukayi ai" na fada ina
shafa gado na, yace "babu abinda suka yi amma chanji yana da dadi ai" nace "to su kuma wadannan din
ya za'a yi dasu?" Yace "I was thinking mu kai wa Umma su ta chanja itama. Ba wai dan nata sunyi wani
abu ba, saboda itama ta chanja taji dadi"
Na cigaba da kallon sa bance komai ba sai yace "common just say yes mana, why are you being difficult"
na juya ido na "ba wai difficulty bane ba, kasan dai yadda muke da Mama yanzu, she is already thinking
komai naka a gurina yake karewa, bana so mu......"
Yace "ai ba ke zanyi wa ba. Kaina zan yiwa da matata da yayana dan jin dadin mu. Am sure Mama will
understand that" na sake bude baki zanyi magana sai yace "na gama magana. And I am the boss" na juya
ido na "yes boss Sir" yayi dariya tare da jan cheeks dina "that's right. I am the boss. Now, je ki kawo min
tea ki dawo sai muyi maganar color da design din da zamu yi"
Washegari da safe ina gyaran daki waya ta tayi kara, na duba naga yaya Mubaraka sai na dauka da
sallama ta na fara yunkurin gaishe ta sai tace "albishirinki Jidda" nace "goro" a raina ina tunanin menene
albishir din? Mama ta yarda da magana ta ko me? Sai tace "Baba ya biya miki aikin hajji" nayi kara tare
da sakin waya na rufe bakina ina jin ƙwaƙwalwa ta ta toshe, Umar ya shigo dakin da sauri, ya dawo daga
kai Yasmin school "lafiya?" Ya fada yana kallona, ya kasa tantance karar da nayi ta murna ce ko sabanin
haka.
Wayar da take kusa da kafafuwana ya sunkuya ya dauka ya saka a kunnen sa "hello?" "Wow. Haba?
Yaushe?" "Kai Baba ya biya mu, Allah ya biya shi shima. Ita da girls gabakidayan su?" Yayi dariya "zan je
in samu Baba, dani ya kamata ayi tafiyar nan gaskiya. Ai ba za'a barsu su tafi babu namiji ba ko?" Ya sake
dariya "kinci goron albishir. Har gida zan kawo miki" sai kuma ya kashe
Nayi tsalle na rungume shi "Baba ya biya min zanje Hajji" yayi dariya "didn't know it will make you this
happy da tuni nayi insisting" nace "happy? Ana maganar one of the pillars of islam kana maganar happy,
ai abinda nake ji yafi karfin happy"
Kuma da gaske nake na jima banji dadi irin na ranar nan ba.
Umar yayi ta lobbying, bayan Baba ya gama ja masa aji tare da yi masa fadan cewa shi har yanzu ya kasa
girma ya kafa kansa yadda zai ke yi wa kansa komai da komai sai kuma yaci sa'a shima aka biya masa
muka tafi tare, duk da dai already dama shi sun taba zuwa tare da yaya Mubaraka.
Maganar tafiya ta Hajji ta baza family na kamar gobarar daji, har gida aka yi ta zuwa ana yi min murna
tun kafin in tafi, ina kuma lura da yadda yan'uwa na suke yi min kallon sha'awa kamar babu wadda
rayuwarta take burge su irina. A lokacin ne mukayi waya da Surayya na bata labari kuma tayi min murna
sannan tace "kiyi amfani da wannan damar Jidda, ki roka wa mazajen mu shiriya" na gyada kai kamar
tana kallona "insha Allah. Yana daga cikin abu mafi muhimmanci da zanyi addu'a akai.
Cikin lokaci kankani aka gama komai muka tafi ni da Umar da Muhibbat, Muhsina da Mufida. Da zamu
tafi nayi niyyar kai su Yasmin gidan mu sai ga mota Mama ta aiko da ita wai za'a dauke su, ban ce komai
ba na hada musu kayansu suka tafi suna ta kuka, kuma ko airport bata je dasu ba ranar da zamu tashi
tace zasu yi rigima in suka gan mu. Muka gama aikin hajjin mu successfully muka dawo, duk da dai su
Muhsina suna ta sha min kamshi amma ni ibada ta kawai nayi ban damu dasu ba ballantana in saka su a
raina. Nayi adduoi sosai, musamman akan Umar, na kuma yiwa kaina addu'a da iyayena da yayana.
Muna sauka na samu labarai marasa dadi guda biyu, na farko an fasa auren Aira, babu wanda ya san
dalili, amma ni na sani, ka kallo daya na yiwa Aunty Afia nasan cewa ita ma ta sani and I felt her pain.
Labari na biyu shine Surayya tahaihu amma dannbai zo da rai ba.
Bansan Umar ya bayar da aikin gyaran gidan mu ba sai da muka dawo, nazo na tarar da gida kamar ba
namu ba, an gyara shi fes anyi fentin ko'ina an chanja furnitures din dakina da kujerun falo an saka
royals masu colours brown, golden brown, da kuma golden, an saka matching rugs da curtains. Komai
yayi kyau kamar dakin wata sabuwar amarya, amaryar ma yar masu kudi. Dakin baƙi ma an gyara shi an
cire gadon ciki an saka twin beds na yara kowa kuma da wardrobe din sa da yar karamar dresser, dakin
yayi matukar yin kyau.
Da gudu nake zagaya gidan ina bi daki daki har naje dakin sa, ina budewa na tsaya ina kallon dakin babu
abinda aka chanja a ciki dan daga alama ma ko bude shi ba'a yi ba tun da muka tafi. Yazo ya tsaya a
bayana ya dora kansa a wuyana yana dariya "don't comment, kar ki ce komai" na juyo "shi nan dakin
laifin me yayi da ba'a gyara shi ba?" Ya shafa kansa Yace "kudi ne yayi min short, za'a gyara shi in an
samu wasu, for now babu wanda ya san ba'a gyara shi ba daga ni sai ke" Na juya ido na "sai na gaya wa
duk wanda yazo" yayi murmushi "ke za'a yiwa dariya ai ace dakin mijinki bai yi kyau ba" na shafa
fuskarsa "I don't care, tunda mijina yana da kyau ban damu da kyan dakinsa ba" yana murmushi ya kama
hips dina ya daga ni ni kuma na makale a jikinsa "da gaske? You think ina da kyau?" Nayi murmushi nima
nace "the most handsome man I have ever seen"...........
Tunda muka dawo kullum sai mun samu baki masu zuwa yi mana barka da zuwa, mu kuma muka bude
jaka mukayi ta rabon tsaraba. Kasancewar dawowar mu da kuma gyaran gidan mu ya faru kusan lokaci
daya sai ya zamana duk wanda yazo mana sannu da zuwa sai kuma ya ga gyaran da mukayi, kowa kuma
ya gani sai yayi santin yadda gidan yayi kyau musamman yan gidan mu.
Umma da Hajiya da Farhan da Amira ne sukafara zuwa, a lokacin ne suke bani labarin cewa Umar Farhan
ya kira lokacin muna Saudiyya yace tazo gidan mu ta hada mana kayan mu za'a zo ayi aiki, ita da Amira
ne suka kwashe mana kayan mu bayan an gama kuma suka zo suka jera mana komai suka gyara mana.
Sannan kuma ya turo mota aka kwashe furnitures din da aka cire aka kaiwa Umma kamar yadda yace
za'a yi. Suka nuna min hotunan yadda aka gyarawa umma dakinta ita ma da kayana, har fenti yaya Tahir
ya saka akayi mata kafin a saka kayan, Bedroom din ta da falonta sunyi kyau fes kamar ba su ba.
Duk hirar da muke yi Hajiya tana jin mu, I was surprised da naji bata ce komai ba sai bin mu da kallo
kawai take yi, da nace su zagaya gidan su gani ma na dauka zata ce ba zata gani ba amma sai naga ta
tashi sun zagaya tare har ma dayi min murna "Allah ya sanya alkhairi yasa a kashe lafiya" nace "ameen"
Da zasu tafi sai na roki Umma ta rokar min Abba ya bar Amira tazo ta dan kwanar min biyu dan in samu
in huta sosai, dan ba karamar gajiya nake ji ba ga kuma baki basa barina in samu isashshen hutu, ga yara.
Ta girgiza kai "ba zai bari ba. Nima na san zaki dawo a gajiye shi yasa da zamu taho na tambayeshi zan
bar miki ita amma ya hana, yace baya son kwadayi" suka yi dariya gaba daya ni kuma naji babu dadi.
Washegari sai ga Mama Sa'a tazo ita da ƴaƴan ta baki daya, na lura Mammy da jakar kaya a hannun ta.
"Dama yau nace zamu zo mu yi miki sannu da zuwa sai kuma Hajiya tace in kawo miki Mammy ta taya ki
zama tunda babu abinda take yi a gida, taji kina complain din gajiya kuma Abba ya hana ki Amira, na
samu babanta ya barta da kyar, sai take yi miki ayyuka kuma take kula miki da yara kafin ki samu ki huta"
Naji dadi tunda nasan ina bukatar taimako, duk da dai ba Mammy naso ba nafi son Amira amma
hausawa sunce a rashin uwa akan yi uwar daki. Nayi mata godiya sosai kuma na kira Hajiya ita ma nayi
mata godiya "nasan yadda kike ji ai, aikin hajji ai akwai gajiyar wa, nima sanda naje da na dawo ai har sai
da na yi jinya" sai ta dauko labarin zuwan su hajji ita da Abba tana bani har da dariya, abinda bana jin ni
da ita mun taba zama munyi.
Naji dadin zuwan Mammy, problem din dana dauka zan samu da ita na rashin kunya da rawar kai duk
ban samu ba, kullum zata gyara min gida ta kula da yara ta kuma yi mana girki, mu kuma muka samu
damar hutawa ni da Umar sosai, sai dai idan munyi baki ta je ta kira ni in basu kulawa in sun tafi in koma.
A haka har na wartsake tas na fito na cigaba da harkoki na, Umar kuma ya koma aikin sa, amma ban ce
Mammy ta koma gida ba sai na barta ta cigaba da zama tunda naga tana son zaman kuma bana samun
problem da ita.
A lokacin ne wani abu ya faru.........
Suddenly without warning Umar ya chanja min gabakidaya ya rikice min. Rana daya ya wuni a office tun
safe har magrib ba tare da ya kira ni ba ba kuma tare daya dauki kiran da nake ta jera masa ba. A ranar
hankali na ya tashi nayi ta sake saken ko wani abun ne ya faru dashi, na kasa hakuri sai na kira Mufida
inji ko yaje gida ko kuma sunji wani labari da banji ba, sai ta gaya min cewa yanzu taji suna waya da
Mama.
Na cigaba da jira, na kuma cigaba da kira amma still bai dauka ba sai bayan magrib ya