Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
ba Umma?" Tayi masa godiya ya fita ni kuma na bishi da harara.
Yana fita Farhan ta mike,"me aka kawo mana a leda? Na san dai sakon mu ne" nace "to shigabar
kwadayayyu, je ki dauko ki gani" ta shiga sai gata ta fito da kaji manya guda biyu da kuma apples a wata
ledar da ban.
Suna nan guri na har bayan laasar sannan suka ce zasu tafi, nace su bari ayi magrib amma suka ki. Umma
tace "kar ki kira shi dan Allah ki rabu da shi, ni ba zan ma iya shiga motar sa ba" Farhan ta bata rai "haba
Umma, ki bar mu mu shiga raɓa mana" Umma tace "sai dai ki shig ke kadai ni ba zan shiga ba" ni dai
inajin su suna tayi har suka gama ban tanka musu ba dan na riga na gama yanke shawarar in sun ce in
kira shi ma zanyi faking kiran ne in ce network babu kyau.
Sai bayan magrib ya shigo. "Yanzu shine kika bar su Umma suka tafi a motar haya?" Na tashi zaune "ai
kasan sun saba da ma, ko ka manta a cikin motar hayan suka zo? Tun muna ciki muke yawo a motar haya
dan haka one more babu abinda zai yi musu"
Ya zauna yana kallona. "You won't stop, will you?" Na girgiza kaina "never" yace "you won't let me
explain ko?" Na sake girgiza kai na "bana bukata" yace "saboda me? Idan banyi miki bayani ba ta yaya
zamu samu fahimtar juna?"
Na mike tsaye "bana bukatar fahimtar ka, na riga na fahimci duk abinda ya kamata in fahimta. Bana
bukatar jin wani bayanin ka, dan bana jin zan kuma yarda da duk wata kalma da zata fito daga bakin ka"
Zan wuce sai ya mike da sauri ya rine hannu na. Na juyo ina kallon sa muka hada nayi saurin dauke nawa
idon, ban taba ganin jikinsa yayi sanyi irin na yau ba. Nace "sakar min hannuna" bai musa ba ya sake ni
na shige daki, sai dana kwanta na kifa kaina a pillow na fara hawaye sannan na tuna na bar Yasmin a
falo.
Na mike ina goge hawaye na na koma falon sai na ganshi ya durkusa a gaban ta ya dora fuskar sa a jikin
ta ta, nazo na saka hannu na ture fuskarsa na dauke yata. Ya bini da kallo bai ce komai ba har na shiga
daki na rufe kofa ta.
Kusan kwanan mu biyar a haka, a lokacin na fara kokarin komawa school dama kuma already ina shirye
shiryen project dina, sai dai yanzu sam mind dina baya kan karatun ko na dauka ma ba iya wa nake yi ba.
Na saba most of the times tare da Umar muke yi kuma shi yake koya min duk abubuwan da ban gane ba.
Yanzu kuwa magana ma sai dai yazo yayi ta yin abarsa in bakinsa ya gaji ya yi shiru.
A wannan ranar ma ina cikin dakina da laptop a gaba na ina ta danne danne wai ni a lallai karatu nake yi
duk da babu abinda nake ganewa. Naji anyi knocking kofar, a bude take kuma nasan waye dan haka na
share shi. Ya turo kofar ya tsaya yana kallona. Na dauke kai pretending to be busy.
"Kinyi bakuwa a falo" na dago kai kna kallon sa, wani barin na zuciya ta yana aiyana min Zuwaira a
matsayin bakuwar da tazo, "Zuwaira ce?" Na tambaya ina kallon sa, sai yazo ya zauna a gefen gadon, na
mike tsaye da sauri tare da nuna masa hanyar fita "go away" na fada da dan karfi, ya mike tsaye shima
da sauri yana min alamar in yi a hankali, na kara daga murya "ka fita min a daki nace" da sauri ya je ya
rufe kofar sannan ya jingina da jikin kofar "Bashir ne yazo tare da Surayya da kawarta, Surayya ita ce
wadda zai aura, ya kawo miki ita ne ku gaisa"
Na koma saman gado na na zauna tare da harde kafafuwana "kaje kace musu ba zan zo ba, bani da
lokacin ka ballantana na abokin ka da budurwar sa balle wata kawarta" ya bude hannu "na riga na gaya
musu cewa kina nan Jidda, cewa nayi bara in je in kirawo ki. Me zan ce musu kuma yanzu?" Ya fada
kamar zaiyi kuka, na daga kafada "oho, ka fini sanin abinda zaka fada ai tunda kai gwani ne gurin iya
tsara magana wadda akayi da kuma wadda ba'a yi ba, tabbas zaka san abinda zaka gaya musu"
Ya rintse idonsa ya bude "Jidda please. Ni fa mijin ki ne. Dan Allah ki je ku gaisa ko minti biyu ne sai ki
dawo ki cigaba da abinda kike yi dan Allah" sai na dauko ear piece na saka ajikin laptop din na kuma saka
a kunne na na fara gyada kai duk da cewa babu kidan da nake ji.
Ya hawo kan gadon, na nuna shi da hannu "ko ka sauka ko in yi maka ihu" ya sauka ta tafi bakin kofa, ya
jima a tsaye yana kallo na sannan ya bude kofar ya fita. Na bi bayan sa da harara sannan na zare
earpiece din daga kunnena.
Amma kuma sai na kasa cigaba da zama, na rasa dalilin da yasa ma kasa yin abinda nayi niyya, sai na
tashi na saka hijab dina na dan gyara fuska ta na fita.
Yana zaune tare da su ya kawo musu drinks, suna magana da Bashir amma daga gani kasan his mind is
not there, na ga yadda ya sauke ajjiyar zuciya da ya ganni sai na tafi gurin yammatan guda biyu.
"Sannun ku da zuwa. Amarsu ta ango sha kamshi" na lura da waddata sunkuyar da kai da kuma wadda
tayi dariya, na zauna muma gaisa sannan na juyo na gaishe da Bashir briefly. I was not in the mood for
chatting, suma kuma yammatan kamar ba masu surutu bane ba sai naji sunce zasu tafi, muka mike
gabaki daya muka fita compound ina saka ran inga sun shiga motar Bashir sun tafi sai naga sun kama
hanyar gate shi kuma yayi musu sallama yace sai sunyi waya, nayi mamaki sosai dan Umar ko sanda yake
nemana ba zai yi min haka ba ballantana yanzu da in da ace mota ta zata samu problem zai iya bar min
tasa shi ya hau ta haya.
Ban iya shiru ba sai nace "ba gida zaka kai su ba?" Ya daga kafada "noo, dama na gaya musu zan tsaya
inyi wani abu anan, so, zasu nemi abin hawa ne kawai" na gyada kai kawai na juya zan koma ciki sai yace
"baki tambaye ni abinda zan tsaya inyi anan din ba?" Na juyo "maybe zakuyi magana ne da abokin ka or
something, I don't know"
Yayi murmushi "eh magana zamuyi, amma da ke zamuyi ba dashi ba" na tsaya ina kallon sa sannan na
juya ina kallon Faruq wanda shima ni yake kallo, sai na girgiza kai nace "babu da wanda zanyi magana,
bada kai ba bada abokin ka ba. You think zan yarda da maganar sa bayan naki yarda da taka? Abokin ka
ne fa? A guri na komai kayi da sanin sa"
Ya hadiye wani abu sannan yace "baki tsaya kinji maganar tawa ba ma ai ballantana ki yarda ko ki ƙi
yarda" na juya na cigaba da tafiya nace "bana bukatar ji dan ko naji ba zan yarda ba" Bashir ya biyo ni a
baya "ta yaya za'a samu fahimtar juna in dai har ba'a zauna anyi magana ba?" Nace "bana bukatar
samun fahimtar juna in dai da shi ne, na riga na fahimci dukkan abinda ya kamata in fahimta"
Ina shiga falon suka shigo duk su biyun, Umar yayi saurin shan gaba na, "please please Jidda dan girman
Allah ki tsaya. Ki tsaya muyi magana dan Allah" na fara zama frustrated. "Dan Allah" ya sake cewa. Na
juya ina kallon Bashir sai ya nuna min kujera yace "dan Allah ba dan ni ba ko dan shi" na kalli hanyar
dakina "yata zan dauko" sai Umar yace "ki zauna, zan ne in dauko ta"
Na koma na zauna ina kallon Bashir, ina so inji wacce karyar kuma Umar ya hada masa shi kuma zai hada
min? Nayi folding hannuna ina kallon sa nace "ina jin ka"
Sai ya zauna shima sannan yace "Umar ya gaya min abinda ya faru, ya kuma gaya min komai da komai
duk da dai already na riga nasan wani part na abin da ya faru. And I totally believe kina da every right da
zaki yi treating dinsa yadda kike yi koma fiye da haka, saboda bashi da wani excuse na abinda yayi. Na
kuma zo ne nan gurin ki badan in baki hakuri ba akan abinda yayi din dan na gaya masa shi yayi creating
mess dinsa shi ne kuma zaiyi cleaning. Nazo ne dan in gaya miki gaskiya, gaskiya to the best of my
knowledge. Sannan kuma nazo ne saboda zan iya cewa akwai wani part na laifi na a cikin maganar"
Na gyara zamana "Umar ya kan yi rantsuwa akan karya. Ban sani ba ba ko kaima halin ka ne hakan?
Tunda abokin ka ne?" Ya girgiza kansa "ban san a ina ne yayi miki rantsuwa akan karyar ba, dan haka ba
zance dai dai ne ko ba dai dai bane ba, amma ni yan zu na rantse miki, wallahi, duk abinda zan gaya miki
shine gaskiyar magana"
Nace "menene gaskiyar abinda yake tsakanin Umar da Zuwaira?"
Yace "budurwar sa ce. Tun muna buk suke tare, he thought he was in love with her, then realized the
kind of person she is and broke up with her. Amma ita a lokacin bata shirya rabuwa da shi ba sai suka
cigaba da kasancewa tare on and off, shi yasan cewa ba aurenta zai yi ba and itama deep inside her
tasan cewa ba auren ta zaiyi ba amma sun cigaba da rayuwa a haka"
"Labarin sa ne ba nawa ba, and like I said am not here to clean up his mess but to tell you the truth. And
the truth is, he finally broke up with her lokacin da ya hadu dake and fall in love with you and decided to
settle down. Yayi cutting every ties da ita. That am very sure of. Kafin bikin ku zan iya cewa sunyi watanni
basa tare. We even though ta hakura dashi finally"
"But jin labarin auren ku shine ya rikita ta, she realized cewa da gaske yake ba aurenta zaiyi ba and
blamed him for all that has happened in her life. Wannan ne yasa tazo gidan nan, har ta fara dasa zargi a
tsakanin ku, kuma ta ganshi yana bacci a reception din Mahmud ranar nan ta kuma turo miki sakon cewa
suna tare, but am telling you the truth, and the truth is basa tare a ranar nan"
"Tare da ni muka je har inda take aiki a saloon din Mahmud, aikin da Umar din ne ya samar mata tun
sanda tayi dropping out of school, kuma ya buga mata warning sosai a kanki saboda ransa yayi balain
baci a lokacin musamman akan sharrin da tayi masa"
"Maganganun daya gaya mata ni a lokacin na dauka ko mai sunansa ba zata kuma kalla ba, wannan shi
ya kara min mamaki last week data turo min message tana nemansa ni kuma na gaya mata cewa baya
gari yana Lagos"
Na dago kai ina kallon sa sai ya gyada min kai yace "yes, ba tare suka tafi ba, Baba ne ya aike shi wata
harkar business dinsa, and I accidentally told her yana Lagos and she followed him"
Sai ya dauko wayarsa yayi danne danne sannan ya miko min
Hira ce a tsakanin shi da Zuwaira, na gane ita ce saboda through Facebook ne da profile din data yi min
magana and it goes like this
"Hi"
"Hi"
"Nace idan babu hello ai akwai hi ko? Amma ku babu hello din ma a gurin ku ballantana hi din"
"Tuba muke yi ranki ya dade"
"Ni na isa! Ransu ya dade dai su masu matsayin"
"Lol. You are funny"
"Funny ko gaskiya. Naji ance ma har an haifa muku Baby. Babu sanarwa m ballantana ma mu saka ran
zamu samu naman suna. To maje mu karba da kan mu"
"Don't even try that, kin san dai abinda yace last time da kika je gidansa ko?"
"Yeah I know. Amma ya zanyi da raina? Mai sonka ai shi yake bibiyar ka ko?"
"Eh haka ne. Kinyi gaskiya. Mun gode"
"Yana ina ne? I have been trying to contact him in yi masa barka na kasa samun sa"
"Baya gari, yaje Lagos wani business"
"Lagos? A can ake jegon kenan?"
"No, shi kadai ya tafi. Jiya"
"Okay. Shikenan. Thank"
"Yeah. Bye"
Na sake komawa sama na ga date din hirar, and it shows washegarin tafiyar Umar. Na mika masa
wayarsa bance komai ba, ya karba yace "wannan shi yasa nace part of it laifi na ne. Ban san me ya faru a
tsakanin su a Lagos ba, yace ta turo miki some pictures, ban san menene a pictures din ba and I am not
saying ko menene yayi a can din yayi dai dai, but koma menene yayi nadama and I think he deserves a
listening ear from you. Ruwan ki ne ki yafe masa ko ki ƙi, but I am begging you, listen to him"
*wannan littafin na siyarwa ne, idan baki siya ba kar ki karanta, in kin siya kuma kar kiyi sharing, in kika yi
kinci amana kuma ke da Allah*
*The Confession 2*
Na dago kai ina kallon sa, trying to study him, sai kuma na juya na kalli Umar wanda ya fito tun dazu
daga daki da Yasmin a hannun sa yana tsaye a bakin kofa yana kallon mu, na sake mayar da dubana kan
Bashir sannan nace "for all I know bakin ku daya, for all I know tare kuka zauna kuka shirya maganar da
zaku gaya min"
"Na yarda cewa ba tare suka tafi ba, na yarda kuma bashi ya gayyaceta cewa ta bishi ba, duk that doesn't
change anything, that doesn't mean anything, taje gurinsa yayi welcoming her with open arms, kuma
bani da wani abun da zai bani guarantee cewa gobe ma ba zai koma mata ba, ko kuma in tazo ba zai
karbe ta ba, ko kuma......"
Ya katse ni "ba zai je ba, ita ma kuma ba zata je gurinsa ba, for that I am very sure of" nace "menene
hujjar ka ta fadar haka? Dan ka ga yana nuna kamar yayi nadama? Da farko ai ba taba tsammanin zaiyi
ba kuma yazo yayi din"
Ya girgiza kai, "tabbas yayi nadama, amma yanzy ba ina magana ne akan nadamar sa ba, ina magana ne
akan abinda ya aikata ga Zuwaira sanadiyyar sakon data turo miki"
Nayi shiru ina kallon sa bance komai ba, sai ya dauko wayarsa for the second time yayi danne danne
sannan ya miko min "kalli nan ki gani. Ban sani ba ko zaki gane wacece wannan?" Na karba na duba.
Facebook ne, wata ce tayi posting hoton wata tana nema mata addu'a daga gurin mutane akan
tsautsayin daya same ta. Na kalli matar cikin hoton, Kallon farko ban gane taba, sai daga baya na gane
ta, Zuwaira ce, sai dai zan iya cewa babu wani abu na fuskar ta wanda bai chanja kamanni ba, gabaki
daya fuskar ta kumbura suntum idonta daya ma ya rufe saboda kumburi ga kuma dinki da akayi mata a
kasan idon nata da gefen kunnenta. Fuska ce kadai, banga sauran jikin ba.
Na dago kai. "Menene hadin abinda muke magana akai da kuma tsautsayin da ya same ta?" Sai yayi
murmushi "ba tsautsayi ne ya same ta ba, mijinki ne ya dake ta"
Na daga kai da sauri na kalli Umar sannan na sake kallon hoton hannuna, na kuma yin scrolling through
dan in tabbatar cewa it is for real. Sannan na shiga gurin comment naga ana ta yi mata jaje, wadanda
suka santa suna ambatar sunan ta.
Na sake dago kai ina kallon sa sai ha daga kafada yace "he told me ya bata mata kamanni kamar yadda ta
bata shi a gurin ki. I never knew how bad sai dazu naga friend dinta tayi posting"
Na mika masa wayarsa sannan nace "ya burge kenan? A ganinsa dan ya dake ta zai burge ni kenan? Ko
kuma dukan ta zai goge abinda yayi" ya girgiza kai "am sure bai burge ki ba kamar yadda ni ma bai burge
ni ba, but that doesn't matter, abinda nake so wannan ya fahimtar dake shine how deep his love for you
is, abinda ya faru a tsakanin su will never match abinda yake a tsakanin ku. And that should mean
something to you. That should make him deserves a listening ear from you"
Na juya na sake kallon Umar sai ya sunkuyar da kansa. Bashir ya mike ya dauki wayarsa sannan yaje ya
mika masa hannu suka yi musabaha sai yazo ya fita.
Falon yayi shiru bayan fitarsa, ni sai naji ma kamar har kukan tsintsayen da suke waje da kuma karar
motocin da suke wucewa duk sun tsaya. Ya tako ya taho inda nake zaune, sai ya ajiye Yasmin a gefe na,
ban kalle shi ba sai kawai gani nayi ya saka guiwowin sa a kasa yayi kneel down a gaba na, ya kamo
hannayena biyu ya rike a cikin nasa biyu sannan ya hade su a kirjinsa tare da dora fuskar sa akai.
"Ban san me zance miki ba Jidda"
Nace "start with the truth"
Yace "ita zan gaya miki, the whole of it"
"Ka yarda kenan ka amince cewa Zuwaira karuwar ka ce bata Mahmud ba? Ka yarda ka amince cewa ka
kawo ta gidan nan ta zauna tsahon lokaci saboda bukatar gangar jikin ka? Ka yarda ka amince cewa you
cheated on me with her a Lagos?"
Na fada ina kuka, kuka sosai wanda na dauka na gama yin irin sa amma yanzu sai ya dawo min sabo. Ya
dago kansa yana kallona, ga mamaki na sai naga shima kukan yake, and that's something I never
expected from him, I never thought it possible for someone as strong as him yayi kuka, I thought kuka na
iri na ne mata kuma masu rauni. Sai naji tawa zuciyar ta kuma tsinkewa, automatically na rintse
hannayensa da suke cikin nawa
"Me yasa kayi min karya?" Na fada ina kara volume din kuka na. "Me yasa tun farko da na tambayeka ko
ka santa ka ce min ba ka santa ba" ya ja hannayena zuwa sides din fuskarsa, ina jin yadda hawayensa ya
jika fuskar ta sa, ya sake jan guiwar sa yana kara shiga tsakanin kafafuwana sannan yace "me kike so in
ce miki a lokacin huh? Me kike tunanin zan iya ce miki? Cewa I have a bad past her? Shine gaskiyar da
kike tunanin zan iya gaya miki? Sannan in zauna in kalle ki cikin kunan zuciya? Regretting marrying me
kamar yadda kike yanzu?"
Na fara kokarin kwace hannu na amma ya hana ni, yana kara matse su a