Chapter 23 Reading JIDDA by Maman Maama HN Novels

JIDDA by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   23 / 101

66K to 69K   out of 300.2K words

karasa, duk wanda kike so ki bude ni na gaji bacci
nake ji" na karba sannan na gyara kwanciya ta a space din daya tashi "ba sai gobe ba ma, yanzu zanyi,
am so eager to meet secondary school friends dina" ya karbe wayar, "bakiji abinda nace ba? Bacci nake
ji. And I am sure going to take that shot kafin inyi bacci"



Na langwabe kai shima yayi irin yadda nayi, dole na fasa abinda nace zanyi din muka rufe komai muka
kwantar da Affan wanda shima yayi bacci sannan muka tafi dakinsa na kuma bashi dukkan kulawar
dayake bukata.
Daga auren mu zuwa yanzu na fahimci Umar yana da yawan bukata, amma sai na jingina haka da dokin
amarci da ake cewa maza suna yi sannan kuma na dage iyakacin iyawa ta nake biya masa duk bukatun sa
a duk lokacin da ya zo min dasu. Ba zan saka shi a layin masu tsananin bukata ba duk da yana da yawan
bukata dan baya fashin dare, kuma ko da rana ne ma musamman in muna gida kuma mu kadai ne to fa
sai yayi amfani da damarsa. Ni kuma a kokari na na ganin na faranta masa kamar yadda shima yake
faranta min sai na dage ta wannan bangaren, duk tsoron da nake dashi na ajiye shi a gefe tunda yanzu
babu sauran zafi, kunyar ma kuma na fara rageta dan shi ko shafi daya bai karanta ba a littafin kunya.
Babu ruwanshi da wai wani kashe fitila and don't even try to say a lulluba da bargo. Shi ko a ina yake son
abinshi anan zaiyi kayansa ko da kuwa kitchen ne ko toilet, yakance "gidana ne kuma matata ce, a barni
in shana"



Watan mu biyar da aure na samu cikin Yasmin, ranar da Umar ya fara gane ina da ciki lokacin ko missing
period banyi ba amma yana taba kirjina yace "Baby we are pregnant" na harare shi "ta haka dama ake
gane cikin?" Ya saka matsawa "sosai ma. Wallahi akwai. Come lemme confirm" sai ya kwantar dani flat
yana mammatsa mara ta, nayi dariya "Doctor Faruq. Idan ma akwai cikin fa bai yi wata daya ba kenan,
how on earth can you feel it" ya kalle ni "shshsh, stop talking and relax. Kina magana ne da Doctor Umar
and am not your average doctor" ya kara dannawa expertly da thumb dinsa can kasan marar,sai kuma
ya danyi kara kadan "Jidda, wallahi akwai. About four weeks. How did I miss this har yayi four weeks ban
san da shi ba"



Sai ya dauke ni ya fara zagaye dakin yna hajijiya dani har muka fada kan gado. Zan iya cewa ban taba
ganinsa cikin wannan farin cikin ba dan haka kullum nake fadar cewa bai taba son wani abu ba kamar
yadda yake son Yasmin.



Sai daya gama murnar sa sannan ya dauko kaya ya fara kokarin saka min,ya fasa kuma abinda da yayi
niyyar yi. Na karba ina karasa sakawa shima ya dauko nasa "ina zamuje?" Na tambaye shi "gwara muje
mu ga lafiyar ta, ko lafiyar sa, ko lafiyar su" nace "tun yanzu?" Yace "me kike tsammani? Yar doctor da
nurse ce fa" nace "ne fa" ya kuma cewa "ce fa. Ni nafi son girl. Kyakykyawa kamar ki" ya fada yana jan
kumatu na.



Asibitin Doctor Bashir muka je. Ranar ne na fara shiga asibitin muka zarce office din da yake a matsayin
na Umar, ya nuna min kujerar marasa lafiya na zauna shi kuma ya zauna a kujerar sa. Sai kuma yayi waya
aka kawo masa sabon file. Tana fita ya hade rai ya tambaye ni "full name please" nace "Umar
Muhammad Gidado" sai yayi murmushi.
Ina ganin shi yayi ta cike cike a jikin form din sannan ya dauko takarda ya saka aciki ita ma yayi ta cike
cike a jiki, duk abinda ake tambaya ya sani, yace "so nake in bude miki file the normal way yadda ko
bana kusa nurses din nan zasu iya duba ki" na gyada kai. Information din patient yana da amfani dan
gudun samun matsala.



Bayan mun gama yayi min scanning, kuma abin da ya bani mamaki shine four weeks din da ya fada sune
dai muka gani, wannan ya kara tabbatar min da cewa umar yasan aikin sa.



Wani abin mamakin kuma shine sai da muka san da cikin sannan na fara laulayi. Laulayi sosai nake yi sam
bana iya cin komai musamman ruwa sai dai insha fruits, su kadai ne abincina. Gashi kuma a lokacin
muna cikin exams din first semester of second year din mu. Umar harda daukan emergency leave danya
kula dani, sannan ya gaya wa Mama ta aiko Mufida wadda a lokacin ta fara zuwa buk dan ta zauna tana
taya ni aiyukan gida. Tunda babu nisa daga gidan mu zuwa makarantar ta, wani lokacin ma da kafa take
karasa wa.



Nayi tayi masa mitar me yasa ya gayawa Mama "yanxu kasa zanyi ta jin kunyarta wallahi" ya yamutsa
fuska "kunya? Menene abin kunya a ciki? Ji nake kowa sai da akayi cikin sannan aka haife shi. Kuma
wannan abin da mukayi aka samu cikin nan kowa ma in ta shiga daki da mijin ta tana yin abinta" na ture
shi na mike "Umar kafi karfina, na sallama wa duniya kai. Zancen Mama fa muke yi"



Sai yayi dariya kawai. Shi babu wanda ya bari. Ai kuwa kunyar nayi taji dan kullum sai ta kira ni
tambayeni ya jiki, haka na lallaba na gama exams din, sai dai kuma dan hutun namu bashi da yawa
fifteen days ne kadai muka yi muka koma school second semester second year. A lokacin na dan rage
laulayi, Umar ma kum ya koma aikinsa amma dai ba wata lafiya ce dani sosai ba dan haka karatun
wahala yake bani sosai, sannan kum babban tashin hankali na shine wannan semester din posting biyu
ake yi, psychiatric posting inda za'a tura mu dawanau sannan kuma da orthopedic posting shi kuma za'a
tura mu dala.



Da na saba duk sanda za'a yi posting into general wards Bashir yana taimaka min a tura ni nan AKTH inyi
zama na a gurin Umar yanzu kuwa dole mu raba gari. Ina ta lissafin yadda zanyi coping a asibitin
mahaukata ga kuma ciki ina fama da shi. A haka har muka gama theories aka yi posting din mu na dauko
takardar posting din na kawo wa Umar.
Yana zaune yana aiki da computer dinsa na mika masa takardar "anyi posting din mu dazu. Gashinan, an
kaini dawanau" na fada ina jin hawaye yana zuwa ido na. Sai ya dago kai yana murmushi, na dauke kai
ina jin haushinsa sai yayi dariya "wa yaga Jidda tana fama da mahaukata" sai na fara kukan sosai "ni dai
ba zan je ba. Haka kawai in wani ya kwace ya dake ni kuma fa. Kasan dai bani kadai bace ba ko?" Na fada
ina hoping albarkacin cikina zai ce ba zanje ba.



Sai ya rufe system din yayi folding hannunsa yana kallona "to ya kike so ayi Madam? Karatun ki ne ya
kama da haka kuma kika sani ma ko a can zaki yi aiki?" Na bude ido "wallahi ba zanyi aiki a can ba.
Chafdi, wallahi sai dai in fasa aikin gabakidaya" yayi dariya "ke kam wannan akwai farar kura. Come
here" sai na taso nazo na zauna a jikinsa na saka fuska ta a wuyansa ina jin dadin kamshin sa.



Yace "za a yi musu magana a gaya musu ga halin da kike ciki, and they won't let you anywhere near
dangerous patients kinji. Akwai wanda na sani a gurin munyi buk tare da shi kuma yana da say sosai a
gurin, already har munyi magana dashi tunda nasan dama can za'a kai ki kuma he assured me cewa babu
problem, zai yi miki hanyar da ba sai kina zuwa kullum ba ma. Kin ga kin samu chance din hutawa ma for
four weeks kafin nan kun kara kwari ke da baby"



Naji dadin maganar sa sosai sai na kankame shi "Nagode sosai my sweet husband. Allah ya bar mu tare"
sai kuma na dago kai ina kallon fuskarsa na bata rai cikin shagwaba "amma yanzu shikenan ba zamu ke
fita tare muna dawowa tare ba. Kuma ba zan ke ganin ka da rana ba"



Ya shafa fuska ta "waye ya gaya miki? Dawanau din ai ba zata yi min nisa ba indai kina can. Zancen fita
da dawowa kuma already nayi solving wannan problem din" nace "how?" Yace "I bought you a car" na
bude ido shi kuma ya kashe min nasa idon "a Rav4"



Na mike da sauri sai ya jawo ni ya dawo dani jikinsa yana dariya "don't even try that" cikin zumudi nace
"da gaske dear?" Yace "eh mana. I wanted to give it to you a matsayin gift din cikin nan amma Allah bai
yi ba, bata zo da wuri ba sai this weekend zata zo insha Allah. Probably tomorrow"



Na kankame shi ina hawaye "Nagode Nagode Nagode" ya dago fuska ta "dama a haka mata take godewa
mijinta?" Nace "to me zance?" Na nuna lips dinsa "a kiss will be very much appreciated" nayi murmushi
sannan na dora bakina akan nasa.
Two days after that kuwa motar ta iso, and it was much more than I expected dan tayi min kyau sosai,
red color wacce tayi matukar dacewa dani. Gidan mu na fara zuwa da ita na nuna musu, gabaki dayansu
suka fito kallon motar har da yan unguwa ma sai da suka fiffito. Ba a cikin yaya matan gidan mu ba, har
cikin mazan nice na fara mallakar mota kuma lafiyayyiyar mota irin wannan.



Sosai kuma naga rashin jin dadin hakan a idon Hajiya "wannan mota haka? A ina ya samu kudin siyawa
matarsa wannan mota? Anya kuwa Alhaji ba za'a binciki inda yaron nan yake samun kuɗi ba. Dama
likitoci suna samun irin wadannan kudaden?"



Abba yace "suna samun kudi mana, kuma misali shi ai iyayen sa suna da arziki dan haka bashi da nauyin
su ko na yanuwan sa a akan sa sai nauyin iyalinsa kadai"



Har cikin gida Abba ya shigo da Umar Umma tayi masa godiya, shi kuma yana ta sussunne kai, a raina
nace kamar gaske dan nasan babu wata kunya da yake ji.



Bamu jima ba muka tafi, kuma tun a ranar ya kaini...............na fara gwada driving duk da cewa duk
basics na driving din na sani dan nakan kunna motarsa a gida har reverse na iya in fitar da ita daga gate.
Dan haka koyon tuki baiyi min wahala ba kuma sai Allah ya taimake ni bani da tsoron titi nan da nan na
dara driving da kaina duk da cewa sai da Umar ya makala min 'L' saboda tsautsayi.



Kamar yadda ya fada haka ce ta kasance a dawanau din da aka tura ni, sun daga min kafa sosai kuma har
wani girma naga suna bani, sun ganni fes fesga galleliyar mota ina hawa. Satin mu hudu a can aka mayar
damu asibitin Dala orthopedic muka sake yin wasu four weeks din sannan muka koma school muka yi
revision sai kuma exams.



Amma wannan karon sai aka samu akasi na fadi courses har biyu, abinda ban taba yi ba tunda na fara.
Kuma hakan yana da nasaba da cikina da sam sam baya son karatu daga na dauko littafi na fara karatu to
kuwa sai dai azo a tashe ni ina bacci.



Inda Allah ya taimake ni suna bada grace na two weeks mutum yayi resitting papers din daya fadi, in still
baka ci ba sai kayi repeat, in kuma kaci sai ka wuce da yan ajin ku. Kuma Umar ya taimaka min sosai
wajen karatun dan shi yake zama da kansa yana karanto min yana yi min vayani dan in ya barni da littafin
bacci zanyi. A haka da taimakon sa da na ubangiji na samu naci exams dina ta wannan semester din.
Daga nan aka yi mana hutu.



A cikin hutun ne nayi baki, bakin da zuwansu ya zamanto tamkar opener ta wami phase na rayuwar
aurena. Bakin da zuwansu ya zamanto tamkar budar ido a gareni akan kaddara ta.



Ranar monday ne, Umar ya fita tun sassafe and he told me that he is going to be late saboda yana da
wani surgery da zaiyi late evening a asibitin Dr Bashir. Dan haka tun rana nake kwance inata bacci na har
sai da laasar tayi sannan na tashi na shiga kitchen nayi masa dinner dan ni ba wani cin abinci nake yi ba
har yanzu.



Bayan na kammala girkin kuma na shiga nayi wanka na nutsu na shirya masa kwalliya irin wadda nasan
yana so sannan na fito na dan gyagygyara gidan duk da dai kafin ya fita ya gyara ko'ina wai dan kar in
tashi ince zanyi bayan ya tafi. Na dauko freshener na fesa a duk gidan sannan na samu guri na zauna na
kunna kallo ina kuma chatting a waya ta, ina ta dariyar yadda ake zabga drama a WhatsApp group din
Maman Maama novels, wanda Aunty Halima ta bayar da number ta aka saka ni kwanakin baya.



Ina yi ina duba agogo, magrib ta gabato sosai amma har yanzu shiru. Nayi tunanin kiransa kuma sai na
fasa, bana so in kira shi yana tsakiyar aiki musamman in surgery ne.



Ina nan zaune naji tsayuwar mota sannan akayi horn, na tashi na leka ta window ina jin dadi a raina
amma sai naga bakuwar mota ta shigo, bakar Panadol extra, na tsaya ina kallon motar har tayi packing
sannan naga wasu mata su biyu sun fito.



Ban san su ba, ban taba ganin su ba sai a ranar. Suka fito suna karewa gidan kallo sannan daya tayiwa
dayar magana suka yi dariya amma banji me suka ce ba. Sai kuma naga sun rufe kofofin motar sannan
suka doso cikin gidan. Naga daya tayi gefe, sai dayar ta kamo hannun ta "ke kamar an chanja entry din
fa. Kinga kofar nan"



Ina kallon su har suka zo sukayi knocking sai na saki labulen da nake tsaye a bayansa na zo na dube musu
kofar. Suka shigo dul su biyun idon su a kaina Kamar yadda nima nake binsu da kallo.
Kyawawa ne duk su biyun, kuma kallo daya zakayi musu ka fahimci duk inda budewar ido ta kai to nasu
idon yaje gurin. Sun sha kwalliya tun daga sama har kasa daya daga cikin su ta sha kitson attachment
wanda akayi shi da colored zare kuma ya sauko har kan kafadar ta. Da maka makan glasses a idanuwan
su. Banbancin su da kedarai kawai a fuska ne amma ba'a yanayin jiki ko kuma shigar da take jikin su ba.



Na fara tunanin su waye wadannan? Ni dai bana jin na san su a yan'uwa ko abokan aikin Faruq dan
yanxu kusan duk collique dinsa na sansu saboda zuwa office dinsa da nake yi.



"Sannun ku da zuwa" na fada. Mai attach din ta sauke glass din idonta kasa tana kare min kallo tun daga
fuskata zuwa kyakykyawan cikina daya fara girma. Sannan kuma tabi falon da kallo tana yamutsa fuska.



Dayar ce ta amsa min "yauwa amarya. Sannu da gida" na matsa baya ina nuna musu gurin zama.
"Bismillah. Ku shigo ku zauna" suka biyo bayana suka zazzauna still suna ta kallon falon, irin kallon
wulakanci din nan.



Naji abin ya taba zuciyata. Who are they? Daga gani sun girme ni nesa ba kusa ba, dan haka a ka'ida ni ya
kamata in gaishe su amma sai naji na kasa gaishe su din. Na tashi na dauko musu lemo da ruwa na kawo
musu bagansu. Dayar tace min "mun gode amarya" na dan yi mata murmushi kadan sannan na zauna.



"Ban gane ku ba fa amma" na fada hoping zasu fahimtar dani sai mai attach din tace "mai gidan yana
nan ne?" Naji raina ya fara baci. Nace "baya nan. Yana office" sai naga sun kalli juna sun kwashe da
dariya. "Su office manya" suka kuma wata dariyar. Yanzu raina ya kai kololuwar baci.



Marar attach din tace "dama munzo ne mu ganki kuma mu gaishe ki. Mu kuma yi miki Allah ya sanya
alkhairi tunda ba'a gayyace mu biki ba sai a media muka ji. Allah ya kawo kazantar daki amma bata
rashin shara ba. Though mun fara ganin alamun kazantar dakin tana hanya" ta fada tana kallon ciki na.



Mai attach din ta juyo itama ta kalli cikin ta tabe baki "in dai akan wannan aikin ne ai sai dai a bashi
number yabo ta kasa. Shi din gwani ne ta wannan bangaren"
Na mike tsaye, ina jin wani irin zafi araina "please in ba zaku fada min ko ku su wa ye ba kuma ku fadi
abinda ya kawo ku gidan nan ba you can take your leave please"



Suka mike a tare, mai attach din ta tako zuwa gaba na ta tsaya tana tauna cingam "kamar yadda kawata
ta fada munzo ne mu ganki mu kuma ga dakin ki. Kuma mun gani. Dama na gaya masa zanzo mu gaisa
but ya dauka da wasa nake masa shi yasa muka zo da yamma hoping ko zamu same shi a gida dan in
tabbatar masa ba da wasa nake ba, but ashe yana 'office' kamar yadda ya gaya miki. Nevertheless, zan
bar masa sako"



"In yazo ki gaya masa Zuwaira tazo ta kawo muku ziyara tare da fatan alkhairi. Zancen su waye kuma mu
idan kin gaya masa haka sai ki tambayeshi shi zai fi kowa yi miki bayanin ko wacece ni"



Sai ta juya gurin kawarta "ko ba haka ba kawata?" Sai suka tafa, kawar tace "naso ace mun same shi
wallahi, naso inga idon sa, munafukfuk" suka sake dariya sannan wadda ta kira kanta da Zuwaira ta duba
agogon hannun ta "mu tafi haka, na bar clients suna jira na, kin san akwai amarya da nace miki zanyi wa
gyaran jiki yau" kawar ta harare ta "kema munafuka daya, ko dai katoton client ne yake jiran ki? Tunda
ance bai dawo daga 'office' ba" suka sake dariya sannan suka kama hannu suka fita.



Suka bar ni a tsaye tamkar gunkin da aka sassaka......



*One more free Episode*




*Episode Eighteen : Zuwaira*

Tun da suka fita ban iya komawa na zauna ba. Ji nake yi tamkar na hadiyi tabarya dan wani dogon abu ne
ya tsaya tun daga makogwarona har zuwa kafafuwana.



Dan cikina naji yana ta tsalle kamar wanda oxygen dinda na ke shaka bata isar mu ni da shi.
Kwakwalwa ta tana ta kokarin assessing maganganun su amma zuciyata taki bata dama dan bugawa
take yi da tsananin karfin da har cikin kunnuwa na nake jin karar bugun ta.



Babu abinda nake so inji irin amsar su waye wadannan kuma menene fassarar maganganun da suka zo
suka yi? Sunce suna min fatan alkhairi amma ko kadan banga fatan alkhairi a tattare da su ba. Me suke
fada akan Umar? Me suke fada akan mijina?



Motar su bata jima da barin gidan ba naji shigowar ta sa. Ya bude kofa ya shigo fuskar sa da murmushi
"sorry Baby, na barki kina ta jirana ko?" Sai ya daga ledar

23 / 101